Showing 1 words to 3000 words out of 85260 words

Chapter 1 - _NIDA_BARRISTER_SADEEQ_Complete

04 Apr 2025

7408




NIDA BARRISTER SADEEQ



Story &written by
mommyn fareesa



*GODIYA*
Alhmdllh Ala kully halin" godiya ta musammun ga Allah S W A daya nunamun na fara wannan littafi lafiya"yah Allah yadda na fara lafiya Allah kabani Aron rai da lafiya nagama lfy....

*GARGAD'I*
wannan littafin k'irk'irarran labarine banyi shi dan wata kodan waniba idan yayi daidai da rayuwarshi Arashine"Aguji sauyashi ta kowace siga sbd hakkin mallakata ne....

dedicate to All members of my groups🥰Ina yinku over guys💃💃

BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Page 1&2

*kano state*
Bakajin motsin komai sai hayaniyar mutane Acikin court d'in Anata kace nace"yayinda wasu sunata fita daga cikin court d'in wasu kuma na tsaye suna mgn"yayinda wasu kejin farin cikin nassarar da Akayi ,yayinda wasu kejin Akasin hakan"cikin nutsuwar data zamewa jikinsa dabi'a yanufi k'ofa yafita" manyan y'an jaridu maza da mata na biye dashi sbd son suyi masa wasu muhimman tambayoyi Akan wannan shari'a....saidai kallo basu isheshiba yana tafiyar ne yana rik'e da hularsu irinta lauyoyi da wasu file's Ahannunsa "yayinda rigarsu irinta lauyoyi ke rataye gefen kafad'arsa"be cika fara'a ba saidai fuskarsa bbu yabo bbu fallasa"kasancewarsa kalar ruwan tarwad'a kuma cikakken kyakykyawan ingarman namiji meji da lokaci had'e da k'uruciya da kuma nera"kallo d'aya zaka masa katabbatar da hutu da jin dad'in rayuwa nabin ko Ina na jikinsa.... *brr sadeeq Lamid'o* kenan! yaro mi jini ajika" me tashe da rik'e gaskiya sbd d'aukakar daya samu Aduniya"doguwar fuskarsa na mak'ale da eye glass bak'i ya b'oye kyawawan idanuwansa Aciki"kai tsaye wajen wata had'ad'd'iyar mota bak'a k'irar Lexus X750 yanufa..…Lamid'o! pls jirani mana"cewar DPO mohd babban Amininsa dake bayansa"d'an tab'e baki yayi yana duba wristwatch d'insa kafin yabud'e driver sit da nufin yasaka files d'in.......Ina maka murnan samun nassarar dakayi Akan mahaifina"saidai Ina maka jajen daka shigo cikin sabgarmu"inaso kasani ba'a shiga gonarmu afita lafiya"sai kasan kayi sanadin mahaifinah yayi 12 yrs Agidan yari"badai Ana wasaka da kuran takaba idan ka shige ma mutum sai yayi nassara...wani saurayi dake tsaye gabansa yafad'a yana huci had'e da bin brr sadeeq Lamid'o da wani irin mugun kallo..... you are very stupid! Brr d'in kake gayama mgn"cewar DPO mohd d'aya k'araso?"kafin Bilal yayi mgn body quards d'in Lamid'o sun iso wajen da hanzari"sadeeq dake tsaye yana sakin wani irin malalacin murmushi me tattare da ma'anoni da dama ya d'allah yatsunsa biyu na dama yana girgiza kansa yazare eye glass nasa ya kalli Bilal dake tsaye yana huci"you can go "shine Abinda yafad'a yana Ajiye files d'in dake a hannunsa "kwafa Bilal yaja yajuya yatafi Azafafe"mohd kuwa yasan kafiya da bak'ar zuciya irinta Abokinsa, sarai yasan bazai k'yale bilal ba da kansa zai d'auki mummunan mataki kansa" congratulation Abokinah! Allah yak'ara baka nassara"Amma yaka mata ka dinga sauraron y'an jaridar nan....k'ayata suka kamaka ne?"cewar sadeeq cikin kamulalliyar muryar da bata fitar da harafin R"saidai mohd be samu damar furta komaiba yaji muryar sarah Abayansa tana kiran sunansa...... yamutsa fuska sadeeq yayi yana jan guntun tsaki yace"kaga mlm idan wajen k'aramar yarinya zaka tsaya nizan wuce mun had'u Anjima A gida"uhmm she is 18 yrs itace yarinyar?"ko dayeke tunda tsohuwar mace kusan sa'arka kake soyayya da ita dole ka kallemun sarah kace mata yarinya...banza Lamid'o yamasa yashige motar batare daya Amsa gaisuwar da Sarah data iso tafara yi masa ba"har ransa mohd beji dad'in Abinda Lamid'o yyi ba"sarah ko bayan soyayya da sukeyi y'ar uwarsa ce, sbd y'ar k'anin mahaifiyarsace sunzo kallon shari'ar ne....bin bayan motar da kallo yayi har yabar wajen body quards nasa na binsa Abaya"mohd ya sauke Ajiyar zuciya yana fad'in baby love zo muje na mayar dake gida ko?"ta b'ata fuska tana fad'in waishi wannan yaya sadeeq d'in zafin kansa yayi yawa bazan koma gaishesa ba...karki damu ransa Ab'ace yake banaso ki dena gaidashi kinjiko?"yafad'a suna jerawa suka nufi wajen motarsa"bayan sun shiga yanufi Anguwar su da ita sbd yamai da ita gidansu dake hotoro....
Doctor hidayat ce zaune Akatafaren parlourn dake side d'inta "Tasha gayunta d'aya b'oye Ainahin shekarunta"kasancewar yau week end ne bataje office ba"tana kallon news da Aka nuna shari'ar dasu sadeeq Lamid'o suka gabatar a court da irin nassarar daya samu" har me girma governor yabashi kyauta da babban matsayi"fuskarta cike da Annuri tana jin dad'i da farin ciki Azuciyarta"Farooq Auta d'an 8yrs ya shigo Aguje,zarah na biye dashi zata dakesa"yafad'a jikin Dr yana fad'in mama kinganta zata dokeni ko?"tunda yaufa Ina gida Ai bazaku barni na hutaba"bazance ku dena ba, saidai wlh kunsan halin babanah idan yaga kuna hakan"da sauri Farooq ya nutsu zarah ta hararesa tana fad'in zanso yayan yadawo na had'ashi dashi Ai"dan Allah Anty zarah kiyi hak'uri"yafad'a cikin marairaice murya sbd yasan beda gaskiya"ta sakar masa harara ta zauna kan kujerah "Ahaka Abba yashigo cikin shirinsa yanata k'amshi ya zauna gefen mama yana fad'in Dr sannu da hutawa"yauwa Alh fita zakayi ne? Eh zanje ziyara a k'auye kinsan najima rabona danaje"naga gara dai na tafi yau tunda week end ne"kuma naga k'arshen shari'ar nan "saidai Ina tsoron Abinda zai biyo baya wlh"kamar yaya kenan?"ke ku bamu waje"babu musu su zarah suka bar parlourn "fuskar Abba babu walwala yace"Alh lukuma n yakirani yanxun ta waya,ya sanarmun nayiwa yaronah mgn ya kula da kansa sosai sbd mutanan Alh lamis basuda Imani"nasanar masa cewa basu isa suyi Abinda Allah be nufaba"dama ita rayuwa haka take"duk wanda yakasance me gaskiya a irin wannan zamanin Tofa tashi tasamesa"hakane Alh zamu dage da masa Addu'a"shima kuma yanayi"babanah nasan jarumi ne insha Allah babu Abinda zai faru dashi"hakane Allah yasa nizan wuce"to Alh Allah yakiyaye hanya idan kasauka zan kiraka"nasan Antyn su(kishiyarta)ita zata rakaka bakin motar ko?"kema idan kinso zaki iya mun rakkiyar doctor"ah ah gara dai kaje kasan tanada zafin kishi tunda kwananta ne "bece komai ba yafita"tabishi da kallo tana murmushi tasan yaji haushin kalamanta saidai zamanta Aganinta zaifi sbd Azauna lafiya....very slowly Lamid'o yashigo cikin layin Anguwar kabuga"tun daga bakin get d'in gidansu zuwa ciki security's ne da masu gadi da masu bama flowers ruwa zuwa masu kula da lambun gidan su....saidai yana k'ok'arin yin horn ya lura da motar suhan dake fake Agefen layin"Atake ya had'e rai yayi ribas yadawo baya yayi parking yafito"da hannu yama body quards nasa mgn su wuce ciki"shi kuwa saman motar ya zauna yana satar kallon motar suhan"can ta bud'e back sit itada k'awarta feedyn suka fito suna sanye da kayan bautar k'asa"suhan ta yafa siririn mayafi saman kanta da aka mata kitso da gashin doki"yayinda feedyn hulace kawai saman kanta"Wanda be saniba zai d'auka yare ce ita"gaba d'aya basuyi kama da y'ay'an musulmi masu cikakkiyar tarbiya da tsoron Allah ba"ta gefen Ido Lamid'o ya lura su biyu ne"hakan yasa yak'ara tamke fuska yana danna waya yana girgiza k'afafuwansa masu takalmi sawu ciki.....tun kafin su k'araso k'amshin turarensa me dad'in gaske daya cika wajen yafara yimusu sallama...baby ! munfi away guda muna jiran isowarka nasan bakaso naje wajen shari'ar shine nazo nan na jira ka"ta fad'a cikin sigar jan hankali tana tsayawa daga gefensa"ya d'auki kusan second 10 beyi mgn ba"feedyn ta tab'e baki tana fad'in Ina kwana?"lafiya! shine Abinda yafad'a cikin shan k'amshi Atak'aice yana dirowa daga saman motar yaga baki d'aya shi suhan ke kallo kamar zata cinyesa"ina son mgn dake ke kad'ai"yafad'a yanata cin magani"tun kafin suhan tayima feedyn mgn tabasu waje tayi saurin barin wajen"kamar yana jira yafara masifa da cewa" suhan meyasa bakyajin mgn?sau nawa zance kidena zuwa gida kina samuna??"hakan tarbiya ne me kyau"idan kinyi hak'uri duk friday ba Ina zuwa naganki ba?"duka ba wata 5 yarage kigama service d'in ba Asaka ranar mu....motsin bud'e get yasaka ya juya yaga motar Abba ce"yasan kuma inda zashi sbd da safe yasanar masa"wanda sarai kuma Abban ya gansu be dena kallonsuba saida motar ta wuce.....yanzun baby sbd nazo na ganka shine laifi?"sai takama kuka irin na shagwab'a" wanda tasan idan tayi duk yanayinsa ke sauyawa....pls ya Isa haka"ki wuce kije zanzo Anjiman"nok'e kafad'arta tayi tana fad'in nidai kataso ka rakani na shiga mota mana"beyi mgn ba ya matso gefenta tayi saurin kama hannunsa guda.....da sauri ya fisge yana binta da wani irin mugun kallon dataji fad'uwar gaba" Adaidai lokacin kuma motar mohd tayi parking gabansu"Lamid'o yaja tsaki yana nuna mata motarta da hannu"Alamar taje tabashi waje"tanata gunguni qasa qasa ta nufi wajen motarta tana lura da mohd yafito daga cikin motarsa Amma Arzik'in ta gaishesa be samuba"cikin b'acin rai ta shigo cikin motar"feedyn tace"wlh iskancin da sadeeq ke miki yakai inda yakai"idan yana wani abun kamar bagidaje..... Lamid'o d'in ne bagidaje feedyn?"kusan hakan mana"yana Abu kamar be waye ba"wai sunan yayi 6 yrs a k'asashen waje"just hugging wannan idan kin masa yana miki surutai shiga na Allah....wlh feedyn ni kaina yana bani haushi idan yana mun hakan"naso ace tun kafin muyi Aure yana biyamun buk'ata Amma yak'iya"Aranar dana masa zancen cewa yayi yarabu dani har Abada"yamun wulakanci da k'yar na shawo kansa feedyn"in bacin Ina sonsa sbd kyawunsa da haibarsa da kuma shid'in waye da tuni na hak'ura dashi"inaso in bama musty kaina saidai dana tuna mukayi Aure yasami niba virgin bace na shiga ukku wajensa"
,,shiyasa kawai nake barin musty muyi iya romance kawai,,
ke kika sani idan yasaka miki ciwon zuciya Ai"sauk'in ki guda beda son mata"

koda yanada son mata wlh zan iya kisa sbd Lamid'o kinji na rantse.

kisafa kikace suhan?"cewar feedyn da mamaki"

Ta gyad'a mata kanta cikin tabbatarwa kafin taja motar suka bar wajen.....

Fuska bbu walwala mohd ya iso gefen sadeeq Lamid'o yana bin suhan da wani irin kallo Aransa yana tunanin" k'ilan farin bleeching d'in datakeyi da k'irjinta yaja hankalinsa" danshi bega Abinda za'a so Atare da itaba musammun halayya"yarinyar dake da shekara 28 Aduniya batayi Aure ba"kuma iya saninsa shekara 2 kenan suna soyayya itada Lamid'o....idan bakada ta cewa zan wuce ciki ni"cewar sadeeq Lamid'o yana tab'e baki sbd yana lura da irin kallon da mohd kebin suhan dashi"yakuma fahimci be sanshi da yarinyar...

Idan har zaka iya wucewa d'in babu damuwa "yafad'a yana d'age kafad'a"

Cikin basarwa Lamid'o yatab'e baki yak'i mgn yana danna waya "

Gaskiya banji dad'in baby love na gaishekaba kak'i Amsawa"

Okay dama sbd kamun k'orafi game da ita kazo nan kenan ?" Cewar Lamid'o yana yamutsa fuska"
.uhmm gara ita ta gaisheka wata ko gaisuwar bata iyaba"bazan b'oye makaba Lamid'o sam baku dace da suhan ba"yarinya babu tarbiya balle kunyar Al'ada Atare da ita"sai girman kai itaga wacce ta waye"kai Aganinka irin wannan macen zata bama yaronka tarbiya"never wlh! Itama tata tarbiyan tana buk'atar gyara"ka nemi yariya y'ar baby beauty daidai dakai tayita maka shagwab'ar dakakeso"sbd nasan kanason shagwab'a"kuma yarinya zata maka biyayya Aganina fa"Amma kamar suhan da idonta yabud'e da wuya ka juyata yadda kakeso.....look mohd! ba wannan zancen nace kamun ba"tunda dai kai kaji kagani zaka iya da k'aramar yayinya damuwaika" raini ne zakayita kwasarma kanka"batun tarbiya da biyayya dakake mgn kazuba Ido kayi kallo Ayi Auren"nidai nasan Ina son suhan Ahaka"okay to shikenan Allah yabamu rai da lafiya" bance duka haka ko wace mace data jima batayi Aureba takeba"saidai halayen suhan abayyane su.....doguwar tsuka sadeeq yaja a fusace yabud'e motar yashiga yana tunanin me ruwan mohd da yana soyayya da suhan??"mohd kuwa murmushi yasaki yashige mota yasha Alwashin bazai nemesaba shine da kansa zai nemesa tunda ya d'auki Abin da zafi.....

wanene brr sadeeq Lamid'o?
Alh Ahmed Abubakar lamid'o Asalinsa d'an k'auyen charanci LG ne dake jihar katsina"bayan ya kammala karatunsa na diploma, kasuwancin siyar da fata yaka wosa garin kano"Anan yayi Aure yadawo da iyayensa da k'aninsa hamisu"Hjy hidayat itace matarsa ta farko kuma mahaifinta uban gidan Alh Ahmed ne"salma itace babbar y'arsu sai hafsat sannan sadeeq,sai zarah da Farooq"yayinda Hjy binta(Anty Amarya)keda yara 4 " Amira,moon,khairiyya da Auta safiya" sun taso cikin had'in kai da girmama juna"dukda hjy binta Allah yayita mace me zafin kishi saidai Dr hidayat dasuke kira da mama bata biyewa"tun kafin suyi Aure da Abba tafara karatun likitah bayan Aurensu taci gaba "data gama kuma tafara Aikinta cikin samun nassara"wanda yanzun tanada Asibintin kanta da sadeeq yagina mata shekara guda data wuce"Ayanzun Acikin garin kano zamu iya lissafa Alh Ahmed cikin manyan hamshak'an masu kud'i...... sadeeq kamulin saurayine me jini ajika kuma d'an kwalisa"yanzun yanada 33 yrs Aduniya "befi shekara 2 ba da kammala karatunsa na low har yakai matakin SAN "sannan yazama lauyer me zaman kansa me tsananin farin jinin jama'a"yana tab'a kasuwanci kad'an"kuma idan yaga dama zai iya kare mutum a kotu batare daya Amshi ko sisinsaba"sannan baya shiga case d'in dayasan babu gaskiya Aciki"sadeeq beson yawan surutu da k'arya shiyasa k'annansa ke shayinsa sosai"yanada bak'ar zuciya sbd be iya fushiba"uwa Uba kuma jarumine na gidan gaba "baya tsoro baya shakka"tun suna yara suka tashi da mohd bacci kawai ke rabasu"bayan sun gama secondry skul kowa yakama gabansa sbd kowa nada tsarin Abinda yakeso yakaranta"sadeeq hand some guy ne yanada kyau natashin hankali da baiwar murya shiyasa mata ke damunsa"a k'asar Australia ya had'u da suhan dataje yawon shak'atawa"ta dinga shige masa dajan ra'ayinsa yafara kulata"bayan sun dawo gida Nigeria suka cigaba da soyayya da ita"dukda dama be tab'a soyayyaba sai Akanta "yanada kuma tsatstsauran ra'ayi game da wacce zai Aura"baya son Auren k'aramar yarinya sbd Aganinsa batada ishashshen hankali da tunani"sannan yana son mace wayayya datayi zurfi a llimin boko"shiyasa lokaci guda yaji zai iya son suhan"yarinyar daba yayin cikakken sati beyi fushi da itaba"lokacin data nuna masa yaci gaba da kusantarta kafin suyi Aure"Aranar taga b'acin ransa"koran kare yamata harda mari da gaya mata bak'ak'e maganganu"saidai dayake batada zuciya kwana 3 dayin Abin ,ta dinga zarya office nashi"yana korarta cikin tozarci"daga k'arshe ta rataye kanta bayan tasanarwa iyayenta kosu kirashi kota kashe kanta"shine mahaifinta Alh garba yaje cikin tashin hankali har wajen Abba yasanar masa"shi kuma yakira sadeeq"shine yaje gidansun yasamu Abinda take k'ok'arin yi"tana k'ok'arin sarkafe kanta"daga nan yaji tausayinta ya yafe mata"yana jin kansa na fashewa wai Akansa zata iya kashe kanta"saidai daga baya yamata nasihar Abinda tayi"takuma sha sanar masa wlh zata iya kisa sbd shi"sadeeq be cika yawan mgn ba sai idan kan Aikinsa ne"yana matuk'ar son tsabta da k'amshi" yana kuma matuk'ar son iyayensa da yimusu biyayya"sadeeq dogo ne wankan tarwad'a"yanada tabon sallah a tsakkiyar goshinsa dake matuk'ar k'awata fuskar tasa"be cika barin sumaba asketa yakeyi"sajensa ne kawai yake gyarawa da mayuka masu kyau.... yaran gidan da su shiga gonarsa gwara su kwana da yunwa"sbd baya musu hukunci me sauk'i"Anty salma da Anty hafsat duk sunyi Aure da yaransu"Hjy hidayat tanada kirki da son jama'a "yayinda Hjy binta ba hakaba, tanada izzah da fahari da nuna ita watace"haka kuma Salma da hafsat suke"basusan talaka ko kuma Ace Asalin mahaifinsu daga k'auye ne"sosai mahaifiyarsu ke tsawatar musu Amma sun kasa denawa"baba hamisu shima Anan Kano yake da iyalansa" sadeeq kuwa yanada son zumunci be kuma cika rakice rikicen Abokaiba"bayan mohd dake matsayin DPO Ayanzun bashida wani Amini sama dashi"yanzun haka ginin katafaren gidan dazasu zauna da suhan yakeyi"har gidan yakaita ta gani tanata shagwab'a da sanar masa irin yadda takeso tsarin gidan yakasance"ya kuma Amsa mata dato"kaf gidansu kowa yasan shi da suhan"zarah ce kawai ke bata sonta da moon sbd rashin tarbiyan ta"mama kuwa sau 1 ta tab'a ganinta"yayinda Anty hafsa da Anty salma keson suhan"sbd Aganinsu itace daidai da k'aninsu....
cigaban labarin
sai wajen bayan sallar Azahar Abba....✍️

wannan shine Ake kira da somun tab'i my fans🤓NIDA BARRISTER SADEEQ yazo da sabon salo me girgiza zuk'ata da sakasu nishad'i maza hanzarta kibiyan naki tanan👇

wannan book d'in na kudine

regular grp 300
vip grp 1000
special group 2k wato 3pages in a day

zaku biya kud'in ku ta wannan acc number👉2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
kituro shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

300 kawai ake turo kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne

banason transfer d'in kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira?

y'an nijar ku tuntub'i wannan number 👉 +227 88 01 90 50
normal grp 500f
vip grp 1000f
special grp 2000f

dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biya ba
2/26/24, 14:08 - Ummu: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

❤‍? NIDA BARRISTER SADEEQ ❤‍?

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾



Story &written by
mommyn fareesa

dedicate to zainab hamisu wada 🥰 Ina yinki over tawan kiji dadinki uwar gida Amarya Agidan DSP💃🏼

Free page 3&4

......sai wajen bayan sallar Azahar su Abba suka iso cikin garin charanchi"kai tsaye gidan mlm Auwal suka nufa kasancewar sun tsaya a hanya sunyi sallar Azahar...mlm Auwal Abokine ga Abba tun suna yara suka tashi tare "shi mlm Auwal iyayensa malamai ne shiyasa beyi ilimin boko me zurfi ba, iya kar karatunsa secondry skul ya tsaya....zaune yake A soron gidansa saman tabarma"yana rubutu a Allo"kallo d'aya zaka masa kasan beda wadatacciyar lafiya k'arfin hali ne kawai yakeyi"yaran Abba su biyu suka shigo da sallama da kayan Abinci A hannunsu"mlm ya d'ago kansa ya Amsa yana kallon su suka Ajiye buhun shinkafa da catoom d'in super getting da macaroni"bayin Allah daga Ina?"Abba dake k'ok'arin shigowa cikin soron yace"daga kano! da mamaki mlm ke kallonsa kafin yace"Alh Amadu kaine ko gizo ne?"nine Abokinah "yafad'a yana Ida shigowa ya zauna gefensa"yaran suka gaishesa suka fita"sai kallon gidan dashi kansa mlm d'in yakeyi cikin tausayawa"Ahankali yace "ya iyalin mlm?"iyali sai godiya Alhamdulillah "Amma jummai ta jima da rasuwa kusan shekara guda kenan..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! gaskiya najima rabona da garin nan"ko wajen wani banjiba"Ai inaga kusan 12 yrs kenan rabona nidai dakai"hakane kayi hak'uri dan Allah zan Amshi number naka Adinga zumunci"madallah" Ina sadeeq?nasan ya Ajiye iyali yanzun ko?"Abba yayi murmushi yace"ah ah "daga nan yafara labarta masa matsayin da sadeeq ke Akai da yadda yake a tsakkiyar mak'iya"daga k'arshe yace"insha Allah zaizo ya gaisheka koda Akwai shawarwarin da zaka bashi"to Allah ya Amince

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login