Showing 75001 words to 78000 words out of 86533 words
yana cigaba da tukinsa
Sunana Safiyya,kefa Mene ne sunanki"
Taji muryar Safiyya na fadar haka
"Rufaida" ta fadi haka tana kokarin zage zib din jakarta da take kara alamun kira taji Safiyya ta canza yare zuwa indiyanci da batasan mai take cewa ba
Rufaida ta daga wayar ganin mai kiran tayi saurin dagawa tasa handfree da sallama ta dora da cewa"Yaya ina kwana"
"Lafiya kalau,kun taho ne?"
"Eh Yaya Abdul muna hanya"
"Dama Ummi tace na kiraki naji tayi miki alala"
"Eh a yimin kasan na dade dama banci shi ba"
Tsaki Abdul yayi yana fadin
"Yanzu fa za'a fara yi mana alala a gida tunda zaki dawo"
"Kai Yaya nifa kadai akewa ko nayi abu na"
"A ina,ni kinga ina Yasir yake"
"Ya kwanta barci"
"To ki kula da kanki,munyi waya da Yaya Hassan yanzu yayi min bayani"
"Insha Allah,Allah ya tsare Ku ya kawoku lafiya daganan ya katse wayar Rufaida ta sauke wayar tana murmushi
Yasir ne ya tashi barci ya fara waigen Maminsa ganin ya hangota yace
Yasa shi kokarin haurawa inda take,Dady Jabir ya kallesa yace
"Aboki ina zaka?"
Yasir yace
"Gurin Mami"
Daganan ya haura ya fara waige waige yana cewa
"Mami ina Dady Hassan"
"Ya koma gida"
"Safiyya da idanunta suka sauka kan Yasir tace
" wannan kyakkyawan Boy din fa Masha Allah na waye,ko kaninki ne"
Murmushi Rufaida tayi kawai
"Safiyya tayi dariya tace
" yaron kine kenan,kyakkyawa dashi Masha Allah "
Ta mika hannu ta dauki Yasir zuwa inda take ta fara ce masa"
"Ya sunan ka?"
"Yasir"
Sunan Abbanka fa jin yayi shiru yasa Safiyya ita ma kyalesa saboda karar wayar ta da taji ta mika hannu ta dauki wayar tasa a kunne
Ta fara magana cikin yaran Hausa.
[9/30, 7:57 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil🖤
52.
Hudu na yamma suka iso Kano Dady Jabir ya kallo Rufaida yana fadin
" a wacce unguwa kuke ne"
Rufaida da ta soma jin barci taji maganar Dady Jabir din tayi saurin fadin
"Muna Rijiyar zaki"
"Dady Jabir yace
" kash gashi mu a nan Zaria road gidan kanin nawa yake, bari mu fara zuwa kuyi sallah,mu huta sai mu kaiki,tunda unguwarku tana gaba da nan"
Rufaida cikin nuna girmamawa tace
"A'a Abba dama ka bari saina kira a kaini gida"
Yace
"A'a ki bari dai muje muga gidansu abokina"
Safiyya da take danna wayarta tace
"Wallahi kuwa Abba,Dady kaga idan muka ga gidan kafin mu tafi saina je,inason yaron dama ta bamu shi"
Dady yayi dariya
"To gaki gata in tayarda ta baki babansa ba"
Rufaida murmushi takeyi , da take jin maganar da suke tattaunawa
A kofar gate din gidan yayi parking yayi Horn maigadin gidan ya bude musu gate din gidan suka shigar da motarsu da 'yan sandan da shigarka cikin gidan zaka tarar dasu zai tabbatarmaka gidan babban dan sanda ne Rufaida da ido take bin ko ina na gidan da kallo
Har suka karasa parking space sukayi parking da suke hango mutanan gidan sun fito tarbarsu ta glass din motar
Suna fitowa Husna ta rugo ta rungume Safiyya da murnarta
Ammar da Abida suka rungume Dady Jabir suna masa oyoyo
Daganan suka koma suka rungume Safiyya suna murnar ganinta
Momy Hannatu da take gefensu Husnan tace
"Yaya Jabir sannu da zuwa"
Ya amsa da fadin
"yawwa Hannatu"
Rufaida da take tsaye tana kallonsu gwanin sha'awa
Dady Jabir ya maida duba inda su Rufaidan suke tsaye
"Gafa baki nan kunyi,tare muke, kinga wadancen sunyi gaba sun barmu tsaye" yayi maganar yana nuna su Husna da su Abida da su kayi cikin gidan
"Momy Hannatu ta dubi inda su Rufaida ke tsaye da taji yarinyar kallo daya da tayi mata ta kwanta a ranta
" sannu da zuwa,ku shigo daga ciki,ya 'dan Boy muje ko?"Momy Hannatu tayi maganar tana kama hannun Yasir ta fara tafiya ita dady Jabir zuwa cikin gidan da suke tafe suna fira yana bata labarin haduwar da sukayi dasu Rufaida a hanyarsu ta zuwa kanon
Rufaida tabi bayansu har zuwa kofar da zata sadaka da Babban falon gidan Momy Hannatu ta bude kofar falon suka shiga da suka tarar dasu Safiyya a falo sun baja kolin zaman fira
Safiyya da taji sallamarsu Momy da Dadyn ta dago kanta ta kai duba ga Yasir tace
"Lah Yasir zo nan"
"Momy Hannatu ta kai dubenta ga Safiyya ta harari Safiyya tace"
" Baya zuwa,wato da baki kuke kika barsu kika shigo abinki ko?"
Safiyya tace
"Lah Momy Ba haka bane nayi kewar Husna ne shiyasa"
Husna ta kai kallonta ga Yasir tace
"Sophie ina kuka samo wannan yaron kyakkyawa,ya sunanshi"
Safiyya tace
"Sunansa yasir,ga mamarsa nan"
Taka rasa maganar tana nuna mata Rufaida da take tsaye tana kallon Familyn gwanin sha'awa
"Husna tayi kai kallonta ga Rufaida da batayi tunanina Rufaida ce Mamar yasir ba murmushi tayiwa ace
" sannu da zuwa ki zauna mana"
Rufaida ta mayar mata tace
"Yawwa" daga haka ta zauna a manyan kujerun falon kusa da wadda su Husnan kekai"
Abida ta ja Yasir gurinta da take da sha'awar yara musamman Yasir da yake kyakkyawa farin bafulatani
"Dady Jabir da ya samarwa kansa gurin zama a daya daga cikin kujerun falon yace
"Husna kaita dakinku tayi sallah,muci abincin saimu kaita gidansu"
Husna tace
"To Abba" daganan ta mike ta saki murmushi ta kalli Rufaida tace
"Muje ko?"
Rufaida ta mike tabi bayan Husna har zuwa ciki"
***********
Abida ce da wata mai aiki suka jera abinci kasan carpet din falon Momy hannatu ta mike ta tsiyaya wa Dady Jabir ruwa a kofi ta mika masa
"Yaya Jabir ga ruwa"dady Jabir da shigowarsa falon kenan ya shiga masallaci sallar la'asar sunyi azahar a hanya,ya amsa ya fara sha
Momy Hannatu takoma ta zauna
"Yaya Jabir ina yini,ya hanya,ya kuma gajiya"
"Lafiya kalau gajiya tabi lafiya"
"Nifa daukata Yaya driver ne zai kawoku,saina ganka da kanka ka tuko motar"
"Eh wallahi Hannatu kinsan drivernsu daya ne,kuma ni nafison na rika tuki da kaina ma"
"Eh hakane,ya kuka baro su Yaya Asma'u,da Ra'uf
"Lafiyarsu kalau,ina Usman din ban ci karo da shiba"
"Bai dade da fita ba Safiyya ta yomin waya kun iso fitarma ta dole ce yayi an kirasa a gurin aikinsu ne,bai tsammaci zuwanku yanzu ba,yanzu Dady haka zamu bar yaron nan Ra'uf kiri kiri yaki yin aure"
Dady Jabir yayi murmushi yace
"Ai halin yaron nan sai shi,Amminsa tace har yau ya kasa mantawa da wannan yarinyar kuma kema kinsan ko giyar wake muka sha ba zamu aura masa yarinyar ba da silar danginta muka rasa farin cikinmu"
"Hakane Dady to mai zai hana a hadasa da Safiyyan da Yaya Ma'u tace kun yanke shawarar hakakwanakin baya tunda shi ya tsaya shirme kamar karamin yaro"
"Eh to Hannatu kinsan dai matsalar Hajiya ba lallai ta yarda ba"
"Ina tunanin zata amince tunda ita ma ta matsa yayi auren yanzu,kuma yanzu Safiyya tana tare damu"
"To zan jarraba na gani,ko Allah zaisa a dace"
"To Amin"
Sallamar su Rufaida ita ta katse hirar dasu Dady keyi suka amsa musu
Momy Hannatu ta dubi Rufaida tace
"Dama yanzu nake shirin kiranku,kuzo aci abinci"
Safiyya tace
"Momy ita tafiya zatayi anzo daukarsu"
Momy Hannatu tace
"Ba Yaya Jabir yace har gida za'a kaiku ba" tayi maganar tana kalon Rufaida
"Wallahi Aunty dazu Yayanmu ya kirani waya na masa kwatance unguwar da muke yanzu,shine naba Safiyya waya ta masa kwantance yace yanzu yana kusa da hanyar zai biyo ya tafi damu"
Dady Jabir da baiji dadi ba yace
"To shikenan amma dai,banso ba naso na kaisu har gidan"
Daga haka suka fito rakata
Har jikin motar Abdul suka kaita da ya shigo da motarsa ciki Abdul ya fita suka gaggaisa ya kwaso kayan su Rufaida a motar Dady Jabir zuwa motarsu bayan suna kokarin shiga motar Abdul ya dubi Dady Jabir yace
"Yalla'bai mungode sosai Allah ya kara girma"
Dady Jabir ya dubi Abdul yace
Amin,amma kun mana laifi daya fa"
Abdul yace
"Yallabai laifin me mukayi"
" zaku tafi da abokina"
"Abdul yayi murmushi
" au Yasir,ai yalla'bai zamu zo nan mukawo ma shi"
Yace
"Nida ba'anan nake ba,saida in zaku barmana shi mu tafi tare,kayima Babansa magana ko zai yarda na tafi da shi,ya shiga ranmu sosai"
Abdul yayi murmushi yace
"To shikenan yalla'bai"
"Ai nasan ba zaku iya ba fade kawai kukayi, nan gidan kanina ina fata zaku cigaba da zumunci tunda garinku daya
"
"Insha Allah yalla'bai"
Husna da take sauraransu tace
"Ai Abba ko busu zo ba,mu zamu je kodan Yasir yaron ya shiga ranmu lokaci daya"
Abdul yayi murmushi
"Haba mai zai hana mu muzo ma"
"To Allah yasa" fadin Safiyya
Daganan suka shiga motar Rufaida a gaba Yasir ya na baya shikadai yana wasa da motar da Da Dady Jabir ya basa su Rufaida suna ta godiya har Abdul zai tada motar Safiyya tasa kanta cikin glass din motar ta dubi Rufaida tace
"Rufee bamu lambarki,saimu rika gaisawa"
"Rufaida ta fado mata tasa daganan Abdul ya tada motar suka fara kokarin barin gidan su Husnan suna dagawa Yasir hannu har saida suka ga barinsu gurin
Abdul da ya soma tukinsa ya dubi Rufaida da take gaban motar yace
" oh Rufaida ban taba tunanin a zamanin nan za'a samu mutane irin wadannan ba,mutanan arziki kiga nifa kamar sun sanmu"
"Rufaida tace
" wallahi kuwa yaya suna da kirki sosai,Yaya yana ga har kayi kumatu bayan rabuwar mu"
Yayi dariya
"kai Rufaida banda sharri"
"Wallahi Yaya da gaske nake"
To nidama kinsan ina da kiba dan duk nafi ku,karatu ne dama ya tsotseni yanzu kuma tunda nagama karatu kuma ina dibar albashi mai tsoka dole na canza"
"Eh lallai hakane"
"Muje gida kiga abun bazata"
"Menene Yaya kodai budurwa kayi ne,tazo tarbata "
"Oh budurwa kuma Rufaida"
"Eh mana Yaya"
"Tab aini ba yanzu zanyi aure ba"
"To Allah ya kaimu lokacin ya hadaka da ta gari"
Ya amsa da Amim
Ya dora da cewa
"Oh Rufaida ya zaman naku,keda su Umma, naga ma duk kin rame"
"Hmm kaidai bari Yaya ba dadi"
"Ai nasan dama bazai dadi ba,Allah dai ya raba ki da auren na kaddara,dan wallahi yanzu ko mai za'ace a kaina bazan yarda karo na biyu ayi wa kanwata wannan auren ba dan saidai muyi fito na fito dasu Abba"
Ido ta zaro
"Kai Yaya su Abban"
"Ko su waye kuwa,kin manta waye Abdul ne ni bana goyon bayan zalinci a rayuwata,dubi fa yadda a kari ka gasa ki kamar biredi,basu a dubi yadda aka rika gasa mu a baya kafin mu samu wannan canjin rayuwar,kina gani yadda har yau ba musan dadin dangi ba,dukda kasancewarsu dangi Ummi da Abba duk daya amma basa nuna kulawarsu gare mu"
"Babu komai Allah yaya komai yana gaf da zama tarihi"
"Rufaida kenan anya kuwa,kina sane fa ko Abba Bukar ba wani sonmu yake ba,ni tsorona kar abinda ake fada akan Ummi ya zama gaskiya"
"Haba Yaya karkai fatan hakan,nina san komai zai wuce"
"To Allah yasa Rufaida"
Daganan suka cigaba da firarsu har suka isa kofar gate din gidan nasu
Horn yayi maigadi ya bude musu gate din suka shiga yana kokarin yi musu sannu da zuwa
******
Gaba 'daya gidan ya rude da murnar dawowar Rufaida kannan nata suka rasa inda zasu sa Rufaida don murna ga Yasir da kowacce kenan nan da shi su Rumaisa an zama 'yan mata tana shirin Candy a lokacin Abdul-Rashid ya tafi gaba da sakandire yana karatunsa a Northwest sai da suka gama murnar suka fara kokarin shigo da kayan Rufaida cikin gidan wannan kenan.[10/3, 10:25 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU D'AYA*
Sadiya Khalil
53
Book 2 page 3
Wannan book 2 ne page 3 yakama 53 kenan
Safiyar litinin
Misalin karfe 11 na safiyar ranar Rufaida tana zaune a falon gidan ita kadai tana kallon wani Film na Sanam teri kasam a Bollywood wayarta ce ta dauki kara ta daga da sallamarta fuskarta da alamun farin cikin ganin mai kiran ta maida wayar a hands free ta cigaba da kallonta
"Kanwata kin buya ko flashing bakya yimin"
"Kai Yaya Malik haka ma zaka ce"
"To ai haka ne ko kina yimin ne,abokina yasa kin mata da 'dan uwanki"
"Kai Yaya duka fa jiya muka fara waya da Zahraddin din fa"
"Koma yaushe ne nasan dai,zuwa yanzu kinyi na'am da abokina"
"Hmm Yaya kenan"
"Meye kuma hmm ko baki sonshi ne,karfa ki yaudararmin abokina,wani yazo yayi wuf dake"
"Kai Yaya fatan da zaka min kenan"
"Ba fata bane Rufaida,nasan irin ku kyawawan mata aurenku rabo ne"
"Kai.Yaya Malik ina wani kyau"
"Hmm Rufaida kenan,nidai yanzu mu koma batun abokina,please karki kishi Rufaida yace wa Mamarsa inbake ba sai rijiya,sannan kuma ma Zahraddin mutumin kirki ne,haka ma iyayensa nasan zasu rikeki amana"
"Insha Allah"
"Yawwa kanwata,yawwa na turawa Safiyya photonki yarinyar da nace miki kuna kama kwanaki"
"Eh nagane"
"Ina turamata photon tace min ta sanki"
"Niko a ina tasanni" ta yi maganar tana zaro ido
"Ashe kwanaki a motarsu kuka zo Kano"
"Dan Allah Yaya Malik,wallahi nima nayi wannan tunanin da naji sunanta,kuma naga yanayinta yayi kama da wadda ka bani labari"
"Eh wallahi itace"
"Suna da kirki sosai,amma nifa banga kamar mu ba"
"Itama tace bata gani ba,amma ni kuma na ganta kune dai kuka kasa gani banda yanayin tafiyarku kuna da siga a fuska ta fannin kalar hancinku"
Dariya abin ya bata tace
"Yaya Malik kenan kanada zakulo kama wato harta hanci zaka ga kama"
"Au dariya na baki ma ko?"
"Eh mana ai abin dariyar kayi,don wannan safiyyan ta fini kyau"
"Ita din ko kafarki bata kama ba"
"Zanfada mata kuwa"
"Yi maza kar kuda ya rigaki,kinga ni ina Yasir ne"
"Yana can suna wasa da Rahima"
"To idan sun shigo falon ki kira ni ki hadamu"
Daganan suka yi sallama Rufaida ta maida hankalinta ga kallon da take yi
******
Sallamar Ummi Hauwa'u ya katse tunanin Rufaida da take zaune a dakinsu saman gado
Rufaida murmushi ta kakalo ta amsawa Ummin sallamar Ummi Hauwa'u ta karasa shigowa dakin ta zauna gefen gado kusa da inda Rufaida ke zauna
"Ummi ina yini" fadin Rufaida tana sinne kai
"Da ban wuni ba zaki ganni ne yini ba zaki ganni ne,ace yinin yau baki leqo ko da falo ba,haba Rufaida me ke damunki ne?"
"Babu komai Ummi"
"Ban yarda ba,nice mahaifiyarki nafi kowa sanin halinki,nasan hakanan bazaki ki fitowa waje ba,Rufaida a yanzu haka baki da wanda ya fini a rayuwarki karki kokarin boyemin damuwarki"
Shiru Rufaida tayi zuwa wani lokaci ta soma magana
"Ummi jiya Ummansu Yaya Malik ta kira ni a waya tana min barazanar kisa tace na fita harkar danta, muddin na auri danta a karo na biyu sai taga bayana,data hada iri da karuwa wadda iyaye da 'yan uwanta suka sallamata gwara ta kashe ni itama akasheta, muddin tana raye bazata bari ta sake hada iri dake ba"
Rufaida takai karshen zancenta tana goge hawayen da suka soma tsiyayowa a idanunta tunowa da kalaman da Hajiya Jamila ta wanzu gurin fadama taajiya ga kuma kalmar sallamawar da aka kira Umminsu dashi da har yau ta kasa manta kalmar wadda a jiya ne kawai ta taba jin wannan kalmar a bakin Umminsu mai Hajiya Jamila take nufi da wannan kalmar nufinta su Gwaggo ne suka sallama Ummi tasu to yaushe abin ya faru bata tunanin abin ya dade da faruwa ta yiyu jiyan nema mai Ummintasu tayi ita kuwa
Ummi Hauwa'u ta kalli Rufaida da alamun bacin rai
Maganar Ummi Hauwa'u ta katsewa Rufaida tunanin ta
"Ke shiga harkar AbdulMalik din kike kenan shiyasa kika ki fitowa waje saboda kun kulla soyayya mahafiyarsa tanason ta rabaku,saboda ke dama wawiya ce,kin manta da abubuwan da suka rika faruwa a baya ban hanaki ki auri AbdulMalik ba dan saboda kina sansa, amma kisa ni muddin kika auri dan ta a karo na biyu ki rubuta ki aje babu ni babu ke"daga fadin hakan Ummi Hauwa'u ta mike tana kokarin fara takawa
Rufaida tayi saurin rike hannayenta tana sheshshekar kuka
" Ummi yakamata ki fahimceni,wallahi ban taba son Yaya Malik ba,shima bai taba cewa yana sona ba,,sai dai idan a zuciyarsa yabar soyayyar tawa a ransa ya kasa hakuri ya bari abokinsa ya aureni ya fadawa su Abba,amma ni abokinsa ne yace yana sona yanaso ya turo gidanmu,abu daya ne yake damu na tun jiya"
Ummi Hauwa'u ta cire hannunta daga na Rufaida ta kalli Rufaida
"Mene ne abun"
"Ummi ki fadamin maiyasa su Gwaggo suka sallama ki da 'yan uwanki,meye dalili mai kika musu maiyasa ake jifanki da kalmar da hatta masu aikata abun ba saso a kirasu da shi,karuwa nasan wannan kalmar ita ta rusa wancen auren nawa, ta kuma hanayi jin dadin wancen auren nawa,dukda wanda na aura yana sona,yanzu haka nasan hanani wani auren zata yi wannan kalmar muddin mijin auren nawa yaji ni nawa asalin mahaifiya ta karuwace"
Ummi Hauwa'u ta daka mata tsawa
"Ya ishe ni haka Rufaida,tunda har 'yar cikina ta fara yarda da abinda wasu mutanan suka yarda dashi harma suke kirana da suna karuwa,bayan basu sanni ba,hasali yawancinsu basu san ni wacece ba"
"Ummi ki gafarceni ba dan ina zargi gareki na furta hakan ba illah iyaka" kukan da ya kubcewa Rufaida yasata kokarin maida maganar da takeson fada
Ummi Hauwa'u da saida ta bari Rufaida ta gama kukanta ba tare da ta lallasheta ba sannan ta komaa ta zauna gefen gadon kusa da Rufaida ta dafa kafadar Rufaidan
"Illah kawai kinaso kisan menene dalilin da yasa na amsa suna karuwa ko,amsar ita ce sunan shi ya dace dani musamman duk wanda yayi duba ga wani abu daya wuce ya zama kamar tarihi sai dai har yau ba a fasa jifana da kalmar da take tunomin da wasu abubuwa da suka faru dani a baya ba ,amsar ki ta farko da kike son sanin dalilin anbatonta gare ni itace ni Hauwa'u Mahmud Danbatta ba karuwa bace
Rufaida tayi saurin dago da kanta
" Ummi Hauwa'u ta daga mata kai
"Kwarai ni sunana haka,Malam bashi ya haifeni ba,kaddara ce ta sa ya zamo tamkar uba gare ni,amma Ra'uf saurayinki na farko shi 'dane gare ni,haka ma mijin Samiha da ne gare ni domin su yarane ga yayyena.
Ina so a yanzu kafin kisan wani abu game da tarihina ki fahimci cewa ni ban karuwa bace ban taba karuwanci ba ba sha'awarshi ba,tun daga yarintata zuwa fara girma na har zuwa yanzu dukda sunan da aka lakaba min banji ban gani ba, kaddara da tun kafin asan da haihuwarka ita ta yi dalilin anbatonta da wannan sunan
LAVARINA YA SAMO ASALI A GARIN DANBATTA KAUYEN KUNYA DA NI DIN GURIN INNATA NA SAMI ASALIN LABARINNAWA
[10/5, 11:39 AM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil
Book 2
page 4
ALAVARINA YA SAMO ASALI A GARIN DANBATTA KAUYEN KUNYA DA NI DIN GURIN INNATA NA SAMI ASALIN LABARINNAWA
Malam Mamuda mutum ne bafulatani dan asalin jihar Kano karkashin wani karamin kauye na fulani kunya dake karkashin karamar hukumar Danbatta iyayensa su uku suka haifa akwai Hadiza da Salamatu shine kadai namiji a cikinsu kuma shine babba, da yana da shekaru goma Allah ya amshi ran mahaifinsa Malam Jauro
Inna wuro da take mahaifiya gasu Mamuda, da tun rasuwar mahaifinsu ta zama uwa uba a gare su sai kuma 'yan uwanta da suke kokarin