Showing 51001 words to 54000 words out of 86533 words
Ummansa ke musu yasa take alakanta su da munanan zantuka,gaskiya bayaji a ransa zaibi maganar mahaifiyarsa ,saboda nufin Alkhairi ya keson yi,toma idan bai aureta ba Rukayya da takeso ya aura shifa basanta yake ba da aure,batayi masa ba a irin matan da yakeson aura,bata da kunya ga raina mutane to ma shi mai zai kaisa yayi sure a dangin mahaifiyarsa da duk halayyoyinsu daya yawancinsu musamman ma Aunty Sha'awa mahaifiyar Rukayya da ta takasu rashin mutuncin,yana sane da kallon wulakancin da Aunty Sha'awa keyi musu idan sukaje Nasarawa Ummansu tace suje gidanta kasancewar mai kudi take aure ,wanda saida mahaifinsu yayi kudi ta dawo tana kaunarsu,shine yanzu akeso a makala masa Rukayya saboda sunga shima ya dago da arzikinsa,dukda Ummansu batasan wulakancin da Aunty Sha"awa ta riqa musu ba idan sunje gidanta saboda basa fadamata amma su suna sane busu manta ba ,da wannan tunanin ya kwanta ba tare da ya kira Rufaida ba da ya fadamata zai kirata idan ya koma gidan da yana dawowa Umman tasu ta shigo ta tare sa da wannan maganganun.
KANO
Abba Aliyu da ya fada'da fara'arsa da shigowarsa cikin falon ya tarar da iyalansa guri guda zaune suna fira shima fasa fitar da ya fito da niyyar yi yana kokarin zama
"Abba sannu da fitowa" yaran suka hada baki gurin fadar hakan.
Da yawwa ya amsa ya zauna kujera yana sauraron firarrakin nasu da kusan duk na yayarsu ne da sai yanzu ya tuna bai fadamusu bikin ta saura sati uku ba da shima jiya Abba Bukar ya kira yake shaida masa dukda baiji dadin abinda Abba Bukar yayi akan 'yar tasa ba ace babu ko shawartarsa a ce za'ayi aure asa biki sati hudu saikace bazawara dukda dai ana hakan amma bawai yanzu ba saboda idan ya shirya shi Uban 'dan to shi bai shirya ba,ga dadin bacin rai shida 'yarsa ba'atashi fadamasa bikin ba sai saura sati uku,saidai inda hankalinsa ya kwanta Abba Bukar din yace shi zai mata komai,shine zuciyarsa ta daina ganin laifin Abba Bukar din,sai dai yanzu zulluminsa guda yadda Hauwa'u zata dauki lamarin da har yau zullumin sanarmata bikin yake,dukda yasan bata kyauta musu ba amma yanzu yana ganin sunfita rashin kyautawa koda ita Rufaida 'yar rikoce gare ta abinda sukayi busu kyauta ba asa ranar 'yarta ba'anemi shawarar ta ba aka zartar da hukunci,sallamar Ummi Hauwa'u ta maidosa daga wancen tunanin nasa,amsa mata sukayi shida yaran suna yi mata sannu da zuwa Rafi'a ta fado jikinta tana yi mata oyoyo
Sauran yaran suna dariya suna cewa
"Kamar Ummin ta shekara a wani gurin"
Hauwa ta hararesu ta riqe hannun Rafi'a suka karaso cikin falon
"Ai tafi ku sona ne kuda ko murna bangani kan fuskarku ba"
Rumaisa tace
"Wallahi Ummi munfi sonki kinga yadda mukai kewarki tanbayi Abba kiji hirarki data Yaya kawai muke tunda kika fita ya jikin Ra'is din namu"
Ummi Hauwa'u ta murmusa tana zaunakujerar da mijin nata ke kai sannan tace yana gurin yayanku yaji sauki"
"To Allah ya kara sauki" cewar AbdulRashid.
"Amin ya rabb
Kallonta ta maida ga Abba Aliyu ta dan dubesa ganin fuskarsa babu walwala ba kamar yadda suka barsa ba,gashi bayasa baki a firar tasu.
"Abban Abdul anya lafiyarka kalau kuwa"
Sai da yaji muryarta sannan ya fahimci ashe harta zauna kusa da shi baisani ba yanacan yana tunani murmushi ya ka kalo
"Me kika gani,bayan nine na fara yi miki sannu da zuwa,ina Ra'is din ya jikin nasa"
"Hmm,akwai abinda ke damunka nake tunani gashi baka walwala,yana hannun Abdul yanzu zasu shigo a rubuto masa magunguna ,anyi masa allurai,sai dai kudin daka bayar busu isa an siyosu duka ba,ni kuma babu kudi a gu...
Bata karasa maganar ba sallamar su Abdul ta katse ta da ya shigo,sabe da Ra'is a kafada da Ra'is din ke shan alawa,daya hannunsa kuma rike da ledar maganin,sallamar suka amsa masa dukansu,kannensa suka masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera ya sauke Ra'is shima kan kujerar yaran suna yima Ra'is ya jiki
Abba Aliyu yayi gyaran murya ,ya kalli Hauwa'u yanasan sanar musu lokacin ranar Rufaida da Abba Bukar yasa,dan boyewar batada anfani tunda Allah ya gani ba shida laifi shi,magana ya soma
"Jiya da nayi waya da Yaya Bukar ya shaidamin sun saka ranar Rufaida wancen satin yau saura sati uku nan gaba"
Abdul da yaji maganar kamar dirar aradu
"What Abba mai kake fada Rufaidan za'ayiwa wannan auran biki wata guda kamar wata bazawara aiko masu kudi da suke tada kai dasu basa irin wannan auran sai....
Abba cikin bacin rai ya soma magana bai bari Abdul ya gama tasa maganar ba don batun yau ba ya fahimci Abdul wata rashim kunya yake ji dashi ma yi masan zaiyi.
" Sai Ubanka kome zaka ce ,dan uwarka yarinyar ta samu miji yana santa sai aki aura mata shi,so kake atasa ta a dunga kallo,kota dinga yi mana jajibe jajiben samari wawaye da busu san darajar dan adam ba"
Ummi Hauwa'u da take jin maganarsu saidai ta kasa tsaidasu saboda yadda ita ma ranta yake bace a wannan lokacin,ita da 'yarta a dauke mata ita kan kuskuren da ita bata ma gansa ba,dan zuwa yanzu ta fara gajiya da halin Aliyu komai za'ayi baza'a shawarce taba saboda son kai irin nasa
Abdul ya dan sassauta murya ganin mahaifin nasa kalaman da yayi masa sun bata ransa har yana zaginsa da kafin kaji Abban nasu yayi zagi to tabbbas zaka dade
"Amma Abba ai karatu zata cigaba dayi da mun kyaleta,aure lokaci ne ai koda ma ba karatun zatayi ba, mu ba zamu gaji da ganinta ba dadai auran Yaya Wahid da zatayi gwara ta shekara goma ba aure, kota auri wancen saurayin nata dukda ba'a sansa nake ba,haba Abba maiyasa kake kokarin manta kiyayyyar da Umma Jamila ke gwada ma..."
Cikin zafin nama Ummi Hauwa'u ta taso daga Inda take ta rufe bakin Abdul ta wankesa da mari,dan idan tabarsa dukda ita ma ranta a bace yake da Abba Aliyu amma tasan Abba Aliyu uba yake ga Abdul bazata bari ya cigaba da sa'insa da Ubansa ba,dan bats yimasa irin wannan tarbiyyarba ita bata tana sa'insa da Abbansu a gabansa ba,dan yau kenan ka haifesa ne amma baka haifi halinsa ba,gashi a gaban kannensa,hannunsa taja da karfi zuwa upstairs tana magana cikin fada
"Abdul baka da hankali mahaifinnaka kake fadawa haka,kamanta duk karkashinsa muke yanada ikon zartar da hukunci akanmu...."
Da wannan maganar suka karasa hayewa Upstairs din da Abba Aliyu ya bisu da kallo da ransa ke masa tukuki yanzu ace Abdul shike fadamasa bakaken maganganu har haka gaban sauran kannensa dukda yasan ya musu laifi amma dai abinda Abdul yayi masa ya bata ransa matsayin Abdul na dan cikinsa koshi sa'ansa ne sai haka ,baya tunanin Hauwa'u tanada laifi wajen lalacewar yaran da yake nema yayi yanzu,saidai zai yiwa tufkar hanci,kofa yayiya mike ya duba magunan Ra'is da suke leda ya dauki kati yaje ya ciko masa ragowar magunan da aka rubuta masa
Yaran da babu wanda ya shiga maganar da tsoro fal ransu ,dansu basu taba cin karo da wannan matsalar ba bare su saba da ita tunda suka taso a gidansu ba akwai girmama juna atsakaninsu amma lokaci guda gashi ana musayar magana tsakanin Abbansu da Yayansu busu san meke shirin faruwa da suba Ra'is da kowa yaki kulasa kuma yaji hayaniya da baisa ba da jiba ya rushe da kuka Rumaisa ta daukesa tahau lallashi dan ko kusa bata yi gigin kaisa gurin Umminsu ba dan a yadda taga bacin rai a ranta ta iya dukanta ma"
Team of Rufaida ,team of AbdulWahid,team of AbdulRa'uf
Team of Ra'uf
Anya ba za'a yiwa AbdulRa'uf sakiyar da ba ruwa ba koda yake dama dai anmasa saidai ya rungumi sorry
Team of Wahid
Ya kuke tunanin zata kasance idan Hajiya Jamila taji labarin.wannan bikin anya zata yarda kuwa?kai akwaifa gwarama a gaba nake tunani. Nidai na fece bani na fada ba😂😂🚶🏽♀️🚶🏽♀️🚶🏽♀️🚶🏽♀️
A suburbudo ruwan comments aga typing nagama sa ayau😂😂 basai gobe baFJininmu 'daya
By Sadiya Khalil
Page 39
"ZARIYA"
"Wasila mikomin wayata naga tana kara an kirani"
Hajiya Jamila tayi maganar da suke zaune da sauran matan gidan a babban falo suna fira wasila da itace ta rage a gidan bata zuwa makaranta ta dauki wayar tana game
Wasilar ta danne wayar silent
"Umma bafa kira a kaiba sakone ke shigowa"
Aunty Amarya da take kusa da Wasila ta le'ka wayar
"Kai Wasila kema kin iya karya ko ga kirannan yana shigowa kin danne wayar a silent"
"Hajiya Jamila jin maganar Aunty Amarya yasata mikewa ta anso wayarta da har wani kiran ya shigo wancen ya katse,tsaki tayi ganin mai kiran Gwaggo Lariya ce kanwar surikarsu ,tasan tunda taga kiranta roko zatayi saida takoma ta zauna ta daga wayar da sallamarta saida suka gaisa Gwaggo Lariyar da labari ke cinta ta fara da cewa
" Gaskiya Jamila kin bani mamaki duk aminci na dake ace za'akai kayan lefen AbdulWahid saidai naji labari gurin Bukar"
Tsaki Hajiya Jamila tayi ka'dan ba tareda Lariyar ta jiba,ita to ta ina zata zama kawar Gwaggo Lariya bare suyi aminci bayan kanwar surikinsu ce itace Autar a gidan su surukin nasu ,shiyasa bata Gwaggo Lariyar bata girmeta ba,kuma Gwaggo lariyar takeso suyi aminci,saidai ita taki jinin mutum mai shishshigin da karya,da son abin hannun mutane, da Gwaggo Lariya dukta kware ta wannan fannin shiyasa yanzu ta kasa gasgata maganar Gwaggo lariyar ta dai daure tace
"Wacce irin magana kike ne,wanne irin laife kuma ni bansan wannan zancen ba"
Da mamaki sosai jin maganar da Hajiya Jamila tayi Gwaggo Lariya ta cigaba
"Kamar ya kina nufin ba kisan auren da Wahid zaiyi ba zai auri Rufaida ta wajen Aliyu"
Cikin firgici Hajiya Jamila ta ce
"Haba Gwaggo Lariya wacce irin magana ki kene"
"Abinda kika ji nace,Wahid zai auri Rufaida yauma su Hauwa'u zasu taho zariya gurin biki nufinki basu fadamiki ba..."
Ba tare da Hajiya Jamila takarasa jin zantukan Gwaggo Lariya ba ta kashe wayar ta mike zunbir
Mai yafaru ne Maman AbdulMalik ,lefen wa za'a kai"
Aunty Amarya tayi maganar cikin rashin sani ,dan itama ko kadan batada masaniya da saka ranar bikin"
Wani kallo Hajiya Jamila tayi mata da haka ta shige daki ta dauko hijabi da dan makullin motarta ta dawo falon tana kokarin fita Hajiya Kubra tayi kokarin riketa
"Haba Hajiya Jamila komai yayi zafi maganinsa Allah,mai Gwaggo Lariyar tace miki ko mutuwa akayi ne, ki fadamana"
Fisge hannun Hajiya Kubra ,Hajiya Jamila tayi daga rikon da ta mata cikin zafin zuciya ta fara magana
"Munafuka cikani,kunje an hada baki daku an munafurceni, wallahi yau sai na kashe waccen yarinyar da take kokarin shiga rayuwar dana,saidai nima yau akasheni ,dan dana hada zuriya dasu gwara na hada da kare"
Tana kaiwa nan ta fice daga falon gurin motarta ta karasa ta mata key ta bata wuta tavar gidan da wani irin gudu
Cikin sanyi jiki Hajiya Kubra ta dawo cikin falon Aunty Amarya ta kalleta bayan ta zauna ta soma magana
"Niko Maman Hussaini mu kira Gwaggo Lariyar muji maike faruwa,sai mukira Abban Wahid mu fadamasa,dan a yadda Maman Abdulmalik ta fita kinsan komai zai iya faruwa"
"Eh hakane kinyi tunani nima zullimin da nike kenan ,tunda gashi har tana kiranmu da munafukai"
Hajiya Kubra ta karasa maganar tana daukar wayarta ta lalubi numbar Gwaggo lariya
Wadda Gwaggo Lariyar tana can cikin zullumi dan sai yanzu tayi danasanin katobarar da tayi na fadawa Hajiya Jamilar dan tana tsoron hukuncin da zata dauka kan wannan maganar,tana wannan tunanin haka taji karar wayarta ta bugu daya ta dauka ta kara kunnenta,
Hajiya Kubra ta maida wayar a handsfree jin ta saga
Magana Gwaggo Lariyar ta fara
"Assalamu Alaikum ,Kubra lafiya kuwa,ina Jamilar ,muna waya naji ta katse ,dama batun auren Wahid fa Rufaida muke da za'akai lefe yau...."
Hajiya Kubra da bata bari Gwaggo Lariyar ta gama maganar ba tayi hantsarin katse wayar ta sake danna lambar Abba Bukar a kidime tana gudun mai zaije yazo,dan tana da yakinin gidan Gwaggo Zainabu Hajiya Kubra ta nufa
shima ringing daya ya dauka da sallamarsa
Ba ta jira sallamarsa ba tace masa
"Abban Wahid yanzu Gwaggo zainabu ta kiramu,tace ka aje duk abinda kake kaje tana san ganinka" da haka ta katse kiran dan bataso ta fadamasa gaskiyar lamarin saboda gudun kada hankalinsa ya tashi,lamarin suke tattaunawa akai bayan gama wayar tasu dan ko ita Hajiya Kubra ba tasan maike faruwa ba itada take 'yar uwarsa ,a ranta tana fadin amma Gwaggo Lariyar bata kyauta ba ,a matsayinta na kanwar mahaifiyarta shiyasa bata fito ta fadawa Aunty Amaryar ba don kowacce matsayinta daban ne agurinta
Tunanin kiran Gwaggo yake da yaga ita bata kirasa ba ta shaidamasa ba,kuma bata Saba yi masa kiranba ma,to mai yake faruwa ganin tunanin ba zai anfanesa ba ya sashi mikewa ya dauki makulle ya fito daga office dinsa ya rufe,massinjansa da ya tare sa,Abba bukar yace
"Ba tashi nayi ba,zanje wani guri na dawo,idan anzo ne mana kace ba nisa nayi ba su jira ni"
"To Allah ya kiyaye hanya masinjan ya fa da ya koma inda yake zaune"
"Amin kawai Abba Bukar ya iya anbata yabar wajen gurin aje motoci ya karasa ya shiga tasa ya tayar ya fito daga cikin makarantar ABU Zaria da a ciki yake aiki da tunani a ransa
****
RUFAIDA
Rufaida ta kalli himmin fulawar da Gwaggo take so ta kwaba tayin doughnut da cin-cin,da ta tasata saita kwaba zata bar gidan zuwa gidan Gwaggo Hajiya mahaifiyar Hajiya Kubra
" Gwaggo Allah na gaji ace aikin nan duk tare za muyi,maimakon ki bari su Aunty Samina su zo tunda yau zasu zo"
Rufaida ta karasa maganar tana kunbura baki
Gwaggo ta 'dago dakanta daga kwabin alkakin da take ta dubeta taga ta kunboro baki ta ta tabe baki tare da cewa
"Yarinya koda ma kuka zaki ba ba kunboro baki ba saidai kiyi,dan sai kin kwaba zaki bar gidan nan"
Rufaida ta dan lankwasa murya
"To Gwaggona naji zanyi yadda kikace amma dan Allah kiyarda na kira Harira ta tayani,muyi mugama da wuri"
Gwaggo ta zaro ido
"Wacce Harirar yarinyar da ko uwarta bata mora mata bare ke ta mora miki daga kawancen unguwa kinajin artabun da suke da Mamarsu ta katanga akan aiki,idan Mamarta tace tayi mata"
Kasancewar su Harirar makoftansu ne da suke shiri da Harirar a Unguwa itada Rufaida
"Eh dukda haka Gwaggo nasan ni zata tayani kinsan muna shiri sosai"
Rufaida tayi hanzarin cewa Gwaggo hakan dan karta kuma fadar wani abun
"To inanan dai zan jiyo ku ta katanga,dan indai Harira ce kinsan ba shiri ba kome kuke idan vatasa kanta ba saita iya watsa miki kasa a ido"
Da haka Rufaida ta mike daga tabarmar da suka shimfida a tsakar gidan ta zura takalmi ta janyo hijabinta jikin igiya tasa tana cewa
"Gwaggo saina dawo"
"To adawo lafiya'"Gwaggo tayi maganar tana maida kai ga abinda take,a ranta tana tunanin halin Rufaida batasan auren yaron kowa ya sani badan komaiba saidan halin mahaifiyarsa amma ko a fuska vazaka gane ba
A bakin kofar zaure Rufaida tayi kicibus Hajiya Jamila da take kokarin shiga ciki hartayi kokarin bangaje Rufaida Rufaida tayi saurin matsamata hanya ta kalli Hajiya Jamilar da kallon daya tayi mata taji gabanta ya fadi ganin yanayin annurin fuskarta babu shi anbaton Allah tayi kafin tayi saurin cewa
" Umma sannu da zuwa"
Hajiya Jamilar ta kalli mai mata sallamar tayi ido biyu da Rufaida da da idonta ya rufe bata san da mutum a zauren ba dan tunaninta yayi cikin gidan gaba 'daya wata irin fisga Hajiya Jamilar tayi mata zuwa cikin tsakar gidan tana cewa
"Wallahi yau sai na kashe ki,dan muddin ina raye dana bazai hada iri da kuba"
Jin maganar Hajiya Jamilar ya ankarar da Gwaggo inda a lokacin take kokarin wanke Rufaida da mari gurin Gwaggo ta karaso da niyyar kwace Rufaida Hajiya Jamilar tayi kukan kura ta angije Gwaggo tana cewa cikin 'daga murya" matsanan Munafuka angungunma ca kike yadda kika munafunci 'yan uwanki nima zaki munafunce nine,wallahi sai dai yau na kashe ta inyaso nima akashe ni dan bazan hada zuriya da wannan mazinaciyar uwarta taba ,",ta karasa maganar tana sake kwada wa Rufaida mari daga visa ni ta shake wuyan Rufaida"
Ganin haka yasa Gwaggo saka kuru ruwa tana ihu makwabta neman taimako
Lokacin yayi dai-dai da karasowar Abba Bukar kofar gidan ganin motar Hajiya Jamilar kofar gidan yasashi saurin kashe motarsa ya rufe ya isa cikin gidan harda gudunsa dan yasan,tunda yaga motar Hajiya Jamilar yasan akwai matsala
A lokacin da ya iso Gwaggo ta sake kukan kura ta nufesu tana kokarin cire hannnun Hajiya Jamilar daga wuyan Rufaida amma ta kasa Rufaidan sai zaro ido take
"Jamila wallahi idan biki saki wuyan 'yar mutane ba to wallahi a bakin aurenki"
Abba Bukar yayi maganar yana karasa shigowa ciki,da babu wanda yaji shigowarsa
Badan Hajiya Jamilar taso ba ta saketa
Ta kuma cigaba da dukanta,da alokacin makwabta sun fara shigowa jin kururuwar Gwaggon da suke,da kowacce take tsaye tana kallon ikon Allah,mai kuma Rufaidan tayi wake dukanta dan busu shaida fuskar Hajiya Jamila ba saboda ta juya bayanta
Gurin da suke Abba Bukar ya karaso ya kwace Rufaida daga hannun Hajiya Jamila da Harira da har da ita a masu shigowar tayi kokarin karasowa gurin Rufaida ta janyeta gefe
shiko Abba Bukar Hajiya Jamilar ya nufa da zafin zuciya ya kwashe fuskar da wani gigitaccen mari yayi ball da ita,ya fara dukanta yana cewa
"Ke dabba ce 'yar mutanan zaki kashe"
ganin yana kokarin cigaba da dukanta yasa Gwaggo rikesa tana basa baki
"Kan wannan 'diyar mazinaciyar ka dokeni ko,wadda danginta suka juya mata baya,to wallahi indai kukai kokarin aura mata 'dana saina kashe ta inyaso nima a kasheni"
"Da ubanki tayi zinar ko,kuma dangin ubanki ne suka juya mata bayan ko,kuma wallahi aure sai anyi shi ,kuma karki sake ki koma min gida ,na tsaneki da zama dake ,fitinanniya babu abinda auranki ya tsinanamin face asara"Abba Bukar yayi maganar cikin zafin zuciya
" Saina koma ,koda saki na zakayi saina zauna nayi zaman 'ya'yana"
Cewar Hajiya Jamila tayi maganar tana kokarin tashi tsaye
"Abba Bukar yace
" Bismillah ki koma wallahi da sai kin yi danasanin da tunda uwarki ta kawoki duniya baki taba yi ba"
Rufaida Hajiya Jamila ta nuna da Harira ke bata ruwa tace
"Kan wannan,Yarinyar da ko acikin dabbobi tafi su iya dabbaci saboda 'yar mungada ce, ka wulakantani gaban jama'a ko,bismillah Ku daura auran wallahi saikunyi danasani fiye da tunaninku" tayi maganar tana dukawa ta dauki makullin motarta ta soma tafiya
"Duk barazanarki ba zata hanani aurawa Wahid Rufaida koda ace vayasonta idan harni inasan ya aureta sai ya aureta,saboda bake kadai keda