Showing 81001 words to 84000 words out of 86533 words
Mama Amina wallahi indai ina gidan nan babu mai taba ki,ki cire tsoro kije ki tunkaresu da maganar,ke ranar girkin ki kike girka musu abincin da tarin 'ya'yansu kece suke kyashin baku abincin da bai kai ya kawo ba,haba kema said kace karamar yarinya"
Murmushi Umma tayi
"Ko 'daya Jabir ni dai banason neman rigima ne"
Nayi saurin sa baki da muke har lokacin muna jinsu
"Umma wallahi idan ba zaki yi magana ba zanje nayi"
Yaya Jabir ya kalleni yadda yaga nayi maganar ba alamu wasa hakan ya bashi dariya
"Kyaleta Hauwa'u zama tayi maganar ku je ku debo kwanuka kuje ku kai a zuba muku,idan Gwaggo Larai ta muku magana ku cemata nina ce azuba muku"
Haka akayi nice naje nakaiwa kula ta zobo mana abinci,Gwaggo Larai mai yi mana abinci,amma banda ranar girkin Ummanmu duk ranar girkin Ummanmu to ranar hutun Gwaggo Larai ne, haka ta zubo mana abinci mai rai da lafiya da aka dade da gamawa aka rurrufe a kuloli a ciki harda wanda za'a kaiwa makwabta gidajen da suke da karamin karfi a unguwar tamu
Koda na dawo Yaya Jabir yana nan sai da ya ga yawan abinci zai ishemu ya mike ya tafi
Gwaggo Larai da ina dawowa ,ta nufi bangarensu Mama Hanne ta sanar musu abinda ya faru Yaya Jabir yace a bamu abinci kuma ta zuba mana
Cikin bacin rai Mama Hanne ta nufo bangarenmu cikin bacin rai babu ko sallama ta kallemu da muke ta zuba uwar lomar abinci nida Yaya Safiya
"Da kyau tsofaffin mayu,kwayi loma mana tunda va'asa ba haduwa ba"
Umma ta doka wa Mama Hanne tsaki nayi mamakin tsakin daya fito bakin Ummantamu ganin bata saba yi wa wani tsaki maganar data fadawa Mama Hanne ta kara bani mamaki
"Kinga Hanne karki kara cewa 'ya'yana mayu don babu batun maita don sunci abincin gidan ubansu"
Mama Hanne da ita ma nasan tayi mamakin maganar Ummantamu ganin bata saba ba
"Idan na sake fada musu mai zai faru?"
"Zamu kwashi 'yan kallo,saboda yadda kike takama mijinki ya kawo abinci da za'a girka nima miji nane kuma wadannan ta nuna mu 'ya'yansane,don haka banga dalilin kiransu mayu ba,kuma abinci daga yau barar fashin kin zuba musu a gidan nan,tunda suma 'ya'yane"ta fadi haka tana tsare Mama Hanne da ido
Mama Hanne tayi dariya
"Yayi mai miji,miji da bai damu dake ba baidamu da 'ya'yanki ba harkike tunkawon mijinki ne"
Umma ta maida mata da martani
"To ai tunda zamansa nake,kuma 'ya'yana nasane to dole na kirasa mai miji na uban 'ya'yana, kuma ni miji na ya damu dani"
"Ina damuwar take ni bangani ko a jikinki ba bare a jikin 'ya'yanki" ta karasa zancen tana nuna mu
"Ai ni ba so nake ki ganta ba"
Fadin Umma ta na cigaba da
"Kuma ki fita ki barmin bangare, tun muna mu biyu
Ganin yadda Umma ranta ya baci yasa Mama Hanne saurin ficewa don tana tsoron su kwashi 'yan kallon da Ummantamu
Tun daga wannan lokacin muka samu saken cin abincin gidanmu amma sai dai wannan abun na kwaranyewa wata rana muna zaune a falo da Ummanmu tana koya mana karatun boko dukda bawai karatun bokon tayi mai zurfi ba ajinta biyar firamare aka yi mata aure amma yadda take da kokari sai kace takai matakin gama sakandire wannan yasa kullum da mundawo islamiyya take zama ta sake koya mana daga na islamiyyar har na bokon
Baffa ne ya shigo babu ko sallama da fadansa
" yanzu Amina abinda kikai kin kyauta kenan,ace tun daga ranar da nace miki akan abinci ki kwantarwa kanki 'yanci kika daina bawa Malika abinci a gidan nan sai dai ki tasa abincin gaba ke da 'ya'yanki ku ci"
Umman ta dago dakanta da idanunta jawur
"Amma Baban Sule ya kamata da aka fadama maganar ka zauna kayi nazari ba wai ka yanke min hukunci ba,ni ca nake sanda ba'a kasa abinci dani da 'ya'yana a gidan,duk ranar girki na ban fasa zuba wa diyayoyinsu ba ko su kansu"
"Nazarin me kuma zanyi bayan nasan fiye da haka zaki iya,akan wadannan 'ya'yan naki wallahi Amina kiji tsoron Allah,saboda kinga na baki dama shine kike kokarin ki zarce ko?"
"Bangane naji tsoron Allah ba da tsoron wa nake ji,kai duk cin zalinmu nida yara na da kake ci baka gani,sai kayi wa matanka suttura biki ko suna ni baka yiwa nawa ko tsinke ba,hatta karatu ma makaranta mai arha kasa su" Umma ta maida masa wannan martanin cikin bacin rai
"Lallai Amina wuyanki ya isa yanka ki dubi tsabar idona kice dani haka wato duk kokarin da nake akan 'ya'yanki bakya gani ko,to daga yau dinki ko sallah ce nadaina yiwa 'ya'yanki,makaranta kuma ta gwamnati zan sasu banda ma........."
Bai karasa maganar ba Kawu Haladu kanin Umma yayi sallama,mu da muke ta zaro ido muna kallon yadda Umma da Baffa keta fada a gabanmu,jin sallamar Kawu Haladu yasa mu saurin tashi muka karasa bakin kofar da Kawun namu yake muka rungumeshi da fara'arsa shima ya rungume mu sannan ya ruko Hannun mu zuwa cikin falon Baffanmu da yake har lokacin tsaye a gurin Kawu Haladu yana kokarin zama a kujerun falon
"Alhaji Ina yini"
Tsaki Baffan yaja ya five fuu da daga dakin namu yana banko kofa
Baffan na fita Kawu Haladu ya dubi Umma da muke zazzaune kusa dashi
"Yaya Amina ina yini"
Umman data dawo daga tunaninta jin maganar Haladu
"Bazan amsa ba" tayi maganar tana harararsa
"Kai Yaya Amina mai kuma nayi"
"Kaima kasani ni ban daukama talakawa na ganinku ba"
"Wallahi Yaya Amina kinsan yanayin sana'ar tawa yanzu ma wani yaro na bari a gurin"
"To Allah ya taimaka"
"Amin"
Mikewa Umma tayi ta shiga ciki
A lokacin muka gaishe muka gaishe da Kawun namu ya amsa yana tanbayarmu karatun mu
Muna cikin haka ne Umma ta dawo falon da abinci a plat da ruwa a kofi ta ajiyewa Kawu Haladu
"Sannu Yaya kamar ko kinsan banci komaiba,bayan abincin safe,ke din ma ban dauka zan samu gurinki na dan yau ko buga iskar motar da keken kadan akayi,kawai nace bari na zarto nan,na kawo miki cinikin ki sayi wani dan abin bukatar,saina jiyowa inna lafiyarsu Hauwa kwana biyu,basu jeba saima na sameku lafiya"
Umma tayi murmushi
"Yanzu har yau baka samu aikin ba,duk kudin da akayita caca,ai komai ya sauya muna samun abinci harma mu bada"
Sai sannan idon Umma ya sauka kanmu mu tsira musu ido muna saurarensu
"Ku tashi ku tafi wasanku,Yanzu nayi baki saina muku fada ku tashi"
Kawu Haladu ya katseta
"Yaya Amina,don sun zauna ai basu da laifi laifunsu su saka mana baki a maganarmu amma idan yaranmu busu ji matsalarmu ba waye zai ji mana"
Mu da muke kokarin tashi muka koma muka zauna,to dama ina zamu gaba daya 'yan gidanmu bamu yawon unguwa harta yayyenmu,imu imu muke wasan mu sai dai mu din a iya bangaren Umma muke wasan mu don dukanmu suke sauran idan mun shiga cikinsu,Umma ganin mun zauna ta bimu da harara
"Ai Yaya Amina kinsan aiki sai ka mika kudi to mu ina muke dana mikawar,kudin da aka kashe a karatu basa zama caca ai shi karatu indai kayi ka anfana koda ba kayi aiki ba zai canza ma rayuwa,dama yanzun nake shirin tanbayarmiki maike faruwa ne najiyo hayaniyar ku zan shigo falon kuma naga nagaida Alhaji Mamudan bai amsa ko dai akan abincin ne"fadin Kawu yana kallon Umma
"Hmm kai bari Haladu bama batun abincin yake fadan ba,tun ranar dana nuna musu basu isa ba suka soma bamu abincin nan ta bashi labari duk abinda ya farun
ta cigaba da
" yanzu akan abincin Malika da ban zuba mata ba,bata gidan lokacin ta kwana gidan Alhaji Audu shine ban masan da dawowarta ba,ashe tadawo a dazu,to yanzu matan suka zugosa ya shigo ya fara fada"shine ka taddasa yana wannan banbanmin yace makaranta ma ta gwamnati zai maida su Nana (sunan da take yawan kiran Yaya Safiyya dashi)kan hakan"
"Amma Yaya Amina, hakuri zaki rika yi komai yayi kansa amma hayaniya da mijinki ba mafita bace"
"Haladu, batun hakuri kam kaima kasan da cewar inayi" labarin duk abinda ya faru da itada mijinnata kafin shigowar Kawu Haladun ta basa
"Kai nidai Yaya Amina bansan halin mutumin nan ba,hakuri zaki tayi wata rana sai labari insha Allah komai zai wuce,kinga da kina sana'a da koda ya canza musu makarantar saiki maidasu wata ta kudin,to matsalar babu kudin da zaki ja jari,amma ki barsa ai duk makaranta makaranta ce"
"Hakane Haladu,wallahi a kullum yaran nan nake tunani banda haka ba zan iya cigaba da zama da Mamuda ba sabida iya biyayyar aure ina gwada yi masa amshi baya gani"
"Hmm Yaya Amina kenan,ai gidan mijinki shine rufin asirinki,duk tsiya gidanki yafi zaman gidanmu,kina gani da ran Baba ma yadda muke rayuwa bare yanzu babu shi,Inna sana'ar saida abinci take idan bake ma so kike ki rika yi ba,hakuri zaki cigaba dayi wata rana sai labari amma ki cigaba da addu'a don ina zargin shiga tsakaninku akayi da mijinki,dan da farko ba haka Alhaji Mamuda yake ba"
"Haka ne Haladu,amma wa make tunani zai shiga tsakaninmu,kishiyoyi na ko suwa?,banaso ka rika tunani irin wannan Allah ne mai yin komai babu wanda zai ma wani abu ba Allah ba,mutum sanadiyya yake zamowa,ni na mika lamurana ga Allah kaima inaso ka zamo hakan"
"Hakane Yaya Amina,amma kiga yadda Alhaji Mamudan yake nuna kaunarsa gareki kafin aurenku da bayan aurenku dama shine nake tunanin ko kishiyoyinki ne suka shiga tsakaninku amma tunda kin nuna ba haka bane shikenan"
"Bawai so ne bana yi ba Haladu,kaima kanka kasan dan Adam yakan boyema halayyarsa,sai daga baya inda tafiya tayi tafiya ka fahimci halayyoyinsa da yake voyema tunani na shima Mamudan haka yayi daga farko"
"Eh hakane Yaya amma dukda haka ki cigaba da addu'a a koda yaushe karki rika sake da ita domin ita takobi ce"
"Haka ne Haladu"
Kallo na Kawu Haladu yayi da tunda suka fara maganar ido na ke kansu dukda na fahimci akan Baffa suke maganarsu kuma ina saurarensun amma bazan iya wani tunani akan maganar ta su ba,tunda shekaru na baikai nan ba, yana dariya ya dubi Ummanmu
"Yaya kinga 'yar nan taki ta tsare mu da ido kamar tana fahimtarmu"
Itama Umma dariya tayi
"Lallai Haladu baka san wayan Hauwa ba,ai sarai tasan maganar Babanta ake tayi tunani inda maganarmu ta sosa sosai ne ba zata iya ba,amma jiya har cemin tayi idan ta girma zata siyamin irin kujerun dakin Mama Hanne dana Mama Suwaiba tunda Baffansu bai siyomin ba,na ce mata ai shima bashi ya siyo musu ba,tace min bata yarda ba tasan shine gashi nan iri daya ne dana dakinshi"
Dariya Kawu Haladu yayi
"Lallai Hauwa har kin zama kece babba ashe"
Dariya nayi
Yaya Safiyya da ta kai hannunta baya na ta makan duka
Umma da take kallon Yaya Safiya sanda take duka na
"Mai tayi miki Nana"
Yaya Safiya da idonta ya cicciko da hawaye
"Umma tun dazu fa ina kallonta tana murmushi taji ana fadar laifin Baffa a gabanta,yanzu shine zata yi mana dariya"
"To sata tayi kuka kamar me tunda,an fadi laifin Baffanku,kuma aiba wani abu akace game da shiba gaskiya aka fada abinda yake ko kar a fada,mai uba"
Yaya Safiyya ta girgiza kai kawai ta tashi daga inda muke wannan yasa nima na mike ma bita don nunyi sabon da ba zan iya ganin Yaya Safiya bata guri ni kuma na zauna ba
[10/13, 8:18 PM] Sadiya Khalil Muhammad🥰: *JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil
Book 2.
6.
Bayan watanni uku
Alokacin abubuwa da dama sun faru na farin ciki da kasinsa a lokacin ne Baffa ya aurar dasu Yaya Fati da Yaya Umma wato Salamatu,a Danbatta Yaya Umma tayi aure Dan uwansu Baffa ta aura, Yaya Fati kuma anan Kaduna dan kasuwa ta aura a lokacin kuma muka koma sabon gidanmu dake sabon Kawo babban gida yana da bangare akalla uku ,amma na tsakiyar da shine babban ciki a ciki gaba daya bangaren matan Baffanmu suke mu hadu a falo ne sai gefen falon matakalar bene bangaren Baffanmu daga gefe batun ko dai rayuwarmu a gidanmu gaskiya zan iya cewa sam babu dadi musamman yanzu da muka koma rayuwarmu dasu guri daya,indai har muka fito falo mu akaran kanmu wannan yayan namu ya doke mu wannan ya zagemu mune kawai ware a cikin gidanmu muda mahaifiyarmu hatta da Danbatta idan muka tafi nanma hakane babu wani so da suke nuna mana kamar sauran a raina nakance kodan mu bamu mahaifiyarmu ba su da alaka da Baffa ne don itace bare kadai a cikin matansa,amma dai ita ma bafulatanarce daga baya saina fahimci ba haka bane kawai dai ta ko ina Mama Hanne ta batawa Ummanmu suna ne da irin wannan rayuwar muka cigaba da tafiya batun makaranta kuwa tuni an sauya mana an maidamu ta gwamnati amma hakan bai sauya kwakwalwarmu ba muna ganewa sosai da haka har Yaya Safiyya ta kammala Secondary dinta sai ni da nike zuwa ko wacce rana ta duniya,Inna Saude da Kawu Haladu kuwa kullum naje gidan kamar na tasa su na dinga kuka ne gidan da suke ciki duk ya rushe amma Sam mai hayar yaki gyarawa yace basa biyanshi kudi,duk asabar da lahadi na kanje gidan Inna Saude na taya ta mikawa masu siyan wainar da tako ma yi da safe,Umma kuwa ita ba samun wani abu take ba gurin Baffa sai dai matan so su samu,haka zaka jisu a babban falo suna ta yiwa Baffa kidayar kudi da suke so yabasu su da 'ya'yansu amma banda mu tamu mahaifiyar duk ranar da kaji suna magana ta sake tayi masa zance kudi saitayi danasani ranar cin mutunci iri iri yake yi mata saboda har lokacin bai manta son kudin da Babansu Umma ya nuna ba lokacin aurenta ba,Kuka zaka ga muntasa ta muna yi,idan munce tazo mu bar masa gidan ta kance ba muda Inda yafi nan,sai muce garinsu ai yafiye mana nan,murmurshi take yi ta kallemu tace"kuma da zaku taimaka musu so zasuyi,rayuwarsu tafi tamu tausayi,takan ce ko a kauyenmu dangin mahaifina idan munje na kallesu na kalli ragowar na kanga kamar sunfi kowa babu,ku cigaba da hakuri ko vayan bani,batun sana'a Kawu Haladu da yaje garinsu Kuka kubeya dakakkun su barkono kanwa duk ya hadowa Ummanmu ta rika siyarwa ta soma a sa'a tana ciniki amma da matansa suka fahimci haka suka fadawa Baffa yazo ya hadamu duka ya fara mana fada "Ya za'ayi bamu rasa ci da sha da suttura ba,gama yadda yake da arziki mu rasa sana'ar da Umma zata rika yi sai saida su kuka, gaba daya ya kwashe kayan da Umman ke saidawa ya zuba a store dinmu na kayan abinci.
Yau kamar kullum da shiri na na makaranta na fito babban falo da na tadda Baffanmu zaune a kujera yana kidayawa Yaya Sule da Yaya Abdu da Yaya Bello kudi na hidindimun bikinsu da za'ayi a wannan watan
Gaishe su nayi sannan na kalli Baffa
" Baffa na fito kudin tara"
Yaya Sule ya duba agogon hannunsa ya kalleni
"Yanzu karfe nawa, 8:00 sai yanzu zaki tafi makaranta saboda shashanci...."
Baffa ya dakatar da Yaya Sule
"Au yanzu Hauwa'u yau ma makarar kikeso kiyi,karfe nawa Larai ke gama muku abinci"
Nayi kasa da kaina
"Baffa karfe shida da rabi"
Baffan ya sake kallo na
"Na lura karatun ne bakyaso ko gata ne yayi miki yawa akaiki a mota a dawo dake to yau a kafa zaki tafi haka ma batun dawowa karma kice zaki jira"
Jiki babu kwari na mike banma jira kudin tara ba saboda nasan tunda Yaya Sule ya hadani da Baffanmu biyar dinsa baya bani
"Na tafi"
Nace masu aiko cikinsu ba wanda yayi min koda magana
Har na fice
****
Ina tafiya ina tunanin rayuwar tsakanin gidanmu da makarantarmu akwai nisa bakadan ba,biyar kuma ba nida ita a jaka ta Horn da naji a baya na yasa ni matsawa gefe Yaya Jabir ya leko da kansa ganin shine yasa ni sauri karasawa inda yake
Yaya Jabir ya kalleni
"Hauwa yana ganki a kasa yau ina drivern?"
"Na makara,shine Baffa yace na tafi a kasa"
Yaya Jabir ya girgiza kai ya bude mota
"Kinga shigo na kaiki,banda abin Baffa ai yanzu ne ma yafi kamata a kaiki a mota"
Daga haka na shige motar Yaya Jabir na zauna gidan gaba,da duk cikin motocin Baffanmu ne ya fito da daya daga ciki
Sai da muka fara tafiya Yaya Jabir ya soma magana
"Ya yau kika makara ne Hauwah vayan ba halinki bane makara makaranta"
Murmushi nayi
"Wallahi Yaya Jabir Exam zamu fara na jima ina karatu daga sallar asuba saina koma na kwanta"
"To Allah ya taimaka"
"Amin" na furta muka cigaba da tafiya
Yaya Jabir ya sake kallona
"Bari na yima wancen abokin nawa magana" daga haka ya gangara da motarsa gefen titi kusa da inda wani saurayi yake tsaye da alama shine abokin nasa kansa ya zura ta motar
"Ibrahim lafiya dai ko?"
"Abokin nasa mai suna Ibrahim naga ya waigo ya dubi Yaya Jabir da alama yasanshi ganin ya karaso inda muke ya leko cikin motar yana fadin"
"Oga Jabir dama kana gari"
Yaya Jabir yayi murmushi
"Gani ma"
Sai a sannan na gaishe da abokin Yaya Jabir din nayi ba tare dana dago kai na ba Ibrahim din ya amsa da fara'arsa
Yaya Jabir ya dora da magana
"Ina zaka nufa ne naga alama kamar abin hawa kake jira"
"Eh wallahi zanje Mallam Madori Road ne"
"Ah to shigo mana na kaika
"A'a bana shigo ba naga bakai kadai bane kuma da alama yar makaranta zaka kai"
"Badamuwa duk hanya daya ne GGSS Dutsima Road kaga zaina karasa dakai ai can Road din,bari ta koma.baya kai saika shigo gaban"
Ni Yaya Jabir ya kalla
"Ki fito ki koma baya ya shigo"
Babu musu na fito daga motar sai sannan na kalli Ibrahim din yana kokarin shiga motar daganin alamu Ibrahim akwai son gayu
Muna fara tafiya makaryaya " jiyo muryar Jabir yana cewa da Ibrahim din
"Dama talakawa na ganinku Ibrahim"
Ibrahim yace
"Kaji ka ai mune talakawan naku"
Yaya Jabir yace
"Hmm,haka dai kace,ina motar taka yau?"
Ibrahim yace
"Tana gurin gyara"
Ibrahim ya juyo inda nake yana fadin
"Yan makaranta ya kike makara makaranta ki daina kin jiko ko karatu bai wuce ki ba za'a doke ki"
Murmushi nayi kawai nace nasa
"Insha Allah na daina"
Daganan ya juya gurin Yaya Jabir
"Danbatta ya bansan wannan ba wai itama kanwar kace"
Yaya Jabir yace
"Eh mana,yanzu bakasan Hauwah ba a gidanmu"
Ibrahim yace
"Nasan sunan amma bamu taba haduwa da ita ba idan nazo gidanku ba"
Yaya Jabir yace
"Diyar Mama Amina ce amaryar Baffa"
Ibrahim yace
"Ah shiyasa duk tafi ku kyau ashe mamarsu ta biyo"
Mamaki ya cikani jin maganar Ibrahim ashe har Ummanmu ya sani amma ni ban taba ganinshi ba,wata zuciyar tace.kila sanda yake zuwa gidan namu muna makaranta