Showing 72001 words to 72723 words out of 72723 words
an share makoki amma me kuka gani?"
Babu wanda yaja da wannan ƙudiri domin babu abin jan in kuɗi suke magana akai Mangal family sunyi musu Zarrah in mulki ne sune mulki domin nasu bana siyasa bane na sarauta ne idan addini ne ko ilimin zamani suɗin kankat ne" wata takarda Ya Hajja ta fito da ita ta mikawa Rafi'ah tace “Wannan Audu ne ya bani kafin rasuwarsa ya gargaɗeni karna baki ita sai bayan an binneshi kuma kada wani ya buɗe ta saike"
Kallon Deeny tayi ya jinjina mata kai tasa hannu ta karɓa ta buɗe.
_“Assalamu alaiki Noor inayi miki wannan rubutun ne ina kukan rasaki da nayi da kuma rasa dama ta tsayin rayuwata wadda na fidda tsammanin dawowarta har numfashina na ƙarshe._
_Na rasa da wacce kalma zan goge kaina nayi haske a gurinki Noor Inasonki kuma zan mutu ne da sonki, ina rubuta miki wannan takarda ne saboda rokon alfarma ta ƙarshe da gajerun kwanakina suke tabbatar min da bazan rasa a wajenki da mijinki ba,_ _Noor inna mutu kiyimin addu'a kuma kisa ƴaƴanmu bakwai su rinƙa tunawa dani a addu'o'insu, idan zai yiwu bazai zama na takura muku ba Abdulkarim da Hauwa'u inason su rayu ƙarƙashin kulawar ki da mijinki Shamsunddeen don Allah ki roƙeshi akwai sabon Companynki na magunguna dana gina miki saboda inajin kin cancanci samun wani abu cikin dukiyata komansa yana gurin Hisham, a ƙarshe ina me ƙasƙan da kaina don Allah ki yafemin"_
Iya abinda aka rubuta kenan ta saki takardar tare da kwantar da kanta jikin Deeny daya riƙe takardar ta sake saka marayan kuka shafa bayanta yayi yace “kiyi hƙr nima wataran zan mutu..." Rufe masa baki tayi tace “Aa Deeny don. Allah karka mutu ka barni wlh nima mutuwa zanyi...."
Miƙewa yayi suka fice suma suka koma gida kwanaki uku sukayi aka gama karɓar gaisuwa sannan suka ɗauki hanyar Niamey harda yaran A cikin gidan sarautar ashe anyi wani musulmin gini na haɗuwa anan suka sauka da yaransu Bakwai Hisham da Ablah sai Jalal da Jamal Hameed da Hameedah sai auta Hurriyah.
Rayuwa ce suka tsarata me daɗi da kwantar da hankalin me kallo lokaci yayita tafiya shekaru suka tura har shekara biyar a lokacin ne Hisham ya haɗa Mastering degree ɗinsa a lokacin ne kuma Mai Martaba Deeny ya zabo masa mata cikin dangin mahaifinsa Nuratu Yar aunty Zahra ƙanwar mahaifinsa ita aka haɗasu aure Ablah kuma da Nura ɗan wajen Aunty Amina.
Ansha biki sati biyu akayi ana shagali aka ɗauki Ablah zuwa Lagos shi kuma Hisham aka kai masa amaryarsa Niamey domin anan yake da zama kusa da iyayensa.
Shekara bata dawo ba saiga Rafi'ah da jikoki Ablah ta haifo danta namiji Nuratu ta haifi namiji itama.
Akasha suna yara sukaci sunan kakanninsu maza Na Hisham yaci sunan Deeny wato Shamsunddeen na wajen Ablah kuma yaci sunan Abdulƙadir"
Ranar sunan yaran ne aka mayar da auren Mommy da Daddy domin tuni ta tuba ta koma saliha sun daidaita da mahaifinta kafin ya rasu wai ashe First Daddy ne yayi mata asiri take wannan barbaɗar tun lokacin daya nuna yanasonta tana budurwa Mal Geloro mahaifinta yace shi bazai bawa ɗan iska auren ɗiyarsa ba shikenan bayan auren ta da second Daddy sai rigima kala kala ƙarshe ma aka farraƙasu ya saketa babu shiri kuma ya ɓata ɓat lokacin da cikin Rafi'ah yana karami don a lokacin ko sati Uku baiyi ba.
Shine fa ta koma gidansu to a zaman iddarta ne kuma abubuwa sukayita rikicewa matar babanta bata da mutumci sukayita rigima karshe dai ta haɗu da first Daddy ya hure mata kunne suka gudu ya ajiye ta ta haihu sukayi wannan barbaɗaɗɗen auren nasu da bai hanasu iskanci ba ashe shine ya fara koya mata bin maza tun tanaki harta haƙura ta saba idan tayo iskancin ya karɓe kuɗin da haka suka raini Rafi'ah, yau dai ƙarshen tukatukituk komai yazo ƙarshe har tayi iddarta tun shekaru da dama baya da farko ita taƙi auren amma yanzu da Rafi'ah ta dameta ta yarda an daura rayuwa sabuwa ta dawo kamar wani abu bai taɓa faruwa ba.
_Tammat bih hamdullah_
_Nan na kawo ƙarshen wannan labari don Allah ina rokon duk wanda na ɓatawa a wannan labarin ya yafemin banyi da niyya ba saidai kunsan dake duk ɗan adam ajizi ne kuyimin uzuri._
_Domin samun complete wannan littafin zaku tura 500 ta wannan acct ɗin 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank._
_*Oum Hairan*_