Showing 84001 words to 85260 words out of 85260 words
me photo"tana shiga ta sami sarah ta iso tasha gayunta"ga wasu friends nasu duk sunzo"kasancewar dama Anan haraban gidan za'a yi taron sunan da k'arfe 4 ko Abinciccika daga hotels Akayi order"yasmeen bata jima da zamaba Aka kirata me photo yazo"taje ta bud'e ward rope ta d'auki mayafi blue sannan ta fita"tasamu sadeeq rik'e da babyn"gefensa ta matsa ta Amshi babyn"ya rungumesu ta baya yana yimata rad'a ita kuma tana d'an zaro Ido had'e dayin dariya aka d'auka"shi kansa me photo d'in saida yace pic d'in yayi kyau sosai"kusan styles kala 5 Aka musu sannan sadeeq yatafi yayi sallar Azahar daga nan ya wuce wajen mohd"bayan Angama musu ita dashi Aka fara yi musu da sauran mutane"kafin taje ta canza shiga zuwa ta super exlusive d'inkin riga da siket da Akayima kwalliyar bich"fad'in kyawun datayi b'ata bakine"sai wajen k'arfe 4 yasmeen ta koma canza wata shiga suka fita haraban gidan, Aka rufe ko Ina Anata rarraba Abinciccika "game DJ yazo "Abin mamaki wasu da yasmeen ta gani wajen taron ko sanunsu batayi ba"haka dai taro yatashi lafiya "me jego da baby sunsha gift wajen mutane da Abokan Arzik'in da sadeeq ke hud'd'a dasu ko ya tab'a taimaka musu Arayuwa....tun bayan sunan yasmeen da sadeeq suka koma bud'e sabon shafin tsabtatacciyar soyayya me had'e da tsantsar kulawar da bbu Algush Acikinta "yayinda kuma ta zage damtse wajen gyaran kanta da kanta"dukda ummanta datazo wajen zaman haihuwa tazo mata da wasu"ita kuma da kanta ta siyi kayan mata wajen y'an meduguri da sakkota"gaba d'aya sadeeq yarikice yanata rawan kai Akanta "saidai koda jini ya d'auke mata be mata komai ba ya hak'ura tayi 40 kamar yadda Akeyi A Al'ada"ya kuma sanar mata ita yakeso ba jikinta ba"Awannan rana yasmeen ta yadda sadeeq na sonta....haka kuwa Akayi saida tayi 40 days chif sannan sadeeq ya Angonce son ransa"Aranar yasmeen taga surkulle iri iri"kuma washe garin ranar yayi nassarar zuwa get house d'in Bilal lamis "suka gwabza fad'a dashi da yaransa"har sadeeq yayi nassarar harbinsa da bindiga shida police sbd ganin zai gudu"Atake ya mutu ko shurawa beyiba....
*bayan shekara 10*
mutanene keta fitowa daga cikin get d'in wata tsadaddar makarantar da yau Aka yaye d'alibai y'an candy ta primary "Aciki kuma harda *Khadija Abubakar Ahmed*(Imaan)"yarinya me tsananin hazak'a dataci kyaututtuka na lambar yabo A tsadaddan makarantar"Ahankali wani matashin babban mutum yafito rik'e da hannun wata yarinya,ita kuma tana rik'e da gifts nata kusan guda 6 A hannunta"sai wata hamshak'iyar mace datayi shiga irinta wayayyun y'an boko ta dad'e da eye glass fari irin na gayu tana biye dasu gefe"sai wata baby girl dake sab'e saman kafad'arta"yayinda wasu kyawawan yara guda biyu duk maza suna gefenta"daka gansu zaka fahimci twins ne"my princess kinga dai my friend yadda ta maida hankali keme cewa twins sun fita k'ok'ari ko?....nayi mamaki wai Ashe wa'annan mutanan family d'in sadeeq Lamid'o ne"ba k'aramin canzawa yasmeen tayi ba"kamar ba itaba ta zama babbar mace"hakama sadeeq Lamid'o"ta d'an tab'e baki tana fad'in dama daddy Ai haka kakeyi kana yabonta kana kushemun yarana ko?"ta k'are maganar suna isowa gaban manyan motocin da suka zo dasu na Alfarma"da sauri body quards d'in sadeeq sukayi k'ok'arin bud'e motar dake farko yaran suka shiga"Adaidai lokacin kuma yasmeen taji Ammata sallama Abayanta"ta Amsa ta juyo suka had'a Ido da wata mace"itama y'ar gayun gaske"har k'amshin turarenta Anaji"da fara'a yasmeen ta Amsa tana tuna kamar ta tab'a saninta"sadeeq kuwa had'e rai yayi ya d'auke kansa yana fad'in my princess idan kun gama mgn ki sameni Amota "daga haka yayi gaba"suhan tayi murmushi domin tasan shi Ai yaganeta sbd tana yawan had'uwa dashi "tunda bayan rabuwarsu ta had'u dashi yafi sau biyar"wani kan hanya ,wani A bank,wani A kotu ,wanima har super market ta tab'a ganinsa"saidai bata tab'a samun fuskar da zata masa mgn ba"bayan sun gaisa tace"yasmeen nasan baki ganeni bako?"Aikuwa naga dai kamar nasan fuskar" ta sunkuyyar dakai tana fad'in suhan ce kishiyarki ta baya....saida gaban yasmeen ya fad'i! Amma saita dake bbu wata damuwa Asaman fuskarta saima tayi murmushi tace"Allah sarki yabayan rabuwa?"Alhamdulillah "d'azun naga Anata kiran yarinyarku tana Amsar girt"sannan na ganku tare kun fito shiyasa ma naganeki"Ayya kema da yaranki kika zone?"ah ah munzo da yaron Anty meenart ne"ni har yanzun ban tab'a haihuwa ba"likitoci sun tabbar mun bazan tab'a haihuwa ba"bayan mun rabu da sadeeq naga rayuwa yasmeen ki yafemun laifina na baya"ki kuma rok'ar mun sadeeq yafiya dan Allah " saida na shekara biyu da rabuwa dashi kafin na Auri wani tsohon saurayina Ammar"wanda yajima beyi Aureba harma ya zama tuzuru" saidai Ammar baya d'aukar raini tun ranar danazo gidansa na gane hakan"saidai yana sona yana kulawa dani"tun bana iya jure d'aukar buk'atarsa harna iya"girki kuma bisa dole kullum saina masa sau biyu"be hanani Aikinah ba inayi"saidai da muka shekara har ukku bamu haihuba danginsa da iyayensa suka tasoni Agaba da tsana da tsangwama ni juyace "Adole mukaje Asibiti Aka bincikeni Aka gano daga nine matsalar"hakan yasaka sukace dole sai yak'ara Aure "badan yasoba yak'ara"ya zama babu zaman lafiya tsakanina da ita sbd dama be sonta Auren zumunci ne Aka musu"naso mu rabu daddy nah yace"idan nakashe Aurenah badai gidan saba"hakan yasaka Ammar yaraba mana gida"shi bashida matsala iyayensa ne da y'an uwansa"harta kai ta kawo bana zuwa sabgarsu sbd habaici da suke yadamun suda kishiyata"saidai ban damuba sbd mijinah na sona yana kuma bani kulawa"kawai damuwata yanzun rashin haihuwa"Abaya munyi kuskuran cewa yara biyu zan haifa dana zo gidan sadeeq "gashi yanzun ko gudan babu"na yadda da Ake cewa duniya budurwar wawa"yanzun haka rufin Asiri nah Aikinah da kuma mijinah"Amma yanzun daddynmu rayuwa ta canza "dan Allah kuyafemun yasmeen....karki damu ni babu laifin dakika mun"in Akwaima na yafe miki suhan"sweety nah kuma in sha Allah zai yafe miki"kiyi hak'uri da duk yadda rayuwa tazo miki"kiyi Addu'ar Allah yabaki yaran masu Albarka in har haihuwar Alkhairi ce ga rayuwarki"Ina miki fatan Alkhairi suhan "Allah yasa mudace duniya da lahira"Ameen yah Allah nagode sosai"daga haka tayi gaba tana bud'e wata mota ta shiga"yasmeen jikinta Asanyaye itama ta shiga motar da Aka bud'e mata....uhmmm Ai dakin k'ara minti biyu danayi tafiyata tunda wannan Abar tafini matsayi wajenki"mi yayi zafi daddy?"sai yanzun na fahimci ka ganeta daka ganta shine kata fo ko?"kayi hak'uri dan Allah ka yafema suhan tayi nadama"ta kuma ga rayuwa yaya sadeeq pls"nifa dama tuni na yafe mata"ganinta kuma jefi jefi inayi bana dai nuna na ganeta"shi kansa wanda take Aure nasan shi"kowa ya tuba dan wuya tubansa beyiba"yanzun ta gama gadarar mahaifinta nada kud'i"yanzun Ina kud'in Ina power?? Amsa duk bbu"sauk'inta biyu"tana Aiki tana d'aukar Albashinta,kuma mijinta nada Abin hannunsa"hakane kam Allah yasa mudace habiby"yana murmushi yace Ameen "to yanzun ka huce ko?"ba dole na huce ba my princess tunda bana iya dogon fushi dake"hakane Allah yabarmu tare darajar manzon Allah S W A....Nima nace Allah yabarni daku mutanena 👏 tamat bi hamdilillahi me karatu Anan nakawo k'arshen wannan littafi me taken NIDA BRR SADEEQ! kuskuran danayi Aciki dani daku Allah ya yafe mana baki d'aya ,ya bamu ladar Abinda ke daidai"ya kuma bamu Ikon Amfanuwa da darussan dake cikin wannan labarin👏👏
Godiya ta musammun gareku mutanena makarantana Ina Alfahari daku! ubangiji yak'ara nauyin Aljihu yabaku zaman lafiya da mazajenku, y'an mata Allah yakawo miji na gari
Ina muku Albishir da zuwan sobon book d'ina dazai zo muku nan bada jumawa ba, me taken POLICE🔥 da zai zo muku kafin ramadan kuma mu gama kafin ramadan in sha Allah.....
wannan book d'in nakudi ne duk wacce ta karanta bata biyaba kota cutar dani ta hanyar fitarwa bazan tab'a yafe miki ba......