Showing 57001 words to 60000 words out of 86533 words

Chapter 20 - JININMU DAYA HAUSA NOVEL

zan amince ya auri yarinyar nan ba,ko ni kaina bama ga Yaya Sule da Yaya Abdu kadai ba suka hana auren ba harda ni kaina mutanan da sukai kokarin lalata mana suna sukai silar rabamu da farin cikinmu rabuwar da sai dai mu kira ta da ta har abada" daga nan Dady Jabir ya fashe da kuka kai kace karamin yaro ne"
Ammi ganin mijinta na kuka yasa hankalinta ya tashi da cewa
"Haba Abban Safiyya me yayi zafi haka kai ba karamin Yaro ba bakomai ba,addua zaku cigaba dayi tuno da abinda ya wuce ba shine mafita ba"
Da wannan kalaman ta cigaba da lallashinsa har ya hakura

*****
Yaya yayaa Safiyya take kwalawa Ra'uf kira da baccin ya fara daukarsa
Ra'uf da yaji maganar Safiyya kamar a mafarki ya vu'de idanunsa ya mike zaune ya dora idanunsa akanta ya dan harareta da cewa
"Sophie Khan ya akai ne,kike kokarin fasamin dodon kunne"
Zama tayi kusa dashi tare da cewa
"Yaya yanzu Intee ta kira ni sunje Us ita da yayanta ankafe suna taga sunanmu nida Husna"
Murmushin Ra'uf yayi tare da cewa
"Kai amma ina miki murna sister,kin fadawa Husnan?"
Safiyya tayi saurin cewa"A'a Yaya,zuwa nayi ka kira ta a wayarka a fada mata"
Ra'uf yace
"Ke ina kudin wayar taki?"
Safiyya tayi saurin cewa
"Yaya ai ba kudi a wayata kamanta ne"
Hararar wasa yayiwa Safiyya da cewa
"Dady jiya ya sa miki kudi ina kika kaisu"
Marairaicewa Safiyya tayi
"Na kira kawaye na tun jiyan"
Tsaki Ra'uf yayi ya mikamata wayar dan sarai ya gano kudin nata ne batasan kashewa na cikin wayar.
Lambar Husna ta kamo ta kira ta shaida mata samun makarantar da sukayi ba karamin murna Husna tayi ba ita ma,daga nan suka cigaba da firarsu saida Ra'uf ya gaji da surutun da Safiyya ke masa a kunne ya anshe wayarsa ya kashe

Sadiya Khalil🖤*JININM U 'DAYA*
By Sadiya Khalil❤️

42.

Ina yiwa masoya wannan littafin fatan alkhairi a kowanne lokaci ina kuma anfani da wannan damar gurin yiwa 'yar uwata Aisha Umar Ibrahim fatan alkhairi na gama littafinta mai suna ZAN JIRATA lafiya Allah ya hadamu da alkhairan cikin littafin ya kawar damu da akasinsa ya shiryar damu bisa tafarkin tsira ya bamu ikon rubuta abinda zai anfanardamu ko bayan bama raye.Amin

42.
ABDULWAHID

Cikin kwarewa yake aikinsa da kwanciyar hankali auren Rufaida,bakaramin farin ciki yake da shi ba,tana nuna kulawarta gare sa,aikin da yake ya ajiye gefe,ya dauki wayarsa da take ringing wanda tunaninsa Rufaida ce,ganin tunda ya tafi aiki busu yi waya ba yadda suka saba,sai tunaninsa ya basa ko itace da taga bai kira ta ba ko ta kirasa,duba screen din wayarsa da yayi ya kaudar masa da tunanin sa ganin sunan da yasa wa Ummansu akan screen din itace mai kiran nasa wata irin faduwar gaba yaji ta ziyarce shi tunda yaga kiran Ummansa yasan sai ta yi masa fada sosai don yasa koda bakin aurensa a ranta sai ta masa don rab. an da ya kira ta yau kwana 7,a bakin Abbansu yaji duk abinda ya faru ganin tana kokarin katsewa yasa shi saurin dagawa
"Assalamu Alaikum,Umma ina yini,ya su Aunty"
Yayi maganar a jere a kuma tsoro ce
"Kazo ka shiga damu barrack din ku munzo yanzu nida Ruqayya"ba tare da ta vashi waccen amsar ba ta tare sa da wannan maganar da haka ta katse wayarta
AbdulWahid da baida wani zabi da ya wuce yaje tararsu da haka ya mike daga office dinsa ya fito ya fito yaje tarar mahaifiyar tasa ba tare da ya tuna da kiran Rufaida a waya ba ya Shiga motarsa ya fito daga headquarter dinsu

RUFAIDA

Jin bugun kofar falon nata yasa ta mikewa daga kwanciyar da ta tayi a kujera da barci ya fara daukarta jin an cigaba da bugawa yasa ta mikewa ganin waye cikin tsakar ranar nan yazo gidanta sai da ta leka kofar ganin mijinta tsaye jikin kofar ya sata kokarin bude kofar da murmushi akan fuskarta,ido biyu tayi dasu Hajiya Jamila da suke bayansa da hanzari tayi kokarin basu guri tana cewa
" Sannunku da zuwa Umma"
Wani banzan kallo suka jefeta da shi,suka karasa shigowa falon wanda da ido suke bin ko ina na kusurwar falon da suke kokarin ganin makusar falon nata
Da wani murmushin ta sake cewa
"Sannunku da zuwa Umma ku zauna mana kunsha hanya bari na kawo muku ruwa" daga nan ta shige ciki
Basu ce da ita komai ba ganin ta wuce yasa suka bita da wani banzan kallo daganan suka zauna a kujerun falon suna ya mutsa baki dukda kayatuwar falon kuwa
AbdulWahid katon akwatunsu ya shigo musu da shi da shima ya najin sannu da zuwan da ta musu basu amsa ba,har karo biyu sharewa yayi ya shige da akwatun nasu ciki dan yana ganin akwatun ya fahimci bada tafiya suka zoba da zama suka zo kofar wani corridor na gefen wani daki ya aje kayan ya shige cikin kitchen din da yake tsammanin Rufaidan na ciki jikin kofar kitchen din yayi tsaye yaki karasa shiga ciki da murmushi kan fuskarsa yake kallonta tana kokarin jera lemuka da ruwa akan faranti mai girma ta juyo zata fito idanunta ya sauka cikin nasa murmushi tayi masa inda take ya karaso ya mika mata hannu ganin haka yasa ta gane manufarsa mika masa plat din tayi ya amsa ya rike dubensa tayi kana ta soma magana
"Haba Yaya yanzu su Umma zasu zo koka sanarmin gashi sunsha hanya,kuma nasan suna jin yunwa yanzu fa sai sun jira na dora"
Murmushi yayi jin kalamanta gaba daya baza kace bata murna da zuwansu ba dukda kuwa yasan hakan ne don koshi da Umma take mahaifiyarsa Rukayya kuma take matsayin kanwarsa baya murna da zuwansu bare kuma ita dan yasan babu alkhairi a zuwan nasu tunanin da yake ya aje gefe kafin yace
"Kanwata sai yanzu suka sanarmin da zuwan nasu tuba nake" ya karasa maganar da murmushi
"Hm" kawai tace tana kara mika hannu ta amsa tray din
"A'a ki kyale zan kai musu ki dauke musu kayan nasu ki kai musu inda kikaga ya kamata su sauka suna corridor" daga nan suka fito daga kitchen din tare

Da sallama ya dawo falon da sallamar ta katse musu firar da suke ganinsa dauke da tray da yake kokarin aje musu akan centre table yasa Hajiya Jamila saurin kallonsa tare da kokarin cewa
"Wahid me zan gani haka,kaine dan aikin gidan kardai daga auren harka zama mijin tace"
Kai ya sosa da kokarin cewa
"A'a Umma wanne irin mijin tace taimaka mata nayi fa"
"Taimako a haka ake taimakon,dalilin gujema auren nan da nayi kenan,haka kurum kaje ka kwaso irin karuwai,ba dole su mallake ka ba,gashi harsun rabani da kai,ko waya yaushe rabon da ka kira ni" cewar Hajiya Jamila
Rukayya tayi saurin cewa
"Wallahi kuwa Umma"
Hararar Rukayya yayi yace
"Ke kuma dake ake magana ya kalli mahaifiyartasa yace mata,
"amma ni Umma wannan va mallakewa bace,kowa yasan akwai taimako tsakanin mata da miji sannan,vatun kalmar karuwanci da kike jifansu dashi ,ina jin tsoron mahaifiyata ranar lahira ta tsaya gaban ubangiji ace tazo da wannan shaidar,biki gani ba ba ayi a gabanki ba,to me zaki cewa ubangiji a wannan,sannan ni Umma wallahi ba ruwan Rufaida da kin wayata dake dangataka da ita daban da taki ma haka,ba ruwanta da mahaifiyata,idan ba itama biyayya zata yi miki ba"
Hajiya Jamila cikin fusata ta dubesa tare da cewa
"To ubana jeramin magana,don ance matarka tana kokarin mallekeka zaka rika jeramin magana" ganin yadda mahaifiyata sa ta fusa ta daga 'yar maganar sa yasa shi sassauta murya gurin cewa
"Umma kiyi hakuri" sai a sannan ya gaishe da Umman tasa,kamar ba zata amsa ba tadai daure ta amsa,Rukayya da dakyar ta iya gaishesa don bakara min haushin abinda yayi mata lokacin ta ji ba amsa mata yayi ya mike yabar falon yana kokarin shiga ciki kiran Rufaida jin har lokacin bata fito ba wanda ta tsaya sake gyara dakin da su Umman zasu sauka ne a hanya yaci karo da Rufaidan zata fito falon bayan gamawarta murmushi ya sakar mata don baya so ta fahimci wani abun ita ma murmushin itama tayi don bata so ya fahimci taji duk maganar da sukeyi a kokarin ta na dawowa falon da tayi jin suna magana ya sata kasa karasawa kuma takasa barin gurin kuma maganarma duk dai akanta maganarsa ta katse tunaninta
"Dama nazo na sanar miki zan koma vakin aiki,ki fito kuyi fira karki varsu su kadai,sai ma naganki zaki fito din"
Ba tare da tace komai ba suka rankayo falon tare
Rufaida da suna isowa ta durqusa har kasa tana gaishesu da sake musu sannu da zuwa harda Rukayya ta gaisar da Rufaida bata tunanin Ruqayyan zata iya gaida ita kamar ba zasu amsa ba Hajiya Jamila ta daure tace mata
"Lafiya"
Daganan ta mike ta nufi Centre table din ta tsiyaya kowacce ruwa da lemo tace musu
"Ga ruwa kafin a dora abinci" babu wadda tace mata koda to a cikinsu ita ma batayi tunanin hakan ba daganan ta mike ta basu guri,AbdulWahid dake tsaye jikin TV yana kokarin canza tasha yana jin duk abinda yake faruwa bai sake saurararsu ba yayi hanyar barin falon
Yana kallonsu dukansu har Rufaida da ta yiwa kanta matsugunni a wata daga cikin kujerun falon yace musu
"Zan koma bakin aiki saina dawo"
"Adawo lafiya"
Hajiya Jamila ta iya furtawa,Ruqayya ko kallonsa bata yi ba bare tayi masa addu'a
Rufaida ta biyo bayansa yi masa rakiya da su Hajiya Jamila suka biyota da wata muguwar harara,musamman Ruqayya dan gani take da tuni ita ce a cikin daularnan fa wannan yarinyar tayi mata shigar sauri a zuciyar AbdulWahid dalilin da yasa take jin wani matsanancin kishi akan Rufaida, har jikin motarsa ta rakasa
Wahid da yake kokarin shiga motarsa ya juyo yana Kallonta cikin nuna tausayawa zamansu da mahaifiyar tasa tun kafin aje ko ina yace
"My wife kiyi hakuri nasan kemai hakuri ce anma ki cigava dayi karki gaji nasan kinsan halin UMMA bana tunanin zaki sha wuyar zama da ita,dama kafin sanin halin mutum shine wahalar kafin nan dai da Abba ya sauko ta koma dakinta"
Murmushi tayi masa ta kallesa
"Haba Yaya ai mamarka kamar Ammi ce koda ba muda alaka ni dakai"
Ya tari zancenta da cewa
"Eh dukda hakan,kinsan zama da uwar wani sai hakuri musamman Umma"
"Haba Yaya karka ce haka uwa uwa ce mu cigava da yi mata addu'a Allah ya ganar da ita Rufaida take fadin haka
" Hakane my wife,bari na koma aikin,sai na dawo"yayi maganar yana yi mata kallo mai cike da soyayya
Kai ta sunkuyar kasa ganin kallon da yake mata
Murmushi yayi yace
"Badai kunya na baki ba dan na kalli mata ta kallon soyayya,wallahi Rufaida ina sanki kinada halayya mai kyau,da yake karamin sanki koda yaushe,gaki kyakkyawa" yayi maganar yana dariya ya shige mota yana kokarin tayarwa yace
"Ya ba kice komai ba"
Ta kallesa race
" to Yaya mai zance?"
Yace mata
"kice wani abu nake so"
Tace
"To ka kulamin da kanka banda kula 'yammata"
Ya dan harareta yace
"Idan na kifa"
"Hmm"kawai tace
Yace
" kinga uwar kishi ni bani da lokacin kula mace,amma ga babbar wadda zaki kishi da ita nan tazo har gidanki Ruqayya,kibi a hankali dama inason fada miki"
"To Yaya insha Allah,ka koma naga lokaci na kurewa"tace masa
" to My Special na tafi
Yana kokarin tada motarsa tayi kokarin yi masa addu'a
"Adawo lafiya Allah ya tsare minkai"
Amin ya fadi hakan da murmushi yayi kokarin barin harabar part din nasu.
Saida taga wucewarsa tabar wajen ta koma ciki tana murmushi tana san mijinta saboda halayyarsa abar so ce ya iya nuna kulawarsa ga mace,dukda tasan tanasan Ra'uf amma yanzu ta manta dashi,dama addu'arta a kullum Zabin Allah sai gashi yayi mata zabi da Wahid ta kuma rungumi mijinta don dama uwarsa ta jiwa tsoro ba auransa ba amma tunda tanasan zama dashi dole tayi hakuri da mahaifiyarsa domin ance maso uwa taso danta haka ma maso da sai take ga taso uwarsa zaifi,dan da uwar bata haifesa ba ita da bata auresa ba
Da sallama ta shiga falon da babu wacce ta amsa mata bata damu da hakan ba ta dubi centre table din yadda ta tsiyaya musu lemukan haka ta tarar dasu
Murmushi tayi tace
"Umma naga buku sha komai ba anan"
"Haka karuwar uwarki ta koya miki bawa baki abinci kenan,amma ta ko yamiki mallake miji ko,to ni bazan jure haka ba saboda akwai banbanci tsakaninmu mu daku,gadon tsiya kawai"
Hajiya Jamila tayi maganganun tana sake gyara zamanta
Ruqayya shewa ta buga ta ya mutsa fuska tace
"Kinga zo ki mikomin ruwan nina sha"
Bata ko tankawa Ruqayyan ba ta shige ciki ta barsu,dan Ruqayya bata kai matsayin da zata sata aiki ba ta yi mata saitayi niyyar dukda durqusawa wada ba gajiya bane saboda a girme ta girmi Ruqayyan amma ita Rukayya da izgilanci tayi mata maganar kuma ita bataga laifin taba takawo musu ruwa ta tsiyaya musu,daukarce zata gagaresu,to ko ita 'yar aikice aikinta iya nan zai kare

Ruqayyan da kallon mamaki tabi Rufaida don tana da yakinin Rufaida ta fara cin ganye ne.
Girki Rufaida ta dora jallop din shinkafa da taji kayan lambu,da suke a fridge,sai kuma lemon abarba data hada,bata yi tsammanin Rukayya zata iya shigowa tayata ba yasa ita ma bata maida kai a hakan ba dan danan ta gama ta zubawa mijinta nasa daban da zai aiko a ansar masa yadda yake yi tun bayan aurensu daganan ta kawo musu nasu ta aje musu a dining ta karaso cikin falon ta sanar musu da ga abincinsu data samesu kowacce ta hakimce a kujera duk sun kwarkwanta suna kallo abinsu sanyin Ac na ratsasu
"Umma ga abincinku can a dining kona kawo muku nan" ta furta babu wacce ta kalleta saima dogon tsaki da suka ja mata
Ganin haka yasa ta barin inda suke ta ta shige dakinta tayi wanka ta shirya cikin atamfarta kalar lemon green da brown daganan tayi sallah falon dake dakinta ta dawo ta kunna TV ta fara kallo ta dauki wayarta ta kunna data suka fara chat da Nasiba Shehu Garba class mate din ta sosai suke chat suna labarin makaranta,bayan Nasiba ta gama cakakin bata fadamusu bikinta ba sai abakin Samiha suka ji can Nasiba tace
"Ke ban baki labari ba Sir Nura ashe Saliha Nasir budurwarsa ce har ankai kudin nagani ina so"
Emoji na mamaki Rufaida ta tura mata kafin tace
"Ke wai da gaske kike kawata,Saliha dai dana sani"
"Kwarai kuwa,Saliha Nasir mutuniya da suke dabi da Sir nura"
"To Allah ya sanya Alkhairi,idan sa ranar bikin yayi dai dai da zuwana gida zanje bikin ai Saliha nida ita da amana"
Rufaida ta rubuta ta tura mata
Nasiba ta turo mata Voice note ta bude taji Nasibar nace wa
"Kai da mun jidadi to Allah yasa,baki cemin ina Sir AbdulRahman ba"
Voice note din ta mayar mata ita ma da cewa
"Ya na ina badai har ansa ranar aurenku keda shi ba"
Zuwa can Nasiba ta dawo mata da amsa
"A'a ko 'daya,amma dai ansakamin rana a Adamawa zanyi aure, wata makwabciyarmu to dan Yayanta zan aura,da yazo gidanta muka hadu,shima anan Abujar yake aiki a central Bank"
Rufaida ta sake tura mata da voice note din
"Wow kice gidan kudi burinki ya cika"
"Murmushi Nasiba ta turo mata na emoji ta kara yi mata voice
"Rufaida kenan kudin da ba baka za" a rikayi kana yawo dasu ba,kedai kawai addu'ar samun miji nagari da kwanciyar hankali bayan auren,danta kudin miji ba kwanciyar hankali aina banza ne gwara ma ace talaka ka aura indai zai mutuntaka"
Voice Rufaida ta sake tura mata
"Haka ne kawata,Allah ya baku zaman lafiya ya tabbatar da Alkhairinsa"
Ganin wayarta na kara alamun kira yana shigowa Wahid ne mai kiran tana kokarin dagawa ta katse
" yasa tayi saurin cewa Nasiba zamuyi chat anjima" Nasiba ta rubuto mata
"OK akwai labari dama inason fada miki"
Da haka ta kashe data tana kokarin bin kiran wani wani ya sake shigowa
"Assalamu Alaikum matata"
Jin muryarsa ya sata murmushi
"Wa'alaikumus salam mai gida ya aiki"
"Alhamdulillah,yanzu kofur Bala ya tawo amsar abinci ki hado da Plat da yawa yau Kabir yace da abincin ki zaiyi launch,dafatan kingama aikin lafiya kuma baigaji dake ba"
"Murmushi tayi jin maganar mijin nata
"To sai yazo nagama komai"
"Yawwa farin ciki na da fatan kin Zubawa su Umma tun dazu"
Tayi saurin ce masa
"Eh ya mijina"
Yace ok take care bye ina aiki yanzu"
Tace masa"agama lafiya take care to u my regard to Yaya Kabir
Da ganan ta katse wayar ta mike ta nufi kitchen ta hada abincin a basket ta dawo falon inda tasa mesu nan ta barsu
"Sannu da hutawa Umma" Rufaida tace tana zama kujerar dake gefen tasu ta aje basket din kusa da ita batayi tunanin zasu amsa musu ba ita ma ta share su jin alamar kararrawar kofar falon na motsi ya sata zura hijabin da ta fito dashi a hannu ta dauki basket din sukw gaisa da kofur bala ta mika masa basket din ta dawo ciki ta zauna inda ta tashi tanaji suna yi mata habaici amma bata saurare su ba ta cigaba da kallonta
Ruqayya ce cikin tsawa ta fara magana tana kallon Rufaida
"Ke yar masu samu tafi iyawa ina ne matsugunnunmu,ko bamu da shi"
Rufaida ta kai muryarta kasa dan yanzu taga rashin kyautawar nuna musu masaukinsu amma dai bata ga fuska ba zata iya cewa tace
"Kiyi hakuri Ruqayya na manta wallahi da kin shiga ciki kin wuce wani corridor to daki na farko shine naku"
Tsaki Ruqayya taja ta mike ta shige ciki Rufaida ma mikewa tayi ta shige ciki,tanason tanbayar Umma ko sun ci abinci amma tana tsoron abinda zaije ya dawo"
Bayan wata 8
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da Rufaida da yanzu take da ciki Na Wata 6 , tsananin hakuri take duk a wannan lokacin da surikartata da kanwar mijinta zaman su da ita kullum dai cin mutunci ne gareta duk yadda take kyautata musu,dan har lokacin basu tafi ba,Ruqayya ce kawai taje gida yin jarabawar jamb tana gamawa kuma ta dawo
shikansa Wahid yana kallon abinda akewa matar tasa sau tari sai dai bai isa yace wani abu ba,ba tun hidima iya yi yana yi musu dan albashin na watan da mahaifiyartasa suka zo yana dauka dinkunan sawa yayi wa mahaifiyar tasa dasu,Ruqayya ko duk yadda ta kai da shishshige masa baya koda saurararta don shi soyayya ba ta damesa ba koda ma auren nata zaiyi matar da ya aura ma da yake sonta baiyi soyayya da ita ba ta azo a gani saboda rashin lokaci bare kuma yayi da Ruqayya,Rukayya kuwa tana kara jin son Wahid har ranta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login