Showing 30001 words to 33000 words out of 86533 words
kukeso da wannan shafin donku akayi*😊
Page 22
arfe 1 na ranar daurin auren aka taho da amarya Samiha da take kuka sosai na rabuwa ita da gida saidai da ziyara haka dai suka taho da yayyenta biyu aunty samira da aunty samina da kannen da yayyyen babanta dana mamarsu biyu da kawayenta cikin harda su Nasiba da Rufaida da bayan gama shagalin bikin da za'ayi a Kaduna yau bayan kai amarya zasu koma kano dasu Aunty Samina duk tare Ra'uf kuwa yayi sa'a motarsa su Rufaida suka hau da Mukhtar yake tuka motar Ra'uf da ya katse shirun motar da fadin
" Da alama Mukhtar kurame muka dauko a motar mu"
"Nima nafi tunanin hakan kuwa" Mukhtar ya karasa zancen yana maida hankalunsa ga tuki
"Saboda me" Nasiba da Zainab suka fa'da itako Rufaida shiru tayi da kwata kwata bata sakewa a motar "
"Yawwa to kudai naji magana ku kun fita daga jerin kurame,saura 'yar uwarku"Ra'uf ya karasa zancen yana sake kallon Rufaida ta gilashi
Nasiba da ta gano nufinsa ta soma fadin
" oh Rufee zakace mana,tana magana sai dai kasan ita sarauniya ce bata magana da kuyanginta matukar bata kama ba amma tunda Sarkin yayi magana to itama ba shakka zatayi"
"Hmm haka dai kikace banga alamun zata yi ba,mu muke kidanmu na lura muke rawarmu ni na aje sarautar a yau amma ita na lura ba haka bane anata fannin"
Wayar Nasiba da tayi kara yasata kin basa amsa ta duba wayarta ganin mai kiran AbdulRafi ne yasata saurin 'dagawa AbdulRafi yanajin Nasiba ta 'daga ya fara da
"Nasiba ina kuke ne kunsan fa yau zamu koma keda Rufaida muke jira"
"Yaya AbdulRafi muntaho kawo amarya Samiha,muna tare da Rufaida ma"
"Amma buku kyautamin ba kunsan zan jiraku"
"Wallahi Momy ce tace mutaho kai amaryar daganan saimu taho dasu Aunty Samina"
Tsaki AbdulRafi yayi ya katse Wayar dan bakaramin lokaci suka bata musu ba da tuni sun manta sun bar sokoto dan sunyi dasu tare zasu koma baisan hardasu aka tafi kai amaryarba dole yasa shida Samir suka yi haramar komawa kano
Nasiba ce ta dubi Rufaida ta soma fadin
"Kin jini da Yayanku ko"
"Eh au ke ba yayanki bane"
"Sorry sister (yar uwa)yayanane mana"
Daganan Rufaida tayi shiru har suka karaso Kaduna bata sake cewa komai ba sai dai Nasiba da Zainab da suke magana tare da Ra'uf ke sa baki a wata firar yana kuma cigaba da aikin kallon Rufaida ta madubi a haka suka karaso Kaduna Isah Kaita Road aka wuce dasu da a unguwar gidan Samiha yake gidan yayi kyau sosai an zuba kudi komai yayi sosai suna isa gidan Samihan suka firfito daga motocin zuwa cikin gidan da mortar amarya aka wuce da ita gidan sirikanta inda daganan sai akawota gidanta Ra'uf ne ya tsaida Nasiba dan ya fahimci tafi sanin Rufaida akan Zainab ita yakeso ta shigar dashi gurinta saida suka gama shiga dakunan gidan da kitchen gidan da yakasance plat saidai yayi kyau dukda babu dorin benen iyayen Samiha ma sunyi kokari sun kashe mata dukiya sosai part biyu ne a gidan nata dana Ahmad din nan suka dawo falo suka zauna suna yaba kyan gidan Ahmad yayi kokari sosai
*****
Ra'uf da farin ciki a ransa suka baro gidan shida mukhtar dan ya samu Nasiba ta bashi lambarta zai kirata ta hadashi da Rufaida suna isa gida kai tsaye ta kofar baya ya shige falo saboda mutane dansu a lokacin suke shagalin bikinsu danma akwai 'yan bangaren Kawu Saleh da yawanci daudalar bikin acan sukeyi kai tsaye upstairs (saman bene) ya haye yana takaicin yadda dakinsu a gidan kakanninsu ya kasance a cikin gidan banda akwai dalilin shigowarsa gidan ba abinda zai kawo sama da gidan Abba Hamisu zai bi su Ahmad
"Oyoyo Yaya ashe kun iso"jin maganar da turanci yasashi gane mai maganar kasancewar yasan wacece Safiyya ce duk tafi sauran 'yan uwansa sonyin turanci ko indiyanci dan ita bata damu da yin yaran Hausa ba dukda kasancewarsa yaransu shiyasama Hajiya Hanne ta kara kin Sofin dan ita batasan iyayi dukda yadda sofin me girmamata juyowa yayi ya dubeta da murmushi fuskarsa yana fadin
"Yawwa Sofee yaushe kikazo gidan"
Bata rai Safiyya tayi
"Amma Yaya kasan banasan acemin Sofee,yanzu Ammi ce ta kirani nazo gaisheda su Hajiya"
Dariya ta basa sai ya gumtse abarsa kar kanwar tasa taji haushi
"Yi hakuri Safee, amma Hajiya bata yi miki fa'da ba ko?"
"Eh batamin ba ai banmata turanci ba kasan Hajiya shine bataso,da zan fito ma cemin tayi har zan tafi"
"Yawwa naji dadi,yanzu ina zaki kuma"
"Gidan Aunty Malika zan koma"
"OK ki jirani a mota zan dauko wani abu a daki na zamu wuce gidan Abba Hamisu,saimu saukeki a can ita Aunty Malikan batazo bane har yanzu
"Tazo takoma yanzu shirin,tafiya Dinner anjima takoma yi"
"Ok" ya karasa fadin haka yana karasa wa kofar dakinsa ya shige ita kuma Safiyya ta karasa waje ta isa mota ta shiga suna fira da Mukhtar da haka yazo ya samesu suka bar gidan a motane yake bata labarin Rufaida da ya nuna mata hotonta itada Samiha da sukayi a sokoto da wanda sukayi tare
"Wow Yaya ai wannan matar taka ko a indiya samunta sai antona tana da kyau,hala 'yar uwar amaryar Yaya Ahmad ce ko"
Murmushi yayi
"Eh cousins sister din race"
"Ah shiyasa naga suna kama"
"Baki cemin tayi miki ba"
"Haba Yaya wazaiga wannan yace bata masa ba"
"To shikenan naji dadi ko kanwata"
Da haka dai suka cigaba da fira yana sanarmata anjima zai hadasu a waya har kofar gidan Aunty Malika suka karasar da ita suka wuce suku ma
******
"Nasiba Allah kina takuramin kan maganar mutumin nan" Rufaida ta fada haka tana kokarin zira rigar material dinsu da suke shirin tafiya dinner da za'ayi da magriba za'a fara tafiya
"Ba wani takura kinaso kina kaiwa kasuwa,ni amshi wayar yace zai kuma kira yanzu" Nasiba ta mikamata wayar tabar dakin tana fita Ra'uf ya kira ta saida takusa tsinkewa ta daga
Ajiyar zuciya Ra'uf ya sauke jin ta daga wayar
"Gimbiya nayi zaton bazaki daga ba"
Murmushi tayi tana
"Saikace kayimin laifi"
"Hmm to bansan laifin ba saidai kona zuciyata data kamu da sonki lokaci guda,idanma laifin ne to itace tayi"
"A'a ni bance ba"
Murmusawa yayi ya Dora da cewa
"Rufaida da gaske nake ina sonki jira nake na koma Kano naje na gabatar da kaina gurin Abba daganan sai su Dady na suzo so nake kafin nakoma Delhi asa ranar bikinmu"
Batada yadda zatayi dashi haka ta cigaba da biye masa tana dan amsa masa maganarsa wadda kusan daga eh sai a'a itace maganarta haka sukayi sallama yace zai zo daukarsu anjima fita Rufaida tayi falon gidan Samiha da mai kwalliya tazo yi musu da Ahmad ya daukomusu"
*SADIYA KHALILULLAH*🖊*JININMU DAYA*
BY SADIYA IBRAHIM KHALIL(SADIYA KHALIL)
*TUNATARWA DUK ABINDA KA RUBUTA TO KODA KA GOGE BAI GOGE BA A LITTAFINKA BA MUYI KOKARIN RUBUTA ABINDA ZAI ANFANE MU DUNIYA DA LAHIRA,MATA MUJI TSORON ALLAH KI DINGA TUNANI AKAN MIJIN NOVEL (LITTAFIN HAUSA)BAFA SAMUNSA AKE BA KARKIJI ANCE KYAKYKYAWA MAI KUDI MAI IYA SOYAYYA KI MAI ILIMI KI ZACI ZAKI SAMU IRINSHI KO KIMAIDA MIJINKI IRINSHI ,MUMA MARUBUTAN KI FAHIMCI YA DANGANTA DA IRIN LITTAFIN DA MUKE DA WANNAN WA'AZANTARWA DA NUSARWA KIKESON LITTAFINKI YA BAYAR SHIYASA AKE SA HAKA AMMA KI SA ARANKI MIJINKI KO WANDA ZAKI AURA YA FIYE MIKI MIJIN NOVEL DARI BISA DARI SHI MIJIN NOVEL KI DAUKA DALILIN KASANCEWARSA KYAKKYAWA MAI KUDI MAI ILIMI MAI IYA SOYAYYA DAN LITTAFI YAYI ARMASHI AKE SAWA KUMA KI DINGA DAUKA DUK DA HAKAN KUDIN NASA DA ILIMIN NASA DA KYANSA DA IYA SOYAYYARSA YANADA HALI MARA KYAU DOMIN DAN ADAM TARA YAKE BAI CIKA GOMA BA YANAYIN SAKON DA AKESON A ISAR NE YAKESA AKI SA WANCEN HALIN NASA MARA KYAU,AMMA BADAN A DORAWA YAN MATA DA SAMARI SAMUN MACEN NOVEL BA KO MIJIN NOVEL,DUKDA ANA SAMUN MAI KUDI MAI ILIMI MAI KYAU IDAN DA RABO MACE KUGA TA AURESA AMMA KISA A RANKI KOMAI RABO NE,SUMA YAWANCI MATAN NOVEL DIN SAIDA SUKA CI WUYA SUKA SAMESA AMMA KARKI SAWA RANKI SAMUN WANNAN MIJIN KO SON KI CEWA MIJINKI LALLE SAIYA ZAMA MIJIN NOVEL SAIDAI IDAN KINSAMU DAMA ALLAH YA KADDARAMIKI HAKA AMMA DAI KI FAHIMCI DOLE KISA MESA DA WANI HALI DA BAKYASO MIJINKI YAKASANCE DASHI,AMMA DAI SHAWARA GAREMU MAZA DA MATA MU CIRE WANNAN SHIRMEN NA SAMUN MIJIN NOVEL KO MACEN NOVEL WALLAHI DUK ZANCEN BANZANE MUMA MARUBUTAN BA IRINSU MUKE RAYUWA DA SUBA RAYUWAR WASU MUKE RUBUTAWA BA TAMU BA FADAKARWA MUKE AMMA TA JAN FADAKARWAR HAR ZUWA KARSHEN MASU AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN LITTAFIN MARA KYAU KO MASU HAKURI IRIN NA MUTANEN LITTAFI HAR ZUWA KARSHENSU MAI KYAU KO MUMMUNA KUNGA ANAN SAI MU GYARA RAYUWARMU IDAN MUNA AIKATA MAKAMANCIN AIKINSU MARA KYAU IDAN KUMA MUNA MAI KYAU SAIMU SAKE DAGE DAMTSE ,"DAMA DAGA RAYUWAR WASU MUKE 'DAUKAR DARASIN TAMU*
*NAGODE WA MASU COMMENT DA SHARE DA VOTE,MUSAMMAN GROUP DIN JININMU DAYA FAN'S,FATI MANSUR TA GROUP DIN JININMU DAYA NAGA COMMENT DINKI DUK SHAFINKU NE WANNAN KUYI YADDA KUKESO DASHI MASOYAN SADIYA KHALIL*
PAGE 23
7pm
motoci suka zo daukarsu zuwa wajen da za'ayi dinner din
Su Rufaida sunyi kyau sosai cikin ankon material sky blue da touch din baki da browan colour(ruwan sararin samaniya da kwalliyar baki da ruwan toka) sai mayafansu farare ya haska su sunyi uka fito kofar gidan Samiha da Ra'uf ya aje motarsa ya kirasu su fito ya karaso da jakunkunansu na kaya a hannunsu da zasu kwana gidan kanwar mahaifin Rufaida Aunty Zainab da take aure anan Kaduna tana zaune a Bayajidda street ita da mijinta da yaronta 'daya.
Ra'uf shima yayi kyau cikin shaddarsa Golden colour yake yasha malum malum dinsa kamar shine angon shine kadai a motar Mukhtar yana can shi zaikaisu Momy Hannatu wajen Dinner din wajen motar suka karaso suka yi masa sallama ya amsa musu ya komar da kansa cikin motar da tunda suka taho yake kallo Rufaida da yake ji sonta yana kara yawa a tare dashi har mamakin kansa yake da farat daya sonta ya shigesa koda yake babu mamaki da ikon Allah kofar motar ya bude musu suka shiga yaja yana yi musu tsiyar sun shanyasa tuntuni yake jiransu
wajen Dinner din suka karasa inda suka bar jakunkunansu motar Ra'uf kasancewar a motar zasu koma suka bada pass dinsu suka shiga ciki sun haska a gurin sosai kuma gurin a tsare yake kujerun da aka jera na karfe da aka jera a hall din suka zauna akansu da aka jera musu abinci kala kala da lemuka akan babban teburin jin abinci da kujeru suka zagaye teburin cikin tsari akeyin komai
Ra'uf ne ya ja Husna da Safiyya su gaisa da Rufaida da suma suke cikin ankonsu golden colour da kalar ce ankon dangin Ahmad maza da mata gurinta suka karasa da Ra'uf yayi musu jagora cikin mutuntawa suka gaisa kamar ta sansu yaji dadin yadda Rufaida ta mutunta 'yan uwansa suma inda suke zaune suka koma suna koda Rufaida kuma suna fadin kyawunta Ra'uf shima cikin 'yan uwansa maza ya koma bayaso taga kamar yana takuramata basu jima a gurin ba aka kira Rufaida ta ba da labarin yadda amarya takasance ba dan tasaba ba tayi magana da harshen hausa cikin kyawawan lafuza da haka takoma da mutane suka fara maganarta Aunty Malika da su Husna suka nuna mata itace budurwar da Ra'uf keso sosai taji ta shiga ranta har daga kallon farko data yi mata har qaguwa tayi a tashi Dinner din ta je gida ta fadawa Ammin Ra'uf yadda surikartasu take dan kafin a kira Rufaida su Momy Asma'un suka bar wajen Mukhtar ya daukesu a mota zuwa gida.
Shima Ra'uf da yake hango sanda take maganganun nata cikin kyawun lafazi sai ya qara jin Rufaidan a ransa itace matar da ya dade yana addu'ar samun irinta tabbas ta hada komai na irin matar da yakeson takasance abokiyar rayuwarsa addu'a daya yake Allah yasa takasance mata a garesa.
Sai da aka yi hotuna da amarya da ango sannan aka fara kokarin tashi daga Dinner din.
9pm aka tashi daga Dinner din aka fara dibar mutane zuwa gida a motoci
*********
"Nasiba yanzu ina zankaiku naji kince min ba gidan amarya zaku kwana ba"
Ra'uf yayi furucin da yake kokarin tada motarsa da yanzu shike tuka motartasa da kansa.
"Eh gidan Auntyn su Rufaida zamu je a Bayajidda street take"
"Ok kice Auntynmu ba"
yayi maganar yana Jan motarsa ba tareda ya kuma magana ba.
Da taimakon Rufaida da take masa kwatance ya kaisu har kofar gidan gidanta maikyau da karamin gate dinsa ,yayi parking din motarsa suka fito su Hudu Rufaida,Nasiba,Zainab,Iklima
Yatsaida Rufaida daya fito daga motar
"Zanje gida zan kiraki wayar Nasiba,ki gaida Aunty idan batayi barci ba idan na kira zaki hadamu"
"To Allah ya kaika lafiya"
"Amin nagode sarauniyar mata"
Da haka tabar gurin tabi bayansu Nasiba
Shima murmushi yayi yabi bayanta da kallo yayi waajen motarsa yaja yabar gurin
"Yam mata har kungama hirar"
Zainab ta furta haka bayan sun kai kofar gidan Aunty Zainab da suke cewa Aunty da Nasiba ke kokarin kiran Aunty Zainab da Ummi Hauwa'u ta turo musu Number dinta.
"Zee banasan wulakanci..."
Wake wulakancin Aunty Zainab da taji Rufaida na fadar haka da ta fito bude musu kofar gate din,shiga sukayi ta rufo kofar"
"Wallahi Aunty Zee ce daga mun gaisa da wani wanda ya kawomu nan yanzu take min maganarsa"
Aunty ta 'dan ha'de rai kana ta furta
"Ni banasan kula kulan nan na abokan anguna ya wanci dukda matansu wasu kuma da wadanda zasu aura ko idan sunada auran da wadanda zasu kara bakuba sakarci ne yawanci yakesa kawayen amarya soyayya da abokan ango gurin bikin kawarsu har su amince musu kuma yawanci da angama bikin zasu manta da yarinyar idan ta zurfafa ita zata jiyo kusan mutuncin kanku" tana maganar tana kokarin tura kofar falon su Rufaida suna biye da ita
Jin tayi shiru yasa Nasiba tayi caraf ta karfe zancen
"Aunty saurayin Rufaida ne abokin Ahmad ne,tun kafin biki suka ha'du da shi da bikin ne soyayyarsu ta kara kulluwa"
Murmushi Aunty Zainab tayi ranta tana yiwa 'yar dan uwan nata Allah yasa na kirki ne ya kuma tabbatar musu da alkhairi
shiga cikin falon sukayi duk suka jefar da jakarsu a saman kujerar falon suna maida gajiya
Rufaida tana ganin Asad 'dan Aunty Zainab a falo ta daukesa tana masa wasa
Ruwa da abinci ta kawo musu suka ci daganan suka gaishe da Aunty Zainab da take musu tsiyar busu fadamata Dinner din ba aida taje wayar Nasiba ce tayi kara ta mika hannu inda ta aje ta ta duba mai kiran ganin Ra"uf ne yasata mikawa Rufaidha wayar saida sukayi yar fira yace taba Aunty su gaisa sosai Aunty zainab taji Ra'uf ya kwanta mata arai nan ta yi wa Rufaida addua a ranta Allah yasa da gaske yake da aure yazo gareta ya kuma kareta da fadawa tarkon mayaudara suna gama wayar Aunty Zainab tayi zaman dirshan suna fira kamar duka tasansu alhalin Nasiba kawai ta sani bayan Rufaidan da haka mijinta Haris ya shigo ya samesu sannu da zuwa suka masa tare da gaishesa ya amsa fuska sake kana yace wa Rufaida
"Ansha Dinner baki gayyace mamarki Ba bare nasa ran zaki gayyace ni ,da mukayi waya da Yaya Aliyu da Mamarku suke sanarda mu zaku zo anjima ku Kwana anan yanzu kuna wajen dinner"
"Uncle Haris ayimin afuwa yanzu Aunty taga ma mana maganar walllahi mantawa nayi kuma kaga bamu baro Sokoto da wuri ba"
"Zaki tuna ne ai Allah ya sanya Alkhairi"
Ya na gama furta haka yabar wajen da Asad a hannunsa da yana shigowa ya daukesa shigewa ciki yayi Aunty Zainab tami ke tabi bayansa
Da Amin suka bi addu'arsa suka cigaba da fira
Rufaida ta dubi Nasiba ta fara magana
"Wai niko Nasiba ina duriyar Sir Abdul-Rahman"
"Ke dai bari mun rabu da waya tun waccen ranar amma bari nakira mana shi mugaisa"
Ta karashe maganar tana mika hannunta inda ta aje wayarta ta dannan number din Abdul-Rahman Ringing biyu tayi ta katse baifi sakan biyu ba wayarta tayi kara ta duba taga Abdul-Rahman ne ta 'daga ta kunna karar wayar da zolaya ya fara yana
"Amare to ya hidindimun biki"
"Sir Alhamdulillah,ina yini"
"Lafiya lau ya biki"
"Alhamdulillah sir"
"Ina Amarya"
"Wallahi Sir tana gidanta yau aka kawota mukuma muna gidan Kanwar Abbansu Rufaida sai zuwa gobe zamu dawo Kano insha Allah"
"To Allah ya tabbatar da Alkhairi ya kaimu naku,ina Rufaidan da take bata"
"Amin"
Nasiba ta mikawa Rufaida waya suka gaisa sukayi sallama.
Aunty Zainab ta dawo falon tace su koma daki suyi shirin kwanciya.
*SADIYA KHALILULLAH🖊️*️*JININMU 'DAYA*
*BY SADIYA IBRAHIM KHALIL*
*(SADIYA KHALIL)*
*PAGE 24*
*WANNAN SHAFIN NAKUNE SADIYA KHALIL CONVERSATION ROOM,DA JININMU 'DAYA FAN'S GASHINAN KUYI YADDA KUKESO DASHI MASU COMMENT KU CIGABA DA COMMENT'S KU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAHIN🥰🥰SADIYA KHALIL NAGODIYA*
*PAGE 24*
***
9am
Suka gama shirinsu suka fito kofar gate din gidan da Ra'uf yazo yake jiransu su fito ya kaisu gidan amarya Aunty Zainab itada mijinta Haris har kofar gida sukayi musu rakiya Ra'uf da ya fito ya gaishesu cikin girmamawa da Aunty Zainab taji kunya sosai tunda ya girmeta kuma taji ya kwanta mata a rai haka suka shiga mota ya jasu ran Aunty Zainab ba dadi bataso tafiyarsu ba.
Ra'uf suka gaisar ya amsa yana tada motarsa
Saida suka soma tafiya ya cewa Nasiba da take gaban motar
"Yana ji Rufee Sarauniyar mata shiru kodai kun mata laifi ne"
Nasiba ta juya ta kalleta daga bisani ta furta
"Ko 'daya ba laifin da aka mata kasan miskilace budurwar taka,saika riqa hakuri"
Dariya yayi ya furta
"Baruwana keda kawarki kuma tana jinki"
"Ai tasan hakane"
Rufaida da tana jinsu tayi banza dasu dan Nasiba akwai surutu sunsan halinta
Basu jima suna tafiya ba suka karasa Isa kaita Road suka shige kwanar gidan Samiha saida Ra'uf ya fita ya bude gate din gidan kasancewar basuda mai gadi kafin yakoma yaja motar zuwa cikin gidan a harabar gidan suka tarar da su Aunty Samina da har sun shirya tafiya Ahmad ya kira Drivernsu zai maidasu gida Sokoto da Samiha harta fara kuka na tafiyarsu kamar wata yarinyar goye bayan basu duka zasu tafi a lokacinba
Sai da suka gaisa kafin Yaya Balki ta furta
"Ku kuma sai yanzu zaku dawo kun daka tasu Rufaida da ita Rufaida a gida take"
"Mama bahaka bane abokin ango ne baizo da wuri ba"Zainab tayi maganar da sigar tsokana
"Ba wani laifinsa basai kun shirya zaku kirasa ba,ku wuce ku shiga mota keda Iklima"
Ra'uf