Showing 42001 words to 45000 words out of 72723 words

Chapter 15 - AKWAI IRINSU COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Jan 2025

6070

ƙishirwarka Please ka barni na nemi magani tukunna" cikin fushi take maganar.




Bai saurara mata ba yaci gaba da jagwalgwalata har Saida ta sakar masa jiki ya shigeta ita dai bataji wani yanayi na ƙafewa ko rashin ni'ima a tattare da ita ba abinda ya bata tsoro da mamaki yanda taga ya haɗe rai ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito ya kwanta tare da juya mata baya.
Bata saba da haka gareshi ba don haka ta tashi zaune ta taɓashi ya juyo ya zubanta idanu tayi ƙasa da muryarta tace “Don Allah ka faɗamin gaskiya AbNoor da gaske banida ni'ima wai bakajin daɗina?" Tashi yayi zaune a hassale yace “Ƙarya zanyi Miki kawai don na cutar da zuciyarmu Noor Kinsan Ni ba maƙaryaci bane
ba kuma zan fara a kanki ba da gaske bana tsintar komai a jikinki sai wahala gsky bazan iya ci gaba da mu'amala dake a haka ba ki nemi magani daga Naira ɗaya har millions zan baki Indai zaki samu lafiya"





Yana faɗin haka ya koma ya kwanta ta sauko daga gadon zuciyarta a cunkushe ji take yi kamar zuciyarta zata fashe saboda tashin hankali ficewa wanka tayi ta ɗauki ɗanta ta fice tanajin yanda kanta yake juyawa kwanciya tayi tana sharar hawaye lokaci bayan lokaci karon farko da taji kewar mahaifiyarta ta kamata ta tashi zaune ta haɗe kanta da gwiwa tana kuka me cin zuciya taji ya buɗe kofar ya shigo ta ɗago ta kalleshi ta mayar da kanta cikin cinyarta yazo ya janyota jikinsa yana shafa bayanta dama yayi tunanin hakan zata iya faruwa shiyasa ya kasa samun nutsuwa Saida ya biyota.
Cikin raunin murya yace “Nasan rashin sanin wanda zaki tunkara da matsalar mu shine ya sanyaki kuka ko Noor?" Da sauri ta ɗaga masa kai tare da sanya hannu ta zagaye bayansa ta buɗe baki cikin kuka tace “Don... Don Allah AbNoor karka rabani da farin cikina saboda wannan matsalar na aminta idan bazaka iya hƙr ba ka ƙara aure Wlh bazan taɓa zarginka ba"
“Meye farin cikinki?" Ya faɗa yana shafa bayanta a sanyaye tace “Kaine Abdulƙadir koda nace zan iya rabuwa dakai Wlh ƙarya nake da sonka aka halicci zuciyata ko kafin na sanka zuciyata bata karbi so ba sai a kanka kuma bazata ƙara karɓa ba ka tausaya min ka barni na rayu dakai koda zanyi zaman ɗana ne" dariya ta bashi sosai yayi kissing goshinta yace “Zaki iya zaman ɗanki tun yanzu Noor" da son tabbatarwa ta daga masa kai tace zanyi Indai akanka ne AbNoor son ruhi da jini nakeyi maka" shafa kanta yayi yace “Na iya sanar da Gana Hajja" da sauri ta ɗago tace “Kayy haba dai" murmushi yayi yace “Banida kunya ko? To ba ita na faɗawa ba Ya Hajja na faɗawa yanzu tace na saki kiyi mata magana a nemi mafita tunda wuri" bata kuma cewa komai ba a wannan daren har sun fara bacci Gana Hajja ta kirata faɗa kam ta Shashi Saida ta rantse mata bata sani ba itama sai yau nan tace mata zatayi masa magana koma me zai faru gobe ta taho Maiduguri zata haɗata da yayanta ya bincika lamarinsu kamar akwai wani ɓoyayyen abu matsala daga wannan sai wannan".....




*SHARE FISABILILLAH PLEASE BROTHERS AND SISTERS*


*OUM HAIRAN*
[11/17, 7:25 AM] OUM HAIRAN: _*21*_



_*Oum Hairan*_



Washegari da wuri ya gama mata komai ta ɗauki hanyar Maiduguri driver ya ɗauketa zuwa gidan gwamnatin ko zama batayi ba Gana Hajja tace su tafi Bolari haka suka fita sun Ishe Mal Hamidan a zaurensa yana ƴan ayyukansa suka gaisa Gana Hajja ta zayyane masa komai ya dubi Rafi'ah sosai yayi mata tambayoyi ta basa amsa.
Can ya ɗago yace su shiga cikin gidan zai ɗanyi wani abu, sun ɗauki kamar awa ɗaya da rabi sannan ya aiko kiransu bayan sun zauna yace “Hajiya Hauwa'u wato yarinyar nan da gaske akwai sihiri a cikin lamarinta da mijinta rabasu akeson ayi gabaɗaya abinda yasa abin yaƙi tasiri dukkansu suna da tsaiwa akan addini to Kinsan komai muƙaddari ne Hajiya Hauwa'u babu me iya canza ƙaddara amma addu'a takansa tazo da sauƙi Zanmuyi bakin ƙoƙarin mu insha Allahu duk abinda zai faru zai zama me sauƙi domin matsafa maƙiya Allah sun shiga lamarin kuma bama mutum ɗaya ne yake wannan shirin ba"
Nan ya harhaɗa mata magunguna yayi mata rubutu galan guda sannan ya bata addu'o'in da zata rinƙayi tana yiwa ɗanta da sukayi godiya tare da aje abin sadaka suka tafi Gana Hajja tace bazata koma ba sai an gama magungunan haka ta zauna har tsayin sati biyar to shima bai takura ba tunda neman magani aka taho zaman daya zame mata kaico kuma tarnaƙi ga rayuwarta da farin cikinta bayan sati biyar ne yazo suka tafi abin gwanin daɗi kamar zai ɗore sai kuma me kullum wata shaƙuwa takega tana shiga tsakaninsa da Billy bashida aiki saina kiranta a waya idan ta fita ina take me take yi? Tun abin baya damun Rafi'ah harya fara damunta musamman daya kasance tare suke fita dashi da safe su kuma dawo da yamma tare gashi kullum Billy ƙara tsanarta takeyi kamar tasa mata wuta.





Wata ranar juma'a ta fita zuwa shagonta saboda akwai bukukuwa sunada ayyuka ranar tabar Billy a gida bata fita ba tana cikin aiki ta tuna tayi mantuwar wasu kaya da zasuyi amfani dasu kamar kartaje tadai yakice ayyukan ta fita ta nufi gida a waje tayi parking tunda komawa zatayi ta fito sojan dake gadin gidan ya buɗe mata get ta shiga da saurinta cikin Sa'a ta ishe ƙofar parlourn a buɗe duk da tayi mamaki bai hanata shiga ba ta kutsa kai tana duban yanda parlourn yayi kaca² ta wucce ɗakinta ta ɗauki abinda zata ɗauka har takai ƙofar parlourn ta tuna da abinda zata ɗauka a nasa ɗakin ta nufi ɗakin hakanan taji gabanta ya faɗi sosai lokacin da takai hannunta kan handle ɗin da nufin buɗewa daurewa dai tayi ta tura ƙofar ta sa kai ta shiga.





Turus taja ta tsaya saboda nishin da kunnenta ke jiyo mata takai idanunta kan gadon take taji wani sinadiri ya saukar mata tun daga kanta har yatsan ƙafarta Saida taji wani tiririn tashin hankali yana taso mata ta dafe bango da sauri tana tattara yawun bakinta jiri ya debeta ta zube a ƙasa tayi saurin sanya hannu ta dafe kanta ta saki wata razananniyar ƙara tace.
“innanillahi wa inna ilaihir raji'un Abdulƙadir Bilkisu dama haka kake kaima ashe kaima mazinaci ne...."
Wani kukane me gunji ya kwace mata daidai lokacin daya sauka a kan Bilkisu ya fara lalubar wandonsa ya saka ita kuma taja duvet ta rufe jikinta, gabaɗaya hankalinsa ya gama ƙololuwar tashi da borin kunya yace “Noor meye ya dawo dake Gida yanzu...." Baikai ga rufe bakinsa ba yaji Bilkisu tana kakarin mutuwa ashe Rafi'ah ce tayi kukan kura ta shaƙeta shaƙar mutuwa.
Da gudu yayi kansu daidai lokacin da tayiwa Billy daukar kara ta watsota kan tiles ta fara wasan kura da ita duk ƙarfin da yakeji dashi yau ya kasa janye Rafi'ah daga kan Billy kuma da gaske neman kasheta takeyi.




Kawai saiya zugo belt ɗinsa ya fara zuga mata yana dukanta tana ƙara shaƙe Billy da yaga da gaske takeyi kawai saiya zari bindiga yace “Noor ki saketa ko na fasa kanki..." Cikin dakiyar zuciya da tsananin fushi tace “Ka kasheni Abdulƙadir nafison hakan don Allah ka kasheni Wlh da wannan baƙar ranar da idona ya ganemin gara na mutu gara nabi sahun matan da suka mutu idan na mutu ka huta Abdulƙadir ka kasheni ka huta nima na huta...."
Jefar da bindigar yayi ya zube gwiwowinsa a ƙasa yace “Don Allah Noor ki saketa ki saurareni nayi miki bayani...." Sakin Billy tayi ta miƙe ta fice daga dakin da mugun gudu ta shiga nata ɗakin ta datse da key ta rushe da kuka me tsuma zuciya komawa shagon da batayiba kenan ta yini kwance a daki juyi kawai takeyi duk sanda ta rufe idanunta majigin wannan mugun gani da tayi ne yake dawo mata Abdulƙadir mijinta uban ɗanta shine kwance da mace ba matarsa ba a gadon da suke kwanciyar Sunnah! Da wannan tunani yazo mata sai kukanta ya tsananta kira kam har gajiya tayi ta kashe wayoyinta domin ta kowanne layi kiranta akeyi Bama ta dubawa bare ta ɗaga har dare yayi nisa tana daki ta fito taki shikuma ya kasa buga mata ƙofa laifi biyu ta kamashi da mace abinda yasan a baya idan aka faɗa mata yana aikatawa zata iya ɗaukar bindiga ta harbe mutum tace yayiwa mijinta ƙazafi sai gashi yau ita ta kamashi da idanunta kamu dumu dumu.





Kasawar da yayi ya tsare jiran fitowarta yakeyi taƙi fitowa har biyu na dare baita fito ba gashi kunya ta hanashi buga mata ƙofa da safe ma bata fito ba hassali ma da zazzaɓi ta tashi me zafi juyi kawai takeyi tana hawaye tanajin yanda mararta keyi mata wani azababben ciwo juyi kawai takeyi ta kasa ko miƙewa jin ana taɓa ƙofar ne yasata ɗan ƙoƙarta mikewa ta tambayi waye. Muryar Nasiba taji ta miƙe tana dafa bango ta buɗe mata ta zauna a bakin ƙofar tana murƙususu da sauri Nasiba ta shiga dakin ta riƙota tace.
“Yace kusan sati guda bakida lfy kuma kin shiga daki kin kulle tun jiya da rana Rafi'ah nasanki bakya fushin banza wlh ban yarda babu abinda ya faru ba don Allah ki sanar dani meye yake faruwa ne a wannan kurman zaman naku ke bakya furuci zurfin cikinki yayi yawa shi kuma kullum shi baya gane yayi laifi"
Kwantar da kanta tayi jikin Nasiba ta rushe da wani marayan kuka tana haɗo kalmominta daƙyar tace “Aunty Nasiba wai haka kowanne aure yake ko kuwa nice ban dace ba? Aunty Nasiba yaushe ne Daddyn Hisham zai sanyani farin cikin da zan manta duk wata sadaukarwa da nayi masa har na rinƙajin a raina ya cancanci fiye da haka daga gareni.
Na manta rabona da samun walwalar zuciya da ruhi a gidansa na manta kulawar miji na manta duk wata dama ta ɗiya mace Aunty Nasiba na gaji wlh na gaji da rayuwar ƙunci a gidannan kawai saboda yaga Allah ya jarabceni da sonsa...."




Tana kaiwa na ta ƙarawa kukanta ƙarfi karo na farko da zuciyarta take azalzalarta data faɗa mawa Nasiba abinda ya faru ko zata samu sauƙi a zuciyarta saidai wani ɓangare yana gargaɗinta da nuna mata hakan kuskure ne kuma daɓawa cikinta wuƙa ne" Tambayar duniya Nasiba tayi mata sai tayi kamar ta faɗa Saita kasa a haka yazo ya ishesu ya tsaya jikin ƙofa ya zubanta idanu koda yakeyiwa Rafi'ah duk abinda yake yi mata ya kasa tuna ranar da yaji soyayyarta ta ragu a zuciyarsa kukanta yana dukan ruhinsa idan ya ganta tana kuka yakanji dama bai zama sila ba, shikam da wacce irin kalma zai bawa Rafi'ah haƙuri yama zai iya zuwa ya tunkareta? Karon farko da yaji yanajin matsananciyar kunyarta, bazai iya tuna abinda Rafi'ah ta gaza masa dashi ba a fannin kwanciya takan damu kanta da son ganin ya samu cikakkiyar gamsuwa koda kuwa ita bazata samu ba tanabin duk hanyar da zata samar masa nutsuwa saidai shi ya kasa bawa rayuwarta farin ciki anya kuwa Rafi'ah bazata kaishi wuta ba? Babban abin daya ƙara tada mishi hankali tun shigowar Nasiba yake tsaye yana jinsu baitaɓa tunanin zata iya ɓoye wannan zunubin nasa mai girma ba wanda ko a wajen ubangiji baya rufawa fasiƙi asiri amma ita ta ɓoye kawai don kiyaye martabarsa"......



_*Oum Hairan*_
[11/17, 7:25 AM] OUM HAIRAN: _*22*_



_*Oum Hairan*_



Takowa yayi gabanta ya tsugunna yakai hannu zai riƙota ta janye hannunta tare da tashi zaune yanayi masa wani kallo da yau shi da kansa ya tabbatar da asalin nadamar zaɓarsa matsayin abokin rayuwa takeyi kafin yakai da gama tantance hakan yaji tace “Nayi regretting na kasancewarka zaɓina inama wani na zaɓa bakai ba..." Damƙar hannunta yayi ya sassauta murya yace “Ko baki faɗa ba Noor nasan lokaci yayi da zaki ƙaryata zuciyarki data yarda cewa niɗin zaɓine na ƙwarai Rafi'ah Ni kaina ina tuhumar kaina da kasa yi miki adalci ina zargin kaina da son kai gami da zuciya Rafi'ah meye yasa na aikata wlh Ni ba haka nake ba bansan daga daidai lokacin dana zama haka ba karki barni na ƙara lalacewa ko ba komai za'a nunani a kirani uban ɗanki a jinsin mutane bantaɓa riskar kaina da tsananin nadamar wani abu kamar abinda ya faru jiya ba kuma bantaɓa jin kunyar wani mutum kamar yanda naji kunyarki ba Rafi'ah wlh ba ƙiyayya bace bansan menene ba don Allah ki yarda dani ki yafemin zanji daɗi kuma da yafewarki zan samu damar neman ta Ubangiji"





Tashi tayi zata bar masa wajen ya riƙota ta fincike tayi bathroom iya bugunsa taƙi buɗe masa ƙofa har Saida Nasiba tasa baki amma tayi masa biris Abdallah ne daya shigo ya dubeshi duba na nutsuwa yaga yanda ya rufe yayi murmushi yace da Nasiba muje gida.
Ficewa sukayi suka barshi yanata roƙonta ta buɗe ga Hisham ya fara kuka amma taki saida ya gaji ya ajiye mata yaron ya fita sannan ta fito ta kulle ƙofar ta ɗauki yaron ta sanya masa nono har yanzu jikinta fada mata yakeyi. A haka Saida suka ɗauki dogon lokaci basa haɗuwa kullum idan ya dawo tana ɗaki idan zai fita ma tana ɗaki babban abinda ya dame shi duk da irin tsanar da yayiwa Billy domin yasan sanadinta ne komai yake faruwa saidai abin takaici baya iya guje mata indai ta kirashi ta nemi haɗuwa dashi sai sun haɗu ya ci ta ita kuma kullum suka haɗu sai Billy ta turo mata da video nasu da hotuna nasu suna holewa tayi block numbers sunfi ba adadi amma duk da haka bata daina tayar mata da hankali ba.
Ga lalura data sanyata gaba ita da Hisham duk sun fige sun rame takai damuwa da ciwo sun hanata zuwa Shago sai yaranta ne ke kula da komi Second Daddy ne yake damuwa da yanayinta ko a muryarta yakan fahimci akwai damuwa a rayuwarta amma bazai nuna mata yasani ba tunda bata nemi kowa ya sani ba.




Yau tunda ta tashi take juwa haka ta daure ta fito ta gyara parlourn tana tsaka da gyaranshi ne taji amai yana taso mata ko kafin takai ga kaiwa bathroom ya kwace mata ta tana tsaka da aman taji an buɗe ƙofar ta ɗago kanta idanunta ya sauka cikin nasa tayi saurin zare nata daga nasa ta tashi ta fara gyara wajen ya ajiye kayan hannunsa ya isa gareta ya ɗagota yana mata sannu batada ƙarfi shine kawai dalilin da yasa ta barshi ya taimaka mata ya gyara wajen ya gama ya ɗauko mata ruwa a freezer ya buɗe ya tsiyaya mata a cup ya miƙa mata yana mata kallon tsanaki kowa ya ganshi sai ya tambayeshi ko bashi da lafiya ne saboda ramar da yayi ashe shi ƙato ne akanta ba ita ba hatta Hisham data sanya musu takunkumin ganin juna yaron ya rame sosai.
“Meye yake damunki?" Ya tambayeta muryarsa a sarke" maimakon amsa sai yaga takai hannu ta ɗauki ɗanta ta nufi ɗakinta yabita da sauri yace “Don Allah ki saurareni Rafi'ah Kinsan kuwa irin halin da kike shirin jefani wlh neman rasa hayyaci nakeyi saboda wannan fushin da kikeyi dani na rantse Miki da Allah Rafi'ah ni ba mazinaci bane bantaɓa zina ba sai akan Billy Please ki tsaya mu tattauna matsalarmu Rafi'ah nifa ina ganin kamar bani bane...."





Durƙushewa yayi yace “Idan bazaki iya yafemin na ki kasheni ki huta ko banza zanji a raina kece kika kashe saboda bazaki iya yafemin ba Rafi'ah wai ya akayi hakan take faruwa ne nayi ina cikin nadamar hakan kuma cikin hakan na kasa dainawa na tsani zina Rafi'ah Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace “Azzina daynoun" in kayi da uwar wani sai anyi da taka in kayi da ƴar wani sai anyi da taka Rafi'ah in kayi da matar wani sai anyi da taka.... A'a Noor don Allah kar ayi dake wlh zan iya kamuwa da ciwon zuciya in ajali bai riskeni ba koda aure wani ya ratsamin ke bare da ƙazanta Please ki bani mafita na rasa wanda zan fadawa damuwata kowa ya kasa fahimtata...."
“Amai ta fara kelayawa daya katse masa hanzarin magana yayi shiru yana kallonta “to shi aman na meye ne?" Ya tambayi kansa ganin yanda ta galabaita yasashi kinkimarta zuwa mota ya koma ya ɗauko Hisham yaron da har yanzu bai shekara ba yaja motar suka bar gidan asibiti sukaje suna zuwa gwajin farko ciki ya bayyana har watanni biyu.
Zuffa ne ya fara keto masa na ɗimuwa ciki kuma ya maimaita yafi a ƙirga yanzu basu fita a wata matsalar ba zasu shiga wata lallai duk yanda za'ayi shikam ba yanzu ba ciki kuma?"




Saurin Saita kansa yayi ya shiga dakin yayi mata sannu ya fita gurin likitan ya nemi ganinsa ya sanar dashi shifa cikin nan a zubar dashi kawai saboda wahala takesha ga kuma ƙaramin goyo da farko likitan yaso bashi shawara saidai ganin ya tubure yasashi yarda suka fita yayi mata allurar da wasu magunguna suka tafi gida aikuwa da dare batayi bacci ba shima bai rintsa ba ciwon ciki da safe ma haka dole. Tasa suka kuma komawa asibiti akace masa allurar zubar da cikin da akayi mata ce take sata ciwon.
Abu kamar wasa ciwo ya rinƙa ta'azzara ciwo sai gaba yakeyi gashi kuma ciki yaƙi ko motsi sai baƙar wahala da abin ya gagara sai admitting ɗinta sukayi a asibiti suka rinƙa kulawa da ita har zuwa lokacin shikuma bai haƙura so yake a zubar da cikin itakam batama san meye yake faruwa ba kawai ta zaci nashi salon ne a haka duk da cewa a wannan karon itama batayi murna da samuwar wannan ciki ba domin kamar yanda yaso bijirewa haihuwa da ita a lokacin cikin Hisham itama yanzu zuciyarta ta ɗiga kokwanto akansa.





Saida ta kwana biyu a asibitin ƙarshe babban likitan da yaga wahalar da takesha ya bashi shawarar su haƙura da cire cikin nan in ba haka ba za'a iya rasa biyu India ciki akaso cireshi yaƙi ciruwa to rayuwa yake nema gara a barshi, kan dole badon yanason wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login