Showing 9001 words to 12000 words out of 86533 words
maganar mai muhimmanci ce tace "amma Ra'uf mai zai hana ka amince da maganar Dadynku ka auri Safiyya",shiru yayi kana yace" Ammi bawai na'ki bane amma banaso yarinyar nan ta shiga wannan zuriya mai 'dunbin son zuciya da nuna fifiko zatasha wahala duba da ita 'din wacece baikamata nina zama silar cutar da wannan baiwar Allah 'din ba"Shiru Ammi tayi tana sake tunanin maganar Ra'uf datasan gaskiya ce itakanta Ammi ta fiso Safiyya tayi aure a inda zata huta da bazata fahimci ita 'din wacece ba koda har abada bazatasan wacece itanba, Da haka Ammi ta mi'ke da cewa to zan bincikoma tana duben agogon falon ta cigaba da cewa" Safiyya fa ta gama shirin tafiya gidan Shureim kai take jira"ya 'dan saki fuska yace "Ammi na manta gwara da kika tunamin danma banason nakasance mai sa'ba alqawari amma da bazanje ba bare naje da Safiyyan"Ammi tace bamai shiga fa'danku kai da Safiyya idan anshigama aji kunya" Murmushi yayi yace ai kuna gaf da daina jin kunyar "Ammi ta fice tana cewa"kanku dai akeji dai"
'Karfe hu'du na yamma Ra'uf ya sake wani wankan ya shirya cikin kananun kaya ya sauko 'kasa masallaci ya wuce ganin bakowa a falon a masallaci ya ha'du da Dady suka shigo gida tare yana tanbayarsa yanayin aikinsa,a falo suka yada zango inda Dady yake sanarmasa company yabiya da shine dalilin rashin dawowarsa gida da wuri wanda Dady yake da hannun jari a ciki Ra',uf yace "To Dady Allah yayi jagora" yace Amin Babban mutum sunan da Dady yafi kiransa dashi Murmushin sunan da Dady yakirashi dashi yayi yana tuno mai kiransa da sunan da yake tuno rabuwarsu ta 'karshe da ita ya'dan dubi Dady yace" Dady dama maganar kayan da za'a turawa Kawu Mukhtar shine nakeso muyi inasan taimakon kasata yakamata ina bada taimako asibitoci ko yaya ne"Murmushi Dady yayi yace "hakan yana da kyau Ra'uf,Dukda kasartamu akwai arzi'ki amma babu taimako kowa da yasa kansa kawai ya sani rayuwar wani bata damesa ba ,shiyasa har yau 'kasartamu babu cigaba duk mai arzi'ki burinsa sa 'ya'yensa makaranta mai tsada koma subar kasar da karatun gaba 'daya maimakon muyi 'ko'karin bun'kasa 'kananan gurabe zuwa manya manya saboda ko 'kasashen nan damuke ciki ta haka sukayi arzi'ki ,amma saikaga mai arxiki a garinsuma bayason zama da wata 'yar dama tasamesa wani ko gini bazai iyayi a garinsuba, saboda yana tunanin 'kauye ne baya tunanin raya kauyen nasu,wani kuma koda yayi ginin sai yace bazai zauna ba koda aikin gwamnati yayi yayi retire ,ko kuma 'dan kasuwa ne da zai iya zuwa yadawo garinsu,ko kuma wani 'yan mola acewarsa su suka koresa daga garinsu abinda babu mai raba bawa da arziki sai mutuwa,amma sai dai yaje ya raya mahaifar wasu, kuma wasu da yawa idan wata dama tasamesa bazai iya turo ta garinnasu ba ko 'kasarsaba a'a sai dai yabarsu garin wasu kasar wasu Suma marasa 'karfin cikinmu basa baws masu son taimakon cikinmu kwarin gwiwa kuma suma tunaninsu su samu damar suyi fiye da abinda wasu sukeyi shiyasa bama cigaba saboda yadda kowa a yanzu haka kansa ya sani da 'ya'yansa, Nagode wa Allah da 'dana yayi tunanin abu mai kyau Allah ya kara dafamana "Maganar Dady ta shigi Ra'uf sosai yana tunanin rayuwa yadda tazama yanzu ya amsa da cewa" Amin Dady nagode da nasiharka gareni"da wannan zancen Safiyya ta iso falon takatse musu firar ta hanyar sallamarta suka amsa mata ,Inda tana kokarin zama tace Dady shine aka ki kirana muyi fira bakomai zamu rama nida Ammi ,Dady yayi murmushi yace yawwa ai dama munfisan haka gwara kowa ya za'bi gwaninsa" dariya tayi Ra'uf yayi Murmushi yace"ke ina shirin naki "Murmushi tayi tace Yaya nifa nagama shirina dama kainake jira kace nafito" harararta Ra'uf yayi yace"wato nine ma zan je nace miki na shirya?kajitafa Dady",Dady yace"babu ruwa na dashiga zancenku"Ammi ta fito daga kitchen da ruwa na gora a hannunta ta iso da sallama ta zauna kujerar kusa dasu tana kokarin bude gorar take cewa "yanake jiyo hayaniyarku Abban Safiyya ince dai yaran nan ne da basa gajiya da kan kara" wato Ra'uf da Safiyya,Dady yace "kamarko kinsani Asma'u" labari ya bata tace ai saika gaji Indai wa'dannan ne gidan Shureim zasu shine suketa wannan lugyigyita maganar"murmushi Dady yayi yace",ai shine nace bamai shiga fa'dansu"Ammi ta kalli Ra'uf tana canza maganar da cewa "kai wai ina sa'kona" Ra'uf yace "Ammi Safiyya natarar a falo na ajewa"ya kalli Safiyya yace" Baki kaiwa Ammi sakon dana aje ba kuma kinsan na tane"Safiyya tace" Ammi na ajemiki saman madubi danaje 'dakin naga kina barci"Ammi tace" to shikenan jeki ki shirya Ku tafi da haka Safiyya ta mi'ke koda Safiyyan ta iso falon har Ra'uf ya mike tabi bayansa suna yima su Dady sai sundawo.
Basu jima suna tafiya ba suka isa gidan Shureim tarba ta musamman aka musu koda cewar su ba baki bane a gidan Irfan Ra'uf ya dauka ya fice shida Shureim daga falon bayan sungama gaisawa suka bar Safiyya da Inteesar. A jikin motar Shureim su Ra'uf da Shureim suka tsaya Shureim da ya 'dan kalli Ra'uf yace"Abokina kai yaushe zakayi aure kadubafa ni gani harda 'da 'daya,Ahmad kuma 'ya'ya biyu haba Ra'uf ka'din baka tunanin kaima kayi aure kobazakayi dan komaiba ai kariqa duba damu abokanka duk munyi amma kaida kurinka bare kace shiya hanaka yi haba Ra'uf har yanzu tunanin wancen mikin nasan shike dawainiya dakai dukda maganar Ahmad bana tunanin a yanzu abin maiyiyuwane dukda kai din banama sha'awar hakan a karo na biyu domin babu tabbacin zama kasamu abin "kalaman Shureim sunkara tasiri garesa bayan na Ammi data masa Saidai shifa har wayau babu wani tunani a ransa na wata budurwa tun bayan abin da yafaru da yake ganinsu kamar yau batare da an shawarceshi ba aka yanke waccen kyakkyawar ala'kar gani yake da yanzune dasai ya yi fito na fito daduk mai gudunsa da wancen ran da yake gani alkhairine a dunbin rayuwarsa da to zan duba yabi Shureim kawai suka kara ta'ba hira daganan suka karasa masallaci said wajen takwas na dare suka yi musu sallama suka koma gida Inda Ra'uf ko a mota bai kula Safiyya ba ita keta zuba surutunta iyakacinsa da ita ey ko a'a har suka isa gida bai tsaya kula kowa a falon ba Ammi tace ga abincin kazo muci yace yaci a gidan Shureim daganan ya haye bene Ammi da Safiyya damai aikinsu basu damu da maganarsaba dan sunsan baida tsawaita magana wani lokacin Safiyya ko zama tayi ta zuba abinci ta fara shiko Ra'uf kai tsaye dakinsa ya sake ya wuce watsa ruwa yayi sallahr isha',i yayi Azkar kawai ya kashe wayoyinsa ya haye gadonsa da yaketa juyi ya kasa barci sai tunani tunanin da kowanne dare saiyayi rabuwa ce ta nuna iko aka yi gurin wanzuwar rabuwar saidai yaci ace yamanta da wannan abun amma Sam yakasa mantawa yakasa manta waccen fuskokin da fuskar da a cikin fiskokin yafi tunawa dama muryar waccen fuskar ya Allah ya furta ya rasa yadda zaiyi ya manta da waccen rayuwar ta baya da abinda yafaru garesa a waccen rayuwar.
SADIYA KHALI✍🏽
comment#
Share#
Vote#*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Ibrahim Khali
7
Kwanci tashi ba wuya gurin Allah yau AbdulAhad kwanansa Hamsin da rasuwa anyi addu'ar Arba'in da Abba bukar ya hutar dakowa sukayi a masallaci,Rufaida da taji karar wayarta ta duba ganin maikiran yasata 'dagawa karon farko Samiha macen da bazata iya mantata a rayuwarta ba tare sukayi rayuwa mai cike da farin ciki da kaunar juna inda lokaci guda wannan rayuwar tazama tarihi ita 'din Samiha jintatake a zuciyarta fiye da tunani,Da sallama Rufaida ta 'daga wayar da Samiha ta amsa takuma kara da cewa "habawa Rufaida ace sai na kiraki zaki tunani"murmushi Rufaida tayi da ita kadai tasan fassarar abinta tace"a'a Samiha ku'din wayar ne babu na kira bama nida caji sai yau nasamu" cikin firgici Samiha tace" Rufaida meke faruwane kiyimin bayani"hawaye shar sune suka biyo kuncin Rufaida batareda tace komaiba kawai ta katse wayar tana tuno cin fuska da cin zarafin da akemata a gidan kuma bata fuskar kowa ba sai Hajiya Jamila da Ruqayya AbdulMalik da Abba basa zama basusan komaiba cajin waya ma basa bari tayi duk dakin datasa caji sai yara sunbita suna kokawar game kwanakin baya jefarmata ita sukayi ta kara tsagewa,idanko tace wani abu saitaga kamar bata kyautaba tunda 'ya'yan Hajiya Kubra da Aunty Amina ke hakan itako a yadda take daukarsu tamkar umminta Hajiya Jamila da Ruqayya ke mata suke uwa da makarbiya,Dakin Hajiya Jamila da take tunanin sawa don samun sauki to tasan ko giyar wake tasha bazata je da zunmar sa caji ba hakananma idan taje kyara ke hadasu bare kuma taje da zunmar wani abu,dukda itama dakinta akwai komai saidai matsalar dayace babu caza tata tana abuja ,tsangwama gori datake sha ga mutane biyun dukshi yafi damunta mutanan datake samun farinciki a gunsu suma hotone idan mai gidan bayannan dan Hajiya Kubra da Aunty Amina basuda hayaniya shiyasa basa shiga abinda za'ayi wata hayaniyar dasu sai daifa idan sunga abin nanema ya tuke suke uwa makarbiya
Samiha data sauke wayar jin Rufaida ta yanke,yasata kurawa wayar ido,tana tunanin mai ake da wacce rayuwar ta baya banda kaddarori mai zaisa ta baro aminiyartata da aka shiga hakkinta gurin lalatamata mafarkinta,kuma akaki sanar da ita dalili dukda batasaniba amma akaran kanta tasan har ya'u akwai tabo a zuciyarta,an zalinci wancen ran,sai dai a yanzu fatanta inganta rayuwar amintacciyarta ta,mai dunbin muhimmanci a rayuwarta tundaga kuruciya har kawo yanzu dukda nisan zangon da sukayi da juna bawai mota ba a'a nisan har tafiya banbancin kasa dake tsakaninsu,Rufaida dataci sunan Rufaida ta fado dakin da take tafa'da jikinta tana cewa Mom Dadynmu yadawo"cikin harshen nasara take maganar dashi suka fi iyawa a yanzu haka,Murmushi Samiha tayi tace to sannunsa da dawowa,Ina Little din"yarinyar ta dan ta'be baki tace yana hannu Dady ni yaqi daukata murmushi Samiha tayi tace mata banda abin Rufaida aike kin girma baki ganki kinkusa fina girma ba" Rufaida ta saki dariya tace Mom ashe nima Little ya kusa fara kirana Mom"tace "sosaima"tana dariya sallamar Ahmad ce ta katsemusu firar sannu da zuwa Samiha ta masa ya amsa da yawwa da murmushi fuskarsa ledar dake hannunsa ta ansa harzata shigar da ledar Kitchen yace tadawo ta zauna zama tayi tsakiyar yaran,da Little ya mika hannu ta daukesa murmushi Ahmad yayi yace" habawa yaro zaka nemi na daukekane nima naki"ya fada yana dungurekan Little yafara alamun kuka ganin haka Rufaida tasa dariya ganin hakan da little yayi 'yar uwarsa tana dariya shima yafara dariyar,suma su samihar dariya abin ya basu ,Ice cream din dake ledar Ahmad yace Samiha ta ciromusu susha ta dauko suka fara sha shida yaran da Samiha tace ita ta koshi,ganin haka yasa Ahmad barwa yaran susha Rufaida itake bawa Little a baki,Kallo Ahmad yabi Samiha dashi jin tace batasha ganin baigano komaiba yasa yace"Samiha maike damunki? kefa kikace da zantafi na tahomiki da Ice cream dinnan" Samiha tace "Eh nice" Ahmad yace "to fadamin maiyasa kikafasa sha" ta dan canza fuska alamun damuwa kafin tace" Dadyn little yanzu mukagama waya da Rufaida da alamu bayan rasuwar mijinta tana cikin damuwa"ya 'dan gyara zamanshi yace "Inajinki damuwa kamar tame"ta basa labarin wayarsu da Rufaida ta kara da cewa masa "nafahimci kamar takuramata ake gidan Abba Bukar" Ahmad da mamaki yace"dama bata Abuja"Samiha tace"Eh kasan Barrack ne gidan ba wanda ta sani sosai acan shiyasa Abba Bukar yace ta zauna harta gama takaba takoma gida"Ahmad yace to gidan iyayentafa ko 'yan uwansu na Zariyan,aita zauna a can badai gidan nasu AbdulAhad ba"Samiha tace"kamanta Abba Bukar yayan Abba ne saidai nikaina saida nayima Momy magana yaza'ayi abarta gidan surikai tayi takaba sai kace batada gidan uba koma gidan Gwaggo ai gwar a takoma Ahmad yace "to tunda duk gidane ai ba matsala kuma kwana nawane"Samiha tace "hakane" nan Samiha ta yanke shawarar turawa Rufaida ku'di ta account koda ka'danne dan itama basu gareta ba dan business din datake nema kudin ke shigo mata"dubu 20K ta turamata acewarta sunyima Rufaida ta wuce karfin kyautar 20k dubu ashirin a wajenta,amma dai tasan sun isheta wasu 'yan bukatun ,dan ita kanta Samiha tasan komai dangane da wannan gadaddar kiyayyar daga Hajiya Jamila,shiko Ahmad tausayin yarinya karama yake kai tsaye batada sa'a a rayuwarta ta 'bangarori da dama zaikirata ,shi kansa da basa tare gari daya abubuwa da dama yasani harma auren nata da AbdulAhad da wani abokinsa Habib yake basa da suke unguwa daya dasu AbdulAhad din"saidai yana mamaki da wuya ko ita Samiha Rufaida ta fadamata abinda akayi mata saita tutance yarinyace mara hayaniya,yana tuno wancen shekarun da yakeji kamar shine a cikin waccen rayuwar
Jin karar wani kiran yasa Rufaida yasata duba mai kiran dan tasan idan Samihace bazata dagaba dan tasan tanbayoyin da zata yi mata sunada yawa akan damuwarta itako batasan dagawa aminiyarta hankaki ganin Luba ce mai kiran yasa Rufaida da sauri daga kiran bayan yin sallama suka dan gaggaisa tana tanbayar Luba na tanbayar Rufaida kwana 2 matsalar caji tafadawa Luba Luba da tasan Zariya akwai wuta kawai jin Rufaida tayi dan tasan akwai dalili babba da ita kanta Luba a dan zaman da sukayi da Rufaida tasan zaman hakuri take da surikarta da yan uwan surikartata dukda ba labari take bata ba amma dai tana fahimtane kuma Abban Yusuf wato Kabir yana dan bata labari wani abun kila wayar suka anshemata duk Luba ke wannan tunanin lokaci guda haka dai suka cigaba da gaisawa har zuwa wani lokacin sukayi sallama,jin karar message suna wayar yasa suna gama wayar ta duba mumushi yayi ganin sakon kudin da Samiha ta turomatane ,Allah sarki Samiha Rufaida ta fada a fili tana gama dubawa ta yanke shawarar kiran Abdulmalik ya tawo mata da charger tunda da kudi a account dinta saitamasa transfer da yake tukinsa hankali kwance yaji karar motar ya tsayar ya duba mai kiran ganin Rufaida yasashi katse kiran yabi saida suka kara gaisawa ta fadamasa sakonta da to kawai yabi Rufaida a yakatse wayar yana fadamata tuki yake a ransa yana tunanin Rufaida tasan tanada bukatar wani abu amma bazata fadaba saidai tace a siyo ta bada kudin haba yayima Rufaida siyayya tabasa kudin ai badai shi Abdulmalik ya amsa ba,shi tunaninsa Rufaida tanada komai bakuma zata nema ba shiyasa bama ya siyamata,itako Rufaida tunaninta idan ta tanbayesu mutanen gidan wani abu kamar bata kyautaba ganin batasan aljihun kowannensuba,Kuma ita idanma ba dole ba batasan tayi tanbayar abata abata dukdai Jini daya suke.*JININMU 'DAYA*
Sadiya Ibrahim Khali
(Sadiya Khali)
8
Rukayya da take zaune a falo itada Hajiya Jamila sauran yara sunyi shirin islamiyya suntafi sai Yasir kadai ya rage a gidan da shiko yana gurin Aunty Amina yanama babynta Ummu kursum da take goyo wasa ,AbdulMalik a haka yashigo yasamesu da sakon Rufaida a hannunsa a leda abindama batace ba saida yasiyomata yayi musu Sallama suka amsa masa Rukayya tace "Sannu da zuwa Yaya Abdulmalik"ya amsa mata kamar anmasa dole da" yawwa"Hajiya Jamila tace "ya aikin naku"yace "Alhamdulillah"daganan yasa kai zai wuce bangarensu ganin sakon Rufaida a hannunsa kuma baiganta a gurinba yasa shi cewa" Umma ina Rufaida naga shiru banji motsinta ba" baki ta ta'be tace "tana kitchen ta doramana abincin dare" ya 'dan juyo ya kalli Ruqayya yace"Umma ita Ruqayya ai yakamata taje suyi tare"tsaki Hajiya Jamila tayi tace"Abdul malik ka kiyayeni fa bandama shirme irin naka ina zaka hada Ruqayya da Rufaida kodai kai wawane sai haka tuntuni nake nunama banbancin dake tsakaninsu"AbdulMalik yace"haba Umma ni haryau bana ganin banbancinsu a zahirin gaskiya ma Rufaida tafi Ruqayya dangantaka da gidannan ta kowacce fuska gaskiya"Hajiya Jamila data fusata tace" to yima Ruqayya gori cewa tazo gidanku cin arziki arzikin da duka yaushe ubannaka yayi kuma kasani komai zakace idan ni kahanani fa'dar banbancin dake tsakaninsu to bazaka hana duniya fada ba,abinda bakowanne biladama zai iya ba saiga wancen matsiyacin yayi da kuma waccen...."AbdulMalik ganin Ummantasu bazata tsaida wannan cin zarafinba yasashi harda saurinsa dan yasan indai zai biyemata tone tone zatayi abinda yasan yana daga cikin kaddarorinsu to akanme za'a dinga jagwalgwala magana dashi haryau yake tantama ga waccen labarin kanzon kuregene da saboda suma suji waccen tsanar kamar yadda ita kiri kiri take nunawa ga wancen rayukan masu matukar muhimmanci a rayuwarsu tabasu labarin da babu kamshin gaskiya a ciki dukda dai mahaifiyarsu ce tabasu,to shi koda ma hakanne shi baiga abin da zaisa yaki 'yan uwansa ba danshi yama jahilci labarin tunfarko kodama gaske ne,Rufaida da take kokarin shigowa falon ta fadawa Hajiya Jamila ta gama abinda tasata mai zata kara dorawa a kunnenta ta fara jiyo maganganun Hajiya Jamila da yaranta data fahimci akanta ake maganar bata karasa jin maganar b takoma kitchen din gudun kada AbdulMalik yazo yasameta anan da haka yasata komawa kitchen din dukda bawai tsaiwar ta gulma bace a'a kowa 'dauka zaiyi itace tana kuma tsoron Hajiya Jamila taji Abdulmalik ya mata magana ta zata ra'be take musu shikenan kuma abin ya zama abin magana a gidan tarasa wannan wanne labari ne kuma wanne tarihi ne dayake shafar rayuwarta har yakawo tsanar da Hajiya Jamila a duk cikin zuriyarsu sai tace tafi nuna musu dukda ita 'din ba zuriyarsu bace kai tsaye a'a aure yakawota zuriyar tasu amma tasan abune babba karon farko ta fahimci shine ya raba wancen ran mai muhimmancin gaske a zuciyarta shine yajawo tafiya mai nisan gaske a tsakaninsu da haryau babu waiwaye,tanbayar zuciyarta take yaushe zatasan labarin waccen rayuwar ta baya da tasan tabbas itace rusa waccen rayuwartata kuma take cigaba da shafar rayuwartata dumin da taji a kuncinta yasata sa hannu ta duba abinda tasan tabbas shine dama ta gani wato hawaye ,tuno waccen rayuwartata dama wadda takeyi yanzu shine abunda a kullum yaake kokarin da gula lissafe lissafen rayuwarta dama tunaninta kai tsaye zama tace Sallamar da taji AbdulMalik yayi kitchen din yasata saurin daidaita nutsuwarta ta goge hawayenta kafin ya karasa shigowa amsa masa sallamar tayi yayi murmushi ya karasa inda take tsaye tana kokarin cemasa "Yaya sannu da zuwa"Ya amsa da" yawwa Rufaida"kafin ya'dan ha'de rai yace "Rufaida"ta amsa da