Showing 18001 words to 21000 words out of 86533 words
wuya ba muna da hanya"AbdurRafi da sai yanzu yasa baki yace"Abba yanzu kaima har dakai a tonan nawa" Samir ya kunshe dariyarsa"Abba Aliyu yace"ai kaine Rafi abu ka'dan kace bakaso har kannenka sun ganoka tsokanarka suke da abunda bakaso,kana girma kana kara rashiin wayau"AbdurRafi yace "ni dai Abba Dan Allah a bar maganar ,kai kuma da kake kunshe dariya ka tafi mana kai ga hanya nan" yacewa Samir,Samir,yace"Allah ya huci zuciyar manya musu tsoron training din 'yan sanda"daganan Samir ya gudu ya bar falon yana dariya dan yasan halin abokinsa sarai indai kan ace ya tafi police ne zaku iya yin baran baran,can majalissar unguwa Samir ya shige kasancewar yasan 'yan unguwar wasu saboda akwai abokan karatunsu acan nan ya zauna suna taba fira"AbdurRafi shima binsa yayi yana tunano rashin mutunci da zaiwa Samir saboda yadda ya rainasa dan kawai yace bayason dan sanda saboda training dinsu yanada wuya shiko riqe wannan bindigar aka barshi da shi ai anbarsa da aiki,Abba Aliyu yayi murmushi AbdurRafi da Samir fadansu sai su ba'a shiga koma ka shiga sabaka kunya ya cigaba da kallon da yake a TV
Rufaida ko Samiha bata jima da fita ba tasa hijabi mai girma tabi Samiha su gaisa da Ahmad a falon ba'ki ta samesu ta gabatar da sallama suka amsa mata ta shiga" ta zauna kusa da 'kawartata Samiha da take a kujera mai biyu shikuma yana zaune a kujera mai 'daya an ajemasa lemuka a plat da ruwa datasan duk aikin Umminsu ne inda Samiha ta tsiyaya ruwa a kofi Rufaida tace"Yaya Ahmad ina yini"ya 'danyi murmushi yace"lafiya kalau Hussaina,ya juma'ar?"
Tace masa" Alhamdulillah Yaya,wato bazaka daina cemin Hussaina ba"wanda tun farkon gaisawarsu da Rufaida da taje gidansu Samiha yace ita Hussainar Samiha ce saboda yadda take basa Labarin Rufaida kona Yaya Saudat bata basa haka,dan shi 'daukarsa suna da ala'ka ma,danshi har kama yaga sunayi,"yace mata "Eh mana ai Ku 'yan biyu ne idan akaga wata za'aga Zahra gashima kuna kama ma inda za'a kara tabbatarwama" ya fadi hakan da sigar zolaya"Rufaida tayi murmushi tace"Samiha kinji fa yaya Ahmad da wani zance"Samiha tace"kema dai kya fa'da nibanga wata kamarmu ba ko 'daya"Ahmad da har yanzu bai fahimci alakarsu ba yace"dama haka zakuce"Rufaida tayi murmushi tace" Ai hakane ma"da haka suka sake ta'ba hira ka'dan sannan Rufaida ta fice daga falon ta basu guri suyi firarsu.*JININMU DA'YA♦️*
Sadiya Khaliy💞
Page 13
Samiha ta shigo 'dakin ko sallama babu ta fada gado tareda cire mayafin kanta Rufaida tace" ke lafiya kuwa"Samiha tace"bansaniba wallahi Rufaida Ahmad ya cuceni"Rufaida ta jinjina kai tace mai kuma yayi miki bawan Allah"Samiha ta ta'be baki tace"kinsan tun kwanaki da yacemin zai turo a tsaida magana asa rana"nace masa ya bari keda Yaya Saudat kuma Ku samu miji tukun"ita da Rufaida abinda dariya ya bata ma,Samiha tace"au dariya ma kike ko"Rufaida tace"Ai abin nakine abin dariya banda abinki mainene dan ankawo kudinki muba'a kawo mana ba,kinsan komaifa lokaci ne,kafin ayi naki bikin sai kiga munsamu namu mazajenmu,"da haka dai Samiha tasamu kan Samiha dan ita Samiha dagaske bata yarda ba sai sun samu nasamu mazajen Ahmad ya jira saboda ayi bikin nasu tare
Ranar da Weekend ya kare Monday litinin su Rufaida suka shirya Abbansu da zai shiga Makaranta suna wani taro a BUK din ya tsaya ya saukesu a Al'AZHAR har bakin gate din makarantar ya kaisu inda hankalin Samiha ya tafi a motar da aka sauke Sir AbdurRahman motace maikyau da tsada drivernsa ya tsaya ya fito Samiha tace"Abba kalli malaminmu maikama da yaya AbdurRafi"Abba Aliyu da ya 'karasa parking ya dubi AbdurRahman kasancewar ya 'dan juyar da fuska bai ganshi sosai ba ya daiga bayansa saida ya sake kallonsa yaga fuskarsa shidai baiga wata kamarsu ba sai dai a fisge"Samiha tace "yawwa Abba ka ganshi ko?yace mata " Eh a ina yaron yake kunsan shine"Samiha ta cemasa"Khalid Bashar way yake kusa da gidanmu wasu ma cewa suke 'dan sane,TP yazo makarantarmu inda kake lecturing yace yake karatu BUK" Abba Aliyu yace"ok,Allah sarki ba lallai nasan yaron ba akwai daliba da yawa kinsan kuma department department ne "tace " eh hakane"da haka suka fice daga motar sauran yaran suna cewa sumafa basu ga kama ba,Abba Aliyu da shima baiga kamaba yaja motarsa ya bar harabar makarantar,a kofar Gate 'din suka ci karo da Sir Samir suka gaishesa suka shige tare da ya shaida fuskokinsu yaran ne ma baigane ba,saboda baya daukar 'yan ajujuwansu,yace"Health prefect da Labour ne ashe"Rufaida tayi murmushi"
Samiha tace"Sir yanzu Abbanmu ya saukemu a mota da har zan kwala ma kira ku gaisa"Rufaida da take zungurar Samiha tayi shiru taki banda shiga ukun Samiha meye na fa'dar hakan bandama koyarwa daganin wannan matashin AbdurRahman zaiyi ji dakai,kuma ga iron motar da aka saukesa da gani dan masu dashine sosai,amma Samiha sai zaqalewa take,tana nema ta wuce gona da iri"AbdurRahman yace"Aiya wani lokacin zamu gaisane"Samiha tace "hakane " tabar maganar daga haka kar dalibai su hangosu a yimata wata fassarar,dan tasan halin 'yan makaranta"
Ana gama a assembly malamin biology AbdurRahman ya shigo yafara koyarwa nan aka aiko wata daliba ta kira Rufaida da sallama 'dalibar ta shigo ajin inda AbdurRahman ya tsaya da koyarwar ya amsa 'dalibar tace"Sir ,Sir Nura yace Rufaida Aliyu Bukar tazo"AbdurRahman yace"to kice tana zuwa"ya dawo ya kalli 'daliban yace"wacece Rufaida Aliyu Bukar"Rufaida ta mike tace"Sir gani"AbdurRahman yace "au Health prefect dama kece Rufaida?" Tace masa" Eh"yace "ok,kije Sir Nura ke kiranki kiyi maza kidawo kinga lesson muke"da haka Rufaida ta fito daga bencin tana cewa"to"shi ko AbdurRahman zama yayi akan kujera ya huta kafin Rufaida ta dawo ya cigaba shi sai yanzuma ya tuno Rufaida itace su Nasiba sukace yana kama da wani yayanta,shi kasancewarma baidamu da sabgar ba yama manta gaba 'daya tundaga ranar baisake tunowa ba ,saida ya dawo ya cigaba da lesson 'din harya gama ya fita ya kira Nasiba"ya bata wani class work daya basu ta rubuta a allo period ta gaba da malamin period din baizo makarantarba zaizo ya duba"daliban da sai zagin Sir AbdurRahman suke don ya fiye takura daga fita abada wani aikin aji suna mita suka rubuta suka fara duba test Book 'din biology ita Rufaida key point kawai ta duba tayi taba Samiha tayi ita kanta Nasiba zagin AbdurRahman tafarayi duk shirin da suke da AbdurRahman din don kusan a ajin sunanta yafi riqewa
Periof nashiga yana shigowa ajin ya fara da duba litattafan daliban benci benci matanma sunfi mazan kokartawa bencin su Rufaida ya karasa da shine ya bari na karshe duk sunfi sauran kokartawa dan da marking zaiyi sune suka cinye duka tundagan suke 'dan shiri dan shi AbdurRahman yanaso yara masu kwazo Samiha har number dinshi gareta da Ahmad ya kawo mata wayarta mai tsada ba laifi infinix ce da a yanzu haka ansa rana da sunyi candy za'ayi bikin dukda yadda Samiha taso a hada bikin koda na Yaya Saudat ne da yanzu haka tasamu saurayinta mai sonta cousin dinsu a sokoto Mujahid dan tuni ta hakura da wancen da suka hadu a biki dan akarshema wayoyinsa daina shiga sukayi,hakanan Yaya Saudat ta hakura da jiran gawon shanun da take ta amince da Mujaheed Abba Hashim mahaifi ga su Samihan shima kansa ya amince da hadin auren kuma abin yayi masa dadi sosai itako Momy Maryam mahaifiyarsu Samihan da Mujahid din yakasance 'dan yayanta tamafi kowa murna da wannan hadin
AbdurRahman ranar da zai gama TP dinsa haka 'yan ajin duk suka ji ba da'di kasancewar sunsan ba lallai su sake cinkaro da Shiba koda a hanya ne don su dai sunsan haduwa da iyalan Khalid Bashar da kamar wuya dan Nasiba Shehu da Hauwa Umar sunada ya kinin gaskiya suka fada musu dukda yawanci yan makarantar 'ya'yan masu da shine amma wasu sunfika kaima kafi wasu sunfika haka rayuwar ke tafiya.
AbdurRahman ya kalli su Nasiba gaba 'daya su shida group 'dinsu harda su Rufaida da yake ji a ransa duk ba dadi saboda yadda ya fara sabawa da yaran da yake jinsu har a ransa gasu masu kwazon karatu donshi ko 'yan ajin basu taba masa rashin kunya ba ko zaginsa sai dai ko a bayan idansa shiyasa yake ji babu dadi bayan ya fito daga ajin nasu inda yake tsaye birandar ajin nasu sukuma sun tsugunna a gefe yace"Nasiba Shehu ya maganar karatun naki ne"tace masa"Sir Jamb zamuyi nidasu Zainab Farouk,da Hauwa"AbdurRahman yace"banji kince su Rufaida da Samiha ba"Nasiba tace "lah sir dama banfa'dama su Samiha aure zasuyi ba" ita da Rufaida"Samiha tace"Sir karya fa suke"AbdurRahman yace"to inma shine aiba wani abu bane"Hauwa'u tace"wallahi Sir bama karya muke ba itafa Samiha bayan candynmu da sati biyu za'ayi bikinta,itace dai Rufaida bamu sani ba"AbdurRahman yace "hala wannan yayan Rufaidan da kuke cewa muna kama zasuyi auren zumunci dashi da Samihan,gashima har zan tafi bamu haduba" ya fada da murmushi kan fuskarsa Dan shi ma tunaninsa sunada dangantaka"Aisha Mudassir tace "Eh Sir laifi su Samiha ne basu hadaku kun gaisa ba amma yarone fa koni nakusa girmarsa"Rufaida ta harari Aisha"tace kinma girmesa kawai zakice"AbdurRahman yace"To masu 'dan uwa,don tace ta kusa girmarsa shine harda bakar magana" Rufaida tace"Sir koni fa shekara kusan biyar ya bani inji Umminmu shine zatace ta kusa girmarsa "murmushi AbdurRahman yayi kawai yacanza maganar da cewa"saura kuma kumanta dani lokacin bikin kuki fadamin"duka suka amsa da Insha Allah zasu fadamasa tunda suna da number dinsa da haka ya musu bankwana ya tafi suna kewar juna*JININMU 'DAYA*
Sadiya Khaliy💞
Page14
Zaune suke gaba 'daya yaran Abba Aliyu a babban falo da yau yake shirin tafiya zariya da yara hutu Abba Aliyu ya dubi kowa na falon yace"kufa nake jira kowa ya tsaida gidan da zaije hutu kar sai munje Ku batamin lokaci naji Rumaisa tace Kaduna gidan Zainab zatayi hutu shima AbdurRashid yace can zashi"Rufaida jin ba'a anbaceta a tafiyarba dan tagama sakankancewa har da ita tace"Abba yanzu ni banda ni"Ummi Hauwa'u ta harareta tace"bikin Samihan zaki bari ki tafi ko kuwa"Rufaida da ta tuno yanzu dan da tunima anyi bikin bangaren su Ahmad sukace a bari ayi hutun Makaranta sai ayi tace" a'a Ummi"Abba Aliyu da shima ya tuno da bikin yace"ni banda zuwa porthacourt din nan kamar dolece ni aka za'ba naje Hauwa'u bazan 'ketare bikin nanba bikin 'yata sukutun da guda"Ummi Hauwa'u tace"hakane Abban AbdurRafi aiga AbdurRafi zai wakilceka"Abba Aliyu yace "Eh hakane,saura kwana nawa bikin ne Ummi Hauwa'u tace saura sati biyu" Abba Aliyu yace haba harma dawoma"Rufaida tace"Abba kona ha'da kayana naje nima"Ummi Hauwa'u tace "wai Rufaida meke damunki raban IV da zaku fara fa a wannan satinfa,kuma kinsan ranar asabar din nan amarya zatayi yininta a Kano,tunda a sokoto za'ayi bikin akaita daga can"Abba Aliyu da yaga matartasa ta hakikance Rufaida bazata hutu ba kamar ba garinsu zata hutun ba shi abinma dariya ya basa dan yasan badan komai take wannan hanya hanyarba don kartaje ne suma su AbdurRashid dan bayarda zatayi tace bazasu bane shi yarasa maiyasa Hauwa'u takasa manta baya dukda yasan abubuwan da suka faru da aurensu dama bayan aurensu,haryau tsoro take kar nata suje gidan da tasha wahalar rayuwa a ciki,suko yaran da basu fahimci dalilin fa'da Umminsu ba dan cikin fada take maganar abinda basu saba jiba gurin umminsu saifa ta tutance dukda suma suna fuskantar tsangwama amma a gidan Abba Bukar da matarsa ke musu shiyasama ko zuwa zariya zasuyi gidan Gwaggo kakarsu suke zuwa da Malam da Gwaggo suke lalla'basu kamar kwai sai duk jikin yaran yayi sanyi jiki ko harda AbdurRafi da yake tuno wasu abubuwa da suka dinga faruwa a zamansu gidan Abba Bukar kafin Abbansu ya samu aiki yadawo Kano,AbdurRashid ya katse shirun da cewa " Abba na shirya kayana tun jiya kuma mungaisa a waya da Aunty Zainab tun kwanaki a gidanta zanyi hutuna",Abba murmushi kawai yayi don ya fahimci AbdurRashid gudun yin hutunsa yake gidan Abba Bukar,tunda yaron yasan acan zasuyi hutun Abba Bukar nema ya bukaci aje ayi hutu a gidansa danshi Abba Bukar mutum ne mai son danginsa banda Allah ya hadasa da mace mara kirki da kusan Hajiya Jamila ke juya gidan Abba Aliyu yace"shikenan"ke Rumaisa sai kiyi a gidan Abba bukar"Rumaisa ta amsa da"to"badan taso ba ita don itama kanta batasan hutu gidan Abba bukar da tasan can za'a kaita tunda Abba Bukar ta fiso tayi a gidan kanwar babanta Aunty Zainab ko gidan Gwaggo saboda tsangwamar da suke sha indai sukaje hutu gidan Abba bukar gurin Hajiya Jamila saukinsu suje gidan kakarsu Gwaggo "Ummi Hauwa'u bataji da'di ba jin Rumaisa ce zatayi hutu gidan Abba bukar dan bata manta rayuwar da tayi a gidan saidai sam bata nuna koda a fuska ba da haka suka shirya tafiya har bakin mota suka rakasu Abba Aliyu ya bawa Ummi Hauwa'u kudin kashewa ko yaransa ragowar zasu bukata sai kuma kudin cefanan kayan miya abun abinci basuda matsala akwai komai ya sake jaddadamata ta kula masa da yaransa sosai dukda yasan baida matsala ta wannan fannin da Hauwa'u haka ma babban dan nasa AbdurRafi yana kokarin kula da yaran indai Abba Aliyu bayanan kobaya kusa fiyema da shi danshi Aliyu sanyi garesa abunda ko zai batawa Aliyu rai to babbane
Ummi Hauwa'u da take zaune bakin gado tana canzawa Ra'is kaya Rufaida ta turo dakin bayan taji Ummi ta amsa masa sallamar da tajira ta amsa tukunno kai dakin Rufaida da Rafi'a mai kusan shekaru biyar ko shida a hannunta ta dubi Umminnasu tace"Ummi nagama shiryawa kudin Napep zaki bamu mu tafi" Ummi Hauwa'u ta dubeta bawata kwalliya fuskarta dan Rufaida ba mace bace mai son kwalliya mai yawa bama taga Rafi'a ba tace"karasa shiryamin Ra'is to na daukomiki "badan tasoba ta zauna gefen gado dan ita macace mai son gayu bataso tayi wanka taga kayanta duk sun cukurku'de sau tari Ummi nace mata zata daina ne data haifi data fara tara yara amsar Ra'is tayi ta fara kokawar sama sa wando Rafi's tana masa wasa ummi Hauwa'u tana kallon yadda take 'bata rai tanasa masa wando sai alokacin ta lura da Rafi'a ta duba inda ta aje kudin tace"har kin shirya Rafi'a ne naga kamar baki mata wanka ba kuma kinsan dai bazata bari ki tafi gidan Momy Maryam ba banda ita kimayi kokarin shiryata kafin ku tafi ko kuma ki tafi da Ra'is" Rufaida tace"Momy biki ga nayi mata kwalliya ba,ai momy gwara yawo ma da Rafi'a dukda surutunta dadai kukan Ra'is yataramin Jama'a ace na satosa"Ummi Hauwa'u tace"ke banfasan wulakanci 'dan autan nawa kike cewa yana kuka ,ta mika mata kudin data dauko taceni anshi kudin ki wuce ku tafi"Rufaida ta dungurar da Ra'is gado ta amshi kudin Napep dari biyar kuka Ra'is ya fara "Ummi wannan mai kai kwal uku shine Autan Ai ko zakiyi auta kyakkyawa ne ""Ummi Hauwa'u ta daukesa tana lallashi tace "ke karfa ki jiwa 'dana ciwo yanzu da akasa yake da tuni ya ji zafi koma yaji ciwo" Rufaida tace"yanxu Ummi daga dungurarwa sai kice da akasa ne saiyaji ciwo tace"eh man baki San tsautsai ba ,kuma ma Ra'is dakike fa'dar muninsa dake yake kama" Rafi'a ta kunshe baki da dariya ta tahomata,Rufaida tace wallahi yarinya kikamin dariya fasa zuwa zanyi dake"Ummi tace"haba yarinya ai baki isa ba kuwa tare zaku itama taje taga kawarta Samima "murmushi Rufaida tayi dan hirarsu da Umminta bata karewa takama hannun Rafi'a suka bar dakin suna cewa da Ummin sun tafi addu'a ta bisu da ita tana kara jin kaunar wannan zuriya tata da Allah ya azurtata da samu*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khaliy
Page 15
ASuna isowa bakin titi suka tari adaidaita zuwa Nasarawa GRA a flyover wajen bada hannu suka tsaya saboda go slow suna tsayawa Rafi'a da ta fara kalle kalle ta hango wata mota dake 'bangaren hagunsu motar akwai daukar ido sosai matashin cikin motar Rafi'a ta soma nunawa Rufaida tace"Yaya kalli waccen Ash din motar kiga mai kama da Yayanmu"Rufaidsa da take ji mai tace tayi banza da ita dan inta daka ta Rafi'a saita ja musu zagima yanzu saida ta kuma maimaitawa sannan Rufaida ta doke hannunta ta kalli motar da bata kalli na ciki ba tace" nagani wadda bata iya gani ta kyale aike dama matsalar zuwa unguwa dake kenan surutu da kalle kalle yanzu idan mai motar yaga kina nuna safa ba kisan koshi waye ba haka kurum kijamin"Rafi'a tace"Yaya Allah da gaske nake ki kalla mai tuka motar sosai kigani"Rufaida da ranta yafara baci tace naji zan kalla amma kinsan Allah naga akasin haka wallahi saina dokeki idan muka koma gida ko kuma nadaina fita unguwa dake kinyarda "Rafi'a tace "Eh"motar da take nunawa Rufaida ta zuru kanta waje taga matukin motar Kallo 'daya Rufaida ta masa ta fahimci kamarsu sosai da AbdurRafi harma tafi wadda ake ganin AbdurRahman malaminsu yanayi da AbdurRafi dan ita saitace ita bama ta taba ganin kamar AbdurRafi da AbdurRahman ba kurum su Nasiba ke haukansu da Samiha take tayasu,amma wannan matashin na cikin motar banda yanayin shekaru da shi wannan na motar zai iya dara Yayan nasu shekaru ba da kuma yanayin hasken fata da wannan ya 'dara AbdurRafi yayansu haske da sai tace shine ma yayansu" maganar Rafi'a ta dawo daga tunanin data tafi tace"Yaya kema kingani ko ki masa magana koma yayanne"Rufaida tace"banda abin Rafi'a daga kama sai ace lallai wanda kasani ne"Rufaida batayi aune ba taji muryar Rafi'a tana dagawa na motar hannu tana"yaya,yayanmu"Rufaida da zata finciko hannunta mai tuka a daidaita sahun da ya gani ta cikin maduni ya juyo da yake jin duk hirarsu kawai shi bayason shiga hurumin da bana shiba ne "yace haba 'kyaleta mana kikasani ko yayan naku ne"Rufaida da takaici ya fara isarta cikin napep din ta maido kanta tanajin haushi abinda Rafi'a keyi tana kwalawa bawan Allah kira da suna Yaya aranta tanaji ba zata kara yawo konan dacan da Rafi'aba karta dinga jawomata abin magana sai da Rafi'a taga ya juyo ya mata murmushi da shima saurayin matashin maganar da Rafi'a keyi ya fara isarsa har yafara tunanin dashi ake shine dalilin waigowarsa ganin karamar yarinyace mai zubin Hausa Fulani ya sakar mata murmushi ya tada motarsa ganin an fara yi masa horn a baya ma'ana danja ta