Showing 126001 words to 129000 words out of 219361 words

Chapter 43 - AJIYA A DUHU COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

5149

? ? ?  Kinga manta da shi Babyna. Muje na baki ina da ita da yawa. Daga yau kuma kema ni Abbanki ne ba nasu su kaWai ba.
? ? Cike da murna tace,  Eh .
Gaba yay da ita zuwa motarsa. Ya fiddo chocolate uku ya bata biyu a hannu, tare da Sare Waya ya sake mi?a mata. Cike da jin daWi ta amsa. Tare da juyawa ta murguWama Ajwaad baki da faWin,  Mai rowa Wan wuta. Nima kuma ga nawa .
? ? ? ? Harararta nan ma yayi. Yayinda su Fawzan sukayi dariya. Shiko Baabu duk kunya ta ishesa. ?arfin halin Maanal da banne a rayuwa. Shegen surutunta da wayonta da suka girmi shekarunta na tada masa da hankali. Duk inda ake neman fitinannen mutum aka samu Maanal an rufe littafi kawai. Sai dai yana mata fatan idan ta ?ara girma ta canja daga hakan.. ?iri-?iri da zai shiga gida yace tazo suje ta?i. Dole babu yanda ya iya ya barta wajen Alhaji kamar yanda ya ro?a.
? ? ? Yini guda Maanal na tare da Alhaji?Aliyu Darma, Tare da yaransa uku da tuni ta saki jiki da su. Musamman Ajwaad da tunda ya fito da kayan wasansa ta nani?e masa. Lokacin da rana tayi sai ga Shahidah da kula cike da alala an kawo musu. Sosai Alhaji Aliyu ya nuna jin daWinsa tamkar ya ari baki dan godiya. Anan ma Shahidah tayi-tayi Maanal ta bita suje gida amma ta?i. Dole ta barta itama ta tafi. Sai da akai la'asar sazu tafi sanan su Fawzan suka rakata har gida da ledan kayan ciye-ciye da kulan da aka kawo musu alala sukai godiya. Yayinda ita kuma ta shiga kuka saita bisu, sai da Baabu ya mata tsawa sannan ta nutsu. Dan a duniya Maanal na tsoron hargagi musamman na Baabu..
? ? ? Wannan rana itace sanadin tarayyar waWan nan ahali guda biyu. Dan kuwa washe gari sai ga itama mahaifiyar su yaran ta biyosu domin yin godiya. Anan ne kuma ta tarar da Ammie nama wata amarya gyaran jiki, itama tace ai sai ai mata kuwa.. tunda tazo Maanal na manne da ita. Kasancewar yaranta ita duk maza ne tana masifar son ?ar budurwar yarinya, shiyyasa tana ganin Maanal da jiya tasha labarinta a wajen ?a?anta yarinyar ta shiga ranta. Ga wayonta da surutunta na sakata nishaWi. Yau Win ma dai da ?yar aka raba Maanal da su, musamman Ajwaad da wasansu na yau yafi na jiya armashi. Dan yau ya saki? jikinsa ba kamar jiyan ba. Haka yake bashi da saurin sabo sam, akanyi ba?i a gidansu kwana da kwanaki babu ruwansa da su, dan shi yarone mai irin shegen tsantsenin nan, ga zuciyar tsiya da ?ulafucin iyaye. Ammafa idan ya soka to yaso ka kenan. Idan kuwa baka masa ba to babu abinda zakai masa ka birgesa ko kaja ra'ayinsa da shi. Shiyyasa a yau Win ma mamakinsa ya kasa barin Oum ganin yanda ya saki jiki a gidan tamkar a gidansu. Dan duk inda kaga Ajwaad yaje yaci maka abinci kansa tsaye to lallai yanayi da masu gidan....

&&&
? ? ? ?? Kafin Alhaji Aliyu ya kwaso iyalansa su tare a sabon gidan nasu daya haWu matu?a gaya sha?uwa da zuminci mai ?arfi ya shiga tsakaninsa da iyalan Baabu ta yanda har suna kallon kansu tamar wasu ?an uwa na jini. Oum ba itace kawai matarsa ba, ashe tana da amarya ma, sai da suka tare su Ammie suka sani. Bayan tarewar tasu kuma sai al'amarin ya ?ara ?arfi fiye da tunanin mai hasashe. Ba sha?uwar ahalin biyu ne kawai abin mamaki ba. Wadda ke a tsakanin Ajwaad da Maanal tafi zama abin kallo ga kowa. Dan takai a yanzu ako ina Waya yake Waya na wajen, shiyyasa idan baka sani ba baka taSa gane ainahin gidan kowannensu. Dan takai yanzu ma Maanal ta?i zama a makarantar da take yi da yan uwanta. Da safe anta dagama kenan tace ita Ajwaad zata bi tasu makarantar. Anyi lallashin, an daka, anyi kurarin duk a banza. Hakan yasa Alhaji Aliyu ro?ar Baabu damar maida Maanal makarantar su Ajwaad Win, kasancewar itama tana tare da Nursery, primary harda da secondary ne a tare. Da?yar Baabu ya yarda dan bashi da yanda ya iya, haka aka maida Maanal makarantar su Ajwaad amma a Sangaren Nursery. Shiko yana a primary 3 ne. To ashe rigima bata ?are ba, dan kuwa Maanal sam bata zama ajinsu saina su Ajwaad. Anyi-anyi amma ta?i, da malaman sukaga tanada ?walwar karatu matu?a, dan duk abinda akayi kafin kace me ta Waukesa a kanta harma tafi wasu ?an ajin sai kawai aka ?yaleta. Dan koma an kaita can Win ba zama take yi ba, sai dai taita jibgar ?a?an jama'a tana kukan ita dai wajen AA zataje. (Dan itace ta saka masa AA daga ji Oum ta faWa ta kama ta haye tana kiransa AA).
? ? ?? Hajiya Maanalu mai abin mamaki kenan. Dan daga Nursery 2 dai tuni tayi jumping zuwa primary 3 abinta. Hakama a islamiyya tuni ta koma ajin su Ajwaad. Dambe da rigima kuwa sai abinda ya ?aru. Duk da tana a cikin waWanda suka girmeta kullum cikin takalar tsiya take. Taimaka rashin kunya kace zaka daketa ka gamu da Ajwaad. Dan duk abinda zai taSa Maanal a duniyar nan Ajwaad baya ?aunarsa. Hatta Ammie idan ta daki Maanal sai taga fushi a fuskarsa. Idan ko su Shahidah ne duk da sun girmesa koda yake kusan sa'an Amaal ne yana girmeta kaWan sai fa yarama mata. Idan kuwa yana gidan tai laifi Ammie tace zata daketa sai yaje yace shi a dakesa a maimakonta, idan kuma ta riga ta ritsata tana duka zaije ya kareta shi a dake san. Idan abu aka bama Waya Waya bazai taSa cinsa ba sai Waya na nan. Hatta da kaya ya koma yanzu iri Waya ake musu, idan kuma ya banbanta na mace da namiji kamar atamfa, lass, yadi to dole a Wakko kala guda. Ajwaad shine tsifar kan Maanal, shine rakata kitso, shine wankin ?ananun kayanta irinsu pant, hula, vest da sauransu. Haka shima nashi idan zai yi tare zasuyi tana jagwalgwalo. Tun ana Waukar abun nasu wasa har kowa ya fahimci ba wasan bane aka kawo ido aka zuba musu. Sai dai iyayen na matu?ar kulawa da duk wani motsinsu saboda tsoron bin wata hanya mara ma'ana da a yanzu har yaran akan samu a ciki....

? ?? Alhamdullah a yanzu dai haka Maanal nada shekara tara cif a duniya, yayinda Ajwaad keda goma sha biyar. Suna a ajin ?arshe na primary. Kasancewar Ajwaad nada tsayi kamar ?an uwansa tuni ya tserema Maanal a girman jiki fintinkau duk da dama can ya fitan. Itako tana tsaka tsaki a tsayi saboda bata gama girma ba, gata muguwar siririya kamar ka hureta ta zube a ?asa. Zuwa yanzu sha?uwarsu ta sake wuce inda ake tunanani, baka isa kaji kansu ba. Hatta abinci tare suke cin abinsu. A hakan ma dan ana tsaye a kansu wasu abubuwan da yawa ana ?o?arin hanasu da tunatar da su halacci da haramcin dake a tsakanin iyakar da ala?arsu zata yiwu. Kuma Alhamdullah suna fahimta da kiyaye abubuwa da dama duk da bawai sun balaga bane ba. Garama shi Ajwaad alamomin hakan sun fara kusantoshi yanzu...

__________________&

? ? ? ? ? Yanda take tura baki gaba ya sashi tsayawa yana kallonta. Sai kuma ya Wauke kansa ya maida ga agogon falon. Ganinfa idan ya biye mata makara zasuyi ya sashi du?awa. Dariya ta saki da siririyar muryarta kafin ta Wane bayan nasa. Lunch box Winta da school bag Win dake ajiye ya tattara ya Wiba sannan ya mi?e. Dariyarta tasa Ammie dake kitchen le?owa. Takaici ya sata tsayawa kawai tana kallonsu, sai da ya kai ?ofa yana ?o?arin fita ta dakatar da shi.
? ??  Yanzu Ajwaad bazaka hutama ranka ba dai?. Ka sauketa ta taka da ?afarta, dan ubanta ba tun jiya ta taka ?afar ba .
? ? ? ?? Cikin yanayinsa na sanyin murya ya ce,  Ayya Ammie ALLAH ?afan bai sakin mataba har yanzu. Bari muje su yaya Fadeel na jiranmu a mota . Kafin ma ta sake cewa wani abu harya fice. Kai kawai Ammie ta girgiza tana komawarta, dan babu abinda suke bu?ata yaran nan sai addu'a. Idan ta tuna mutuwa zata iya Waukar wani a ciki tabar wani har tausayi suke bata. Idan kaga Ajwaad na farin ciki ko surutu to tare yake da Maanal. Dan duk rashin son maganarsa sai da ta sakashi ringa yi, idan ma baiyi ba addabarsa take har sai ya tanka zata barsa. Kokuma taje ta takalo masa faWan da dole ya tafi ramo mata......
'?.

? ? ?=??=??>?#?Eh lalle su Maanal an tsula tsiya a nahiyar arewacin Najeriya =??








('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayen
mu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


........Tuni su Fawzan har sun shiga mota. Da sauri driver ya amshi kayan hannunsa, shi kuma ya ?arasa gaba ya buWe ya sakata dan nan ne wajen zamanta dama. Sai da ya gyara mata skirt Win ta sannan ya rufe ya zagaya kusa da ?an uwansa ya zauna. Cikin tsokana da dariya Fawzan ya ce,  Oh oh Lilly bestyn Auta (Dan haka suke kiranta). Auta bestyn Lilly. Idan yaran nan kuka girma munada kallo a anguwar nan wlhy. ALLAH yasa dai kar ku haWiye juna ko ku ?one mu saboda eh...... ya ?are maganar cikin sha?iyanci. Banza Ajwaad ya masa, sai ma ?o?arin fiddo books Win Maanal yake yana dubawa. Yayinda Fadeel da suke kira (Babban yaya)? yay ?ar dariya, hakama driver. Tsagal Maanal ta ce,  Yaya F minene eh...? Kuma sai mu cinye kammu kamar mayu .
? ?? Dariya Fawzan Win ya sake kwashewa da shi. Tare da faWin,  Lilly ba yanzu zaki san eh.. ba. Sai nan gaba. Ke dai ALLAH yabar tare .
? ? ? ? Cikin rashin damuwa tace,  Amin . Sai kuma tai kneeling a kan kujerar ta saitin Ajwaad da yay kamar baya a motar tana lekensa. Cike da shagwaSa ta ce,  Besty! .
?? ?agowa yay kawai ya kalleta batare daya amsa ba. Wuyansa ta nuna masa tare da faWin,  Baka sa tie Winka ba fa .
? ?? Kansa ya maida ya cigaba da gyara mata abinda batai dai-dai ba a assignment Win da aka basu da tayi, dan jiya fushin faWan da yayo mata bai tsaya ya koya mata ba sai Amaal ce ta mata. Kafin a hankali ya ce,  Zan saka sai mun sauka .
? ? ? ? ?  Ohhh .
? ?? Ta faWa tana cigaba da kallonsa. Duk abinda taga zai gyara mata sai tayi tambaya. Shi kuma ya bata amsa. Har ya kammala ya maida books Win shima ya maida hankali a kanta. Gaba Waya ta addabesu da surutu. Baka jin muryar kowa sai tata. Sai ko dariyar driver da Fawzan masu tayata dan shima Babban Yaya halinsa kusan irin na Ajwaad ne. Baida yawan magana. A haka dai har suka iso makarantar dan akwai Wan nisa. Kasancewar a tsohuwar anguwarsu makarantar take. ?yawunta da son da suke mata yasa iyayen basu canja musu ita ba. Kullum driver zai kawosu ya dawo ya Waukesu.
? ?? Yanzun ma dai shine ya goyata, Fawzan ya taya shi da Waukar bags Win su da lunch box Win abinci data kasance Waya. Sai da ya rakasu har aji da kayan sannan ya wuce sashensu na yan secondary inda baban yaya Fadeel ya nufa. Ajwaad kam na sauke Maanal a mazauninsu dan kujerarsu Waya ta jawo bag Winsa. Zip Win baya ta buWe ta ciro gogaggen tie dan uniform Win nasu kamar suit suke. Sai dai na mata skirt ne na maza wando. Zama yay a kujera tana daga saman desk ya mi?o mata wuyansa. Tsaf ta Waura masa dan tuni ta iya. Idan ka gansu dolene su birgeka kamar ba ?ananan yara ba. Ta gama ta gyara masa rigar da faWin,  Wai Besty mi akai maka kake ta fushi. Inma dan ?afatace ba nace maka na daina jin zafin ba. Tun jiya fa ka daina dariya why? .
? ? ? ?? Shiru yay baice mata komai ba. Hakan yasa takai hannu saman sumarsa daya gyara ta shiga harmutsata. Hannunta yay ?o?arin ri?ewa amma ta?i ta bari. Dole sai da yay dariyar da take so sannan ta barshi. Cikin dariya ya ce,  Besty wannan wane kalar kuturun wula?anci ne .
? ? ?? Itama cikin dariyar ta amsa masa da,  Kamafi ?yau a haka ALLAH .
?? Rankwashi ya kai mata, ta kauce. Yay ?ar ?wafa da faWin,  Zan rama ALLAH ya kaimu Friday .
? ??  Mi zakayi? .
Ta tambaya tana ?o?arin Sare lollipop daga cikin ledanshi.
? ?  Meyi baya faWa ai .
Ya bata amsa yana fige alawar ya saka a baki. Hararsa tayi, shima ya rama. Sai kuma suka ?yal?yale da dariya. Saida sukayi mai isarsu sannan ta zare alawar daga bakinsa ta sha. Sake maida masa tayi a bakin. Haka sukaita yi har suka shanye kafin malami ya shigo musu su nutsu kamar basu ba.
? ? ? ? ?? Kowa yasan a ajin basa taSuwa. Maanal rashin kunya da tsokanar masifa, gashi itace ?ar ?aramar ajin dan duk sun girmeta tunda rigimarta ce ya kawota cikinsu ba shekarunta ba. Ka taSata ka haWu da AA. Yanada zuciya ga ?arfi, dan in har ka taSa Maanal ka taSoma kanka kuwa. Gashi da shegen naci akan faWa dan baya barin saita kwana. Surutun Maanal yasa kullum sai an sakata a cikin ?an surutu na ajin. Idan kayi surutu naira ashirin, in sha ALLAHU kafin a tashi sai ta tara Wari biyu. Idan ance ta bayar ta?i biya, idan shugaban ajin ya biye mata suyi faWa AA ya kamashi ya daka. Dole class master Win su ya maida shugabancin ajin akan Maanal Win, aiko tunda ta samu damar nan take tsula tsiyarta. Ta cikama ?an aji kunne da surutu su suyi ta maka sunanka. Azo biyan kuWi ka?i biya Ajwaad yay maganinka. Hakan yasa ake tsoronsu, ta gefen ?o?ari kuwa sune masu zuwa na Waya dana biyu, basu taSa tsallake wannan positions Win ba. Ada kafin Maanal tazo ajin AA ke Waukar na farko, wata yarinya na Waukar na biyu. Amma tunda Maanal tazo shikenan fa matdayin yarinyar ya rushe. Kullum sune dai su biyun nan, babu ?o?arin da wasu basuyi ba ganin an turesu amma abin ya gagara.
? ? ? Ada saboda kalar fatarsu tazo Waya kowa Wauka yake Maanal ?anwar su AA ce ta jini. Duk da babu ta inda suke kamanni na halitta sai dai fatansu yana kama sosai. Sai da tafiya tai tafiya kowa ya fahimci yanda ala?ar take. Duk da su Win yara ne da yawan mutane kai tsaye suke fassara ala?ar zuwa wani abu daban. Duk da su dai yaran babu wani abu makamancin hakan a tattare da furucinsu na baki, mawuyacine ma ace su sun san minene wata soyayya, amma hatta iyayensu na ganin zuwa nan gaba Wannan sha?uwar zata iya rikiWewa ta koma hakan....

? ?? (To bari muga ko hakan zata kasance=??
? ? ?
&&&

? ?? Kamar kullum ?arfe uku dai-dai aka tashe su. Suna ?an farko-farkon fitowa. Dan sun san driver Win su baya wasa. ?arfe biyu da rabi yake isowa. Uku a gate take masa. Ilai kuwa sun samesa inda yakan jirasu kullum. Dan su Fadeel ma har sun rigasu fitowa. Cike da tsokana Fawzan dake kallonsu ya ce,  A'a ?ar gurguwar Besty an warke ne? .
? ? ?afar tata ta kalla sai kuma ta kalla Bestyn nata. Harararta yay itako ta ?yal?yale da dariya tare da matsawa kusa da Fawzan. Nuni ta masa daya du?o dan ya fita tsayi nesa ba kusa ba. Haka suke dogaye dan iyayensu ma duk dogayene. Shiyasa ko shi AA Win dake 15 years ya shallaketa sosai. A cikin kunne ta gwargwaWama Fawzan,  Dama fa dan ya goyani ne Yaya F. Dan yanzu idan nace yamin goyo sai yace wai na girma. Kaga yanzu ai na samo dabara .
? ?? Mi Fawzan zaiyi ba dariya ba. Harda kwanciya jikin mota. Yayinda Maanal ta shige mota da sauri itama tana tata. Tsaf AA ya fahimci abinda ta faWa dan yana kallon motsin bakinta. Dan haka baice komai ba ya saka bags Win su da lunch box Win cikin booth kawai shima ya buWe motar ya shiga. Dai-dai nan Yaya Fadeel ya iso shi da abokinsa. Ta saitin da Maanal take abokin nasa ya Wan le?a yana tsokanarta dan mutuniyarsa ce. Kafin ya mika mata chocolate da in dai suka haWu sai ya bata. Cike da Woki ta masa godiya tare da bye-bye. Ta buWe chocolate Win ta, kamar yanda suka sabama juna duk abinda Waya ya samu sai ya raba da Waya ta raba biyu ta juya ta mi?ama Ajwaad rabi duk da tasan ba lallai yasha wannan ba. Ilai kuwa maimakon ya amsa harararta yayi ma. Ta taSe baki kamar zatai kuka da faWin,  Wai miyasa baka son amsar abun hannun Ya Abdull ne Besty? .
? ?? Banza ya mata bai tanka ba. Maimakon hakan ma sai ya ciro headphone Win daya saka a kunnesa. Dariya Fawzan yay da faWin,  Kishi mana Alaji. Kinga Lilly bani nasha tunda shi na mazan ya motsa .
? ? ? ?? Bata wani fahimci mi Fawzan Win ke nufi ba ta mi?a masa duka chocolate Win ta juya itama a dole tayi fushi. Shiko ya ce,  Uhhm gaba takaini, ban nasha faWan masoya hutu .
? ? ? Harararsa Babban Yaya yayi. Cikin Wan zaro ido ya ce,  Babban Yaya mi kuma na maka kai kuma? .
? ?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login