Showing 21001 words to 24000 words out of 86533 words
kawo kenan,Rafi'a ta shigo cikin motar ta sannan mai napep din shima ya tayar Rufaida tace"kingama shirmen naki kenan,zuwa dake kuma unguwa yayi kai ko zanyi sai an dade mai napep din da yake tu',kinsa yace"haba ke kuwa yayanta fa ta gani take kiransa,kinsan harkar yaro sai ana hakuri ,dukansu ba wanda ya kuma tofa alif itama Rafi'a tsoronta kar takuma wani laifin da za'a daina fita unguwa da ita gaba 'daya suna isa Nasarawa GRA ya shiga Latin Khalid Bashar Majiya ya danyi tafiya a layin kadan ya kuma shiga wata kwana nan ya tsaya ya Rufaida ta mikamasa kudinsa bayan ta fito tace " gashi bamu canji"amsa yayi ya duba aljihunsa ya mika mata canjin yayi gaba Rufaida hannun Rafi'a ta kama tanata mata fada akan suruntunta yayi yawa kofar gate din gidansu Samiha suka tsaya suka kwankwasa mai gadi ya karaso kofar yace"waye"Rufaida tace"baba su Rufaida ne"ya bude kofar jikin gate din da ake wucewa yana cewa "ah'ah yau kuma antuna da zumunci kenan" Rufaida da suka shigo ciki race"ai Baba dama munayi ko sati ba'ayi ba da zuwa na aka cemin kaje kauyenku ,yaronka baya jin da'di"yace"wallahi jikata jikin yaron ne usaiba yaki dadi da yaji sauki sai ciwo ya dawo to yanzu dai da sau'ki nazo dashi asibitin cikin birni an dubashi ance typhoid ce da aka rubutan magani Abbanku ne ma ya siya yanzu dai jiki ya fara warkewa"Rufaida da taga ne nufinsa Abba Hashim Abbansu Samiha wato yake nufi" cikin nuna tausayi tace"Baba Allah ya kara lafiya,shi kuma Abba Allah ya kara masa budi"yace amin amin 'yata"Rufaida tace au Baba bamu gaisa ba gaisawar sukayi Rafi'a ma ta gaishesa daganan suka cigaba da tafiya cikin gidan aranta tana tausayin talaka dukda su 'dinma ba masu ku'di bane can dan albashin mahaifin nasu tasan a gurin wasuda yawa masu kudin kudin kashewa ne na siyan kayan kwalliya da kayan saws dukda yawan kudin wasu ma sai an karo linkinsu amma dai sai tace sudai Asirinsu a rufe yake mutum ashirin ma zasu iyaci a karkashinsu da wadannan kudin albashin nasa shima Abbansu akwai tausayin mabukata yana da alkhairi Allah Rufaida take kara godewa da ni'imar da suke a ciki ita a koyaushe na kasa dasu take hanga
Da sallamar Rufaida ta shiga falon su Samihan da yasha kayan alatu amma taga har wani gyara ma akai masa da ta tance tundaga kallo daya"Samiha da gudu ta karasa gurin Rufaida ta rungumeta tana Oyo Oyo 'yar uwata ,Rufaida ta tureta daga jikinta tace"keni cikani karkijimin ciwo"
Samiha ta dubi kanta"tace ina naga auki banda abinki"Nasiba da tazo gidan tana falon zaune da sauran kawsyensu tace"kema fadamata Rufaida ai bansan yaushe Rufaida zatayi hankali ba abu kamar yaqi yanzu da ta maujeki fa muna haka tayi mana nuna shigowa"
Rufaida ta ratsa Samiha ta shige falon ta zauna cikin kawayensu Nasiba shehu Garba da Aisha Mudassir da suke unguwa 'daya su biyun kusan shiyasa duk unguwar da zasu indai gidansu kawayensu na makaranta ne ko kawayen unguwa tare zaka gansu 'dokin ganinsu take dan indai ba Samiha ba bada wadda suke haduwa rabon da duk ta gansu tun Candynsu,hira suka fara yi ta bayan rabuwa, Samiha ta dawo cikinsu ta zauna tana cewa"wato kun manta dani da ko"Aisha tace"haba wazai manta da amarya sukutun da guda"Samiha tace"kwaji da shi dai magulmata"Rufaida ta mike daga zaman da tayi"Nasiba ta dubeta tace "Malama ina zuwa kuma,zamu fara fira kuma kinsan zamuyi rabon IV ma ya'u za'a fara"Rufaida tace" zanje mugaisa da momy ne,kuma bazanje wani raban IV ba,tunda bata fadamin yau ne ba"Samiha taja tsaki tace"kunji tafa Aisha dan Allah da wacce wayar zan mata waya ba waya gare taba,yanzu da muka tsaida magana ayi yau a huta kunaji ina kira Ummi tace sun taho"Rufaida tace"oho miki dai ta haye sama gurin Momy da Rafi'a suna zuwa can ta nufa taje taga Samima autarsu Samiha da suke kawance a makaranta da suke aji 'daya kuma tsararrakin juna ne"Rufaida da saida suka gama gaisawa da Momy tagama bata lokacinta danda batayi niyyar zuwa raba IV 'dinba sai da Nasiba tazo suka yima Momy sai sun dawo addu'a tayi musu tace Musa zai kaisu da yake 'da ga Abba Hashim 'dan qaninsa da Abba Hashim dinne ma ya daukosa yake riqonshi ta aiki Samir da dashi sukayi zai kaisu kai IVn a mota hirarsu duk sukeyi Musa yana tayasu dan shi akwai da barkwanci,Wayar Nasiba ce ta fara ringing ta zira hannunta jikin jakarta ta duba mai kiran AbdurRahman ne malaminsu aiko da murmushi ta kalli sauran kawayen nata Rufaida da Samiha da take tsakiyarsu tace musu"Sir AbdurRahman nefa mai kiran"Samiha tace "Allah sarki sir mun rabu da gaisawa "Aisha da take gaban motar ta juyo tace"Nasiba ko dai dashi za'ayi kinga tuwonmu manmu"harararta Nasiba tayi ta 'daga wayar suka fara gaisawa su Samiha sukayi dariya ,Musa ya kalli Aisha yace"ba ankusa bikin Nasibar ba ne,dawa kuma kuke hadata" Aisha tace"a'a Yaya Musa ba'ako kawo mata kudi ba ,wani malaminmu ne a AL'AZHAR da yazo mana TP"yace "ok inda rabo sai kiga ya aureta"Aisha tace" wallahi kuwa"gaisawa Nasibar suka cigaba dayi da AbdurRahman har take shaidamasa sunzo unguwarsu gidansu Samiha yanzu sunfita rabon IVn bikin anan yake sanarmata sunyi tafiya basa gida baiso bikin Samihar yazo baya nan ba hakuri ya bawa Samiha da Nasiba ta bata wayar su gaisa yake cewa"amma bata fadamata bikin ya matso ba"murmushi tayi kawai ta mikawa Rufaida wayar su gaisa"saida ya tanbayeta ina yayanta da suke cewa yana kama da shi"tace yana lafiya"yake cewa yaso a bikin su ha'du sai dai hakan bai samuba sai dai anata"tayi murmushi ta mikawa Aisha wayar suka gaisa ta mikowa Nasiba inda yace ta turomasa account number din su yanzunnan ,Nasiba suna gama wayar tace "Wallahi Aisha ki rufamin asiri,da maganar Sir AbdurRahman ai kema kinsan bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane ina ni ina 'dan Khalid Bashar ai kema kinsan yafi karfina,irin su Sir AbdurRahman ai saidai 'yar minister" Aisha tsaki tayi ta juyo tace"kamarya na rufa miki asiri,kuma ta ina yafi karfinki kin manta tsarin Allah kenan suma Allah ne ya basu dukiyar Ba karfinsu ba ba dabararsu ba idan mijinkine bawani shi 'dan masu kudi ne ko wani abu indai da soyayyah tsakaninku ki fadama ,kuma kema aiba yar talakawa bace"Su Samiha suka ce yawwa Aisha"fadamata dai,mutum ya dinga yanke tsammani kai tsaye"Nasiba ta 'dan tabe baki alamar bata damu da maganganun nasuba tace"kanku akeji"Musa da yake tukin da yake jin duk abinda suke cewa yace"Nasiba Allah karki yanke tsammani"tayi murmushi tace "Yaya Musa kenan, Dan Allah fadamin Account number din ka mu turamasa"Musan ya fado mata ta rubuta ta turamasa"gidansu wata kawarsu suka fara zuwa suka shiga ya fito ya tsaya bakin motar yana danna wayarsa alert yaji a a wayarsa ya shiga cikin sakunan ya duba sakon AbdurRahman ne ya turo ya turo dubu 100 a account dinsa suna fitowa daga gidan suka Shiga motar kafin ya tada motar ya kalli Nasiba yayi yace"ya turo kudin yanzu dubu dari ne" ido suka zaro su duka suka ce"Yaya Musa dubu 'dari fa dan ba wacce tayi zaton zai turo haka dukda idan yayi ma ba abin mamaki bane dariya a gareshi dariya abin ya bashi yace"dan mai kudi yayi kyautar dubu 'dari aiba wani abu bane linkinsu billion ma zai iya" sukace masa "Eh hakane yaya Musa amma gani mukayi mu dalibansa ne bakomai ba"suna haka kiran AbdurRahman ya shigo wayar Nasiba tanbayarta yayi kudin sun shigo tace masa" Eh"godiya tayi yace babu komai ba yawa ma"ita kam Nasiba gani take dubu dari dukda mahaifinta mai wadatar ne amma dai tasan bazata samu dubu dari ba kai tsaye a hannunsa sai dai ko harkar karatu suna gama wayar Samiha tace ta barwa kawayen nata da yayan nata kudin danko ita batasan mai zatayi dasu ba bata da matsalar komai anyi musu cikin girma iya dai dai karfin mahaifansu kuma Ahmad yana kokari gurin yi mata komai iya arzikinsa kawayen nata ne dai ta fahimci buga buga kawai sukeyi dan ko anko cikinsu ba wadda tayi duka shima yayannata Musa tasan hakanne tunda a karkashin mahaifinta yake har yau karatu ma yake a FCE KANO aiko Samiha tanaji anan take kowacce daga cikinsu ta fara lissafa abinda yakamata tayi da kudin akarshe ma Musa suka barwa sallaho ya siyo musu kayan da suka lissafa da kudin ciki harda gudunmawar da zasu bawa Samiha dan babu boye boye tsakanin Samiha da kawayen nata kaf dinsu sai Yamma lis suka gama raban IVn da mazan ajin nasu suka kira wani daga cikinsu ya ansa zai rabawa sauran har kofar gida Musa yakaisu Nasiba ya sauke ita ko Rufaida bayan sun koma gidansu Samiha Momy maryam cewa tayi ta kwana anan saboda duhun magriba zata kira Ummi Hauwa'u ta fadamata Rafi'a da dama haka takeso murna tayi koda Momy Maryam ta kira Ummi Hauwa'u nunawa tayi babu komai ai duk gidane kuma Rufaida ma 'yar tace bama saita kira ba sosai Momy Maryam taji dadi yadda Hauwa'u take daukarta kai bazakace ba ya da kanwa bane kuma duk wannan zumuncin 'ya'yane silar hadashi.
SADIYA KHALIY✍🏽*🔗JININMU 'DAYA🔗*
BY SADIYA KHALI🖊️
Page 16📄
AAhmad dake dannawa wayarsa da yake gefen gado zaune ya maida dubensa ga AbdurRa'uf daya kwanta a makeken gado yana lumshe ido yace"yanzu brother bazaka fito koda fall bane muyi fira ba wato dai har yau bazaka canza ba daga wannan tafiyar nasan cewa zakayi ka gaji ne fa"AbdurRa'uf ya bude idanunsa duka ya kalli Ahmad yace"Gaskiya yaron nan ka rainani da yawa yanzu duk a wannin da nayi a jirgi shine zakazo kana takuramin na fito ayi fira ni kaga Malam tashi ka bani guri na huta"Ahmad ya yi murmushi saboda yadda yasan AbdurRa'uf da akwaishi da son girma kamar wasu shekaru ya basa duka duka baifi shekara daya AbdurRa'uf ya bashi ba sassauta murya yayi yayi yace"haba Yaya AbdurRa'uf ayimin afuwa"AbdurRa'uf baki ya yatsina yace"shikenan,in Kasan me kuwa"Ahmad yayi saurin cewa"A'a"AbdurRa'uf yace"Kano ta birgeni sosai babu cikowa daga zuwana na fahimci haka,anya bako a Kano zan nemi mata ba na aura,idan mundawo Nigeria nayi gidana na zauna anan"shi Ahmad ma dariya abin yaba shi amma sai yayi murmushi yace"Mutumina tanbayar da zanma kenan ya kaga garin Kanon,matsalar tsohuwar can ta hanani gini anan wallahi"dariya AvdurRa'uf yayi yace"gaskiya takwareka ka samu mace 'yar Kano amma tahanaka zaman Kano"Ahmad yace "a'a wai Samiha kake nufi ai ba 'yar Kano bace 'yan sokoto ce"to amma ai rainon kano ce ai Malam angama magana,nifa yadda naji kano farar daya garin yayi min hakama matan cikinsa inada yaqini akansu zakaji dadin zama dasu da yardar Allah" Ahmad yace"gaskiya kuwa"amma kasan matar nan dakyar ta amince na aureta ,ai indai matarnan na raye bazata bari muyi abin kanmu ba,wai haka tayiwa su Abba ne"AbdurRa'uf yace" da alama dai hakan tayi musu ai fitinanniyar tsohuwa su Abba Allah ya hadasu da ita"Ahmad yace sosaima kuwa kaima kasan Karimar Baffa Sule takeson hadaka da ita,itama naji ance Karimar tana sonka jira Hajiyar take kazo ayi magana"ido AbdurRa'uf ya zaro yace "to wallahi ba Wanda ya isa yayimin auren dole tun wurima ta canza sheqarta,shiyasa naga tunda Hajiya ta samu labarin zuwana indai na kirata mugaisa saita hadani da Karima mugaisa" Ahmad yasa dariya Abdurra'uf yace"au dariya ma na haka cikin bacin rai" Ahmad ya sassauta murya yace "haba Babban mutum kaima kasan yadda akeji dakai a gidannan Baffa Sule bazai amince ba bare kuma kasan Baffa Alhaji bazai amince ba Indai bakaso"AbdurRa'uf ya dawo da nutsuwarsa da taso gushewa da yace" Eh hakane Ahmad"Ahmad da wayarsa tayi kara yasa shi fasa maganar da yayi niyyar yi ya duba mai kiran ganin sunan da yasawa Samiha yasa shi murmushi ya kara daga ya kara a kunne dan yasan ganin bata kiransa ba hardare yasata kiranshi tunda sukayi magana a WhatsApp tace masa zasu tafi rabon IV ya sauka ba tare ma da yabata amsa ba yafara cikiniyar tarbar Dan uwan nasa AbdurRa'uf Sallamarta ita ta katse masa tunaninsa ya amsa mata ta gaishesa cikin girmamawa ya amsa kana yace Madam ansha yawo yau to ya gajiyar hanya Samiha da take zaune tana duba dinkinsu ita da Rufaida da Rufaidan ke 'dagawa tace masa "aini fushi nake dakai yau gaba 'daya ko Flashing ko text dinka babu a wayata naka" murmushi yayi yace"tuba nake amaryata"itadai Samiha kunyar maganar taji da Ahmad yayi cigaba yayi dacewa,kinsan Yaya AbdurRa'uf yau ya sauka a Nigeria shine dalili"Samiha tace" wallahi na manta shaf kace masa ina masa sannu da zuwa"da murmushi kan fuskar Ahmad yace"zaiji da kyau,gashinan a gefe na"da haka suka cigaba da firarsu "AbdurRa'uf da yaji firar ba mai karewa bace mikewa yayi yana cewa"na lura bazaka daina cikamin kunne ba" Falo ya nufa "da nan 'dinma kayan auren Ahmad da AbdurRa'uf shine ya ha'da komai ya vayar tun wancen satin a kawo su Nigeria sai a jiya suka iso da yanzu shirin mikasu ake gidansu Samihan,haka ya zauna inda kowa yaba kayan yake yasan dama Safiyya da Amminsa ba bayaba gurin iya zaben kaya shidai murmushi yake kawai muryar yakumbonsu yaji tana cewa
" Masha Allah Babban Mutum anyi zumunci kaya sunyi Allah ya bar zumunci ya nunamin naka nadau danka"murmushi yayi kawai yace kindaina auren nawa kenan"Dariya tayi tace"kadubeni kaga aina tsufa gwara na barka ka auro budurwa son kowa kin wanda ya rasa,dukda na rasa irin matar dama kaika keso tunda indai India ne akwai kyawawa " murmushi yayi yace "Yakumbo kenan,nifa nafison mai kyakkyawan hali" Momynsu Ahmad sai yanzu tasa baki tace"aiko zaka dade baka samu ba tunda baka nema,kullum mukai waya da Yaya Asma'u saita yimin kukan hakan"Dariya abin yaso basa ma yace"Ai Momy komai lokaci ne,kuma wani jinkirin Alkhairi ne"Yakumbo tace"Hakane amma sai a dage da nema har Allah yasa a dace,amma idan baka nema ai ba lallai ace kasamu kanada ga zaune ba"yace hakane Yakumbo,zan riqa dubawa insha Allah"tace masa yawwa kag shekarun sunfara ja a kalla kayi talatin da doriya"ido ya zaro yace"haba yakumbo har yau ko talatin bankai ba"tace "kaidai kawai yaron zamani da basa san shekaru" Momy tayi dariya tace"A'a Yakumbo ba'kin shekaru suke ba shekarunsa kenan wancen AbdurRa'uf 'din dai kike tuna shekarunsa",Yace yawwa Momyna fadamata gaskiya dai tsohuwar nan ta rikice"
"Duban Yakumbo Momy tayi ta suka kalli juna itada AbdurRauf dan sunsan Yakumbo halinta sarai bataso ace ta fara rikicewa Harararsa tayi tace" tsohuwartawa kake ciwa fuska ko harda ta rikice ma ko?"
Yace"tuba nake Momy"
Yakumbo ta hararesu gaba 'daya tayi ta wasan nan tace"Hannatu harda kallona kafin kiyi magana ja'irar yarinya nasan da bani hardake za'ayi maganar gwara na tattara na koma dan-bat.....
Husna data shigo falon ta katse maganar ta zauna kusa da Yakumbo tana dafa ta tana cewa"keda waye haka Yakumbo kike sababi haka harda maganar komawa Dan-batta"
"Nida wa'dannan ne ta nuna su Momy da AbdurRa'uf harda kallon juna kafin Hannatu tayi magana,gwara na tattara nakoma inda nafi wayau ai" dariyar abin yaba Husna da itama Yakumbon dan ayi tayi dariyar take wannan maganar"Husna ta juya ga AbdurRa'uf tace"Yaya kaji fa,ina Yaya Ahmad din ne"
"Ina jinku,Yana ciki yana amsa waya"
"Hala da Samiyy suke wayar ko?
"jeki tanbayesa kiji"
Tasan bakar magana ya fadamata hakan yasa tayi shiru ta mike ta kunna TV shi ko da Momy suka cigaba da firar zuwansu Ammi cikin wannan satin,dawowa Husna tayi ta zauna tana cewa"amma Yaya harda Safiyya za'azo ko?"
Yace "Bansaniba kin kagara tazo kenan ko,a fara Isar mutane gida kamar gidan kallan Kwallo don hayaniya" Dariya tayi tace"ai haka yafi ni ni kadaice gidan bayamin da'di"
"Shiyasa kike damin mutane ba" Ahmad da yashigo falon shima ya nemi guri ya zauna suka cigaba da firarsu.
LIMAT SADIY 🖊️*🔗JININMU 'DAYA🔗*
By Sadiya Ibrahim Khalil🖊️
Hikima writers asso......
17
"Yakumbo gaskiya kamata yayi kiya hakuri da tafiya mu tafi tare daganan gurin bikin murmushi" Kallon Husna Yakumbo tayi da ita ke maganar kana tace" kyayi kya gama yarinya sauranma sunyi sun gama"Husna ta mike tana 'bata rai" daya daga cikin matasan falon yacewa Husna "Haba Amminmu dawo ki zauna,meye abin fushi,
Tace "amma Yaya Bello daga fadar gaskiy.." Yace "kinga kyaleta"
Yakumbo data mike tayi hanyar barin falon,dan ta fahimci bata mata lokacin yaran sukesan yi
Su AbdurRa'uf da Dady da Momy har bakin mota suka raka Yakumbo Husna ta biyosu da jakar Yakumbo tasa a gidan baya addu'a sukayi musu Allah ya saukesu lafiya suna zolayar Yakumbo"cewa ta kagara taje taga Baffa shiyasa ta damesu da saita koma 'Danbatta yau" Murmushi tayi tace"to meye a ciki tunda Ahmad yafara nuna baya auren dani tun kafin ku juyan baya harda Babban mutum da Bellotu gwara naje nima na rike mai gidana kar matanku su yimin kwace nan gaba "AbdurRa'uf yace" wato Yakumbo hardani duk yadda nake auren nan dake"Bello dake kokarin tada mota yace" Yakumbo cefa ai duk ciki indai akan Baffa ne zata iya dena aure da kowa su Dady murmushi sukeyi su dai da haka motar su tabar gidan ran kowannensu babu dadi
ABDURRA'UF JABIR MAHMUD DANBATTA
Haifaffen garin Kaduna inda aiki yakai mahaifinsa AMBASSADOR JABIR MAHMUD DANBATTA a matsayin jakadan Nigeria a India da Matarsa daya Asma'u da akayi musu auren zumunci,inda a yanzu suke da zama a New Delhi babban birnin India AbdurRa'uf yayi karatunsa a fannin likitanci ya karanci Medicine a UNIVERSITY OF MEDICAL SCIENCE NEW DELHI yanzu ya zama kwararren likita a asibitin CHAUDHARY BRAHM PRAKASH AYURVED HOSPITAL,asibiti ne babba da yake zaman kansa,AbdurRa'uf shine 'da 'daya tilo gurin Asma'u ta haifi na farko ya rasu daganan ta haifesa ta yi masa kanne wajen hudu duk duk suna rasuwa a karshe haihuwar ta tsaya mata,Safiyya a garesu kuma 'yar riko ce"Shureim Khan Salim Abokin Ra'uf ne a India tare suke a makaranta hakama a gurin aiki Shureim haifaffen dan India ne shi
AHMAD USMAN DANBATTA daya kasance Aboki kuma 'dan uwa na jini ga AbdurRa'uf tundaga yarinta har zuwa girma kasancewar halayyarsu da ta zamo daya itace takara assasa abotar dukda da tazarar shekaru daya tsakaninsu bai hana su abota ba tundaga primary har zuwa secondary da suna shekarar karshe a makaranta Jabir yasamu Ambassador
USMAN MAHMUD DANBATTA mahaifin Ahmad Kani ne ga Jabir