Showing 33001 words to 36000 words out of 86533 words

Chapter 12 - JININMU DAYA HAUSA NOVEL

yaji dadi da yaga Yaya Balki bata goyi bayansu ba ya kuma fahimci Zainab da wasa tayi maganar dako anan yana kyautata zaton ya samu shiga murmushi yayi
Da haka su Zainab suka shige suma sauran matan da Yaya Balki suka shige motar har jikin motarsu su Rufaida sukaje yi musu rakiya sukuma suna zolayar Rufaida said bikinta zasu zo Kano itadai murmushi tayi Ra'uf da matso shima yayiwa su Zainab da iyayensu sallama bayan sunyi ne ya zaro kudi masu yawa ya mika musu sunji godiya suka yi masa da haka motarsu tabar gidan motarsu
Cikin gidansu Aunty Samina suka koma da ita da Aunty Samira da Nasiba su sai anjima Ahmad yace musu Ra'uf zai ajesu gida da shima yau zaikoma Kano

*******
"Rufaida gaskiya kinyi sa'ar masoyin gaskiya samun masoyi kamar Ra'uf a wannan lokacin abu ne mai matukar wahala Dan inada yakinin da gaskiya yazo aurenki zaiyi dan Allah ki riqesa hannu bibbiyu dan yanada kyakkyawan hali,Ahmad yasha fadamin kyawawan hali irinna Ra'uf kuma yafadamin da gaske yake sonki har sun kira Abbanmu sun shaidamasa zasu je tanbaya kuma yanaso kafin yakoma Delhi ya tura magabatansa asaka rana ayi komai""
Rufaida da take kokarin gyara kayan jakarta takalli Samiha
"Gaskiya ne Samiha insha Allah zan riqesa da hannu bibbiyu ina godiya kawata"
"Babu komai kawata nidake tamkar abu daya ne,ina tunanin nama fiki jindadin hadin nan"
Ido ta zaro
"Eh mana dan yaya Ra'uf yace min bakya wani sansa kike nuna masa"
"Kijimin da mutumi idan ba goyasa ya keso na riqa yi ba bansan maiyakeso nayi ba"
"A to kidai gyara dan gaba kadan mijinki zai zama dan nama rage miki zance ban fadamiki Abba dazu ya kira Ahmad a waya yake shaidamasa Abbanku ya masa izinin zuwa gurinki zance yamace basai sunzo Kanon ba,kinga nanda wata shida zamusha biki ni tuwona maina abu namu"
Ni kinga ki kyaleni haka da wannan maganar tayi maganar tana mikewa
"Au zamu rabunma shine zaki mike kibani guri"
Hannun Rufaidan ta riko
"Yi hakuri kawata dawo ki zauna,tunda abin na laifi ne dan na miki maganar rabin ranki kuma gaskiya na fadamiki"
"Wani gaskiya indai irin wannan maganarce banaso"
"Zaki sone malama ki kyaleta samiy ina tunanin tafara jin kunyar mune shiyasa bata san mu riqa mata maganar Ra'uf din"
Nasiba tayi maganar tana karasa zama a bakin gado dan duk tanajin mai suke cewa dan ta shiga bandakine sanda suka fara maganar"
"Allah ya kyauta min jin kunyarku ai indai naji kunyarku gaskiya na fado"
"Eh lallai fa munyarda,kuma indai ba kunyar bace mai zaisa kice abar maganarsa"
Inji Nasiba
"Saboda kuna sawa zuciyata da kunnuwana da idanuna son ganinsa dan jin muryarsa da sauraron sakon da zai isar ga zuciyata"
Rufaida tayi maganar kamar ba ita tayiba Dan tagaji da maganar Ra'uf da suke mata dukda yadda xuciyarta ta aminta dashi lokaci guda da har mamakin kanta take dukda cewa kuwa tun ranar data taba sasa a idanunta take yabon halayar saurayin a ranta dan ko alamun fushi bata gani ba a fuskarsa ba tadai kawar da mamakin son da take masa da ya shige ta farat daya Dan babu mamaki da ikon Allah,dariyarsu ce ta maidota daga tunanin da take"
Dariya maganar tata da tayi ta basu kuma sunga tayi shiru kamar ba ita ta yi maganar ba,nan suka hada baki gurin cewa
"Allah ko yayi masoya"
"Nasiba ta furta
" ni kunga bari nayi sallar walhar nan nayi alwala na zauna fira"
",dadai yafi miki da kin zauna in kunji kunji"
Rufaida ta karasa maganar tana kokarin barin dakin
*"**"**********
Abba Aliyu yayi murmushi bayan ya cire wayarsa daga kunnensa ya maida kallonsa ga Ummi Hauwa'u da Abdul-Rafi da suke saurarensa suji mai zaice musu dan sunsan dai da ganin murmushin fuskarsa akwai magana mai dadi a bakinsa
"Hauwa'u kinsan dawa na gama waya,Alhaji Hashim ne yanzu ya kirani ne akan cewa wani abokin Mijin Samiha ya ga Rufaida wajen bikin yace yana sonta to yanzu dai Abba Hashim din yace ya ari bakina ya cumin albasa gurin amincewa yaron fara zuwa zance,su dan fara fahimtar juna kafin ya turo magana
Abdul-Rafi ne ya soma magana dalilin da ya sa Ummi Hauwa'u ta maida maganar da take kokarin yi sai dai murmushin farin cikin dake kan fuskarta sai kuma taji Abdul-Rafi 'din yayi wata magana
"Allah yasa nagari ne" fadin Abdul-Rafi da tunda aka fara maganar yaji ransa yafara baci da baisan dalilin fadin hakan ba"
"Wacce irin magana kake ne wai Abdul" Ummi Hauwa'u tayi maganar tana kallonsa
"Ummi addu'a nayi mata fa"
Injishi yana kokarin mikewa danko maganar ma saiyaji duk ta gundiresa
Abba Aliyu yasa baki a lokacin yana fadin
"Saboda haka ake addu'ar dama ko,kai wai maiyasa bakada wani tunani kafin kafurta abu kamar wani karamin yaro,duk fadan da akema bakaji"
"Abba kaya hakuri bada wata manufa nayi maganar ba"yana maganar yana karasawa wajen dining
" ai dama haka zakace sakarai kawai"
Ummi tayi maganar cikin bacin rai
"Abdul yana kokarin zama a kujera yaji furucin Ummi Hauwa'u yaji le'ben kasa matukar haushi kalmar Sakaran da ummin nasu takirashi dashi yaji
" Haba Hauwa me ye haka ya zaki ce masa sakarai yanzu da a gaban kannensa kika fadamasa ai rainasa zasu yi"
Abba Aliyu ya fadi haka.
"Allah Abban Abdul yaron ne baida tunani wani lokacin ko daya sai shegiyar wauta ya iya"
"To naji dukda haka kidaina cewa yaran nan haka mu riqa musu addu'a"
Da haka suka canza babin firarsu ko maganar Rufaidan busu sake bi takan taba

11AM
Ra'uf ya fito falo cikin shigarsa ta shaida Ash ruwan toka Hajiya ta dubesa da take zaune a falon itada Yakumbo da Mama da sauran yan biki da busu gama tafiya ba
"Kai mai kake nufi ne wai,badai tafiyar zakaiba,wa zaka tarar a gidan idan kaje ca nake ita kanta Hannatun sai zuwa gobe zasu koma"
"Mama tasa baki a maganar
"Keko Hajiya Hanne banda abinki saurayi kamar Ra'uf kya tanbayesa ina zashi,gida bakowa idan yaje,kika sani ko amarya muka samu a kano zashi gurinta"
Murmushi yayi yace
"Kamar ko kin sani Mama,na samo muku amarya tunda ku kun tsufa"
"Hajiya Hanne ta ha'de rai ta kallesu gami da furta
" wanne irin amarya bayan ga Karima nan ban fadama maganar ta ba tun kwanaki"
"Eh kin fadamin amma nasamu Karima da maganar tace tanada wanda takeso"
"Kodai kai ka fadamata kanada wadda kakeso ba"
"Haba Hajiya ku daina gardamar nan kibar kowa da zabinsa mana, mudaiyi musu addu'a Allah yasa Alkhairi a zabin nasu"wata saga ciki tayi maganar mai suna Habi
Shikenan Habi wallahi donke kikai maganar nan ne amma kinsan cewa Karimah bazata furta wa Ra'uf tanada wanda takeso ba,sai dai idan shi ya fadamata yanada wanda yakeso dan dama shiba dan mutunci bane uwarsa tagama lalatasa shi kuma ubansa an mallakesa,bare ya tabuka wani abun"
Ra'uf ganin bazai iya jure kalaman kakartasa ba yasashi barin falon dan indai ya cigaba da sauraron kalamanta to zai iya fadamata duk maganar da tazo bakinsa,Yakumbo da Mama suma baya suka rufowa jikan nasu da sunaji Hajiya Hanne nace musu munafukai jika dai natane ko mace tace natane to tafi iko dashi bare ma kuma harda su karere wato Mama Suwaiba murmushi sukayi da fitowarsu harabar gidan har Ra'uf ya karasa wajen da motarsu take ajiye dan da saurinsa ya fito falon Mama Suwaiba ce ta kirasa da sunan da ita dince kadai take kiransa da sunan wato Babban mutum,dan sunan babban danta garesa danko da wasu sun fadamasa to gurinta sukaji tana fadamasa suka kwakkwaya ,gurin da suke tsaye ya koma hakuri suka shiga basa akan halin Hajiya Hanne shima hakuri ya basu dan yasan sums suna matukar hakuri da ita fiye dashi namiji tunda shi koda yana kadunan ba zama yake ba a gidan idan sunzo shida Amminsa bare kuma yanzu da basa ma kasar dan Hajiya Hanne wata macace mai wuyar sha'ani halinta kwata kwata babu wani wanda za'a yaba gata da zafin kishi da son zuciya da sonkai da take gaskiya da haka sukayi sallama suka rabu cikin tunanukan rayuwa kala kala haka Mukhtar yaja motar suka bar gidan zuwa Bayajidda street gidan Ahmad suna zuwa daga kofar gidan yacewa Mukhtar ya tsaya anan,wayar Nasiba ya kira yace su fito ba jimawa suka fito harda Samiha da Ahmad inda Ahmad ke masa tsiyar yaki shigowa ciki,ko kulasa baiba shima jin hakan yasan ran mazane ya baci,da haka suka shiga motar Mukhtar ya fito yasa musu kayansu a boot ya hau yana kokarin tada motar Ra'uf yace sai sunyi waya shima a lokacin Ahmad kai ya 'daga Ra'uf ya murmusa dan ya fahimci Ahmad haushi yaji addu'a Samiha take musu da idonta ya cicciko da kwalla da Rufaida gudun kar a banbareta jikin Samiha suna kuka yasata riga kowa shiga motar tanajin sheshshekar Samiha itama ta fashe da kuka a motar a haka suka bar kofar gidan da Ra'uf ya juyo ya kalleta kallo daya ya maida kansa da kukannata baya sansa ko alamu saidai a gaban su Aunty Samira baya tunanin ya iya lallashinta saboda yanada yakinin suma zasu bata hakuri haka ko akayi su Aunty Samina ke kokarin bata hakuri da suma sunsan shaquwar Samiha da Rufaida ranar da daya zai rabu da daya Dole suyi kuka.

*LIMATU KHALILULLAH*❤️💞*JININMU 'DAYA*
BY SADIYA IBRAHIM KHALIL
Wattpad:Sadiya Ibrahim Khalil

*PAGE 25*

DAN ALLAH KUYI HAKURI KUYI MANAGE BA YAWA MORE COMMENT'S MORE TYPING


3pm suka sauka a Kano kai tsaye gidan Aunty Samina suka ajesu da take a Sharada phase 1 da sai sun huta kowacce zata tafi gida Ra'uf yace wa Rufaida su jira zaizo ya kaisu gida badan taso ba ta amince Ba jimawa da shigarsu gidan Ra'uf ya turo Mukhtar gidan Aunty Samina da lemuka da yoghurt dasu Ice cream Nasiba ce ta fito ta amsa tayi godiya ta koma ciki.

Aunty Samina ta dubi himin kayan
"Kai wannan hidima haka baya gajiya shidai kiduba Alkhairin da yayiwa su Yaya balki kuma da siyayyar da yayiwa su Khalil (wato tana nufin 'ya'yansu Khalil,Kalim)"
"Wallahi kuwa Allah yasa dai yasa ya dore har aurensu ya kuma sa ya kasance mijin nata indan shine mafi alkhairi a gareta amma gaskiya naga alamun yanada kirki"
Cewar Aunty Samira
Aunty Samina ta amshe da "Amin dai"
Itako Nasiba harta bude tafara shan ice cream dan yunwa take ji gashi taga Aunty Saminan batada niyyar cewa su dora girki itako Rufaida Kitchen ta Shiga ta dora girki don gidan Aunty Samina Ba bakonta bane Iran suka zo da Samiha bata musu iyaka da komai dan sun maida Rufaida kamar Samiha su,kuma aranta bata tunanin zata iya cin kayan dan gaskiya yunwa takeji bazasu kosar da ita ba tadaifi gane ko zata cisu sai dai da marmari

5pm Suka shirya suka fito gidan Aunty Samina ita da Aunty Samira da Nasiba da Ra'uf ya turo Mukhtar Driver ya kaisu gida,kasancewar mijin Aunty Samira baya gari a lokacin shine dalilin shiga motar ya ajeta a gidanta da take rijiyar zakin itama da sai ka fara zuwa gidansu Rufaida kafin nata
******
"Oyo oyo Yaya Rufaida munyi kewarki"
Su Rafi'a suka cacimeta suna fa'dar haka
"Nima nayi kewarku,gashi ba nida waya bare mu riqa gaisawa"
"Dama dole kiyi kewarsu gashinan harkuna angijemin dana ba"
Ummi Hauwa'u ta karasa maganar tana karasowa gurin da Ra'is yake yana kuka da yake can gefe da shima hardashi a rugowa tarar yayartasu da akayi gefe dashi
Daukarsa tayi ta'aje jakar hannunta tana"Ummi yi hakuri kinsan halin dai su Rumaisa da Rafi'a"tayi maganar tana shiga cikin falon da ta zauna kujera
"Kodai halinki ba"Ummi Hauwa'u tayi maganar itama ta nemi guri cikin kujerun falon ta zauna
Murmushi Rufaida tayi kawai ta gaisheda Ummintasu da Abbansu da shigowarsa gida kenan,Rumaisa kuma ta kinkimi jakar Rufaida tayi Upstairs(saman bene)da ita
Da murmushi Abba Aliyu ya dubeta bayan sun amsa gaisuwartata
"Wato saida kuka huta gidan Samina kukayo hanyar gida ko saida Umminku tagama girkin tarbarki kika zarce gidan Auntynku"
Dariya tayi "ni bangama Yaya Abdul 'din ba" d shine ya kira Nasiba sanda suka dawo har suke shaidamasa suna gidan Aunty Samina,
"Eh yanzu suka fita shida Abdul-Rashid Umminku ta aikesu,da naji yana zasu biya daukokuma keda Nasiba"
Sallamarsu Abdul ita ta katse maganar da Ummi ke kokarin yi
Amsa musu suka yi ya shigo falon
Abdul ya dubi Rufaida da take masa sannu da zuwa yana fa'din
"Yar rainin wayau bazan amsa miki ba,banda rainin wayau kinsan tahowa zakuyi kika samu wahala kukace zaku jira nazo daukarku saida muka je Aunty Samina tace drivern daya kawoku yadawo kaiku gida"
"Yi hakuri Yaya Abdul mun kikkiraka mu fadama bata shigaba"
Abdul yace dama mana haka zakice waye yakawoku gidan ne,Aunty Samina tana fadamin ko driven Ra'uf ko waye bandaiji sosaiba"
Rufaida tace"Eh drivern gidansu Ahmad ne mijin Samiha"
Shiru suka yi nawani lokaci
Ummi Hauwa'u ta katse shirun da cewa nasan dai kuncika cikinku gidan Samina bakya bukatar abinci yanzu"
Murmushi tayi tace" Wallahi Ummi a cike cikina yake,maikika girkamin"
Ummi Hauwa'u tace"Alala"
"Allah Ummi zanci zubomin ko dayane"
Harararta Ummi Hauwa'u tayi
"ni zan zubomiki ma lallai yarinya,nida ko tsaraba baki kawowa 'dana bama"
"Rufaida tace" Ummi kinsan banida kudi,yanzu Aunty Samira data siyawa Kalim chocolate a flyover ta bani nakawowa Ra'is tana jaka ta"
Abba Aliyu yacewa Abdul-Rafi
Kaga Abdul taho mu hau sama naga an manta damu uwa da 'ya sai fira suke ba'asamu ciki"
Rufaida tace
"Yi hakuri Abba bahaka bane"
"Kinga kyalesu Rufaida,muje dining kici abincinki"
Cewar Ummi Hauwa'u
Abdul dai baice komaiba dan har lokacin Ummi Hauwa'u bata daina fushi da shiba kan maganar da yayi akan saurayin Rufaidan,wanda shikuma a ganinsa addu'a yayi ma yar uwartasa"
Maganar Abba Aliyu ita ta katse tunanin Abdul
"Shikenan gwara ku tashi kubarmu muyi firarmu muma"
Dining Area su Ummi Hauwa'u suka koma Rufaida ta zuba alalan tafaraci suna taba firar da Ummintasu

SADIYA KHALIL*JININMU 'DAYA*
NA SADIYA IBRAHIM KHALIL
Wattpad :Sadiya Ibrahim Khalil
26
*WANNAN SHAFIN NAKI NE AISHA UMAR IBRAHIM(AUI) ALLAH YABADA SA'A YA KARA BASIRA A'I..MARUBUCIYAR ZANJIRATA ,DA NABARWA ZUCIYATA ALLAH YA BAR ZUMUNCI*

*Shafi na Ashirin da shidda 26*

Sallamar da Rufaida taji Ummi Hauwa'u tayi yasa ta aje Alqur'anin da take Karantawa kan sallayar data idar da sallar isha tayi hanzarin amsa mata ciki ummi Hauwa'u takarasa shigowa ta dubi Rufaida cikin kulawa tace
"Tilawa kike ne"tayi karasa maganar tana zama bakin gado"
"Eh Ummi"
"To Allah ya taimaka su Rumaisa sunyi sallah ko nagansu sun sauka kasa suna kallo"
"Eh Ummi sunyi tarema mukayi"
"To shikenan kizo Abbanku yana kiranki Ummi Hauwa'u takarasa maganar tana mikewa
Rufaida Alqur'an din ta dauke tasa cikin loka tabi bayan Ummin nasu

*****
Assalamu Alaikum Rufaida ta gabatar da sallamar a kofar dakin mahaifinsu saida ta jira aka amsa ta tashiga cikin dakin a zaune ta samu Ummi Hauwa'u saman Carpet da shigar ta kenan itama kusada mahaifiyar tata ta zauna tana cewa "Abba Sannu da hutawa"
Ya amsa
"Yawwa Rufaida"
Kafin yayi gyaran murya ya soma magana
"Rufaida Alhaji Hashim ya kirani yayimin maganar wani yaro kun hadu wajen bikin Samiha ya nuna yana sanki shine ya kira Alhaji Hashim ya nemar masa izinin fara zuwa fira wajenki,kuma yace daga gobe zai fara zuwa,ina fatan dai da izininki yayi maganar kuma kinasanshi kar azo yafara zuwa zance yayi karfi azo asamu Matsala dukda cewar ba a fatanta"
Murmushi tayi bata ce komaiba dan ita bata San mai zatace ba ga dokin San ganin Ra'uf da take don akwana dayan harta fara sabawa dashi saboda ya iya kalamai masu tausasa zuciya
Jin tayi shiru yasa Ummi Hauwa'u cewa
"Ai Abban Abdul ta amince tunda kaji tayi shiru"
Abba Aliyu ya girgiza kai
"A'a ki barta dai tayi magana shiru aiba amincewa kadai yake nufi ba akwai shirun da zakayi ba son abinda aka fadama kawai kake nufi ba,ki bata wayarki ta turomin message idan takoma dakinsu"
Ummi Hauwa'u tace"to amma wayar na gurin Rumaisa tana game"
"Na hanaki bawa yaran nan waya bakyaji ko wacce irin game ace har Rumaisa sai anbata....da wannan fadan da Abbansu yakewa mahaifiyarsu tabar dakin.
Kai tsaye kasa ta sauka ta amsa wayar gurin Rumaisa da yaya Abdul ke musu karatun hadisi amma Rumaisan hankalinta nakan waya saida ta mangareta ta amsa wayar danma bataso ta hadata da yaya Abdul din zama tayi nan ta turawa Abba Aliyu text ta amince anan ta cigaba da zama anan karatun da ita a zuciyarta tanajin sha'awar rayuwar gidansu dukda mahaifiyarsu ita kadai gurin iyayenta baisa sun lalatamata tarbiya ba sunbata tarbiya da suma yanzu Ummintasu ce jagaba gurin basu saida

Abba Aliyu da yakaranta text message din ya kalli Ummi Hauwa'u data fito bandakin da taje hadawa Abba Aliyu ruwan wanka yace
" kinga message (sakon)Rufaida tace ta amince"
Itama murmushi tayi tace
"Dama nasan da saninta tayi maganar munyi waya da Zainab a jiya da safe tace saurayin Rufaidan sun gaisa da yaxo daukarsu jiya da suka kwana gidanta"
"Eh dukda hakan kinsan dai zuciya Hauwah zata iya sauyamata tunani mudai yanzu fatanmu Allah ya tabbatar musu da Alkhairi ya kawar da dukkan sharruka"
"Amin ya Allah"cewar Ummi Hauwa'u

Jin karar wayar Ummin nasu yasa su gaba dayansu maida dubensu ga wayar da take kusada Rufaida ganin me kiran Yaya Abdul-Ahad be yasata rigasu dauka Yaya Abdul ya dubeta yace mata
Wai waye ne mai kiran"
Tace masa
"Yaya Ahad ne"
Ko kallan wayar bai sake yi ba ya cigaba da abinda take
Da haka ta daga wayar da Sallamarta shima daya bangaren Ahad jin muryar Rufaida a wayar yasashi amsamata sallamar da murmushi kamar tana ganinsa ta dora da gaishesa ya amsa ya dora da cewa Rufaida 'yan Candy kunyi Candy bamuzo walima ba bai karasa maganar ba Rufaida taji muryar Hajiya Jamila har kunnenta kasancewar yana zaune cikin 'yan uwansa a babban falo suna fira kamar ko yaushe
" Cikin fada Hajiya Jamila tace masa
"Ahad tanbayar Candy zakayi ko cewa tabawa Hauwa'u wayar kayimata maganar zuwanku gobe, kar a sake kwatanta waccen zuwan fa"
Ahad aje wayar yayi saurin yi Wanda atunaninsa ya katse kiran ya aje yace"Umma ki bari mana anajinki fa"
Hajiya Jamila tace "ni rufemin baki sakarai ajini mana karyanayi inba tsabar iskanci tasan da zuwanku tasakai tabar gidan itada mijinta,ni mutane naban mamaki da sun samu wata dama saisu fara manta Alkhairi duk abinda mahaifinku yayi musu sun manta shi"
Murmushi Rufaida tayi mai ciwo ta kuma kasa cire wayar a kunnents ita ta rasa menene laifinsu me suka aikatawa dangin su suke musu horon aibanta Umminsu tuni batun yau ba bayan itama mahaifiyar tasu 'yar dangi ce ita iya saninta Gwaggo kakarsu data haifi Ummnsu zaune take da kowa lafiya hakama Ummintasu amma haryau takasa fahimtar maiyasa ake cin fuskarsu ake aibatasu ake waresu kowa musamman cin fuskar da zarafin da akewa mahaifiyarsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login