Showing 30001 words to 33000 words out of 219361 words

Chapter 11 - AJIYA A DUHU COMPLETE HAUSA NOVEL

13 Jul 2025

5202

ma bai san da zaman Hajiya Yaya a falon ba yake kallon labaransa yana shan fruits da Ammie ta haWo masa. Hakan ne ya sake sakata fusata, cikin matu?ar Sacin rai ta ja remote Win dake a Centre table ta kashe tvn gaba Waya. Karo na farko ya juyo ya kalleta fuskarsa a matu?ar haWe. Itama kallon nasa take tana huci.
? ? ??  Sadiyya bar falon nan kafin ranki yafi haka Saci . Har cikin ranta taji tsoron fitar kakkausar muryarsa. Amma sai ta dake dan gara dai ayita ta ?are. Itama a fusacen ta ce,  Babu inda zanje wlhy. Dan nifa na gaji da abinda ake min a gidan nan. Ubana ya dasa inuwa wasu banzaye suzo su zagayeta domin sha suna min gadara.
? ? ??  Hummm .
?? Ya faWa kawai yana mi?ewa. Bedroom Winsa ya shige tare da rufo ?ofar ya barta a falo tana jidali ita kaWai. Haka dama yake mata, ita kuma sai take Wauka kamar tsoronta yake ji ko tafi ?arfinsa ne. Bata san yana hakan bane kawai saboda wani dalilinsa daban, amma badan gorin da take masa ba akoda yaushe. Tsautsayi rabon faWan nan ya koma kan Ammie sai gata ta shigo sashen batare da tasan Hajiya Yaya na nan ba. Aiko ina wuta Hajiya Yaya ta saka Ammie, nanfa ta shiga mata gori da cin mutunci. Ita dai Ammie komai batace da ita ba ta ajiye basket Win hannunta dake Wauke da kayan abincin maigidan a saman d/table. Rashin tankawar da batai ba itama sai ya sake fusata Hajiya Yaya, a matu?ar zafafe ta nufi d/table Win da niyyar kifar da kayan abincin Ammie ta tare tana girgiza mata kai.
? ? ??  Kiyi ha?uri Hajiya kar kiyi haka dan ALLAH. Koba komai shi Win abincine, yana da darajar da wula?antashi kuskurene takowace irin fuska .
? ?  To mama Asiya shawara kike bani ko umarni?
? ?  Babu ko Waya da nake baki a ciki kiyi ha?uri .
? ? ? ??  An?i ayi ha?urin munafuka kawai, kullum sum-sum ita a dole ta ALLAH amma dafinki yafi na ba?in kumurcin maciji. Kin mallake min miji da bin bokaye, kin cika mana gida da agololi har kina shirin ganin kin mannawa Wana. Wlhy Asiya sai naga bayanki a gidan nan .
? ? ??  Idan ta juya ba.....
? ? Alhaji Usman daya fito ya faWa a zafafe. Juyowa sukai su duka suna kallonsa. Fuskarsa a Waure ya cigaba da faWin,  Idan ta juya kam zakiga bayanta Sadiyya. Amma kiga bayanta akan zama dani har gaban abada bazakiga hakan ba da iznin UBANGIJI. Asiya ajiye abinci, idan kin isa dan ALLAH ki zubar da shi ni kuma wlhy yau sai na baki mamaki irin wanda baki taSa zato ko tsammani ba. Ke Sadiyya bafa wai ina tsoronki bane a gidan nan. Karki ?ureni a wannan karon wlhy idan ba hakaba zakiyi matu?ar dana sani.
? ??  Dana sani na nawa kuma ai nayi dana sani tun daga randa na amince na aureka.... sai kuma ta fashe da kuka  Kai dai burinka kullum ka wula?antani a ?asan ?anwar bayana koma nace sa'ar Wana ko, shike nan ga gidan nan na bar maka, ka kwaWata ka cinye dan ALLAH fuuuu ta fice daga falon. Tsaki yaja kawai tare da juyawa zai koma bedroom Winsa. Hankalin Ammie ne ya tashi, cikin sauri tabi bayansa, kusan a tare suka shigo bedroom. Jin yanda ta faWo masa ya sashi juyowa yana kallonta.
? ? ??  Dan ALLAH ka bita karta tafi Win da gaske, na ro?eka Abban Hameed. Bana fatan kowacce matsala ta kasance tsakaninka da matanka a dalilin.....
? ? ?  Asia! .
? Ya faWa cikin katseta. Kanta ta shiga girgiza masa sai ga hawaye. Zata sake magana kawai ya jawota jikinsa ya rungumeta. Sosai take bashi tausayi, mace ce mai ha?uri da juriya akan komai na rayuwa. Tana da kawaici da saurin sallamawa koda abu zai cutar da itane ko zuri'arta. Duk abinda kaga ta masa musu a kai to ka duba wannan abun kuwa. Komai yace ita mai biyayya ce a gareshi ko bai dace da ita ba. Wannan halayen nata ne suka mamayesa cikin ?an?anin lokaci yake jinta ?ololuwa a saman matan da ya aura tun yana da jajayen sawunsa. Hanata duk wata damar sake magana yayi, ba kuma ta sake yi Win ba ta ha?ura saboda ita Win mai biyayyace a garesa. Fitowarsu falo babu jimawa tana zuba masa abinci sai ga Asalamiyya ta shigo tana kuka ita da Basirah.
? ??  Daddy dan ALLAH ka kazo ka hana Mamma tafiya. Gata can ta haWa kaya zuwa mota zata tafi Daddy .
? ? A birkice Ammie ke kallonsu, sai kuma ta yun?ura jikinta na rawa zata nufesu. Cikin bada umarni Daddy da tun kallo Waya da yay ma su Asalamiyyar bai sake ba ya dakatar da ita.  Asia koma ki zauna .
? ? Kallonsa Ammie tai kamar zata fashe da kuka.  Daddyn Hameed kana fa jin abinda suke faWa .
? ??  Cigaba da zuba min abinci nace. Ku kuma ku bar falon nan!!! . Ya ?are maganar a tsawace. Zabura sukai saboda tsawar ta shigesu. Har rige-rigen fita suke daga fallon. Kallonsa Ammie ta sake yi zatai magana ya Waga mata hannu. Dole tai shiru ta cigaba da zuba masa abincin hannunta sai rawa yake. Tsaf yake kallon yanda hannun nata ke rawa amma sai bai tanka ba. Tana gama zuba masa abincin yaja ya fara ci hankalinsa kwance.. Abu ya ishi Ammie ta rasa ina zata kama, sai kallon Daddy kawai take. Can dai ta jawo wayarta ta shiga rubutama Yazeed text massage.....

______________&

? ? ? Yau da wuri Nene ta dawo asibitin. Dan haka ta kora su Amaal gida suma saboda mijinta daya shigo Abuja. Daga nan ma asibiti da yazo ya duba Maanal Waukar Amal Win yay suka wuce masaukinsa. Itama Shahidah da mijinta yazo sai suka wuce kawai. Hakan yasa Maanal ta kasance daga ita dai Nene a Wakin. Sai kuma duk kaWaici ya isheta. Dan Nene da zaran tayi sallar isha'i zakaga ta fara gyangyaWi abinta. Gashi babu waya a hannun Maanal Win, tana Kaduna aka barta, bakuma a kawo mataba har yanzu. Shiyyasa ma taima Shahidah maganar a sayo mata kayan zane-zanen ta dan ta iya sosai, shine Yazeed yaji ya hana Shahidah siyowa shi ya sayo mata. Tun Wazun daya kawo mata su ta ajiye bata sake bi takansu ba. Sai yanzu ta jawo ledan? ta fiffito da su. Komai da take bu?ata akwai, harma da wanda batace a sayo ba ya sayo. Dan haka sai ta gyara zama kawai ta fara zanenta dan shine hubby nata tun tana yarinya. Maanal ta masifar iya zane ta yanda idan ta zana abu sai ma ka Wauka ba itace ta zana Win ba. Da farko Wakin jiyyar tata ta fara zanawa harda Nene dake zaune a kujera tana famar gyangyaWi, sai ita kanta a yanayin da take zaune. Koda ta gama taga komai ya mata sai ta tsinta kanta kuma da fara zana agogo. Abinda ta jima batayiba a rayuwar zanenta kenan. Ta zana guda biyu tana akan na uku RK da Doctor Ranjet suka shigo Wakin. Firgigit Nene ta farka, yayinda Maanal tai ?o?arin rufe zanen nata amma sai caraf RK ya rikesa.
? ? ?  Woow!, this is amazing . Ya faWa yana kallon zanen cike da matukar mamaki. Sai kuma ya kalleta.  Dan ALLAH da gaske kece kikayi Baby? .
? ?? Kafin ma Maanal ta bada amsa Nene ta cafe cikin taSe baki.  Yo in dai Manaalu ce ai baka rabata da zanen aljanai Rafeequ. Tun tana yarinya uwar tayi tayi amma ina harma an barta taitayi itace zata ?are da mafarkinsu ai ba wani ba .
? ? ?  Nene ai abune mai ?yau wannan Win.....
? ?  ?an nan a al'adar yahudu da nasara ba. Amma mudai a musulunce banjin cewar abune mai ?yau duk da ni Win ba malama bace .
? ? ?? Dariya RK yayi, sai kuma ya mi?ama Nenen zanen yana faWin,  Amma Nene kinyi fa ?yau a wajen nan kamar wata sarauniya a kujera .
?? Ba ?aramin zare ido Nene tayi ba tana kallon kanta an zane ras harda yanayin atamfarta. Duka ta kaima Maanal itako ta kauce tana ?ara Sata fuska. Aiko ta shiga zazzaga jaraba shi dai RK da Dr Ranjet na dariya abinsu. Manaal dai ta miskile fuska kamar ba ita tai tsiyar ba. Sai da Nene tayi mai isarta sannan ta fice dan idan anzo duba Maanal Win fita takeyi. Bayan fitar Nene Dr Ranjet na duba Maanal RK daya kasa ajiye zanen ya dubi Maanal cikin serious ya ce,  Amma basirar nan naki bai kamata ya tafi a banza ba kawai, yana da ?yau mutane su amfana da shi .
? ? ?  Kamar ya? .
Ta faWa a ?asan ma?oshi. Bai damu ba, dan zuwa yanzu ya sake fahimtar miskilancinta mai lasisi ne.
??  Akwai Companyn da nasan suna matu?ar bu?atar aiki da mai irin wannan basirar taki .
? ?? A da?ile ta furta,  Ba bu?ata .
? Cikin Wan girgiza kansa ya ce,  Wlhy seriously Baby akwai companyn da zakiyi wannan aikin fa kuma anan Abuja ne, Please kada kice a'a dan ko kina gida zaki iya musu aiki ma .
? ?? Rasama abinda zata cemasa tayi, dan yanda ya wani marairaice fuska ya tsareta da manyan idanunsa sai ta ji ta kasa furta komai. Dr Ranjet ne ya saka baki a zancen nasu,  He is telling you the truth my patient.. Ko game da ciwonki idan kin samu abinda zai dinga maidaki busy zaisa ki rage saka damuwar abubuwa a ranki da har zai dinga yawan tashi akai-akai .
? ?? Shiru kamar bazatace komai ba. Sai zuwa can ta sauke ajiyar zuciya tana Wan girgiza kanta.  Su Ammie bazasu amince ba ne. Kadai ji abinda Nene ta faWa ai .
? ? ?  In dai har kin amince zakiyin ki barni dasu kawai .
? ?  Mi zakace musu? .
 Ke dai kawai ki amince zaki ji ai .
 Zanyi tunani .
Ta faWa a ta?aice tana zamewa ta kwanta. Bai sake magana ba shima sai Waukar hoton zanen da yay a cikin wayarsa kawai. Bayan fitarsu kafin barci yay awon gaba da Maanal tai zurfi matu?a a tunanin zancen RK Win da Dr Ranjet.....

? __________&

? ? ? ?? Lokacin da Yazeed ya iso gidan sha Waya saura na dare. Dan haka ya samu Daddy ya ma kwanta. Sai ya zarce sashen Ammie, samunsa yay shima a rufe, hakan na nufin tana sashen Daddy kenan dan su Waleed ba nan suke kwana ba suma. Dole sashen Hajiya Yaya ya nufa inda ya tadda ?annensa zaune a falo jugum-jugum. Hatta da television bata aiki a kashe take yau. Da gudu Amrah tazo ta shige jikinsa tana sakin kuka mai ban tausayi. Rungumetan yay shima yana Wan shafa bayanta. Kusan mintuna biyu sannan ya Wagota tare da kama hannunta suka ?arasa cikin falon. Nuni yay ma sauran da su zauna dan suma duk sun mi?e tsaye. Shima ya kai zaunen Amrah a gefensa.
? ??  Mike faruwa ne? .
?? Kafinma ya rufe baki su duka sun saki kuka. Wadda ke bimasa da suke kira Suhana ce ta fara masa bayani muryarta na rawa.  Yaya muma bamu san ainahin abinda ya farun ba. Kawai dai Mamma taje sashen Daddy, babu jimawa sai gata ta dawo kuma tana hawaye. Mun tambayeta bata kulamuba ta hau haWa kayanta. Bamu sani ba ko sakinta Daddy yayi .
? ? ?  Saki? .........
'?
? ? ??
? ? ?

('ZAFAFAN DAI ('

1 ?ALBIM (Mamu gee)
2 ?IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)


Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000

0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

?an NIGER 1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=؞?AJIYA A DUHU....=؞?_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??


.......... Haka muke tunani Yaya. Tunda bamu taSa ganin Mamma ta haWa kaya tabar gidan nan ba dan sun samu matsala da Daddy.
? ? Basira ta bashi amsa cikin kuka. A take zufa ta gama wanke masa jiki, harma ya gagara cewa komai. Badiyya ce ta sake katse masa tunani da faWin,  Yaya kuma wlhy koma minene ya faru da sanya hannun waccan munafukar matar a ciki. Dan tana a sashen Daddyn komai ya faru, ko sanda Mamma zata tafi da muka je kiran sa itace ta hanashi .
? ? ? Cikin mamaki ya ce,  Ita wa? .
? Kai tsaye ta bashi amsa da,  Amaryarsa mana .
Hararar daya zuba mata ya sata kame bakinta tana turashi gaba. Dama sun san ai bazai yarda ba tunda agolan ?arta ce budurwarsa. Bai sake cewa komai ba ya mi?e, sai da ya kusa kaiwa ?ofa ya juyo yana kallonsu.  Kutashi kuje ku kwanta zuwa da safe koma miza'ai sai ayi. Ku kulle nan Win .
? ? ?? Wasu sun amsa masa da to, wasu ko da hararar ?asan idanu suka rakashi dan sun san babu damar yi a zahiri mutum yaci dukan banza a daren nan balle ma babu Mamma.....

? ? ?&&&

Washe gari koda Yazeed yazo ganawa da Daddy sai ya samu har ya fita. Sashen Ammie ya nufa, inda ya taddata zaune jihum alamar tana tare da damuwa harma da Sacin rai. Gaisheta yay da girmamawa kamar yanda ya saba. Itama ta amsa masa cikin kulawa tana danne damuwarta.
? ??  Yanzu ka iso ne? .
??  A'a tun da daddare. Around eleven na samu kunyi barci shiyyasa na ha?ura har sai da safe. Yanzu kuma naje sashen nashi naga alamar a rufe yake .
? ? ?  Nima nazo na haWa masa breakfast na koma naga yabar gidan. Ka ganni tun Wazun nake kiransa yana rejecting daga ?arshe ma ya kashe wayarsa gaba Waya.
? ??  Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un . Yazeed ya shiga ambata yana mai dafe kansa da dukka hannayensa biyu.
? ? ?  Yazeed nikam da zakaji daka ha?ura da batun auren nan na Maanal. Dan idan zamu duba gaskiya duk batunsane tushen wannan matsalar. Kayima Hajiya biyayya ALLAH sai ya baka wadda tafi Maanal .
? ? ?  Amma Ammie ina sonta, wlhy matu?ar so nakema Maanal dan ALLAH kar kice haka, ke da Daddy ne ?warin gwiwata. Sannan shima Daddy ai yanada hakki a kaina kuma yana son auren. Miyasa Mamma bazata fahimta ba. Miyyasa bazata fahimci Aunty Sabuwa tana zugatane kawai saboda ta samu biyan tata bu?atar na auri tata ?ar bane? .
? ? ? ??  Amma Yazeed ?ar uwartace fa, uwa Waya uba Waya. Taya bazata tayata son abinda take so ba.
? ?  Amma wlhy Ammie akwai manufa a zuciyar Aunty Sabuwa. Mamma Win ce kawai ta kasa fahimta .
?? Rasa abincewa Ammie tayi, dan itakam wannan cakwakiya ta ma fara gundurarta wlhy. Tabbas tana matu?ar son Maanal ta auri Yazeed kodan ?yawawan halayyar yaron. Sai dai tana tsoron halin Hajiya Yaya gaskiya. Sannan tana tausayi da fargabar jefa rayuwar yarinyarta mai raunin ciwo a cikin wani hali. Yazeed shi kaWai ke son auren nan sai mahaifinsa. Amma ?an uwansa da mahaifiyarsa da mafi yawan danginta basa so sam.....

? ?? ________________&

??  ALLAH nazata wasa kikeyi da kikace min gaki nan tahowa Zaria fa.
? ??  hhhh aina fahimci hakan a muryarki. Bazaki ganeba fitowar ta dole ce. Gidanmu ne keci da wuta na gasken gaske kwana biyun nan .
? ??  Tofa wuta kuma Aminiya tami? .
?  Uhhm ke dai bari, tushen matsalar daga auren agolar gidanmu ne da maigidan yace zai ?ulla kusan shekara uku kenan.....
? ?  Kar kice na katseki wai ?ar amaryar ku? To da wa? .
??  Ita fa, dawa kike tunani idan ba Wan sonsa Yazeed ba. Tunda fa akai maganar dama uwar tasa tace bata yarda ba. Shi kuma Daddyn Huznah bai maida kai ba yarinyar dai tana cigaba da karatu, shi kuma Yazeed yana manne da yarinya. Bayan ta kammala karatun akaso tada zancen bansan miya faru ba dai kuma aka dakata ta wuce service. Indai ta?aice miki batu ta gama service Win ne yanzu zancen ya sake tasowa shine aketa dam-barwa. Ita uwar Wan tace bafa za'ai ba, kwana takwas da suka shige sukazo itada ?ar barikin ?anwar nan tata sabuwa suka cima uwar ?ar mutunci randa muka bar nan kenan shine itakuma yarinyar ta yanke jiki ta faWi ta kama aman jini .
? ? ??  Aman jini kuma? .
??  Uhm kin san sunce wai ai tana da ciwon zuciya .
??  Tir?ashi, eh lallai dole kice gidanku naci da wuta. Ke nan yanzu yaya ake ciki kuma? .
? ?  Yarinyar na asibiti a Abuja yanzu haka. Ba shine nake faWa miki nakoma Abuja ba nima harma naga ?anin Majdiya .
??  Oh ?warai anyi haka. Ko shiyyasa itama taje Abujan ita da yara duka dan gulma shine suka wuce gidan Yaseerah wai ganin Waki. Aiko sai da na mata tujara daga ita har mijin nata data dawo .
? ? Dariya sosai suka kwashe da ita suna tafawa. Hajiya Basariyya ta ce,  Ai kinmin dai-dai wlhy. Kinga gobe ai ta kiyaye .
? ??  Karma ta kiyaye na koya mata hankali. Mu munafuncin kishiya wanne bamu sani ba kuma .
??  Wlhy kuwa. Sai dai wanda kuma aka Soye a zuciya. Yanzu kin san miya sani zuwa Zaria Win? .
? ??  A'a sai kin faWa .
??  Jiya uwar gadaran gidan namu ce ta wuce gida harda kaya cike da akwatina. Dan ya hanata girki a gidan sai mu biyu mukeyi, shine jiya girkin ita shegiyar ne ita kuma taje ta samesu tai musu Wibar karan mahaukaciya. To ban sani ba ko sakinta yayi shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login