Showing 15001 words to 18000 words out of 86533 words

Chapter 6 - JININMU DAYA HAUSA NOVEL

muka ha'du dashi jiya ke kinganshi kuwa kyakkyawa kalar namijin da nakeson aure dogo kyakkyawa"tsaki Rufaida tayi tana dokin jin labari amma Samihan ta tsaya shirmen banza tace"ni fadamin a'ina kuka ha'du yimin bayani naji kinki yimin bayani yadda zan gane "Samiha tace " aike bakya cin ribar zance dama sai kin nuna kin gaji"Rufaida tace"naji dai nidai fa'damin" Samiha tace"na fito Momy ta aikeni gidan su Fahat Hassan na nan ajin"Rufaida tace"Eh naji dai na gane jeki zancenki"Samiha tace"gidan Aunty Ummi na bayani gidanmu a kofar gidan muka ha'du ya tsaidani da kamar bazan tsayaba sai naga baikamata na masa hakaba tunda naga Hanif din Aunty Ummi a hannunsa ,shine na tsaya,muka gaisa,Har yake shaidamin yana sona ganin bankulasa ba shine ya bini gidansu Fahat yacemin Auny Ummi cousin dinsa ce Baban Aunty Ummi da mamarshi wa da 'kanwa ne ,yace yana ganina a unguwar idan yazo yace har a gidan Auny Ummi ya taba ganina ni dake,danshi tunaninsa mu 'yan biyu ne ni dake amma zai shiga mota ya tayar zai fitamu shiyasa bamu gaisa ba dan alokacin mun shiga gidannevgaskiya gayen nan yayi a kasar waje UK yayi karatunsa yace min zaizo gidanmu yau idan ya shigo unguwar da wuri dan yace bays rabo da unguwar"Rufaida tayi murmushi tace "kai amma kawata na tayaki murna Allah ya tabbatar da akkhairi,saidai kibi a hankali karki cika nuna kinasansa ,kuma karki sakankance dashi sosai,ki rika abu da wayewarki" Samiha tace "haka ne " year uwata amma duk ina kikasan wannan sirrikan soyayyar keda bakyayi?i"Rufaida tace"a gurin su Nasiba kinmanta natafi yajin aiki bencinki"Nasiba Shehu Abubakar India batun soyayyah ne ko a ajin azo gurinta yanzu haka ma bikinta za'ayi"Samiha tayi dariya danta tuna sun ta'ba wani fa'da da Rufaida tabar mata bencin Hauwa'u Umar ta koma Samiha tace "kai Rufaida aji tsoron Allah bakya mantuwa kinsan da yanzu ne bazanyi fa'da kan yoghurt ba" Rufaida tace"naga alama fa nidai na baki shawara kibi a hankali ki tsare mutuncinki a gurinshi karki cika nunamasa sosai"Samiha tace"to shikenan kawata,Amma nifa koshi zan aura tare za'ayi bikinmu nidake banaso nayi aure nabark"Dariya maganar taba Rufaida ma tace"banda abin Samiha ai da Allah nima yakawomin kusan hadawa ma za'ayi,yanzu dai Da yaya Saudat za'a ha'daku tsaki Samiha tayi tace "kewai Yaya Saudat zan zauna jira inama saurayin nata ya ta'ba zuwa gidan mu kurum daga haduwa a bikinsu Yaya Samina tace lallai shi take so,ke kin ganshi kuwa kato dashi da gani ma ya fara tsufa" Rufaida tace"kai Samiha banda sharri fa?"Samiha tace"Allah da gaske nake dandai bakije Sokoto bikinba da kinganshi kato tsawo da kiba"Rufaida tace"koma dai ya yake ita tanasan kayanta bare ma dai nasan bahaka bane"Samiha tace"au shigarwa Yaya Saudat yau kike kuma"murmushi Rufaida tayi tace"Eh mana"da haka dai suka kara taba hira har aka dawo break da sabon malaminsu ya shigo Sir AbdurRahman ganin sabon zuwane yasa duk ajin akayi shiru sai yayi tanbaya idan sun sani su bashi amsa don basa so daga zuwan AbdurRahman ya fara fahimtar halinsu gasu Nasiba sun gwangwadamusu cewa shi 'dan babban gidane shiyasa suka fara ganin girmanshi dan Khalid Bashar Majiya ba laifi kam yayi suna a cikin garin Kano.

SADIYA KHALI✍🏽*JININMU DAYA*
By Sadiya Ibrahim Khaliy(Sadiya Khaliy)

11

Rufaida Aliyu Bukar Hafaffiyar garin Zariya ce da aiki ya dawo da mahaifinta Aliyu Bukar cikin garin Kano yana aiki a babbar makaranta wato jami'ar Bayero University dake Kano wato BUK inda yake zaune a gidansa mallakin kansa dake Rijiyar Zaki shida matarsa 'daya wato Hauwa'u da suke da yaransu shida AbdurRafi shine babba sai Rufaida mai bi masa sai AbdurRashid,Rumaisa,Rafi'a,Ra'is shine karaminsu.

Samiha Hashim Sarki 'kawar Rufaida ce tun daga primary har zuwa Secondary da suke tafiya tare aji 'daya benci 'daya dalili mai karfi da ya jawo amintarsu harta zama sun zama kamar 'yan uwa hatta iyayensu wasu 'yan makarantar tasu ma 'daukarsu 'yan uwa ne Samiha hafaffiyar garin Sokoto ce aiki ya maido mahaifinsu Kano Unguwar Nasarawa GRA da mahaifin nasu yake kwararran likita a asibitin Nasarawa matarsa 'daya Hajiya Maryam da yaranta Samira,Samina da sukayi aure,Samir,Saudat,Samiha,Samin,Samima.da a yanzu haka Hajiya Maryam ta aurar da 'ya'ya biyu Samira da Samina kowacce da 'danta 'daya,Sai Samir da yake aboki ga AbdurRafi da suke babbar makaranta Jami' a Yusuf Maitama Sule Northwest dake nan Kano wannan kenan

Samiha da take kokarin sa'ba Jakarta a baya ta dubi Rufaida tace "malama ba kyaji antashi kuma kinsan yau juma'a a gidanku zanyi hutun karshen mako" Rufaida da murna batasan sanda tazari jakarta ba saboda murna Aminiyarta zatayi hutun karshen mako a gidansu mikewa tayi tana cewa"Nifa bansan dagaske kike ba"Samiha ta harareta tace"aikema kinsan bana miki karya irin wannan"da haka suka fito ajin da suka hadu da sauran 'yan class dinsu suna firar yadda Sir AbdurRahman ya iya koyarwa suna gane lesson dinshi da shine malaminsu na karshen period yau da wannan firar suka fito zuwa kofar makarantar inda suka hangi motar Abbansu Rufaida dasu yake jira suka karasa sunayiwa abokan tafiyartasu sallama"sauran 'kannen Rufaida har sun shige bayan mota su Rufaida gaban mota suka shige Abba da yake kokarin tada motarsa ya kalli Samiha da take gaishesa ya amsa yacigaba da cewa"wato Samiha mungane saboda kawarki kike zuwa gidanmu duk hutun karshen mako kike yi mana acan?"murmushi Samiha tayi kawai dan tagane Abba ya gano saboda Rufaida take zuwa gidan Abban hutun karshen makon dan ita tana matukar son kawarta da a yanzu take jin Rufaida kamar 'yar uwarta ta jini dan ko Saudat da Samihar ke binta bata saba da ita kamar Rufaida ba ,Samiha ta canza maganar tace "Abba ya maganar Jamb 'din namu" Abba da ya maida hankalinsa ga tuki yace "oh Samiha anfara ne"Rufaida anan tasa baki tace" Wallahi Abba ba'afara ba Samihan ce batada hakuri kofa yau saida ta tanbayi wani malaminmu" Samiha tace" eh mana dole kice banda hakuri tunda ke bakyasan cigaba da karatun yanzu idan bama tunawa Abba har a gama bamuyi ba"Rufaida tace"ba wani nan wallahi ai kinsan Abba baya mantuwa a harkar karatu barema harda Yaya Saudat za'ayi kinsan tunda tayi candy bazai manta ba,ke dai azalzalar kice,"Abba murmushi kawai yake yana jin firar tasu yadda sukeyi wanima sai ya rantse ya da kanwa ne ko 'yan biyu saboda halayyoyinsu da sukazo daya a fisgema har yanayi suke da juna yanason wannan abotar yaran nasa da ta zama yan uwantaka bama gasu ba harga su iyayensu sun hada aminci tsakaninsu kai kace 'yan uwa ne a yanzu haka idan ba har an baka labari ba,Abba yana saukesu d ,yace zaije gurin abokinshi yaje ya dawo su fa'dawa Umminsu a dawo lafiya suka yi masa ya amsa da amin yasakan motarsa yabar gidan su kuma suka shige cikin gidan a fall suka sami Ummi suka yi mata sannu da gida Ra'is mai shekaru biyu yana ganin Samiha yayi gunta da yasaba da ita saboda yadda take masa wasa daukar Ra'is 'din tayi ta haye dashi sama tana mass wasa yana dariya Samiha kaya kawai ta canza ana Rufaida dan girmansu daya hakama kayan sawarsu iri daya ne yawanci saboda yadda iyayensu suke aminta sosai kaya ma kusan tare suke dinka musu Rufaida data fito daga bandaki da towel jikinta ta watso ruwa ta kalli Samiha tace "ya haka ba zakiyi wanka bane" Samiha ta dafe cikinta tace"yunwa nakeji nayi anjima "Rufaida tace" ba wani anjima ,bakyasan yin wanka sai dole kike 'daya badan kinso ba haka Ahmad 'din zai aureki ki bakyason yin wanka wallahi ya daukeki kazama"da Rufaida da tasan sunan Ahmad saboda labarinshi da Samiha take basu nashi kullum indai sun ha'du a makaranta to indai kana ajinsu sai Kasan labarin Ahmad saurayin Samiha a bakin Samihar "Samiha tace to"yi maza ki fadamasa"Samiha ta fice tana jiyo dariyar Rufaida

Samihan kai tsaye kitchen ta nufa ta samo abincin rana da miya taliya kawai tagama sai miya da take kan wuta da shigowarsu Ummi ta zuba markadan kayan miyan gurin datasan ana aje ragowar miya ta bude ta diba ta fito kai tsaye babban falo ta karasa bayan fitowarta kitchen din da ta samu AbdurRafi shi ka'dai ta masa sallama AbdurRafi ya amsa mata ya maida dubensa ga kallon ball din daya kori kannensa a falon yanayi ganin ancanza masa tasha ya juyo ya 'dan kalleta da ta zauna a kujerar dake gefen tasa ta tankwashe kafafunta akan kujerar ga remote tana dannawa tana lalubo tashar da takesan kallo yace cikin ha'de rai " waike Samiha ina kallo ya zaki canzamin tasha"Samiha tace"ai kaine Yaya AbdurRafi ko gaishe da nayi kaki amsawa kana can hankalinka yana kan kallon ball"AvdurRafi yace"ke Samiha banafa son karya a ina kika gaishe ni sallama kawai naji kinyi,ke dai kawai kinzo ki takurawa mutane indai kikazo gidan mutum bashida kata'bus"Samiha tace"kai Yaya AbdurRafi gaskiya bakayimin shaida maikyau ba amma bakomai nakusa daina zuwa ai"tsaki AbdurRafi yayi yace"yaushe ai sai dai in anyiwa wadda kike zuwa gunta aure ko an yimiki"Samiha tace"kai nifa Yaya AbdurRafi kadaina maganar idan munyi aure zamu rabu da Rufaida ga gida ga gida zamu zauna"AbdurRafi yace"Ku auri miji 'daya kawai zaifi"Samiha tace"kai Yaya"AbdurRafi yace"eh mana zaifi ai"Samiha ta canza firar da cewa "wai niko Yaya Rufaida ta baka labarin wani saban malaminmu da kuke kama yazo TP da ake turo masu Degree?" Tsaki AbdurRafi yayi yace "ke nifa kinga banasan shirme wallahi ni ka'dai Ummi ta haifa kuma ni ni ka'dai ne bada wanda nake kama a duniyar nan ma gaba 'daya kawai kuje Ku jajubo wani bakusan shi waye ba kuce ina kama dashi?" Samiha tace"haba Yaya AbdurRafi wannan dogon turanci haka daga nace kana kama da wani Allah ya baka hakuri,kuma ka masan shi waye 'dan Khalid Bashar ne" AbdurRafi yace"ke nifa Samiha ki dainamin maganar shi banaso,dama dan haka kikashemin kallon ball din danake"Samiha tace"Allah ya baka hakuri,amma nidai Allah naga kamarku"AbdurRafi ya mike yace"sai kiyi tayi ni kinga tafiya tama yayi gaba ya fara tafiya"Samiha da taga yana kokarin ficewa a falon da taga bayaso ace yana kama da kowa ta tsokanesa tana cewa "Yaya AbdurRafi Allah kuna matukar kama" murmushin mugunta yayi yana tuna abinda zai mata ya karasa ficewa daga falon gaba daya"Samiha ta bishi da dariya Ummi data shigo falon tana lallashin Ra'is da yake kuka taji Samiha na dariya tace"dariyar me kuma kike kuma kike kinje kin bawa yara yaro na sun yarmin dashi shine kike dariya ko?"Samiha tace"Ayya Ummi wallahi Rumaisa ce ta anshe shi da muka hau sama"Ummi Hauwa'u tace"to gashinan dai kin basu yarona sunyi fa'da da Rafi'a sunyarmin dashi,na 'daukama dariyar kike masa"Samiha ta anshi Ra'uf a hannun Ummi Hauwa'u tana lallashinsa tace"Haba Ummi ya kinsan nida Ra'is da amana,Yaya AbdurRafi nakewa dariya saboda nace yana kama da wani malaminmu yake jin haushi bayaso ace yana kama da wani"Ummi Hauwa'u tace"au wai saboda ance yana kama da wani yaji haushin Allah ya kyauta"Samiha tace"Amin dai Ummi" Samihan ta fara lomar abincinta data zubo tana bawa Ra'is Ummi ta wuce kitchen ta cigaba da aikin abincin da take Abba Aliyu ne yashigo gidan da motarsa ganin AbdurRafi ya budemasa gate "yace ya shigo ya shirya su tafi masallaci kasancewar yau Juma'ah yana shigowa falon yayi sallama,Samiha ta amsa masa takuma ce "Abba sannu da zuwa yace" yawwa Samiha ina sauran mutanan gidan" Samiha tace"Suna ciki Ummi kuma na kitchen"Ra'is da yaga Abbansu ya sauka daga hannu Samiha ya tafi gurin Abban nasu,Abba Aliyu ya daukesa yana cewa"nifa Ra'is shirin masallaci zanyi amma bari na tafi dakai na bawa ko Rufaida kai ne ko Rumaisa tunda kunfara batawa da yayartaka" murmushi Samiha tayi kawai ta harari Ra'is da haka Abba Aliyu yayi saman bene dashi 'dakinsu AvdurRashid kai tsaye Abba ya shiga yace ma AbdurRashid yayi shirin masallaci ya bawa Rumaisa Ra'is daya sameta a falon saman AbdurRashid yana fitowa daga dakinsu saboda tafiya masallaci yaga Samiha a falo da kwanon abinci a kan teburin tsakiyar falo tagama ci tana lashe hannu yace" uwar ci 'yanci kawai"Samiha tace"naji dai da ulcer ta kama nifa"AbdurRashid yace"ba wani aike cinki yayi yawa kuma ci babu kuf kullu jiya i......"jin karar takalmi yasa AbdurRashid kin karasa maganr yamayi had ficewa daga falon kar wani ya shigo yaji yana yiwa Samiha rashin kunya Samiha tace zaka dawo kasame nine mara kunya ganin AbdurRafi ne ya shigo falon ya wuce ko Samiha baikula ba tana kunshe dariyarta ganin wai shi ala dole yayi fushi da ita Rufaida tana zura kaya barci ta haye gado barci ya 'dauketa kasancewar basa taya Ummi abinci da rana saboda makaranta.


SADIYA KHALIY✍🏽*JININMU 'DAYA*♦️
By Sadiya Ibrahim Khaliy💞

Page 12

Sallamar Samir shi ya dawo dasu Rufaida daga cin abincin ranar da suke tare suka amsa gaba 'dayansu Samir ya gaisheda dasu Ummi Hauwa'u da Abba ALIYU sauran yaran suka gaishesa ya amsa yana murmushi Rufaida da bayan gaisuwar tace "lah yaya Samir yau Kaine a tafe a gidanmu hala makuwa kayi" AbdurRashid yace"Nima "yaya Rufaida na dauka makuwa yayi" Samir ya harari AbdurRashid yacewa Rufaida "ke dai bari Rufaida wannan yarinyar ce tasa saurayinta yazo gidanmu kuma tasan ba'anan take weekend" Abba Aliyu da Ummi Hauwa'u suka ce ai dama munsan ba'a aikin banza a kano banda haka yaushe rabon duniya da ayyaraye"Samir yace "wallahi bahaka bane Abba bahaka bane mutumin nawane AbdurRafi shima baya zuwa inda nake tunda aka samu hutu"AbdurRafi yace" kai Samir kaji tsoron Allah zuwa na nawa nayi gidanku"Ummi Hauwa'u tace kanku dai akeji"ta dora da cewa"AbdurRashid jama yayan naka kujera mana ya zauna yaci abinci shima Samir ya zauna yana cewa" Yawwa AbdurRashid"ya dora da cewa Ummi kamar kinsan banci abinci ba Ahmad yazo Momy tace nataso na rakosa gurin Samiha kinganni ma Ummi bako waya bare key din mota a hannu na sai dai idan mutumin nawa zai kaini gida ya fada yana kallon AbdurRafi da yagama yiwa karya"ganin baice komaiba yafara lomar abincinsa da Ummi ta zuba masa,Abba Aliyu yace "Hauwa'u baki tanbayesa ya budema bakon falon baki"Samir yace "Eh Abba na budemasa" Abba Aliyu yace "yawwa Samir ,Hauwa'u azuba ruwa da lemo akaimasa" Ummi Hauwa'u tace to, da haka Abba Aliyu ya cigaba dacin abincinsa"Samiha da take zaune tana ji duk abinda suke fada bata sa baki ba da tunda aka ce mata Ahmad yazo take cin abinci hankalinta raba da rabi ta qagara Abba ya mike taje taga sahibin ran nata,Jin maganar Ummi yasata tsaida tunanin nata da Ummin ke cewa
"Ya haka Samiha ko bakyacine kin koshi kiyi maza ki gama kinga yaron ke yake jira"AbdurRashid yace" Ummi ai dole ma ta koshi ta ci fa 'dazu bandana Yaya Samiha ci gare ta"Ummi tace"AbdurRashid bafa nasan raini kaike kawo abincinne" ya girgiza kai AbdrRafi jin haka yasa sh tuno abinda tayi masa dazu yasa shi cewa"wallahi Ummi Ba Karya AbdurRashid yake ba kifadawa Abba ya karo buhun shinkafa"Ummi ta gallawa AbdurRafi harara,Samiha jin hakan yasata hade rai ta mike ta fara barin falon ta haye sama"Yara ne sukayi dariya Rufaida tace"wa yaran dama kofar guduwa take nema Abba Aliyu da ya gama cin abincinsa ya mike ya bar falon a ransa yana kara jin san iyalensa,da kuma matarsa Hauwa'u ha'ki'ka yayi dacen samun mace tagari, Ummi ta shige kitchen ta shirya kayan da za'a kaiwa Ahmad falon baki ta kira AbdurRashid ya mikamasa Rufaida upstairs saman bene tabi Samiha dakinsu ta tura ta shiga da sallamarta inda ta sami Samiha tanata cacca'ba kwalliya kai kace gidan biki zata"Rufaida tace "Samiha wannan kwalliyar fa harkinyi wankane kinsan dazu fa baki yi ba"
Hararar Rufaida tayi tace"waike Rufaida ni kwado ce kamarki zantayin wanka ina laifi nayi daya tunda nayi da zan tafi makaranta ai ya isa"
Murmushi Rufaida tayi daga bisani tace mata"ai wanka jindadin jiki ne,kuma ai kinsan fa munshawo rana a makaranta,kyaeje gabansa kita warin rana"
Tace"ke ni banshawo wata rana ba,inma nasha haka zan fita,tunda turare yana magani ai"
Rufaida tace "nufinki turare na zan baki ki fesa kin da'de wallahi"
Samiha tace"kwantar da hankalinki nima inada turaren ai"jakar makarantarta dake kan lokar gado Samiha ta zage ta de'bi turare ta feshe jikinta dashi ta bude Sib ta samo mayafi mai girma kalar kayan jikinta ta yafa"
Rufaida da take tsaye tana kallonta Samiha ta kalleta tana bu'de kofa ta kashe mata ido tace"aini ba'ayimin gatse"Rufaida tace" naji kimaza ki tafi kinsan ajan aji ake barin arha,kuma wannan kashe idon ai Yaya Ahmad zaki yiwa"Samiha tace "kuma fa hakane,bari na wuce na tafi said kinzo gaisheshi ko?" Rufaida tace"bafa zanzo ba kigama fa'damin magana"Samiha ta dawo ta dafa Rufaida tace"haba kawata Yar uwata ki taimaka kizo"ganin Samiha zata cigaba da 'batawa kanta lokaci tace"zata zo su gaisa"da haka Samiha ta fice ganin Abba a cikin falon suna hira dasu Samir yasata dan jin kunya ta koma da baya ta tabi ta kitchen zata fita tanan ta wuce Abba Aliyu da idonsa na gun Samihan yayi dariya inda ya tuno halayyar matarsa Hauwa'u tana kama data Samihan amma azamanin baya tunkafin aurensu can yake tunowa sai gashi Rufaida gudan jininta bata biyo cakwakkwayyar Hauwa'unba sai Samiha da babu dangataka ta kusa kota nesa tsakaninsu,Dariyar da Samir keyi ita tadawo da Abba Aliyu daga wancen tunanin nasa"Abba Aliyu ya dubi Samir yace "lafiyarka kuwa Samir" yace "Abba lafiya ta kalau,Samiha ce data ganmu a falo taki wucewa tabi ta kitchen zata wuce tayi arangama da Ummi " murmushi Abba Aliyu yayi yace"kasan yaran suna da kunya duk cakwaikwaiwar Samiha tana da kunya diyartawa"Samir da baice komaiba Dan ya fahimci Abba baisan rashin kunyar da Samiha keyi a gidansu ba akan Ahmad"Abba Aliyu ya tsaida shirun nasa da cewa"Muna magana da Abbanku da muka hadu shekaran jiya yace min yaron ya turo magabantasa to bamu gama maganar ba aka kirani a waya....."Samir yace"Eh wallahi Abba yazo tsaida rana za'ayi Abba yayi bincike akansa baida Matsala babansa shine sabon Commissioner of police a Zariya Road suke da zama"Abba Aliyu da yaji dadin Labarin kamar akan 'diyarsa ya faru ,danshi dama yadda yakeson Rufaida haka yakejin Samiha har aransa baiji bakin ciki ko kyashin wannan labarinba,yace cikin murmushi mai yalwa a fuskarsa"To Masha Allah,ai kaga idan AbdurRafi zai ya tashi tafiya police (Dan sanda)ai bazamusha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login