Showing 204001 words to 207000 words out of 219361 words

Chapter 69 - AJIYA A DUHU COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

5186

akafi sha?uwa Win nan. Su duka hawaye suke yi, hawayen kewa da begen juna da farin cikin sake haWuwa a gaSar da babu zato babu tsammani musamman ga ita Ammie.
?ayan ?aramin falon Ammie dake a rufe dan kar mutane su Sata Amaal tazo ta buWe. Sai da su Oum suka gaggaisa da mutane anan falon sannan suka shiga. Gaba Waya Ammie ita tama rikice, ta rasa ina zata kama ina zata saka su Oum. Yayinda su Oum keta sake mamakin ganin yanda ta canja, duk wanda yasan Ammie a shekarun baya ya ganta a yanzu za'a iya kwana ana gaddama da shi akan ba ita bace ba. Gaba Waya ta zama matar manya. Tayi ?iba ta ?ara haske da cikar kamala. Dan ita kanta Mamy a wannan gaSar jitai ta raina kanta. Saboda ko suturar dake a jikin Ammien ka kalla kasan lallai nagaba yayi gaba yanzu kam, na baya sai labari. Gefe kuma ga ganin Hajiya Majdiya a tare da Ammie Win ya sake tabbatar ma Mamy lallai dama Oum na tare da su Ammie kenan take munafuntar ta (kun san idan mutum nada halin banza kullum gani yake haka kowa yake ma=??)....

? ?? Salla suka fara gabatarwa saboda gudun fitar lokacinta. Kafin a cika musu gaba da abinci kala-kala. Kan Ammie dai a matu?ar Waure yake da ganin sanayya tsakanin Hajiya Majdiya da su Oum. Daga ?arshe dai ta kasa ha?uri ta magantu. Dariya Hajiya Majdiya tayi, kafin ta warwarema Ammie komai. Matu?ar mamaki da al'ajab ne ya nema kashe Ammie, ta dinga raba ido tsakanin Hajiya Majdiya da Oum. A lallai tabbas bata san ?annen Oum ba a fuska a tarayyarsu har suka rabu, saboda lokacin su suna ?asar waje, amma tasan labarinsu, tana jin kuma tana ambatar ?anwarta datai aure amma tana acan kasar wajen mijin kuma na nan Nigeria saboda yanada mata biyu a Zaria amma yana zuwa can wajenta dan yana kasuwanci a ?asashen ?etare. Cikin kasa daurewa Ammie ta ce,  Aunty! Dama Maman Najma ce kike yawan bani labari da mijinta ke Zaria amma ita tana can Paris .
? ? ??  Tabbas itace Asiya. Shekara shida kenan da dawowarta Nigeria har ma da su Abbu. Dan yanzu haka su suna Kano ne .
? ??  Ikon ALLAH kenan, shekaru biyar kenan muna tare amma bamu san akwai muhimmiyar ala?ar data taSa haWa ?addararmu ba. A lokuta da dama wasu al'amura na Maman Najma kan so sakani a ruWani wlhy. Dan sai kita dawo min cikin idanu duk da bakwa kama ko kaWan a fuska.
? ? ? ??  Gaskiya ne bama kama da Majdiya da Rafeeq sam. Garama Sulaiman shi kam da kin gansa zaki san akwai ala?a. Mu kamar mun kwaso Mah-mah ne. Itako Majdiya da Rafeeq Abbu. Wai ni naga kowa banda Baby na fa, ko bata zo bikin bane? .
? ?? Murmushi Ammie tayi.  Tazo, suna tare da su Najma Nene ta aikesu.....
?? Dai-dai nan kira ya shigo wayar Ammie. Ganin Daddy ya sata Wauka batare data ?arasa maganar ba. Fuskarta da murmushi ta ajiye wayar tana kallon Oum.  Aunty dama harda su Yaya kuke tare? .
? ? ??  Ai mu duka gidan ne ba'a bar kowa ba. Halan har an Waura auren? .
? ?  Eh an Waura harma sun shigo. Amma inaga su basu ?arasa wajen walima bane ba. Dan yace gasu nan a hanya a shirya musu abinci a sashensa.
? ? ? ? ??  Oh oh ji son bama mutane wahala. Maimakon su ci acan kamar kowa . Mamy ce mai maganar. Dariya Ammie tayi, da faWin,  Babu wata wahala Mamy, hakan ai shine dai-dai suzo na gansu shekara nawa . Daga haka Ammie ta fice. Da wani shegen hararar ?asan ido Mamy ta bita, sai ko karaf a idon Hajiya Majdiya. Mamaki sosai ya kama Hajiya Majdiya dan abu ne da basu taSa gani ga Mamy ba. To kodai sunada matsala ne da Hajiya Asiyan? Kai to amma a dukkan labarin da Oum ta bata na ala?a da tarayyarsu babu wani saSani ai, hasalima Mamy bata da yawan shiga sabgar mutane. To kodai idonta ne ya gane mata ba daidai ba? Kai to gaskiya hakanne. Da wannan tunanin ta saki zancen a ranta suka cigaba da hirarsu.....

? ?? & Har cikin gida motar su AA ta shigo dan suna biye da Daddy ne. Yanzu kam Fawzan ne ke driving Win. AA na gefensa Abah da Babban yaya na baya. A kusan tare duk sukai ?o?arin fitowa. Hakan yayi daidai da fitowar su Huznah daga sashensu. Cak taja wani kalar wawan birki. Itama dai cikin kwalliya take, sai dai Wan kwalinta a hannu ta yana siririn veil a kanta. Tare take da wasu ?ammata guda biyu. Sai wata dake biye da su da makeup box a hannunta, da alama dai kwalliya zatayima Huznah Win. Dan su sauran biyun da kwaliyarsu raWam a fuska. Bakinta har harWewa yake wajen ambaton  AA Darma! A gidanmu? .
? ? ? ? ? Duk kallonta ?awayen nata sukai, wadda ke'a gefen haggunta ta ce,  AA Darma naki da kuka haWu a Abuja lokacin bikin Yaseerah? .
? ? ? Bata iya ta bama ?awar tata amsa ba. Jiki na rawa ta juya sashensu da sassarfa. Wani iri zallo zuciyarta keyi kamar zata fasa mata ?irji ta fito. Hajiya Basariyya na falo tsakkiyar ?awayenta su Maman Yaseerah Huznah ta faWo musu. Tama manta a cikin taron mutane suke. Yanda take ?wala kiran  Ummy! Ummy! yasa Hajiya Basariyya mi?ewa zaram. Tareta tayi tare da girgizata tana faWin,  K Huznah lafiyarki kuwa? Wane irin kirane wannan? Jibafa yanda kike shigowa kamar wadda aka biyo.
? ? ? ??  Ummy AA Darma fa na gani a gidan nan .
? ?? Rasama inda Hajiya Basariyya zata kamo AA Darma tayi. Ta ce,  Waye kuma AA Darma?.
? ? ? ?  Ummy AA Darma Win ne baki sani ba? Mijin da zan aura na Abuja .
? Ai sosai Hajiya Basariyya ta waro idanu waje, hakama Maman Yaseerah zaram ta taso inda suke. Hannun Huznah Win ta kama sukai cikin bedroom, Hajiya Basariyya ta take musu baya.
? ? ?  K Huznah nutsu, da gaske kike kuwa .
? ?  Wlhy da gaske nake Mamah.
 Tab Win jan, eh lallai malam yayi gaskiya. Hakan na nufin aiki yayi kenan . Maman Yaseerah ta faWa tana kallon Hajiya Basariyya.......


_In dai da gaske aikin nan yaci nima ai arakani wajen malamin nan zai min aiki akan makaranta AJIYA A DUHU musamman ?an Discussion House da ?an AREWABOOKS ina son a musu ASIRI su fara son Uncle RK>?q?>?q?>?q?>?*??#?=?M?_

__________&

? ? ? A yayinda haWuwa ta kasance tsakanin AA Darma da Huznah, Ammie da Oum acan Kaduna. Anan Kano RK ne tare da Alhaji ?arami yayansa da Abbu mahaifinsu suka kai ziyara gidan Baba Sardauna. ?ya?y?yawan bafilatanin dattijo mai tarin cikar kamala data addini. Anga jiya anga yau ana fatan ganin gobe. A yanzu shine uba kuma jigo da gaba Waya ahalin Baffa Ishaq Darma ke kallo a matsayi na kamar mahaifi. Shine garkuwa kuma shine al?ali mai tsawatarwa da zartarwa akan a tsakanin wannan zuri'a. Hakama matarsa ta karSi wannan girma bisa ga bashi dukkan goyan baya ta hanyar amincewa ita Waya daga cikin wannan zuri'ar ce ba matar Wa dake kallonsu a matsayin dangin miji ba. Dan bata da abin cewa ga wannan zuri'a sai godiya da fatan alkairi. Ita kanta mantawama take ba daga tsatsonsu ta fito ba.
? ?? Baba Sardauna ya girmi Abbu sosai, dan sai dai suyi sa'anni da Baba Umar mahaifin Abah kenan. Ga kuma girma irin na matsayin yayan mata a tsakaninsu. Harara Baba Sardauna ya makama RK bayan ya gama amsa gaisuwar Alhaji ?arami.
? ? ? ??  Ni bazan amsa gaisuwarka ba ai Rafeeq. Dan lokaci kaWan ma ya rage kai da wannan Wan naka Ajwaad da Najeeb na sakaku a Waki na zane ciki da bai sannan nakai hotunanku massallaci ko za'a samu mai taimakonmu ya baku matan aure koda guragu ne. Kun wani ajiye gemunan ?arya kamar na ALLAH. Ku yanzu dan ALLAH Moddibo da Saleem basa birgeku, da ?ananun shekarunsu amma yaran bibbiyu....
? ? ? ?  Ayi ha?uri Baba a mana afuwa. In sha ALLAHU zamuyi .
? ?  Haka kullum kuke faWa. Har gara kai ma kana bada ha?uri da nuna zakayi, amma waWan can biyun inaga sai mun haWa da ro?on ALLAH dan da alama akwai iska marasa san aure a tare da su .
? ? ? ?? Abbu dake murmushi ya ce,  Ai kaima dai ka faWa Yaya. Ni wlhy canai idan suka wuce wannan shekarar kawai a samu wanda suka dace a aura musu sai dai akai musu Wakunansu, ba sai suyi yacce zasuyi da su ba .
? ? ?  Shawara mai ?yau wlhy Kasheem. Dama jiya-jiyan nan muke maganar nan da Kamila da tazo. Sai kuma ga Khadijah ta kira waya Itama tana mun complaine akan Raihana da Nuwaira.
? ? ? ??  To ai sai asan mafita kawai Yaya, duk da shi yazo da nasa batun ne yanzu haka wai acewarsa. Ni kasan ba kama zancensu nake ba su ukun nan dan munafukan bakinsu Waya da kake gani. Najeeb da Ajwaad da Rafeeq ba, ALLAH kaWai zasu gaya min akan aure na yarda dasu .
? ? ?? Dariya Alhaji ?arami yay da faWin,  Kai Abbu, ALLAH kun kasa fahimtarsu ne kawai.....
? ? ??  Ohhh yanzu na gane, Sulaiman kuke Waure musu ?ugu kenan ku yayun nasu .
? ??  A'a wlhy Baba. A dai yi ha?uri, in sha ALLAHU wannan karon komai ma yazo ?arshe. Ina kuma goyon bayanku dan muma ba son zaman nasu muke haka ba .
? ? ??  To Alhamdullah ai haka muke son ji . Cewar Baba Sardauna yana gyara zama. Sai kuma ya kafe RK da tunda ya du?ar da kai bai Wago ba. Cike da kulawa ya ce,  ?an nema, zonan naji Wuminka, dama kwana biyu nayi kewarka kaje ka ma?ale a Abuja wajen Wan uwanka .
? ? Murmushi RK yayi, tare da mi?ewa ya isa gaban Baba Sardauna, zai zauna ?asa ya kamashi ya zaunar a kusa da shi, tare da Wan rungumesa.  Fitinanne wai ni kake jin kunya kuma? .
? ? ? Dariya RK ya fashe da ita, hakama Alhaji ?arami da Abbu. Aifa nan baki ya buWe aka shiga gaisuwa. Sai kuma hira ta Salle. Suna cikin hirar sai ga Baba Umar. Shima dai nutsatstsen mutum mai cike da kamala. Dan zasuyi shekaru Waya da Abbu. Shi mutum ne da baida yawan magana. Dan duk cikinsu ya fisu ha?uri. Bazaka taSa cewa ya haifi kamar Abah ba, abinka da ana jin daWi.
? ? ? ?? Sosai suka tattauna akan al'amarin dake damunsu na rashin auren RK, AA, da Najeeb daya kasance ?ani ga Abah. Shima dai ya?i auren, har ga ?annensa biyu sunyi har da yara. Shine ?ani na uku a wajen Abah, sai Saleem da Moddibo sannan matar Alhaji ?arami data kasance Auta. Shi yama girmi su AA Win. Sosai Baba Sardauna da Baba Umar suka ji daWin kawo matar aure da RK yayi. Sun kuma tabbatar da babu wasa a satin nan zasuje Kaduna nema masa aurenta. AA da Najeeb kuwa su zasu zaSa musu matan aure dan ayi bikin rana Waya dana RK Win.
? ? ? A wani irin farin ciki mara misali RK ya tsinta kansa. Har ji yay ya ?agara su baro gidan Baba Sardauna dan ya samu ya kira Maanal ya sanar mata wannan albishir, duk da yasan suna a cikin biki yau. Kasa ha?uri yayi tun suna a gidan ya tura mata daddaWan text massage, Dan basu baro gidan Baba Sardauna Win ba sai da sukai sallar isha'i a massallacin ?ofar gidansa. Suna ?o?arin fitowa kuma sai ga Hussain yazo gidan tare da matarsa da yaransa biyu shima. Nanfa kuma aka sake zaman sabuwar gaisuwa, dan RK da Hussain Win sun jima ba'a haWu ba. ?arshe dai sai goma suka baro gidan.
? ?? Sanda suka iso har Mah-mah da Rufaidah da yara sun gaji da jiransu sunci abincinsu. Suna a falo suna hira, yara kuwa sun tafi sun kwanta. A rayuwar Mah-mah da Rufaidah sam babu surukuta, zama ake irin na uwa da ?a. Dole rayuwar gidan su Rafeeq tai matu?ar birgeka, dan rayuwace mai cike da so da ?aunar juna. Babu munafunci, babu makirci. Kowa na ?o?arin bama Wan uwansa hakkinsa dai-dai gwargwado. Zama Abbu da Alhaji ?arami sukai anan falo wajen Mah-mah, yayinda RK yay sashensa dan burinsa kawai yay kiran Maanal ya mata albishir........
'?



09032345899



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??



______________


........A falon Daddy akama su AA masauki, kafin Daddyn ya Waga waya yay kiran Ammie akan a kawo musu abinci. Da to Ammie ta amsa masa, tare da ajiye wayar suka cigaba da haWa abincin ita da su Shahidah da Hajiya Majdiya. Hakan kuma yayi dai-dai da shigowar su Maanal, Amrah, Najma, Aneesah, Zezaah (?awayen Maanal kenan na sarvese). Dole ne matasan ?ammatan kai musu kallo Waya ka ?ara. Dan babu wacce batai ?yau cikin tata shigar ba. Taku suke cike da nutsuwa sun kamo kuloli na waina masa da Ammie tasa akayi a gidan Nene, yayinda Almajirai uku ke biye da su da wasu kulolin manya da sukafi biyun da suka kamo. Gaishe da mutanen dake a falon sukayi sannan suka ?arasa kitchen inda akace musu su Ammie na nan.
? ? ?  Kai yaran nan ALLAH yay muku albarka, kamar kun san yanzu nake tunanin kiranku . Ammie ta faWa tana kallonsu. Amsa mata duk sukayi da Amin. Maanal ta matsa jikinta ta rungumeta. Kallonta tai da mamaki.  Lafiyarki kuwa Maanal? .
? ? ? Fuska ta Wan Sata, sai kuma ta kamo hannun Ammie ta Wora a saman ?irjinta dai-dai saitin zuciyarta. Kamar zatai kuka ta ce,  Ammie zuciyata ce ke bugawa da sauri, gabana kuma nata faWuwa. Sai nake jin kamar wani abu babba na kusanto ni .
? ? ?? Shiru Ammie kawai tai tana kallonta. Itama zuciyar tata na raunana. Dan bata raba Wayan biyu kasancewar Ajwaad a gidan nan ya sakata jin hakan. Ya rabba wannan wace irin tarayya ce haka?. Amma dai bari tai mata tambaya. Fuskar Maanal Win ta shafa, cike da kulawa ta ce,  Dama yana miki haka? .
? ? ? ? Kai ta girgiza ma Ammien tana sake narke mata a jiki. Ammie ta sauke ajiyar zuciya, tare da shafa mata kai ta ce,  Kairan in sha ALLAH kinji my babie .
? ? Kai ta Wagama Ammien sannan ta saketa saboda umarnin da Hajiya Majdiya ta basu na Waukar abincin da aka shirya su kai sashen Daddy. Manaal da Najma ne a gaba, sai dai Najma Win ma ta gota Maanal, dan itace ta fara shiga falon da sallama Maanal biye da bayanta. Da wani irin sauri Najma ce ta tsaya cak tana mai waro idanunta da faWin,  Lah wa nake gani kamar su Yaya Fawzan da Yaya AA? Abah! Babban Yaya .
? ? ? Da wani kalar sauri itama Maanal Win ta tsaya, hakama su Amrah duk suka tsaya suna kallon inda Najma Win ke kallo, sai ma ta ajiye kular hannunta ta nufi inda suke cike da mamaki da farin ciki. Ba ?aramin girgiza zuciyar Maanal tayi ba, dan nata idanun akan AA Win suka fara sauka. Kamar shima kuma ance ya kalletan sai nasa idanun a kanta. Da sauri ta janye nata zuciyarta na zallo. Cikin ?arfin hali ta maida su akan Abah da ya furta,  Finaly yau dai gani ga Autan Oum .
? ? ? ?? ?asa Maanal tayi da kanta tana murmushi, sai kuma ta cigaba da takowa cikin falon ta ajiye kayan hannunta inda su Amrah suka ajiye, gaban Abah taje ta dur?usa, har cikin ranta itama tana jin daWin ganinsa. Abah ubane da bazata taSa mantawa ba a rayuwarta. Ya nuna mata dukkan gata da soyayyar da ko ita Win a cikin ahalinsa ta fito iyaka kenan. Shiyyasa har gobe shine uba mafi kima da daraja da take kallo a cikin idannunta. Hatta da babu sunan mahaifi kawai yake amsawa a zuciyarta. Amma uba na gaske da bugun ?irji a nunama duniya Abah ne farko. Cikin rawar murya alamar tahowar kuka ta shiga gaishe shi. Shima a mamakin duk wanda ke'a falon idanun Abahn cike suke da ?walla. Amma sai yay jarumtar sakin murmushi tare da kai hannunsa ya kamo nata. Kamar abinda take jira kenan hawayen suka shiga rige-rigen sakkowa.
? ? ??  My daughter nima so kike nayi kukan? . Ya faWa cikin taushin murya da kulawa. Kanta ta girgiza masa. Kafin ta share hawayenta ta Wago ta Wan kallesa. Murmushi ya sakar mata, itama sai tayi murmushin.  Abah nayi kewarka matu?a . Ta faWa a hankali. Gefe ya kauda kansa, yasa babban yatsarsa ya Wauke guntun hawayen daya ciko masa idanu shima. Har cikin ransa yana ?aunar yarinyar, Waukarta yake tamkar yaransa guda uku daya mallaka a duniya. Sake juyowa yayi gareta da murmushin dai.  Nima nayi kewarki Maanal. BantaSa kwana na tashi babu ke a zuciyata ba. A kullum ina ji a raina akwai wani giSi da babu a cikin ?a?ana. ALLAH yay miki albarka, ya kare rayuwarki, ya azurtaki da farin ciki mara yankewa. Ya rabbi kasa iyakar jarabawar kasancewa a nesa da juna da mukai kenan.
? ?? Jiki a sanyaye kowa dake a falon ya amsa. Yayinda kan AA ke a ?asa babu mai ganin fuskarsa balle yanayinsa. Gaishe da su su Aneesah sukayi suka fita, sai Najma da Manaal dake gaban Abah suna magana ?asa-?asa da kowa baya ji. Dan hatta Daddy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login