Showing 69001 words to 72000 words out of 86533 words

Chapter 24 - JININMU DAYA HAUSA NOVEL

wadda tarasa mafadi,kuma kenan gidan ubanki ne? da kikazo kikayi shame shame kina cin arziki mai kika hada danan gidan,to ita din ta fiki matsayi da komai anan gidan,donke arzikin Umma kikeci,don koni Rufaida ta fiki matsayi a zuciya ta"
Cikin bacin rai da hawaye taf idon Ruqayya tace
"Naji ta fini matsayi anan gidan amma ita da ba'ada tabbaci akanta shine,zaka fadamin magana akanta"
"Tabbacin ubanki ne va'ada shi akanta,ke ba'ace ba'ada tabbaci akan Ku ba,saike zaki fadawa wata"fadin AbdulMalik
"Wallahi mu anada tabbaci akanmu,ita da uwarta take karuwa fa niko mai uwata tayi wallahi muna da banbanci nida ita fiye da tunanin mai tunani"
AbdulMalik jin maganar da Rufaida keyi yasa ran Abdulmalik ya kara baci ya mike ya nufi Rukayya zai doketa Rufaida da hawaye ya cika idanunta ganin haka yasa Rufaida mikewa tayi gurinta tace
"Yaya AbdulMalik karka doketa kaya hakuri"
Hannu AbdulMalik ya dagawa Rufaida ya shiga dukan Rukayya
Da kyar Ruqayyan ta kwaci kanta tayi gurinsu Hajiya Jamila tana kuka wiwi
Abdulmalik ya bita shima Rufaida ta biyo bayan sa tana kiransa ya dawo amma baya jin ma mai take cewa tana hango Rukayya tana maida lumfashi yayi kanta ya fara dukanta cikin zafin zuciya ba tare da ya bi ta takan mutanan dake rirriqesa ba
Tsawar da Abba Bukar ita tasa AbdulMalik sakinta yana maida lumfashi
Bai saurari kowa ba ya fara tafiya da niyyar barin gurin Abba Bukar yace
"Dawo nan"
Dawowa yayi ya sunkuyar da kansa
"Rukayya me ya hadaku"cewar Hajiya Jamila
Rukayya tana rusa kuka ta dago kanta ta nuna Rufaida wata hararar Rufaida Hajiya Jamila tayi Rufaida ganin haka yasa Rufaida kai kallonta kasa
Ganin ta nuna Rufaida Abba Bukar ya kalli Rufaida yace
" Rufaida mai ya hadaku da Ruqayya?"
Idon Rufaida ne ya ciko da hawaye Abba Bukar yace
"Kiyi min bayani ina sauraranki,banaso wani hawayen banza kiyi laifi kizo kina hawaye"
Jin maganar Abba Bukar yasa Rufaida goge hawayenta ta zayyana masa duk abinda ya faru
Abba Bukar yana gama ji ya dubi Ruqayya cikin bacin rai yace
"Yanzu Ruqayya dama baki da mutunci ina ganin kamar zaki fita daban a cikin 'yan uwanki,shiyasa ma ke na amince ki zauna na lokacin da Jamila tace min zaki yi wato ashe har kin fisu ma,dama zaman danki kuntatawa Rufaida kika ce zaki yi"
Rukayya tace
"Abba dan Allah kaya hakuri ba haka nake ba Aunty Jamila ce take cewa na rika yi mata"
Abba Bukar ya jinjina kai yace
"Wato ita ke baki labaran karya da karai rayi akan Rufaidan ma ko?"
Rukayya ta girgiza kai tana kallon Hajiya Jamila da take girgiza mata kai kar tace ita ce
"Ki fadamin gaskiya bana son karya ita ke baki ko kuwa kifadamin wake baki"
Abba Bukar yayi maganar yana kallon Hajiya Jamila yadda take girgiza wa Ruqayya kai
Rukayya da duk ta tsorata tace "Eh Abba ita ce,tuntuni take bamu wannan labarin"
Abba ya jinjina kai ya kalli Hajiya Jamila ya soma magana
"Jamila kin bani mamaki amma ba abun mamaki bane nasan fiye da haka ma zaki yi saboda bakya tunani kafin ki aiwatar da abu sannan zai wuya idan kinyi badaidai din ba kiyi danasani,amma nasan akan wannan maganar tabbas zaki yi dana sani koba yanzu ba,sannan babu wani matakin da zan dauka akanki amma tabbas ranar dana sani zata zo miki,sannan yau ba sai gobe ba inaso Rukayya ta barmin gida na dama mahaifinta yayi min waya yanaso Rukayya ta koma gida saboda maganar aurenta da zai aurawa dan abokinsa ita da kune kuke ziga yarinyar karta yarda da auren,batun Rufaida kuma baza ta bar gidan nan ba sai sanda na tsara zata bari"
Da wannan maganar Abba Bukar ya maida kallonsa ga Abdulmalik yace
"Malik nasha fadama kai ba mace bane ka daina shiga fadan mata,banason karajin irin haka ta faru"
Abdulmalik yace cikin ladabi
"To Abba zan kiyaye insha Allah" amma a ransa baya tunani zai hakura muddin yaga ana kwarar Rufaida don shi mutum ne da bayason zalinci
Da haka Abba Bukar ya bar gurin Abdulmalik da Rufaida suka take masa baya
Hajiya Jamila jikinta duk yayi sanyi ta kama hannun Ruqayya,Ruqayya tayi saurin fincikewa daga rikon da Hajiya Jamillar tayi mata ta bar gurin don gani take duk Hajiya Jamila ce ta jawo mata koma mene yanzu ba ta da wata daraja a idon kishiyoyin Hajiya Jamila dama Rufaida ga uwa uba Abba Bukar,da gatanta da komai bawai arziki za'a nunawa mahaifinta ba bakomai ba amma ta ja an yi mata wulakanci har haka kum AbdulMalik ne yayi mata suma sauran matan gidan sumi sumi suka bar wajen aka bar
Hajiya Jamila ita kadai ita mikewa tayi ta bar gurin.A daki ta samu Ruqayya tana hada kayanta Hajiya Jamila ta dafa Rukayya tayi saurin cire hannun Hajiya Jamila daga jikinta ta soma magana
"Kinga Aunty don Allah ki kyaleni,kinsa an cimin mutunci,nima kuma kina zuga ni na ciwa wata,dama nina gaji da zaman gidan nan koda ba'a koreni ba,tafiya zanyi,gwara naje nabi umarnin Abba da na cigaba da zama anan,ki riqa gulmata na tare a gidan ki bayan wanda nake so dinma baya duniyar,amma kinsa ni na zauna ina goga kishi da matarsa bayan ita bata damu da muba"
Hajiya Jamila da ranta ya fara 'baci ta kalli Rukayya tace
"Kinga Rukayya a haife dai kinada tabbacin nayi 'yata hudu ma dake,ba zai yiyu ki zauna kina jeramin magana ba nina jawo miki dukan?ince dai ke kika jawo wa kanki,sannan dama fa ba wanda ya rike miki kafa kuma karki min sharri ni bance ki zauna a gidana ba,dama a zagwaigwai dinki ne yasaki zama a gidan nan,amma sanin kanki ne na nuna miki banaso saboda nasan baki da hankalin iya zama da mutane,baki iya rufe sirri ba,kinzo ni kin hadani da miji na cikin kishiyoyi kin kwance min zani"
"Au haka zaki ce,kin mata harna hada kayana kila kika ce na zauna,ke ai abinda kika yi na fada nifa kinsa danki ya kwance min zani a kasuwa ya kuma yimin shegen duka kika zaunar dani"
"Karfa kimin rashin kunya Rukayya ni zan sa AbdulMalik ya doke ki bakin halinki dai yasa ya doke ki"
Dariya Rukayya tayi tace
"Su bakin hali manya rashin kunya manya,aishi dama gwano bayajin warin jikinshi,nifa bari kiji baki isa ba wallahi ki fadamin magana na kyaleki,idan kina yiwa Rufaida tana kyaleki,to ni baki samu wannan damar ba ba kuma zaki sameta ba"
Haka dai suka cigaba da musayar kalamai tsakanin Ruqayya da Hajiya Jamila saida Hajiya Kubra ta jiyo tazo ta yi musu magana ta kuma shiryawa Rukayya kayanta haka aka rabu da Ruqayya da Hajiya Jamila kaca kaca harda su gore gore (to dama ba dan Allah aka shirya zaman ba)
Da Ruqayya ta fito saida ta shiga dakin Rufaida ta shiga da sallamarta Rufaida ta dago da kanta daga kallon wayar da take ta yi murmushi ganin Rukayya ce ta amsa mata sallamar jikin Rukayya a sake ta karaso inda Rufaida take zaune a kujera itama ta zauna kusa da ita ta kalli Rufaidan ta soma magana
"Rufaida don Allah ki hakuri ki yafemin abubuwan dana rika yi miki Wallahi Umma ke zuga ni"
Murmushi Rufaida tayi tace
"Haba Rukayya karki bata bakinki nidama ban taba rikonki da komai ba"
"Yawwa Rufaida nagode"
"A'a ki daina yimin godiya,yanzu yaushe ne bikin naki ban taba jiba ko a firarku keda Umma"
"Hmm kedai bari nice dama banason auren da tuni ma anyi har ankawo kudi fa jin yaya Wahid zai yarda da auren my shine naki yarda asa ranar,to jiya Abba ya kirani yace na shirya na dawo gida,shi bazan bashi kunya ba yasa bikina nanda wata biyu masu zuwa"
"Allah sarki,a ina zaki yi auren?"
"Adamawa ne"
"Lah kinga inada kawa tana aure acan, zan hadaku insha Allah"
"OK 'yar inace?"
"Kano"
"OK,ki bani Lambarta"
Rufaida ta duba wayarta ta fado mata lambar Nasiba tasa a tata wayar tayi saving daganan Ruqayya ta amsa ta Rufaidan taayi saving da haka Rukayya ta mike tana cewa
"To Rufaida nizan tafi,sai kinzo biki na nasan sannan kin dade da fita takaba tunda yanzu ma baifi saura kwana goma ba ki fita"
"Eh hakane,amma kinsan indai na koma Kano ba lallai Abba ya yarda"
"Nasan zai yarda insha Allah,sai dai.idan kece bazaki zo ba zaki ce"
"A'a zanzo dama yardarshi nakewa kokwanto "
"Idan lokacin yayi zan kira ki ki hadani da Ummi kinga saita fadawa Abba"
"Murmushi Rufaida ta yi mata tace
" to shikenan"
"Kinga zan tafi va muyi sallama da yasir ba"
"Eh wallahi babu rabo hakanan suka jashi Tahfiz yau din"
"Babu komai Idan kunzo biki zan gaji da ganinsa ma indai da zan iya hakan"
Dariya Rufaida ta yi tace
"Oh saikace idan munzo din shekara za muyi"
Da haka Rukayya ta fito sukayi sallama da Rufaida Rukayya tana sake rokar Rufaida ta daure tazo bikinta
Bayan fitar Ruqayya Rufaida ta dan goge kwallar data taru a idanunta bata taba tunanin abubuwa zasu sauya lokaci kusa haka va,yanzu ko a mafarki idan aka ce mata Rukayya zata sota sai ta Musa saboda irin kiyayyar da Ruqayya ta rika nuna mata,lallai Allah shine mai juya al'amura tana da yakinin watara na komai zai zama tarihi,insha Allah kamar yadda kiyayyarta da Ruqayya ta zama labari.[9/25, 10:23 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil
49.
RA'UF POV
"Ammi na yunwa nake ji" Ammi Asma'u ta juyo ta harari Ra'uf ta cigava da tafiyar da take
"Ammi magana fa nake,ina jin yunwa,ki samamin abinci na ci" Ra'uf ya sake maimaita maganar
Sai sannan tace
"Ni zan kawo ma abincin kenan,kana kwance sai dai ayi ma komai"
"Oh Ammi yanzu ba zaki kawon ba,shiyasa banso aka tafi da Safiyya ba da tuni ta kawomin"
"Ita ce zata jure dama"
"Au banda ke Ammi,shikenan bari na kira Dady a waya na fadamasa"
"Au Da Dadynku zaka hadani yaro ka dade baka hada muba".
Da ganan ta bar gurin
Ra'uf ya saki murmushi ya tashi zaune daga ki shingidar da yayi jikin kujera ,wayarsa ya jawo ya danna ya kara a kunne a ringing biyu aka dauka muryar Safiyya ta shiga kunnensa da ta soma magana da yaran indiyanci da kuma turanci
"Assalamu Alaikum,my Yaya"
"Wa'alaikumus salam,kanwata ya gida da kowa da kowa"
"Lafiya kalau"
"Ya Nigeria,ina daru Hajiya"
"Tana lafiya,amma Hajiya fa ta rage daru,muna zuwa ta fara korafi kai yaushe zaka zo"
"Kina nufin bata bata ranki ba"
"Eh tanbayarta taka ce kawai muna zuwa"
"Kai amma naji dadi"
"Yaya ysushe zaka zo,wallahi sun damu kazo Family 'dinka,gaskiya suna sonka sosai, dana ga yadda suka damu dakai nima sai nakeji ina ma ace watarana na hadu da nawa Family..."
Ra'uf da hawaye suka tarar masa jin maganar da Safiyya keyi yace
"Haba Sophie maiyasa kike da son dawo da abinda ya riga da ya wuce,mune familynki a yanzu haka,dan Allah ki cire komai a ranki"
"To shikenan Yaya insha Allah"
"Yawwa kanwata,yanzu kina ina ne"
"Ina gidan Aunty Malika a can na sauka"
"OK ina Auntyn"
"Ta shiga kitchen"
"Oh shine ba zaki je ki taya ta aiki ba"
"Oh yaya kasan nafi iya abincin nan,karna mata jagwalgwalo tace ba dadi"
Yayi dariya yace
"Oh Safiyya idan kinyi aure fa,kuma kinsan dai a gida za'ami ki aure gwara tin wuri ki sauke wa kanki iyayi"
"kai Yaya ba fa iyayi bane"
"To menene"
Canza maganar tayi tace
"Yaya jiya munje asibitin daka gina da Abba ,yayi kyau sosai ni ban dauka yayi kyau haka ba dana gansa a waya sai da naganshi a fili"
Dariya Ra'uf yayi yace
"Ya kikaga sunan asibitin yayi kyau kuwa"
"Sosai ma RJM DANBATTA"
Dariya Ra'uf yayi yace
"Yawwa kanwata idan zan sake gina wani,SJM DANBATTA zansa"
"Kai amma naji dadi Yaya"
"OK yaushe zaki tafi Kano"
"Abba yace tare zamu tafi,sai ranar Asabar ta sama zai kaini 'danbatta nayi kwana biyu"
"Ok Allah ya kaimu"
Sun jima suna waya daganan su kayi sallama
suna gama wayar kiran Ahmad ya shigo wayarsa ya daga
Ahmad yana jin Ra'uf ya daga yace
"Oh kodai da budurwa kake waya ne,ina ta kira ana suna nuna min user busy"
Ra'uf yayi Dariya yace
"Ni budurwa,Safiyya ce muke fira"
"Ok sun tafi Nigeria ko?"
"Eh mana,kai yaushe zaka koma ne,kaje garin mutane kayi zamanka"
"Wallahi sun hanani tafiya sun riqeni"
"Oh kai tafiyarka mana"
"Eh dama haka kawai za muyi shiryeye muke, Ni kaina nayi kewar gida over"
"To yanzu ya little Rufaida ban tanbayeta ba"
"Tana lafiya wato bazaka tanbayi little ba sai Rufaida"
"Eh mana,ai ita takwarar masoyiyar farko ce,ko zaku bani aurenta tunda na rasa waccen
Ahmad yayi dariya yace
"Tsohon zan bawa 'yata sai dai kaje kayi zawarci gurin Rufaidan"
"Ina ma za'a bani ita yanzu da sai naje wallahi"
"Lallai Yaya Ra'uf bazawarar zaka aura,sun hana ka aurenta tana budurwa yanzu kawai tana bazawara kaje ka nemi aurenta"
"Eh mana dama Allah yayi bani zan fara aurenta ba ne,kuma laifin fa su Abba Sule ne sune silar da aka hanani aurenta"
"Haka dai kake tunani,amma dai sunyi niyyar dama aura mata dan uwanta ne kawai"
"Karkayi wannan tunanin Ahmad,haka Allah ya tsara dama"
"Haka ne kam,wallahi Yaya Ra'uf Rufaida abar tausayi ce,gaba daya abinda 'yan uwanta ke mata basa kyauta mata gashi Umminta bata isa tayi magana ba,Samiha tana bani labarin komai,kwanaki ma har kudi Samiha tasa na turawa Rufaidan ni na rasa meye matsalar"
Ra'uf da jikinsa yayi sanyi yace
"Maike faruwa ne Ahmad kayi min bayani ba Rufaidan na kano ba"
"Ko d'aya tana Zaria"
"Amma su iyayenta sun manta da abubuwan da suka rika faruwa suka barta acan"
"Zumunci suke tunani shiyasa suke yin shiru nake tunani"
Cikin bacin rai Ra'uf yace
"An taba zumunci da zalinci,ni wallahi mutane mamaki suke bani don da bana ka bane idon yana tare dakai kaita zalintarshi"
Da haka suka cigaba da tattaunawa akan maganar

RUFAIDA
AbdulMalik da shigowarsa falon kenan ya idanunsa suka sauka ga Yasir yana zaune shi ka'dai a falon sallama yayi Yasir da yake game a waya ya dago kai yana murmushi yace
"Wa'alaikumus salam,oyoyo Dady Malik"
AbdulMalik yace
"Ina Mamarka AbdulMalik yayi maganar yana kokarin zama a kujerar falon
" taje kitchen ta zubo min abinci"
"Oh kaifa ina ka baro ci ina zaka ci ne"
Yana cikin maganar Rufaida ta dawo falon da plat da abinci a ciki idonta ya sauka ana AbdulMalik AbdulMalik ya sakar mata murmushi itama murmushi tayi masa ta mikewa Yasir abinci ta nemi guri a kasan carpet ta zauna tare da cewa
"Sannu da zuwa Yaya Malik,ba dai harka dawo ba?"
"Yawwa Rufaida,Eh nadawo yau kinsan friday"
"Au nama manta,bari na kawo ma ruwa,a'a bar abinki,na biya gidan Aunty Zainab daga can ma nake nayo Zaria"
"Ok"
"Baki tanbayeni labarin,mai kama dake ba,munfa sake haduwa yau nagansu ita da Auntyn ta a unguwarsu Aunty Zainab"
Murmushi Rufaida da mamaki tace
"Dan Allah fa"
"Yace
" serious har magana mu kayi"
"Please ka bani labarin ya akai kuka hadu"
Murmushi AbdulMalik yayi yace
"Bayan na fita daga gida naje gurin aiki shine nayi kokarin biyawa gidan Aunty Zainab,kafin na shiga Layin su Aunty Zainab na ganta tsaye kofar wani gida a bakin titi shine na tsaida mota ta a kusa da gidan na fito na karasa gurinta na mata sallama,bata yi min magana ba sai dai naga alamun amsawar a labbanta ina cewa Ranki ya dade wata mota ta karaso ta shiga shine na bi bayansu a mota ta har saban kawo" jin yayi shiru yasa Rufaida cewa
"Uhmm ina jin ka"
"Ke kinga kofar gidan da motarsu ta tayi parking kuwa,ina ganin kyau da tsarin gidan nasan dole yarinyar tayi jin kamshi indai gidan ya kasance gidansu ne,ina gani aka bude musu gate din suka shiga ya rufe ni kuma ina ganin haka na fito a mota ta na kwankwasa kofar gate din maigadin ya leko yace min was nake nema nace masa budurwar da suka shigo nan gidan yanzu a mota,maigadin ya kalleni sosai yace na shigo,gurin kallon gidan na 'bige Rufaida"
Rufaida tayi dariya tace
"Yanzu akwai gidan da zai rudaka Yaya Malik,bayan kuma gidanku mai kyau ne sosai"
"Ke ana miki maganar gaba fa da gabanta akace fa,kuma kinsan komai gareka akwai wanda ya fika haka rayuwa ke tafiya
"Eh hakane To cigaba da bani labari na kagu naji koda sunanta ne"
Ya cigaba da cewa
"Maigadin ne yayi wajensu da har sun fara fitowa daga motar ita magana naga yayi wa wadda nagani din kamar ba zata zoba naga wata mata ta mata magana,sai gata ta biyo bayan maigadin,maigadin daya rigata karasowa yace min cikin girmamawa " yallabai gatanan"yana barin gurin ta karaso tayi min sallama muka gaisa"nace mata Suna na AbdulMalik da wata kanwata dama naga suna kama shine na mata magana"tace min
"Ok nagode,amma yanzu ina sauri ne wani lokacin saika hadaDariya kanwarta ka ko a waya ne nace to ai bani da number dinta"shine ta samin ta fadamin sunanta Safiyya amma fa yarinyar batajin Hausa?"
Dariya Rufaida tayi tace"sai kaita mata turanci"
"Au van dake,anjima zan hadaku a waya"
"To Allah ya kaimu lfy"
Daganan suka cigaba da firarsu zuwan Hajiya Jamila falon shiya tsaida firarsu,Rufaida ta mike taja hannun Yasir suka zasu bar gurin da ta fara ganin hararar da Hajiya Jamila ke aika mata tun kafin aje ko ina,don tunda abin da ya faru dasu da Rukayya komai ya kara sauyawa don habaici zagi bakar magana shan su take gurinta,da yanzu yau kawai ya rage mata tabar gidan zuwa gobe
AbdulMalik ya tsaida Rufaida da cewa
"Ina zaki ne,muna fira"
"Firar me kukeyi kuma,nifa AbdulMalik vangane maka ba fa"Hajiya Jamila tayi maganar rai bace tana kokarin zama
Jin haka yasa Rufaida saurin barin gurin tana ji AbdulMalik na cewa
"Kamar ya Umma vaki gane minba"
Daganan dakin Hajiya Kubra suka shiga aka bude faifan fira


Sadiya Khalil🥰
[9/26, 9:37 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*



By Sadiya Khalil

50.
Masoyan wannan littafin ina godiya gareku,Allah ya hadamu da alkhairan dake kunshe cikin wannan littafin.

RUFAIDA POV
"Wallahi ina murna yau matuka Samiha
Rufaida da take kwance kan gado da waya a hannunta take furta hakan
Wayar da take a handsfree Samiha tace
" to fa murnar me kike yi"
Tsaki Rufaida tayi
"Kiji 'yar rainin wayau kin manta gobe zan koma gida"

"Na shafa'a 'yar uwa sorry,ke dawa zaki tafi ne?"
"Ba muyi maganar da Abba Bukar ba bai shigo gida ba"
"Ok to ko Yaya Samir na masa waya ya biyo tanan daga sokoto yazo ku tafi tare"
"A'a ki barshi nafi tunanin Abba zaisa Yaya AbdulMalik ya kaini gida"
"To badamuwa Allah ya jikan Yaya Wahid yasa can ta fiye masa nan,Rufaida!na rokeki ki cire duk kan damuwar mutuwar nan a ranki duk da nasan dole ki damu tsawan lokaci amma ki tuna da cewa ubangijin da haliccesa yafi ki sanshi shiya karbi kayansa,haka dukkanmu lokaci muke jira shida ya tafi vaiyi gaggawa ba mu da muke raye amu yi jinkiri ba"
Jikinta duk yayi sanyi ta fadi
"Hakane Samiha,Allah ya sa muyi kyakkyawar cikawa"

"Amin kawata, sannan sai maganar aure don Allah idan kin samu miji kin tabbatar da nagartar halayyarsa ki auresa ki zauna gidan mijinki kiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login