Showing 66001 words to 69000 words out of 86533 words
ta haihu yau"
Cikin murna Ra'uf yace
"A'a Ammi wayata yau gaba daya a kashe take,mai aka samu"
"Nima dazu Ahmad ya fadamin yace min ya kira lambarta ka bai samu ba,Namiji aka samu"
"Kai Amma Ammi naji dadi mun samu aboki Allah ya raya mana shi"
"Amin ya rabb,kai yaushe zaka yi auren ne?"
Jin tanbayar da Ammi tayi masa da bai zace taba yasa shi kallonta
"Ammi aure kuma?"
Cikin karfin gwiwa tace
"Eh aure,ko haka kake so kayi ta zama,shekarunka kullum ja suke,amma kai naji ko maganarsa bakayi ga abokanan daga mai 'ya'ya biyu sai mai 'daya"
"Ammi ba nida budurwar ne har yau bansamu wacce tayi dai-dai da tsarina ba"
"Ai ba zaka samu ba kuwa,tunda ba nema kake ba,nida nayi ma sha'awar kaje kanemi auren Inteesar ba ki kayi ba,sai kaje ka nemawarwa abokinka soyayyarta,gashi nan ya aureta suna zamansu lafiya harda karuwa ma tsakaninsu"
"Ammi tayi maganar da nuna bacin rai
" amma Ammi na fada miki,Inteesar Shureim ya dade yana fadamin son da yake mata,kinga bai kamata naje na nemi soyayyarta ba"
"Amma ai tun a lokacin na fadama kaje ka samu wata ga 'yam mata nan a gari"
"Ammi bawai 'yam matanba samun ta gari a wannan zamanin shine aiki,kuma idan nasa mu banaso a sake kwatanta abinda ya faru a baya"
Sai yanzu Ammi ta soma fahimtar Ra'uf wato har yau dai bai manta da waccen yarinyar ba kenan bayan ta mayi aurenta ta dai kauda wannan tunanin tace
"Ra'uf kenan wato har yau ka kasa manta abunda ya riga da ya wuce,ya kamata ka manta da baya fa a yanzu ka tunkari gaba ka fahimta cewa bafa laifin su Yaya sule bane a waccen abun da ya faru,haka Allah ya kaddara tun fil'azal ita ba matarka bace"
"Hakane Ammi,amma na baki damar ki dubomin wata"
"To zamuyi magana da Dadynku Allah ya yima albarka"
"Amin Ammi na" shiru ne ya biyo baya
Shigowarsu Husna ya katse shirunsu
"Husna ce ta karasa wajen Tv tana cewa
" Ammi sai kace gidan makoki Tv a kashe bari na kunna"
Ammi tace
"Tunda kinzo sai ki kunna ai uwar iya"
Safiyya ta karasa kujerar dake saitin tasu Ammi ta zauna tana cewa da yaran indiyanci da shine yaran da sukeji sosai
"Ammi sannu da hutawa,yaya sannu da zuwa"
Cikin hadin baki suka ce yawwa
Sophie ta karaso tana cewa
"Yaya welcome"
Da murmushi kan fuskarsa Yace ur welcome Ammi na"
Daga haka ta zauna da murmushi kan fuskarta tace
"Yaya munfayi 'da"
Yace "Eh Ammi ta fadamin"
Safiyya tace "amma zamuje wannan karanma ko yaya?"
Yace"Anya kuwa Sophie"
"Kai Yaya don Allah muje munjema haihuwar Rufaida bare wannan aboki fa kayi"fadin Safiyya
Ammi ta harari Safiyya tace
" to sarkin da'din baki,karatun fa,kunsan zaku shiga first semester level 400"
Husna tace
"Kai Ammi kwana biyu fa zamu yi"
Harararta Ammin tayi tace
"Ba zaku ba fa,karatun zaku bari"
Ra'uf yace
"Ammi daina wahalar da bakinki nima ba zuwa zanyi ba bare su sa rai"
Safiyya ta fara magana kamar zatayi kuka tace
"Kai Yaya don Allah kayi hakuri"
Dady Jabir da ya karasa falon kowa da upstairs ya karaso falon yana kokarin fita jin hakurin da Safiyya ke bayarwa ya sashi saurin karasowa gurin da suke yace
"Ra'uf bazaka kiyayarmin Auta ta kuma kanwata ba mai tayi mana ne"
Ra'uf ya harari Safiyya yace
"Dady don ance fa bazasu UK ba gurin sunan matar Ahmad shine take ta'bara,kamar ita ka'dai aka hana zuwa"
"Kunga ku je ku shirya mu fita mu qyale su"
Da sauri suka mike ba sukayi Upstairs
Dady ya zauna a kujera yana murmushi ya kalli Ra'uf yace
"Ra'u har yau baka sami wacce kake so bane,ga kannenka nan su Husna da sun kammala degree dinsu aure zan musu ga babban wansu a gida ya zama gwauro?"
Ammi tace
"Wallahi Abban Safiyya nima maganar dana gama masa kenan"
Ra'uf yace
"Dady zan nemo insha Allah"
"Yawwa kayi kokarin hakan kaga Husna tanada saurayinta tsayayye Bello,yanzu saura Safiyya itace bata fito da miji ba,idan kuma kana santa sai ayi 'yar gida"fadin Dady Jabir
Ra'uf ya dan bata rai jin maganar Dady yace
" kai Dady,badai Safiyya ba zan nemo dai"
"To meye aibun Safiyya ne" Ammi tayi maganar tana tsare Ra'uf da ido
"Ammi kinsan dai wacece Safiyya kuma kinsan Hajiya bazata yarda ba kuma ma kinsan ko Baff...." Jin sallamrsu Husna yasa shi yin shiru da maganar Dady mikewa yayi ya kalli su Ammi yace
"Mu zamu fita"
Suka hada baki gurin cewa
"Allah ya kiyaye hanya" suka fice
Su Ra'uf suka cigaba da firarsu.
RUFAIDA
Rufaida tana kokarin fitowa daga kitchen taji yo muryar Yasir daga daki yana cewa
"Mami,Mami Samiha na waya"
Dakin ta shigo da tasa mu Yasir da wayar a kunnensa yana kokarin fitowa kawo mata wayar wayar ta amsa tasa a kunne ta gabatar da sallama Samihan ta amsa tare da ce mata
"Oh kin barni da surikina yana ta zuba min gwaranci ko little Rufaida ta fisa iya magana,ina kika je ne"
"Dama ina zai hada kansa da.wannan 'yar taki kamar ta saida mutane,wallahi na shiga kitchen ne"
"Au haka zaki ce,keba 'yar ki bace,tunda dai takwarar kice ai ba damuwa"
"Ato ai ni bana da damai surutu,tunda da 'ya tace bazatayi surutu ba,ya babyboy yanzu shine 'dana yana lafiya,an masa suna yau,naga baki kirani kinji sunan yaron bama"
"Sorry Samiha,kokarin da nake kenan dana baro kitchen din sai kuma naga kin kira,ya sunanshi?"
"Sunanshi AbdulRa'uf"
Jin sunan yasa Rufaida tuno da wancen Ra'uf din Allah sarki rayuwa,jin tayi shiru yasa Samiha cigaba da magana
"Ahmad ne yace sunan Ra'uf zaisa tunda nima nasa sunanki,kuma yace yanaso Rufaida da Ra'uf wadannan suyi rayuwa babu rabuwa sai mutuwa tunda sun fito ciki 'daya"
Rufaida jin maganar Samiha yasa ta sakin murmushi kamar tana ganinta tace
"Gaskiya,bansan irin kaunar da kuke mana ba,a tsawon rayuwarku"
"Soyayya ce dan Allah,ina Yaya Wahid din ne ko ya fita aiki ne"
"A'a baya jin dadi ne"
"Subhanallah kice ina gaidashi,ga Rufaida ku gaisa
Little Rufaida da take da surutu ta amshi wayar data matso a bata dama ta fara magana
"Mami,ina kwana"
"Lafiya kalau,Namesake,ya baby boy"
"Gashi nan,yanzu Mami ta daina daukata sai dai ta dauki,Little"
Dariya Rufaida tayi tace
"To ai yanzu kin zama babba yanzu"
"A'a mami ban yarda ba" ta karasa maganar kamar zata yi kuka
Dariya Rufaida tayi tace
"Ga Yasir nan na miki dariya,Rufaida tayi maganar tana bawa Yasir wayar"
Sun jima suna hira akarshe suka yi sallama jin turo kofar dakin nata yasa ta maida kallonta ga kofar dakin ganin Wahid ne ya shigo da shirin fita aiki yasa Rufaida kallonsa da mamaki tace
"Badai aiki zaka fita ba ko?"
Yayi murmushi ya rungume Yasir da rugo gurinsa yace Dady zan bika
"To my son jirani a falo na fito" don yawanci duk fitar da Wahid zeyi da Yasir ne hatta da gurin aikin yana fita da shi lokaaci lokaaci jin Yasir din ya fita ne ya sashi kallonta yace mata
"Eh mana My wife ko karna je"
"Eh mana,kasan baka jindadi"
"To ai nasamu sauki"
"A'a gashinan dagani kowa yasan bakada lafiya nasan karfin hali kawai zakayi don Allah ka hakura"
Kai ya girgiza yace "kiran gaggawa nasamu a office"
"To naji kabari nayi ma driving karkayi da kanka"
"A'a my wife kibari na kira kofur Musa yazo ya yii min driving 'din"
"Badai kaso nayi kawai zaka ce"
"no my wife banaso ki wahala ne,kinsan kece silar haskaka zuciyata fa kinga wazai so hasken rayuwarsa ya wahala"
"Hm kaga ma dadin bakinka dai"
"To ba kicemin nine haskenki ba?,koda yake nasan bani bane inaji a jikina zaki zauna da mutumin da zai zama sanadiyyar haska rayuwarki"
"To ai ba wani bane bayan kai ni Kaine haske na"
"Kinga ban yarda ba bani bane"
"To waye nidai nasan kaine" yana kokarin cewa wani abu yaji karar wayarsa ya ciro wayar a aljihunsa ya duba ganin lambar kofur Musa yasa Wahid cewa kinga bari naje Kofur Musa ya iso nake tunanin shike kirana yanzu
"To Yaya Allah ya kiyaye ya tsaraminkai take care bye"
"Amin ya rabb my wife take care too"
Da haka ya murda hannun kofar zai fita ya juyo ganin tana zaune yace
"Oh yau babu ko rako"
"Eh fushi nake dakai"
"Baki ya dan tabe yace kina fushin dani kika yi dogon fira dani"
"Ke dai kawai bakyason fita waje zaki ce"
"Kaje yana jiranka fa?"
"Shi waye mai jiran nawa?"
"Kofur Musa mana"
"Shikenan take care" ya fada da murmushinsa ya fice"
Itama kallonta kofar yayi bayan ya FIFA da murmushi akan fuskarta sai tace batajin a yanzu tana da sauran damuwa ta samu miji na gari mai kaunarta damuwarta daya sanin mai Umminsu tayi ta zama saniyar ware a cikin danginsu har ake mata kazafin karuwace don tana da yakinin shine ya ruguza waccen maganar aurenta,sai kuma son da take tasan mainene alakarsu da Danbatta family,dukda wannan yasa take rayuwa da Wahid bawai don soyayyarsa ta mamaye zuciyarta ba illa iyaka yayi mata halarci ya kauda kansa ga wancen abubuwan da ake fada akan mahaifiyarsu ya amince ya aureta dukda yadda ake fadar Umminsun takasance,wasu hawaye masu dumi ta goge wannan shine kawai damuwar da tayi saura a zuciyarta
*****
"Ra'uf
Koda maganar saka sunansa da Ahmad yayi ga dansa ta riske sa bakaramin farin ciki yayi ba a ransa yana ayyana cewa Rufaida da Ra'uf sun hadu a wata duniyar da babu wanda ya isa ya rabasu saboda sunzo a ciki daya tabbas yasan san Rufaida da kaunarta ba zasu gushe ba a zuciyarsa har zuwa ranar da zaiyi numfashi na karshe ya rasa gane wannan soyayya wacce iri ce,sai dai yace Allah ne ya hadata kawai bawai mutum ba,Dukda yadda iyayensa keso yayi aure yaki yi sam,gani yake baida lokacin ma tsayawa kula wasu 'yammata don gaskiya aure ba shine a gabansa a lokacin ginin asibiti da ya fara a Nigeria yanzu shine a gabansa ba maganar aure ba yanzu abinda ya damesa ya bunkasa kasarsa ta hanyar cigaba ta kowanne fanni shi kuma aure yasa a ransa lokaci ne,yanaso daya kammala gininsa ya koma gida ya samu ya sami nitsatstsiyar mata a kasarsa ya aura don shi gaskiya baya kawo wa ransa zai auri Rufaida saboda tayi aurenta ita tuntuni harma yaga kyakkyawan Baby boy dinta a Dp din Samiha daya na gani yaga kamar yaron da Wahid da bai manta kamanninsa ba shekarun baya da suka wuce ,Husna ta koma Nigeria a can zatayi bautar kasarta,data gama kuma za'ayi bikinta zata auri cousin dinsu Bello,Hajiya tayi tayi Ra'uf yazo Nigeria yaki sam bayajin son zuwa kuma koda ma zashi don su Yakumbo da Mama suwaiba zashi ba dan itaba
***********
"Rufaida meyasa ne Umma take so ta matsamin akan auran nan,yanzu fisabillah hakan ya dace"
Rufaida jin maganar da Wahid keyi yasa ta aje wayarta gefen gado ta maida kallonta gare sa
"To mene ne ya faru kuma?"
Yace
"Sam ta kasa fahimtata tace min nine na fadawa Abba karya amince da auran nan vayan kuma ,ba mu taba maganar da ta shafi aurena da Ruqayya ba nida Abba,amma zancen da ni ke miki yanzu ya kafe kaida fata ba zan aureta ba,ita kuma Umma ta kafe sai nayi auren nan"
"To yanzu ya za'ayi" fadin Rufaida
"Ina so zanje gida gobe saboda inaso Umma ta fahimceni maganar waya bazata wadatar ba"fadin wahid
" amma Yaya gobe gobe banyi kusa ba"
"Wanne kusa kanwata kinsan dai wacece Umma idan banje ba kinsman abinda zaije ya dawo ba karami bane"
"Eh da kuma hakan,Allah ya kaimu lafiya" jin karar wayarsa yasa shi mikewa ya karasa inda yasa caji a falon ya dauko wayar ya dawo inda yake,ganin mai kiran ya sashi saurin dagawa ganin Ummansa ce
"Assalamu Alaikum Umma ina yini"
"Wa'alaikumus salam lafiya lau ya aiki"
Bai dama tsammaci za ta ce yasu Rufaida ba hakan yasa shi saurin ce mata
"Alhamdulillah ,Umma"
"Yawwa dama so nake na fadama inason ganinka gobe,saboda Ina so Bukar ya amince da auran nan kana sane indai ba amincewarsa babu abinda zai yiyu"
"Eh hakane,Umma dama yanzu make maganar zuwa na da Rufaida"
Jin ya anbaci Rufaida yasa ta jan dogon tsaki dan ita ko sunan Rufaida bata so ma a fadama ta shigar mata cikin rayuwar danta wato ma saboda zaizo gida sai yayi maganar da matarsa kila ma har shawara ya nema,tsaki taja a karo na biyu tace
"Ok"
Wahid dinne yace
"Yasu Wasila da karamar kanwata"
"Wacce kanwartaka kuma kana da kanwa da ya wuce Wasila ne"
"Eh mana Umma,akwai 'yar Aunty da Mama"
Tsaki tayi tace
"Naji"
"Yawwa,Ummi kema yaushe zaki min kani,ko kanwa"
"Kamar ya ai yanzu nabar muku kudai kuyi,yanzu idan ka auri Rukayya,ai shikenan zan fara tara jikoki,kaga ai gwara na bar muku tunda wuri"
"Eh hakane gama ,Umma amma ga Yasir nan ai yafara zuwa"
Hajiya Jamila jin an sako maganar Rufaida da batasan jinta sam yasa ta cewa
"Kaga sai anjima"daga haka sukayi sallama ya katse wayar
Ya dubi Rufaida yace
" Allah Rufaida banason zuwa Zariya akaran kaina dandai akwai muhimmanci a zuwan nawa,amma inajin kar naje Umma tace min na sake ki,jikina yana bani wani abu zai iya faruwa Indai nasanar da Umma abinda Dady yace"
Rufaida ta kallesa da hawaye ya taru a idonta tace
"Yaya Wahid,ka daina wannan tunanin ni dakai mutu ka raba,nasan Umma ba zata ce haka ba"
"Idan to batace hakan ba, idan kafin goben na mutu fa,Rufaida banaso na mutu na barku"
Rufaida da ta fara hawaye tace
"Yaya dan Allah ka daina maganar mutuwa,bazaka mutu ba,tare zamu mutu"
Murmushi Wahid yayi yace
"To zan daina amma kinsan da cewa mutuwa dole ce duk mai rai zai zama gawa,kuma na fiso na rigaki mutuwa saboda ke din yanzu kikasa kafa a cikin rayuwarki ni kuma nafara kwana biyu"
"Eh,a'a Yaya ni baka tsufa a guri na ba so nake mu rayu mu mutu tare"
Dariya yasa ya nuna ta
"Oh kinganki dama kina sona sosai haka"
Murmushi tayi tace
"Yaya idan banso mijina ba wazan so"
"Ra'uf mana ai ni duk a tunani na gangar jikinki na aura"
Harararsa tayi tace
"Kai Yaya,Wannan Ra'uf yaki fita a ranka shi yana can ya manta da shafin rayuwarmu kaiko kana tason sawo mana shi a cikin rayuwar mu,bayan ba muda alaka dashi"
"Rufaida kenan ba zaki fahimci yadda nake son Ra'uf a raina ba inajinsa har a jinin jikina"
"To fa saboda me" fadin Rufaida tana zaro ido
"Saboda inason abinda kikeso Rufaida nasan kin soshi koda a yanzu baya ranki,kinsan mene fata na"
Kai ta girgiza yace
"To bazan fada ba ma nafasa"
"Yaya Dan Allah ka fadamin"
Yayi dariya yace" badai shagwaba zaki ba to dama abinda zance shine koda bana raye ki zauna da mutumin da zai zama sanadiyyar haska rayuwarki"
"Oh Yaya kwanaki ma fa ka fadi haka,dan Allah kadaina fadar mutuwa duk sanda bana tare dakai zan zama banida ragowar farin ciki"
"Ai hakane Rufaida zaki samu haske da zai haskaka ki a rayuwarki,Rufaida mutuwa dole ce,amma tunda bakyaso na daina fada yanzu dai ina Yasir"
Rufaida da murmushinta tace
"Ya kwanta a falo,bari naje nadaukosa"
"Kyale kawai zanje na daukosa yau ni zan masa shirin barci ma"
"Yaushe rabon duniya da ayya raye yau wacce rana m
Yace " asabar" yana kokarin fita da dariyarsa
*JININMU D'AYA*
By Sadiya Khalil
48.
DAWOWA LABARI
*RUFAIDA POV*
Abdul Malik ne ya dubi Rufaida da suke zaune a harabar gidan suna fira kasancewar yau an tashi da zafi garin kuma ba wuta babu inji yara kuma duk sun tafi Islamiyya Tahfiz da yau lahadi babu boko harda Yasir suka tafi
Abdulmalik din ya soma magana
"Rufaida yau fa naga mai kama dake"
"Ni kuma yaya AbdulMalik" Rufaida tayi maganar da mamaki akan fuskarta
Ya sake kallonta yace
"Kwarai kuwa,da farko dana ganta tana tafiya tunani na bani yayi kece ma,harna fara tunanin maiya faru a kadunan kikazo saida ta juyo da fuskarta naga bake bace,tafiyarku ce sak daya amma a fuska bakwa kama sai dai a fisge"
"Oh kodai Samiha ce,ana cewa muna kama nida ita?"
Harararta yayi yace
"Samihan ce bansani ba"
"Aunty Amarya tasa vaki a firartasu tace
" oh maiyasa baka tsaya yi mata magana ba,kaga aida ko lambarta saika samowa Rufaidan"
AbdulMalik yace"wallahi kuwa Aunty kinga dana hada su kawance,amma zan rika bi ta hanyar kozan sake ganinta,kamar tayi yawa duk da babu a fuska amma akwai a siffar jikinsu"
Hajiya Jamila da take jin firarsu tasa baki gurin cewa
"ai babu mamaki ko a cikin yawon da akayi ana abun kunya aka sameta"
Jin maganar Hajiya Jamila da Rufaida ta jita kamar dirar mikiya yasata mikewa daga gurin gaba 'daya kanta a kasa
Ganin Rufaida ta mike daga gurin tayi shigewarta falon gidan kallon data tarar a kunne shi ta kashe tayi kwanciyarta da ita sai yanzu tasan andawo da nepar data san an dawo da wutar ita kam mai zai jama ta zama a can sam shiyasa batasan zama koda a fall ne indai Hajiya Jamila na gurin dan saita fadi bakar magana akanta
Ganin Rufaida tabar gurin yasa AbdulMalik kallon Hajiya Jamila ya soma magana
"Haba Umma hakan baida ce ba"
Hajiya Jamila ta hararesa
"To ubanka nace da baida dace ba a cikin maganar,don na fadi gaskiya"
AbdulMalik zai sake magana Hajiya Kubra da sai yanzu tasa baki tace
"Kaga AbdulMalik kyaleta karka sake yin wata magana"
Hajiya Jamila ta harari Hajiya Kubra tace
"Kinga nifa banason shishshigi 'dan kine ko nawa,ki barsa ya fadi abinda zai fadama na,a haka a nuna ana sonka sai an ware a fara gulmarka"
AbdulMalik ya dubi Hajiya Kubra yace
"Mama don Allah kar kice komai"
Ya maida dubensa ga Mahaifiyarsa yace
"Haba Umma daga ban hakuri"
Hajiya Jamila tace
"To ubana,hana ni na maida martani"
Ganin ba zata fasa maganar ba yasa shi mikewa ya bar gurin don yasan indai yana nan ba zata gaji da magana ba ya nufi falo
A falo ya sameta a kwancea a kujera kamar mai varci ammma da gani ba barci take ba zama yayi kujerar dake kusa da wadda take kwance yace
"Rufaida kiyi hakuri don Allah,nasan Umma ba ta kyauta ba"
Murmushi tayi ta bude idanunta wakeke waken da Rukayya ta fito daga kofar kitchen da Kofi a hannunta tanayi shi ya tsaida maganar da Rufaida
Rukayya ta kai kallonta ga Rufaida da take kwance da hankalinta vaikai ga ganin AbdulMalik ba Rukayya ta fara magana cikin bacin rai
"Malama ke wacce irin kidahuma ce ya zaki zo ki tarar na kunna kallo ki kashe min ki kuma kwanta wa mutane shame shame a kujera kamar ta gidan ubanki,sakarai kawai ana mata kora da hali kina nacewa mutane..."
Ganin Rukayya ba zata yi shiru ba yasa AbdulMalik gyaran murya da zuciyarsa take tukuki jin maganganun Rukayyan
Rukayya da sai yanzu ta san AbdulMalik na gurin tuni ta fara zaro ido ta soma magana
"Yaya AbdulMalik wa...."
cikin bacin rai AbdulMalik ya nuna nuna Ruqayya da ya tsa yace
"Ke daka ta munafukar banza ke waya kai kidahumanci,inba kida humanci ba mai zai kawo mace budurwa gidansu saurayin da taso don ya mutu kuma bama zuwa gaisuwa ba a'a zuwa a zauna kamar