Showing 6001 words to 9000 words out of 86533 words

Chapter 3 - JININMU DAYA HAUSA NOVEL

bangaren Abba Bukar da sallama Hajiya Kubra ta shiga Abba Bukar yadubeta bayan amsa sallama inda tanemi guru gefen gado ta zauna shida yake tsaye jikin Sib yana duba wata takadda da yake nema duk ma'adanar litattafansa yaduba batanan ya dubi Hajiya Kubra da mamaki ganin cewa sun gaisa kuma yanzu suka rabu baidai cemata komaiba yanaso yaji ta bakinta takunna shirun sakanni sukayi kafin Hajiya Kubra tace"Abba dama shawara nakeso na baka amma karkace na Shiga abinda baruwana koya batama rai"murrmushi Abba Bukar yayi yace"Haba Kubra kifadi koma menene bazai batamin rai ba kuma indai dayuyuwa zan dauki shawarar taki" nisawa tayi kafin tace" gani nake gwara yarinyar nan Rufaida takoma gidan Gwaggo zatafi kula da ita amma nan kasan akwai damuwa azamannata saboda kowannenmu bazai kula da ita kamar Gwaggo"Abba bukar ya nisa yace"hakane saidai zaman nata anan zaifi saboda nanne yakamata ta zauna bayan gidan mijinta tunda idan Abujar ne babu wanda tasani kuma nanma koba ta auri danmu ba ai gidansu ne,Kubra daga gareki bana tunanin wata baraka zata taso Dan Allah kirike ta amana har Allah yasa tagama takabar nan takoma gaban iyayenta tunda yar nan kema yar kice kuma da na kowane bakasan wazai taimakeka ba a gaba"Hakane cewar Hajiya Kubra da haka dai suka cigaba da fira Abba Bukar nakarajin kaunar matarsa saboda yadda tafita daban acikinsu badan wata alaqa tasu ba yasa yake kaunartasu ba a'a halayyarta itace dalilinsa babu Wanda cikin nasa zaice ga laifin ta bawai don tasu bace yasa hakanba kawaidai ita bamai son kai bace yana alfahari da matarsa.*JININMU 'DAYA*


By Sadiya Ibrahim Khali
(Sadiya Khali)

4

Abdulmalik ne ya Shiga dakin Hajiya Jamila cikin saurinsa dako sallama baiba duk ya rude jin rashin lafiyar Rufaida yar uwa a garesa, inda Aunty shema'u da Aunty Maimuna sakonta data ya aje mata ganinsa cikin saurin bako sallama yasa ta tanbayar ko lafiya zai shigo mata daki haka yace "Kiya hakuri Umma Rufaida ce yanzu Abba yake fadamin batajin da'di zamu tafi asibiti"Hajiya Jamila da ranta ya gama baci tace tunda gani uwarka banda lafiya aika rude kakasa yimin sallama wallahi Abdulmalik kashiga hankalinka babban kwabo kawai ko Abdussalam da AbdulJabbar bazasuyi haka ba" AbdulMalik yace "kiya hakuri Umma"Aunty Shema'u da sai yanzu tasa baki tace" toma banda iskanci da raini akanta aka fara cuta"Aunty Maimuna da tasa baki itama tace" Haba dan Allah tunda ya amsa laifinsa ai saiku hakura ku kyalesa"kafin Aunty Maimuna ta fada tana karasa zancen da cewa muje Abdulmalik na dubo jikinta dan balallai kuje asibiti kudawo kusamemu bamu tafi ba"Aunty Shema'u tace"lallai Maimuna wannan dakece babbarmu bamusan ikon da zaki nuna akanmu ba"Maimuna da bata saurari yayartata ba dan tasan rai zai iya baci idan takulata dan ita bata goyan bayan rashin gaskiya suka fice itada AbdulMalik Hajiya Jamila ta kalli Shema'un tace" gaskiya Yaya ,Maimuna bansan ina tasamo wannan halinba bare ace yafi 'dan uwa dama da masu asali ake abin tashiga toda da sauki"Aunty Sha'awa tace "ni bama wannan yafi damuna ba kidubafa kiga yadda Abdulmalik ke rudewa akanta karfa yace shima yarinyar nan yakeso wallahi tun wuri kiyi maganinta kar wannan bakar kayar tasake kutso kai zuriyarki tazo ta sake miki shigar sauri"Hajiya Jamila da sai yanzu hankalinta yakai nan tace hakane Yaya amma daraina bazan amince ba in anyi nafarko anyimin fin karfi wannan bazan bari ba kodan duba da banbancin dake tsakaninmu mai dunbin yawa" da wannan firar tasu ta cigaba da wanzuwa har Rukayya ta shigo dakin da za'a barta anan

Aunty Maimuna data kalli Rufaida da take rawar Sanyi tace subhanallah Rufaida zazzabin ne har haka kafin ta bude Sib din jikin bango ta samo mata hijabi tana cewa"anshi maza kisa AbdulMalik yana falo yana jiranki"tare suka fito falon da Rufaida ba wanda take ma iya yiwa magana AbdulMalik cikin nuna tausayi ga matar yayannasu da kasa ta rufesa da take masa takaba yace"Aunty kinga ashe har haka jikin Rufaida yayi zafi"Aunty Maimuna tace"AbdulMalik rasa miji ba abine mai sauki ba dole akwai ciwo da zafi na rabuwa da abokin rayuwarka yanzu dai kayi maza ku tafi asibiti Allah ya bata lafiya idan kun taddamu shikenan"AbdulMalik ya amsa da to Aunty Allah ya saukeku lafiya"duk tare suka fito shida Rufaida sukayi hanyar harabar gidan ya tada mota suka nufi asibitin

Da murmushi matashin likitan mai suna Zahraddin ya dago kai daga rubutun da yake zaune a daya daga cikin kujerun office din yana cewa"Malam AbdulMalik lafiya kuwa Zahraddin ya fada yana bawa AbdulMalik hannu da likitan bayan sunyi musabihar ne ,suka zauna a kujerun dake gefen na Zahraddin din kafin AbdulMalik yace"Eh Wallahi zahraddeen nine Matar Yayana da yarasu kwana 4 nakawo bata jin dadi ya nuna masa Rufaida "Zahraddin yace" Allah sarki Mama ta fadamin rasuwar to Jiya nadawo daga Kano shine banzo gaisuwa ba banma ko a waya ba tunda naje ban huta ba wani aiki ne aka turamu Allah ya jikansa ita kuma Allah ya bata lafiya ya fada yana kallen fuskar Rufaida da yaji lokaci guda tausayinta ya kama shi "AbdulMalik yace "Amin abokina babu komai nagode amma ban yarda ba saikazo yimin har gida" Zahraddeen yace" to shikenan zanzo yau din nan ma in Allah ya amince amma waima tsaya kasan da abotar kaki shigowa koka kirani a waya nazo har gida koka fadamin kuna nan a waje nasa a shigo daku yanzu da yadda nace nagama duba kowa da saina fito naganku naji kunya"AbdulMalik yayi murmushi yace"abokina kenan yanzu muka zo badadewa mutane kadan na tarar idan kuma na shigo kaga zan shiga hakkinsu ,idan nayi haka kuma kaga bankyautaba bansan uzurin kowa ba ,kuma bawai alfarmace ko matsayi ace dan kasan wani a guri kai tsaye bawani dalili kazo ka wuce wasu guri kuma bayan sun rigaka zuwa kaga akwai hakkinsu akanmu da munyi hakan"murmushi Zahraddin yayi yace"Uztaz AbdulMalik kenan"AbdulMalik yayi murmushi yace"gaskiya ce ba wani uztaz ni duba min mara lafiyata mu tafi na biyema hirarmu bazata kare ba bare muyi abinda zai anfanemu"Murmushi Zahraddin kawai yayi ya juya ga Rufaida ya mata tanbayoyi ya gwada Blood pressure dinta ya rubuta mata magunguna yace ta rage damuwa sannan ya mata nasihohi kafin su mike su fito Zahraddin yana cewa sai ya karaso zuwa anjima koda yamma ne

Daki kawai Rufaida ta shiga bayan fitowarta mota da ledojin magungunan da yoghurt da AbdulMalik ya siya mata da zata sha maganin dashi da tuni lokacin su Aunty Maimuna sun dau hanyar Nasarawa tana shan magungunan gado kawai ta haye ta kwanta AbdulMalik ya da'de a motar kafin ya fito a ranshi yana matukar jin tausauyin Rufaida tunanin da zuciyarsa ta fara shiyashi sakin murmushi ya fito daga motar ya wuce bangaren mahaifinshi don alokacin ya tabbatar su Aunty Maimuna sun tafi don yaga message din data turamasa har ran AbdulMalik yakeso Auntynsu Maimuna saboda tafita daban a cikin yan uwan mahaifiyartashi gwarama Haulatu ba laifi da nata kirkin saidai zugata da yan uwanta keyi shine yake sauya ta dandanan gata da daukar zafi lokaci guda ita ko Aunty Maimuna tana da kafiya akan gaskiya.*JININMU 'DAYA*

By Sadiya Ibrahim Khali(Sadiya Khali)

5
AHajiya Jamila ta dan dubi Aunty Amina da Duke zaune Suna karyawa a falo tace Amarya Ruqayya zaki mikawa abincinta kibawa Rufaida ta mika mata"Abba Bukar da baice komai ba sai da yaji karashen maganar Hajiya Jamila yace "kamar ya a mikawa Ruqayya abincinta?ita bazata iya fitowa ta ciba"Hajiya Jamila ta 'dan yatsina kafin tace masa" kasan tunda akayi rasuwar nan yarinyarnan Ruqayya bata cikin nutsuwarta gani take data fito falon na ganin wancen yaron zatayi"Ganin ya gane AbdulAhad take nufi yace mata"dakata Jamila ita Ruqayya AbdulAhad din mijintane ita matartasa daya mutu ya bari take masa takaba ita ta fito take cin abincin da ita yaushe ta warware ince Jiya har asibiti aka kaita"ganin kowa na falon jin amsar zata bayar yake yasata cewa"Ba haka bane Abba kaima kasan akwai banbanci tsakaninta da Rufaida mai tazara saboda ita Rufaida ta auresa tana zaune dashi ita kuma Ruqayya yarasu tana son aurensa"shiru Abba Bukar yayi yana tunanin halayyar matarsa kiri-kiri take fito da komai yace" Wasila jeki kira min Ruqayyan danni tun fil azal iyalina guri 'daya sukecin abinci bakuma za'a ware ba saboda zuwanta ya fada"Wasila datake cin dankali ta ajiye ta mike tana cewa "to Abba "sai da yaga shigowar Rukayyan falo da take ta sissinke kai ya mike yabar dakin da Ruqayyan take gaisheshi ya bita da lafiya lau ya fice daga gidan yaran suna binsa da adawo lafiya Aunty Amina ta bisa yi masa Rakiya Aunty Amina ta dubesa tace"amma Abba abinda Ummansu Abdussalam take sainaga kamar bata kyautawa akan yarinyar nan kuma a gabanta take komu inzamuyi mata kamata yayi ta hanamu tunda koma menene matsayin surikarta take dukda mai rabawa ta raba" nisawa yayi yace "hakane Amina zanyiwa tufkar hanci da wuri kuma kema karki sa baki dukdai kulawar da kukaga yakamata a matsayinku na iyaye gareta Ku bata tunda koba komai Aliyu da Hauwa'u na wane" tace masa hakane Insha Allah zamu kara datse damtse fiye da yanzu"yana murmushin jin da'di yace yawwa Amina"Allah yayi miki Albarka" tace "Amin" da haka yaja motarsa ya fice ya nufi gurin aikinshi.

Rufaida da take zaune a gurin tanaji yadda Hajiya Jamila suke fira itada Ruqayya ko daya batasa baki ba dan ko tasama gwaleta zatayi jefi-jefi dai take sauraran firar tasu hirar ragowar yaran dakin take shiga da kusan ta karatu sukeyi hakan yasa ta sake tsunduma cikin tunanin rayuwarta yau babu ginshikan rayuwarta dukda suna raye,amma akwai tazara mai dunbin yawa a tare dasu, Yasir shida Ubaidullah suke wasa 'dan Aunty Amina dukda Ubaidun ya girmema Yasir da wajen shekara 'daya da wani abu,AbdulMalik ya dubi Rufaida yace"kinsha maganinki kuwa" tace "Eh Yaya nasha" yace mata yawwa kinsan Zahraddin yace ki riqa shan magani akan lokaci Allah ya kara sauki dazu da mukayi waya yace a gaisheki"tace"Amin Yaya AbdulMalik to ina amsawa" da haka suka cigaba da firarsu zuwa wani 'dan lokaci.


Jingina kansa da jikin kujerar dake office din yayi sanyin Ac na ratsasa yana tuna abun da haryau ya kasa mantawa dashi a rayuwarsa dukda shekarun da suka fara tafiya amma baya tunanin ya manta da wancen ran da yasa shi a sahun mai sa'a a rayuwarsa a hankali ya fara tunano wayarsu da Ahmad da yakasa fahimtar yanzu menene a cikin ransa dukda yadda ya da'de da yanke tsammani kuma har yau baya tsammanin cikar muradinsa ABDURRA'UF RJM kwararran likita MEDICAL DOCTOR kenan matashi mai kimanin shekaru talatin da 33zuwa 34

Mi'kewa yayi da wannan tunanin nasa ganin baida sauran marasa lafiyar da zai duba key din mota ya dauka kawai yana kokarin ficewa daga office 'din yana kallon agogon hannunsa 2:pm dai dai yayi mamakin kaiwarsa karfe 2 bai koma gida ba gurin wayarsa da take caji ya karasa yana kokarin cireta daga cajin yaga kiran Safiyya karasa cirewa yayi inda yayi caraf ya 'daga wayar yana murmushin mugunta dan yasan flashing Safiyyan tayi ako bangarenta cewa tayi cikin yarensu Na India tana cewa" kai Yaya Ra'uf daga flashing harka kama dama ammi ce tace na kiraka karma taho kamanta sakonta"ya dan saki fuska kamar tana kallonsa yace"ai ban ta'ba ganin 'kanwa tana gudun yayanta yaci ku'din wayarta ba sai akanki"jin yaji sakon yasa Safiyya katse wayar tana murmushi shiko Ra'uf da yake jiran amsar Safiyya jin shiru ne yasa shi duba wayar ganin ta katse yasa shi murmushi ya bude kofar office 'din ya fice yana tura kofar office din yasa key ya rufe " a harabar asibitin ya tsaya kiran waya bai jima yana wayarba ya katse ya karasa gun motarsa ya tayar yabar asibitin sa'ko Ammi ya tsaya ya amsa daba komai bane face turare daganan kai tsaye gida ya nufa

Da sallama ya isa falon gidan da yaketa kamshi wandaa Key da wayoyinsa suke a hannu sai sakon Ammi da yake hannun nasa"Safiyya da take falon da Pakistan riga da wando a jikinta da dankwalin kayan akanta ta amsa masa sallamar da cewa "a'a Yaya Ra'uf sannu da zuwa kaga yadda kayi kyau kuwa kamar rana bata dokeka ba" Hararar ta yayi yace"banasan raini fa naje aikin na dawo ki fadi haka"tace Allah Yaya dagaske make"yace "to naji ina Ammi" tace masa" tana ciki"da haka ya aje sakon da wayoyinsa anan yace yana zuwa zai watso ruwa Safiyya tana ganin shigewarsa ta 'dauki wayarsa da tasan ba pattern tsaron waya ta fara kiran kawayenta da suka jima busu gaisa ba saboda hutun dasu keyi sai da taji alamun saukowarsa daga saman bene ta ajemasa wayar ta cigaba da kallon da takeyi dashi da Ammi suka sauko inda Ra'uf ya kalli Safiyya ya harareta yace" da ganin fuskarkin kowa yasan kinyi laifi"Ammi ta kallesa tace" kai Ra'uf kadaiji tsoron Allah mai kuma Safiyyar tayi"labari yake bawa Ammin har suka karasa gurin cin abinci suka inda suka fara cin abinci Ra'uf suna cikin cin abincin yace "Ammi yanaga Dady bai dawo ba" Ammi tace "yana hanya nafi tunani" Ra'uf yace "bari dai na kirasa naji ke Safiyya daukon wayata na kira Dady"Safiyyance ta mike daga cin abincin da take ta dauko wayar ta mikawa Ra'uf da hannu biyu da tuni tafara tsorata dan tasan ta cinyewa Ra'uf katinsa
Ran Ra'uf inyayi dubu ya 'baci ganin ya kira Dady sun shaidamasa ba kudi shiko yasan da kudi ya aje wayarsa Safiyya ya fara tunanin tacinyemasa kudin duben Safiyya yayi ya ha'da rai yace" wa kika kiramin da waya"cikin tsoro Safiyya tace Yaya kaya ha'kuri 'kawayena ne"yasake cewa "ban hanaki ta'ba min waya ba ke kwata kwata bakyajin magana" cikin tsoron hukuncin Yayannata tace" kaya hakuri bazan kara ba"Ammi tasa baki tace to bata baka hakuri ba ai saika hakura kasa wasu"Ra'uf yace" amma Ammi kina gani fa ta mikon wayar na fara kira maimakon tacemin babu kudi amma taki fa'damin saboda ta rainani"Ammi tace"ai tunda ka kiyin aure 'yar Safiyya ma sai tazo ta rainaka bama Safiyyanba"Safiyya da 'kiris ya rage tayi dariya ganin Ra'uf ya tashi daga gurin yasata yin shiru tana jin bata kyauta ba ganin itace taja abinda ransa ya'baci Safiyya tace cikin Sauri"Yaya kaya hakuri bazan 'karaba" ganin zai karasa matakalar bene murmushi yayi batare daya juyo ba yahaye been ya karasa 'dakinsa kawai ya zauna bisa 'daga cikin kujerun dake falonsa ya jingina kansa da kujerar yana tunanin mikin da aka dasama zuciyarsa babu kwakkwaran hujjar dasawar kuma har yanzu har abada kuma bazai iya mantawa da bigiren ba har wayau kuma bazai ga laifin bigirenba koda duk duniya kowa zai lankaya laifi gashi bigiren ba an shiga rayuwar daya dade yana mafarkin samu ba tareda sanin hujjaba kawai anyi anfani dason zuciya gurin cusguna masa tabbas akwai zalinci mai yawa a wannan rayuwar da ake yi to ta ina zaiyi wata rayuwar da yasan zalintar duk wadda zata zauna dashi zaiyi,babu aure a yanzu haka a tsarinsa koda zaiyi bayanzuba kasancewar yasan tun asalinsa shi bamai sa'a bane da wannan tunanin barci ya daukesa koda dady ya tanbayi Ra'uf Ammi tace da kanwarsa ne ita tamasa laifi ta bashi labari fa'da sosai Dady yama Safiyya tace idan ya fito anjima zata sake basa hakuri da haka hirarsu ta kasance kasan zuciyar Ammi yana tunano wani lamari daya maishe da ',dan nata haka mikin da ya harbi zuciyarsa abunda yafi kama da nuna iko da har yau takasa fahimtar wannan dalilin ikon da aka nuna ga gudan jininta da akai anfani dashi gurin zalintar zuciyarshi da danamasa mikin da har yayi tsamarin da batayi tunanin zaikai haka a zuciyar 'dan cikin nataba.*JININMU 'DAYA*

BY Sadiya Khali
6

Bugun 'dakinsa da yaji anayi shine yasa shi farkawa da anbaton Allah a bakinsa,duk jikinsa yayi masa nauyi dan koda can a baya da rayuwar bata kai haka ba jindadi ba shi baisa ba da kwanciya a kujera ba,koda a yanzu tunani yasoma tu'kewa a zuciyarsa har yake neman shafar jin da'di rayuwartasa baisa ya saba makamancin rayuwa Irin wannan ba,jin muryar Ammi tana cewa"wai bazaka bude min kofar ba" ya danyi mi'ka ya mi'ke yana cewa "Ammi a bude fa take" yakarasa jikin kofar ya bu'de matsawa yayi ta karasa shiga ciki ya maida kofar ya rufe kallon Ra'uf Ammi take har tanemi guri saman kujera ta zauna shima kujerar da yatashi ya koma ya zauna

Nisawa Ammi tayi kafin tace"Ra'uf yanzu abinda ka za'barwa kanka kana tunanin ya yima kullum kai kenan ka rufe kofa ka zauna kayita tunani bayan komai na duniya hakuri ake dashi duk yadda al'amura suka tu'ke da wanzuwa", Murmushi kawai yayi kafin yacewa mahaifiyartasa"Ammi ni tuni na da'de da barwa Allah komai dukda har yau ban fidda rai ba ga samun waccen sa'ar da nake tunanin ada na rasa ta sai dai yanzu ina mafarkin samun abinda na rasa kona samu Wanda ya fishi" Kai kawai Ammi ta girgiza tana gwada maganganun Ra'uf ama'auni sai dai dukda ta gano abinda yake nufi baisa ta tada maganar ba dan ita ba maison tayadda abinda ya rigada ya wuce bane tun fil azal,Sauya maganar tayi da cewa,"To yanzu maganar aure na lura sai dai an zaboma macen da zaka aura tunda gashi nan shekarunkafa tafiya suke"dan jim yayi kafin ya ce "Ammi ni yanzu banida wani za'bi kiyi duk yadda kikaga ya dace zan amince",Murmushi tayi tace" to Allah yasa karka kara bani kunya,Kamar wancen lokacin Murmushi yayi mai sauti kafin yace"A'a Ammi ai wancen karanma inada dalili mai karfin gaske"ta 'dan murmusa tace"ni banga laifin Intisar ba kai dai kawai kaki ta sai gashi abokin ka ya aureta"yace yawwa Ammi kin gani ko,Inteesar dama tuntuni Shureim yake fadamin son da yake mata kinga kuwa ni din baikamata na cusa kaina ba gwara dai dana barwa aboki na ya muradinsa ya fa'da yana tauna la'b'bansa na 'kasa yana sake tuno wancen mikin da baya kwana bai tuna shi ba abinda yafi kama da al'ajabi da tarin tanbayoyin da bazai gushe ba yana tanbayar kansa ,Ammi tace "to shikenan Allah ya kawo mace tagari" sake maida dubanta tayi ga Ra'uf ta tattara dukkan natsuwarta dukkan nutsuwarta gareshi da alamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login