Showing 3001 words to 6000 words out of 86533 words

Chapter 2 - JININMU DAYA HAUSA NOVEL

farkowa daga doguwar sumar da tadau lokaci bata farko ba tun karfe biyu har yanzu da duhun yamma yayi Gaba daya suka fara yi mata sannu muryoyinsu ne suka fara yi mata amo a kunnenta cikin rashin tsammani wannan yasake tabbatar mata mutuwar AbdulWahid mijinta gaskiya ce idanunta tasake budewa tangaram ta maida dubenta ga Umminta da Gwaggonta da Momynsu sai kuma Luba da Yusuf kekan jinyarta tana jijjigasa dukkansu babu cikakkiyar walwala a fuskarsu Rufaida da sabon kukan da ta fara ya ruda mutanan dake dakin tuni zuciyar Hauwa wato Umminta ya kara tashi wanda dama tun bayyana musu mutuwar AbdulWahid hankalinta yake a tashe har sukazo Zariya da hankalin nata ya sake tsanantar tashi ganin 'diyarta ta Rufaida a cikin mawuyacin hali da yanzu hakan zuciyarta ta karaya na tausayin 'yar ta kuka itama ta fara cikinsu aka rasa mai lallashin 'dan uwansa Gwaggo ce take kokarin lallashinsu tana ban baki tana cewa duk fa wanda ya mutu baya dawowa kuma duk mai rai hakika mamaci ne muma lokaci kowannenmu yake jira hakuri zakuyi da yi masa addu'a halinsa na gari ya bisa danshi AbdulWahid tashi tayi kyau da izinin Allah,da wa'dannan kalaman ta cigaba da lallashinsu har ta fara janyo hankulansu,da haka tasamu kansu hatta Rufaidan shiru ne tayi sai hawayen dake bin kuncinta tanamai sake tuno rabuwarta da mijinta da hirarsu ta karshe yanzu shikenan mutuwa ta yanke kauna itada mijinnata yayi tafiya mai nisan da babu waiwaye tafiyar ta kasance a bigiren da ba'a dawowa har abada ba'a dawowa mutuwa kenan mai yanke buri wani irin hawaye masu dumi suka cigaba da zubo mata lalle mai rai ba a bakin komai yake ba duk wanda yamanta da wannan ranar saidai yayi maza ya koma ga Allah domin yau dai ga wannan bawan Allahn ya tafi ba tareda yasan yau zai mutu ba mutuwa kenan da bata kwankwasa kofa kome kake idan tazo haka zata daukeka Allah yasa idan ta mu tazo mu cika da kyau da imani


Bangaren Hajiya Jamila

Yasir dake zaune a falo ya takure a tsakanin kujera inda yake kallon Hajiya Jamila da mutane guda biyu dasuke kanne a gareta Kaltume da Haulatu da 'daya take aure a Kaduna daya kuma a makarfi hira suke Hajiya Jamila tana basu labarin yadda taga fuskar dan nata kafin rai yayi halinsa kai baza kace Hajiya Jamila bace da dazu take kururuwar mutuwar amma cikin awannin da busu kai ga kwana ba harta mance tafara bada Labarin mutuwarsa itada 'yan uwanta kuma a gaban karamin yaro,Kaltume ce da itama Umma take cewa Hajiya Jamila a matsayinsu duk ita ta rikesu harta aurar dasu,ni yaron nan bansan kukan da yake ba yabarmu muji da mutuwar da akayi mana yaki,Hajiya Jamila tace yaron da aka cusa masa kiyayyarmu taya zai daina Hajiya Jamila ta fashe da kuka,Haulatu ta miqe tayi kansa taja hannunsa da karfi ta cankadasa kofar da zai sadaka da dakunan gidan Hajiya Kubra da take kokarin fitowa ta zauna falon saboda masu zuwa gaisuwa makofta nan Yasir ya fado jikinta,Hajiya Kubra ta kalli haulatu tace Haulatu mai yayi zafi har haka,sai kace ba jikanku ba kuma maraya Zaki cankadosa yanzu da Allah bai kawoni ba kila har fasa baki zaiyi idan da tsautsayi,Kaltume dake zaune tace Mama sunan da suke fadawa Hajiya Kubra ta cigaba da cewa yaron da mahaifiyarsa da kakanninsa suka cusa masa kiyayyarmu a ransa,Hajiya Kubra tace yanzu dai komai yawuce wanda ake abun danshi yau ina yike bayanan,yanzu cigaba da maganar nan dawo da bara bana ne da jawo Bacin rai yanzu muji da mutuwar da akaimana babu ko daya daga cikinsu da tari ya sille masa saboda koba komai dai mutuwar su akayiwa amma zuciyar ko wannensu da tunanin da yake akan matakin da zasu dauka dan ita bangaren zuciyar Hajiya Jamila yadda zatayi ta fitarda su Rufaida daga rayuwarsu take dukda ga mai hadawa nan Yasir ya riga ya hadasu wanda ko ya mutu acewarta ya mutu ta rayayyun 'ya'yanta take a yanzu domin badan yadda taga gawar AbdulWahid ba to da hankalinta bazai tashi har yasa ta kasa maida raddi ba gurin Hajiya Kubra Hajiya Jamila macace mai matukar son duniya shiyasa ma mutuwar dan nata baisa ta rage kudure kuduren duniya ba da take yi kuma babu daya kwakkwara na gari da za'ace

Hannun Yasir Hajiya Kubra ta kama zuwa cikin gidan tana lallashinsa har dakin dasu Rufaida ke ciki ta kaisa inda yana zuwa ya fada jikin Rufaida uwa a garesa yana kuka itama Rufaida hawaye take sai dai bata bari ya gane ba ta cigaba da jijjigasa har barci ya daukesa,nan Hajiya Kubra ta cigaba da yimata nasiha a haka ta fice daga dakin tana goge kwallar tausayin yarinya karama Rufaida gashi ta zama bazawarar da yau Allah ya dauke mata mijinta da yabarta da da da yanzu yazama maraya dukda bazaman farin ciki tayi da mijin nata ba to ina sirikar tabarta tayi haka amma hakan baisa yarinyar korafi ba daidai da rana daya ba hakuri gareta mai yawa dukda wannan abun da yafaru wanda ake danshi baya duniyar baisa kiyayyar da Hajiya Jamila kewa su Rufaida raguwa ba batare da Hajiya Kubra tasan laifi 'daya kwakkwara ba dayaja hakan ba rayuwar dama haka ta gada wasu kome zakamusu bazasu kaunaceka ba

Abba Bukar da yake zaune gefen gado wajen karfe tara na dare da haske ya gauraye 'dakin na lantarki Hajiya Kubra ta shigo 'dakin dauke da sallama da Flask riqe a hannunta Abba Bukar ya 'dago fuskarsa da take cikin damuwa ya amsa mata kafin ya maida kansa ga inda yake kallo a kan lokar jikin gadon 'dakin Hajiya Kubra ta zauna ta fara magana cikin sanyin murya da cewa"Abba dukkan mai rai mamacine AbdulWahid ya tafi inda ba'a dawowa damuwar bazata dawo dashi ba Addu'a ce yakamata mudinga yi masa"
Kai Abba Bukar ya 'daga alamun ya gamsu da abinda Hajiya Kubra ta fa'da kafin yace" Kubra mutuwar yaron ce tazo shiba ciwo yayi ba rana tsaka yayi hatsarin motar nan ni koma a waya bai fadamin zaizo ba ashe ajali ne yakirasa,gashi kaf cikin yarana babu wanda kai tsaye zakace yabar abu ya bari kai tsaye inbashi ba gashi da kokarin kyautata mana dason yan uwansa"Abba Bukar ya karasa maganar yana zubda hawaye lalle duk abinda zaisa Abba Bukar koda hawayene babban abune tabbas duk abinda Abba Bukar yafada gaskiya ne saidai kuma ya za'ayi wanda yafimu sanshi a amshi abinsa,Hajiya Kubra ke wannan tunanin a cikin ranta Hakuri ta cigaba da basa kafin yace su Haulatu mungaisa sunyimin gaisuwa dazu kuma abin shirmen anan da mazajensu da suka kirani a waya yimin gaisuwa suka fadamin cewa sai anyi bakwai zasu koma saida ma na dinga fada tunda wanda ya mutu bazaidawo ba,amma ko wacce tabaro yaranta ta taho,kuma suda ba jin magana suke ba kafin su koma sai sun hargitsamin gida najima da halin yar uwartasu danike aure wannan ai shirmene da anyi uku duk kowa zai koma gidansa Hajiya Kubra hakuri ta shiga basa

Washe gari da wuri Kabir ya shirya zasu koma Abuja shida matarsa sai ana gobe addu'ar uku zasu dawo su kwana ayi addu'a su taho inda Luba zata tahowa Rufaida wasu daga cikin kayan sawarta Yasir ganin Kabir zai tafi yafara cewa Kawu akaini Dady na kukan da Kabir yake maqalewa yafarayi inda tun a falon da yaje musu sallama zuciyarsa ta karye da ya tuna cewa shida AbdulWahid suka saba zuwa muddin wani dalilin yakawosu Kaduna sai sun karaso Zariya kai kobama haka ba gidansu AbdulWahid kamar gidansu Kabir ne tun sanda suka hadu a jami'ar Ahmadu Bello University shiyasa yake tuno falon gidan dakoda yaushe zuri'ar gidan suke zaune a ciki bazaka rasa koda mutum daya ba a kowacce rana ta duniya ba barema zaman ake da yawa ana hira cikin so da kauna harda Abba Bukar uba garesu hakama idan sun biyo da Kaduna a wannan falon zasu zauna aita fira cikin raha da wasa da dariya da girmama juna yau ga yadda abun yakasance gasu a falon amma babu jigon da yayi sanadiyyar sanin wannan a halin da yayi yau yanacan a wani bigiren na daban da muma jiranta muke wannan bigiren na mutuwa da kowa jiran lokaci yake
Kabir da harya Shiva mota amma yanajin sautin kukan Yasir nan Abba Bukar da kansa yasa Yasir a mota su tafi tare da shi

Koda Labarin mutuwar yazowa gurin aikinsa sunji mutuwar sosai dan AbdulWahid mutumin kirkine yasamu shaida mota sukayi washe gari suka nufo Zariya suda wasu 'yan sandan da suke a cikin barraq din nasu buhun shinkafa katan din taliya couscous da kudi masu yawa suka kawo musu a riqa dafawa wani babba a cikin su nauyin karatun Yasir ya dauka da za'a bashi yaron da yafi kowa son hakan domin duk abinda zaiwa AbdulWahid bazai biyasa shi abinda ya masa ba sanda ya shiga matsala ya taimakamasa sosai sun nuna halalci sosai abokan aikin nasa sosai koda Kabir yakoma abokansa da suke aiki tare haka suka riqa yimasa ta'aziyya kwanansu daya su Kabir suka juyo saida aka lallashi Yasir cewa Abbansa yatafi wani aiki sai yayi girmaan za'a kaishi gurinsa da haka aka samu yafara hakura sai dai jefi jefi idan yana rigima ya riqa maganar mahaifin nas_JININMU DAYA_
(Labari mai dauke da son zuciya)
Na
Sadiya Ibrahim Khali

3
_A ranar da akayi ukun AbdulWahid ranar Abba Bukar yacewa su Haulatu kowacce tabi mjinta takoma saboda ya fahimci ganin cigaba da zaman nasu zai iya kawo hargitsi,koda Hajiya Jamila taji haka abinda Abba Bukar yace bata tada wata fitinar ba dan a yanzu ne mutuwar 'dan nata take dokarta don tafara zubar da makaman aiki saidai bata zubar dana 'kiyayyar da takewa Rufaida ba har yau kai bama ga ita ba harga jininta kiyayyar ta shafesa,wadda dama 'kiyayyar tadade da wanzuwa,_

_A ranar ukun ne yan uwa da abokan arziki suka zowa Hajiya Jamila gaisuwa daga mahaifarta Nasarawa Lafiya ciki ko harda Ruqayya da a ganinta tafi kowa jin mutuwar AbdulAhad sunzo da niyyar suyi kwana daya su juya dalili mai 'karfi da yakarasa su Kaltume da Haulatu jin haushin tafiyar tasu su da sukaso suyi fira da 'yan uwansu yau amma ga yadda Abba yace banda suna ganin girman Abba da bazasu tafi ba,sai dai matsayin da yake a gurinsu na mahaifi da tunda iyayensu suka rasu suka dawo hannunsa harya aurar dasu bazasu iya ja da maganarsa saboda koba wannan Abba Bukar ba kalar wanda za'ayiwa wargi bane da haka kowacce ta hada kayanta tabi mijinta nata_

_*Abangaren Rufaida*_

_Nasihar da Abbanta Aliyu yake mata sosai take shigarta hawaye take zubarwa daga idanunta dake cikin hijabi,inda shi bai lura ba,dukda shi a karan kansa nasihar yake amma tausayin 'yarsa yana mamaye a zuciyarsa haka ya mike daga 'daya daga cikin kujerun falon 'dakin dasu Rufaidan suke ciki tundaga mutuwar yana yi mata sallama da kyar batare da ta dago kaiba ta iya ma Abbannata addu'a wadda nasihar Abbannata jinta kawai take bata fahimtar komai dan yau mutuwar sabuwa tadawo mata fil gashi yanzu haka kowa watsewa zaiyi a barta cikin tsangwamar da tasan zata riska gurin surikarta akan abinda ba tada masaniya,Da haka Umminta Hauwa'u da Momynta Hajiya Maryam suka fito daga Bedroom din falon da jakunkunasu a hannu kowaccensu fuska babu walwala dasu ma tafiyar zasuyi nan Hajiya Maryam ta kama hannun Rufaida ta 'dago fuskarta ta fara kokarin share mata hawaye kafin tayi mata nasihar itama da haka suka fice suna yi mata Sallama saboda shi kansa Aliyu su yake jira su kama hanyar Kano kodan su isa koda da la'asar ne da haka su Luba da Gwaggo suka fito yi musu rakiya da itama Luba anjima zasu tafi itada Kabir bandama yaje gurin wani abokinsa inda ya tafi da Yasir da Yusuf toda tuni ma sunkusa Abuja Gwaggo kuwa da take a gari sai magriba Abdulmalik zai maida ita gida dukda yadda Abba Bukar yaso Gwaggo ta zauna har Rufaida tafita takaba amma kiri kiri taki amincewa sai dai ta rika zuwa akai akai duba ta_

_Karfe tara na dare gaba daya dakin yayi shiru daga ita Rufaida sai Yasir da yagama rigima yayi barci saiko karar sunnah TV da take sauraron wa'azi saiko wayarta dake gefe da sai yau Luba ta bata da ta kira su Umminta da Momynta Hajiya Maryam sun sauka lafiya nan ummin nata Hauwa'u ta dora da yimata nasiha Luba ma ta kira ta sunje gida lafiya sai kuma kiran kawaye da abokan arziki da 'yan uwa da sukaji mutuwar basu sami damar zuwa ba da take amsawa ganin Number 'din Samiha a screen 'din wayar da take ta gwada number 'din Rufaida tun bayan gaisuwar da tamata a wayar momynsu Maryam da bawani damar yi mata ta'aziyya tasamu ba,sai yau da number din ta kira ta samu ta shiga, ita kanta Samiha taji mutuwar kamar itace mijinta ya rasu dan yadda ta dauki Rufaida a zuciyarta ba abin akwatanta bane badan busu jima da komawaba da saita zo yi mata gaisuwa,da haka Rufaida ta 'daga wayar da muryarta me cike da rauni tayi sallama da kadan ya rage tayi kuka Samiharce ta amsa ta kuma kara yi mata ta'aziyya da cewa "Rufaida Wanda duk ya mutu baya dawowa yanzu Yaya Ahad addu'arki tafi bu'kata damuwa bata maye gurbin komai sai sawa zuciya ciwo domin duk abinda ka rasa bazai dawo ba addu'a itace mafita akan komai" da haka ta cigaba da bata hakuri sosai Rufaida taji da'din wayar tasu tana cewa"nagode Samiha kuma insha Allah zai dauki shawararki yasu Little din da Rufaida karama" cikin farin ciki Samiha tace"duk suna lafiya Ahmad yace yana miki gaisuwa da mundawo gida zamu zo gaisuwa shima yaji mutuwar yace gaisuwar waya ba zata wadatar ba sai anzo har gida"Rufaida ta har ranta taji dadi tace"koma ta hakane tayi ai ina Yaya Ahmad 'din"Samiha tace aiko ba tayi ba ,Yana gurin aikinsu yanacan yauma yana cuku cuku samun takaddar da za'a bashi yadawo gida"Rufaida tace"yanzu bazai hakura ba ai duk dayane nanda shekara biyun da suka cemasa"Samiha tace "wanne duk 'dayane bayan bama ganinku a kusa damu ai bawani cikakken farin ciki ba ahalinka a tare dakai anyi nisan daya wuce na ahau mota sai dai jirgi mai saukar ungulu" da haka suka cigaba da ta'ba hira wadda yasa Rufaida jin da'di dan har ranta matsayin data dau Samiha ya wuce tunanin mai tunani haka sukayi sallama kowannensu a cikin farin ciki_

_koda ta sauke wayar tunani ta cigaba dayi irin yadda rayuwarta takasance kalubalen data riska har kawo yanzu da wannan tunanin barci ya dauke ta_

_'Bangaren Hajiya Jamila_
_Aunty Shema'u da take yaya ga Hajiya Jamila ta dubi Hajiya Jamilar da sauran mutanan 'dakin tana cewa"Wai ita yarinyar nan Rufaida bazata zo gaishemu bane har takwas ta gota komu take nufi zamu je gaisheta yarinya tasamu guru said wulakanci"Hajiya Jamila tace " naga alamar hakan take nufi" nan sauran 'yan uwan Hajiya Jamila suka samu kofar cigaba da magana Mara dadi akan Rufaida dukdai akan dalilinsu nacewa batazo gaishesu da safe ba Aunty Maimuna kanwar Hajiya Jamila ita tasa baki cikin maganar tace" Aunty ai kamata ayi mata uzuri amatsayinta name takaba bakuma asan dalilin nata nakin zuwa ba tunda tasaba zuwa koda banwai Sani ba"wa'danda da suka fara korafin cewa bata zo dinba sai duk suka fara cewa hakane yakamata suje dubata Idan sungama shirin tafiya da sukeyi Aunty Shema'u ta 'dan ta'be baki suka canza fira_

_Hajiya Kubra ta dubi Aunty Amina amaryar Abba Bukar da suke kitchen suna kacaniyar girki su da wata mai tayasu aikace aikace tace" Amarya niko yau banji motsin yarinyar nan Rufaida ba"tace " nifa kinsan bana shiga harkar da baruwana saboda ina tsoron najawa kaina rigima gurin Hajiya Jamila gwara ke manyan 'ya'ya gareki nifa"Murmushi Hajiya Kubra tayi tace"Amarya rufamin asiri yanzu Hassan ya sake Kodan yatsa ya 'daga wa Hajiya Jamila basai ankoremu nidashi a gidanba kinsan Abba bazai 'dau irin wannan ba,Kawai dai gani nayi 'dana kowa ne kuma mahaifiyar yarinyar nan tana ganin girmanmu kuma nidai tunda nike bazance ga abinda sukayi mana ba yakamata muma mukula da ita tunda yanzu ita abar tausayice"Aunty Amina tace " toda wannan amma dai ina tsoron wannan yare yaren" murmushi Hajiya Kubra tayi tace" ashe dama tsoro kawai kikeji ni kinga bari naje dubota" "to sai kindawo" kawai Amarya ta fa'da ta cigaba da aikinta"_

Shiga Hajiya Kubra tayi dakin tana sallama sai dai bataji motsin mutum a falon ba yasata karasa shiga bedroom din a takure jikin gado ta iske Rufaida tana rawar sanyi gefe kuma Yasir ne dayaketa barcinsa babu abinda ke damunsa"Hajiya Kubra tace Subhanallah Rufaida meke damunki"cikin rawar murya tace"Mama zazza'bi nakeji da ciwan kai"Hajiya Kubra tace" amma baki fada ba" tace" yanzu nafara jin zazzabin" Hajiya Kubra tace "hala bakicin abinci haba Rufaida mutuwa fa dole ce Wanda mutu bazai dawoba kuma ke bakaramar yarinya bace da za'atasa ki kici abinci ko aduramiki,bari nakira Hassan idan mota tana hannunsa akaiki asibiti" waya ta 'daga da take hannunta ta lalubo Number Hassan ringing biyu ya 'daga tanbayarsa tayi kana inane yanzu nan yake shaidamata yana bangarensu ko abinci aka gama su fito ci tace a'a Rufaidah ce balafiya ta dauka mota tana hannunsa yace tana hannun Yaya Abdulmalik Abba ya aikesa nan yace Allah ya kara sauki Hajiya Kubra tace Amin ta katse wayar shima Hassan wayar ya aje yana kara tausayin 'yar uwarsa dama haka mace take komawa idan mijinta yarasu lokaci guda Rufaida ta rasa duk walwalarta shi dama za'a bashi ita ba abinda zai hanasa aurenta Koran su rike yaran nan cikin kulawa bazai fahimci yayi rashi ba"
Hajiya Kubra AbdulMalik ta kira ganin bai dagaba yasa ta fahimci tuki yake Abba Bukar takira tasanarmasa nan yace bari yashigo dakin ya gaisheta gefen Gado Hajiya Kubra ta zauna ba jimawa ya shigo ya dubata yace idan Abdulmalik yadawo zasu tafi asibiti Yakuma umarci Hajiya Kubra tadauki yasir ayi masa wanka da haka suka bar dakin suna karamata Allah ya kara sauki bayan mikawa yara Yasir ta nufi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login