Showing 69001 words to 72000 words out of 72723 words
kawai abinda zamuyi addu'a akai Zaujh Allah baya sabon aiki muyi masa godiya kuma ka karɓi matarka da duk alkhairin da tazo maka dashi"......
“A Fito Gimbiya Ummi ta iso masarautar Zinder" Guɗar da aka rinƙa kwaɗawa ce ta sanya kalaman Rafi'ah datsewa ta janye a jikinsa ta faɗa bathroom ta kulle ta zauna kan komin wankan taci gaba da share hawayenta tare da zaro wayarta ta latsa wayar Mommy da tuni ta nutsu ta tubarwa Allah tana dagawa ta sawa kukanta jiniya tace “Mommy kishiya...." Saida Mommy ta miƙe tace “A ina Rafi'ah?" “A gidana mijina Mommy Daddyn Jalal ne yake aure yau" wata irin ajiyar zuciya Mommy ta sauke tace “Innanillahi wa inna ilaihir raji'un, to yanzu Rafi'ah shine baki faɗamin ba sai yanzu" cewa tayi “Ba haka bane Mommy shima baisan da naɗin sarautar tasa ba bare auren sai yau ɗinnan da muka dawo muka iske komai"........
*End book One*
Littafi na biyu sai December zan fara post nashi in kuma na gama Research na Project ɗina kafin December ɗin to kuyi hƙr uzururruka na ne bana shirya musu ɓakatatan suke faɗomin.
_*Oum Hairan*_
[11/25, 8:03 PM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU...*_
_*Oum Hairan*_
Jinjina kai Mommy tayi tace “To ai shikenan inma dai ke baki sani ba to tabbas shi yasani don babu yanda za'ayi ayi masa naɗi batare daya sani ba yanzu dai rage kishi saisaita zuciya tunkari aikin gabanki Rafi'atu na kishiya baƙar kadara ce mara daɗin azanci wlh duk daɗinki da miji indai akayi miki kishiya saikin ragu kuma dama raguwar akeso kiyi shiyasa akayi miki to ki nutsu ki kula da lamuranki kar kibada ƙofar fahimtar ɓaraka tsakaninku Uwar mijinki bata sonki danginsa ma haka to yanzu duka zasu tattare wajen kishiyarki ne zakiga abubuwa iri iri kiyi haƙuri zai wucce ki danne zuciyarki da yawan ambaton sunan Allah da neman ɗaukinsa"
Godiya tayiwa Mommy sukayi sallama fitowa tayi da mamakin ganinsa zaune gefen gadon ya haɗe kai da gwiwa ta matsa gareshi ta rusuna ta ɗago kansa tsoro ya kamata ta ja baya da sauri tace “Kuka Deeny meye yayi maka zafi haka?" Maimakon hawayen yayi ƙasa saima ƙaruwa da yayi ya riƙota ya ɗagota jikinsa yace “Wlh ke kaɗai zakiyimin takaba Rafi'ah bazan zauna da ita ba na faɗa miki Rafi'ah meye yasa ba'ayimin auren dole tun a farko ba saida aka nemi yardata koda zuciyata bata ga Rahina amma na samu nutsuwar zama da ita, Ƙurrah sai yanzu zaayimin auren dole"
Kwantawa tayi luf a ƙirjinsa ya matseta yace “shekarata sha takwas da aure ƴaƴana Biyar Ni Rafi'ah ni auren dole?" Murmushi tayi tace “Aa fah Mai Martaba kayi hƙr zaka sota...." Rufe mata baki yayi da nasa tayi ƙoƙarin ƙwacewa ta kasa da haka suka shiririce daidai lokacin da Hajiya Kilishi ta shigo ɓangaren tana zage² faɗi takeyi wlh tallahi indai Ni na haifeka yau sai ka rabu da wannan karfar yarinyar na tsani zamanka da ita uwarme take tsinana maka uwar me kake tsinta a wajenta..."
Angaza ƙofar tayi daidai lokacin da sukayi nisa cikin duniyar ma'auratan da suka macewa ƙaunar juna maza tayi taja bargo ta rufeshi yayi luf a jikinta yau ta zame mata rana mafi muni cikin rayuwarta tayi maza ta zame a jikinsa ta shige bathroom ta sakarwa kanta ruwa shiko baima iya tsayawa wankan ba ya zura wandonsa da jallabiyarsa ya fice yana fita Kilishi ta daukeshi da wani masifaffen mari da yasa Rafi'ah dafe kuncinta daidai lokacin da take fitowa tayi saurin zura doguwar riga ta nufo hanyar fitowa saboda shirun da taji parlourn ya ɗauka a kuma sa'ar ne Kilishi take cewa “Wlh Indai ba Rafi'ah ce tayi naƙudarka ta haifeka ba to yau kuma a wannan lokacin saika bata takardar sakinta in kuwa kaƙi Deeny zan tsine maka zan kuma Barka da mace tunda ita ka zaɓa, yanzu Deeny ni zaka wulaƙsnta ni zaka tozarta na nemo maka auren ƴar ƙanina ɗiyar tarbiyya tsatson arziƙi bana iya duniya ba amma ka rasa dame zaka gode min saida daddagewa ka rubuta min saƙon godiya ta hanyar rattaɓawa Zainab saki har uku rigis lokaci guda...."
Numfasawa tayi ta ɗora da cewa “Duk da nasan kasani itama makirar matar taka ta sani bana ƙaunarta cikin zuri'ata amma ban shiga rayuwarka da itaba sai itane ta shiga tsakanin biyayyata dakai Shamsunddeen na faɗa maka ka rubuta ko ka furta duk ɗaya ne saki uku kayiwa Zainab kazalik uku zakayiwa Tsinannar matarnan taka" shigowar Jamal da Jalal Hameed da Hameedah ne suka sanya Deeny zubewa bisa gwiwarsa yace “Kilishi duba fa kingansu fah don Allah karki tursasani yin abinda zai zama ya wargatsa rayuwar farin cikin iyali na Kilishi Rafi'ah rayuwata ce uwar ƴaƴana ce idan kika rabani da ita dawa zan rayu kuma wace zata bani farin ciki? Kilishi ƴaƴanmu biyar da ita ta zama jijiyar rayuwa ta...."
Ɗaga hannu tayi zata kuma ɗauke shi da mari Rafi'ah tayi mazantakar riƙeta idanunta na zubar da hawaye tace “Ko babu ɗiyansa a gurin Hajiya Deeny yafi ƙarfin duka akaina meye burinki ne? So kikeyi ya sakeni inadai shine burinki? Ok Ammy bazaki tsinewa Deeny akaina ba inason a gaba dani dashi muyi umarni ga ƴaƴanmu suyi mana biyayyar yanke take shine kawai Deeny kayiwa Allah da Manzonsa kayiwa Ammy biyayya...."
Janyota yayi ta fado jikinsa ya matseta yana cewa “Kinji Ƙurrah zuciyata bugawa takeyi idan hakan ta faru komai zai iya faruwa dani Please...." Tureshi tayi tace “Alkhairi da albarka zai tabbata gareka idan kayi wannan biyayyar Deeny akwai abinda ka kasa hange akaina ƙila wanda Ammy take hango maka zai zame maka mafi sauƙi idan ka sakeni a lokacin da nasan bada ra'ayin kanka bane tursasaka akayi Zaujh me kake tsoro wlh indai nice na gama aure matuƙar bada kai zan rayu ba inasonka kamar jinin dake gudana a jikina Please Deeny Ni takace karyawa Ammy rantsuwarta...."
Maimakon ya furta sakin sai kawai ya miƙe ya nufi hanyar barin parlourn saboda idan yaci gaba da sauraren su zuciyarsa tanada matsala zai iya samun matsala wannan ne kawai yasa yaji ya fice yafi alkhairi amma maimakon hakan sai Ammy ta shaƙoshi tace “Deeny ko zaka mutu saika saketa" wani abu ta matse a hannunta ɗaya ya juyo da sauri idanunsa da muryarsa duk sun nuna gazawarsa domin hawaye yake zubarwa da gaske muryarsa na rawa yace.
“Shis...shi...ke...nan... Ƙur...rah... Ammy na saki Ƙurrah Sakiy...." Yanke jiki yayi ya faɗi sukayi kansa gabaɗaya daidai lokacin da Mai martaba ya iso parlourn domin labari ya isheshi na sakin da yayiwa Zainab ganin ɗan nasa kwance cikin mawuyacin hali yasashi ƙarasawa Rafi'ah ta matsa gefe tana Girgiza kai gabaɗaya jikinta ya mutu wannan saki yafi wanda Abdulƙadir yayi mata Girgiza ruhinta tambayar kanta takeyi ita meye tayiwa mutane da suka tsaneta haka ne meye abinta kuka take sosai ta shiga ɗakinta ta fara haɗa kayanta ta ɗauki Hurriyah ta goyata yaran dukka suna kallonta ta Kama hannunsu duka dai kuma ta fashe da kuka tace “Jamal Jalal don Allah ku kula da kanku kunji hukuncin ubangiji ya sauka tsakanina da mahaifinku kunji" Hameed ne ya matsa gabanta yace “Mommy ina zaki karki tafi ki barmu Ammy batason mu...." Bankado kofar da tayi ta shigo ne yasa yaron yin shiru ta nuna musu hanya tace “Bakar mayya da kikaga na rabaki dashi shine kika kama sa zaki lashe kowa ya rasa to kuwa ta Allah ba taki ba insha Allahu Deeny ya rabu da kwallon mangwaro ya huta da ƙudaje, sai aje abi wani sarkin ko a koma Igabi bakin gada aci gaba da karuwanci..."
Hawaye ne ya wanke mata fuska taja zuciya tace “Iya hakama Ammy na gode ko iya nan rayuwata da Shamsunddeen ta tsaya nasan kinyi farar haihuwa kuma kin haifi ɗan halal mijina farin cikina uban ƴaƴana inason Deeny domin shima ya soni" daga haka bata kuma cewa komai ba ta ɗauki jakarta ta fita zuwa mota ta shiga taja da gudu tabar gidan tana hawaye ta isa wani hotel ta kama gurin kwana yau kwanan zaune tayi a ranta tana raya aure be karɓeta ba, babbar damuwarta yanzu tayi ƙarfi a Niger ya zatayi da dukiyarta data baza? Siyarwa... Abinda yazo ranta kenan, haka ta kwana ta hantse bacci ko barawon bai ɗauketa ba washegari tun asuba ta sanar da Daddy abinda ke faruwa yayi caraf yace “Ok maza kiyi gaggawar baro ƙasar ina Abuja ki sameni acan saimu wucce California" taji daɗin hakan sosai wannan karon ko Mommy bata sanarwa abinda ke faruwa ba tayi shirinta ta nufi Abuja zuciya duka babu daɗi tana sauka wanka tayi taci abinci Daddy yake tambayarta meye ya faru? Nan ta kwashe komai ta sanar dashi yayi jim can yaja fasali yace.
“Shikenan Ummana Allah yasa hakan shine yafi alkhairi kin sanar da Bara'ah kuwa Girgiza kai tayi yace “Meye yasa ki kirata ki sanar da ita tana Gombe ma ina tunani" tashi tayi ta koma ɗakinta ta zubawa Hurriyah idanu tanason sanin halin da Deeny ke ciki saidai batasan hanyar da ya kamata tabi ba, Gimbiyar Dutse ce ta faɗo mata ta ɗauki waya da sauri ta kirata kira ɗaya ta daga tace “Rafi'ah ina kika shiga kika barmu da tashin hankali?"
Zuciya taja tace “Ina Zaujh Gimbiya ya tashi hope yana lfy na kira wayarsa a kashe" Numfashi taja tace “Wanne lfy jiki ya rikice ai tunda ya farka ya nemeki Kilishi ta sanar dashi kin tafi tun daren jiya shikenan ya sake rikicewa wlh yana cikin yanayin da duk me imani saiya tausaya masa likitoci ma sun tabbatar da cewa zuciyarsa ta samu matsala fiye da ko yaushe.
Hawaye ne ya wanke mata fuska taja zuciya tace “Iya hakama Ammy na gode ko iya nan rayuwata da Shamsunddeen ta tsaya nasan kinyi farar haihuwa kuma kin haifi ɗan halal mijina farin cikina uban ƴaƴana inason Deeny domin shima ya soni" daga haka bata kuma cewa komai ba ta ɗauki jakarta ta fita zuwa mota ta shiga taja da gudu tabar gidan tana hawaye ta isa wani hotel ta kama gurin kwana yau kwanan zaune tayi a ranta tana raya aure be karɓeta ba, babbar damuwarta yanzu tayi ƙarfi a Niger ya zatayi da dukiyarta data baza? Siyarwa... Abinda yazo ranta kenan, haka ta kwana ta hantse bacci ko barawon bai ɗauketa ba washegari tun asuba ta sanar da Daddy abinda ke faruwa yayi caraf yace “Ok maza kiyi gaggawar baro ƙasar ina Abuja ki sameni acan saimu wucce California" taji daɗin hakan sosai wannan karon ko Mommy bata sanarwa abinda ke faruwa ba tayi shirinta ta nufi Abuja zuciya duka babu daɗi tana sauka wanka tayi taci abinci Daddy yake tambayarta meye ya faru? Nan ta kwashe komai ta sanar dashi yayi jim can yaja fasali yace.
“Shikenan Ummana Allah yasa hakan shine yafi alkhairi kin sanar da Bara'ah kuwa Girgiza kai tayi yace “Meye yasa ki kirata ki sanar da ita tana Gombe ma ina tunani" tashi tayi ta koma ɗakinta ta zubawa Hurriyah idanu tanason sanin halin da Deeny ke ciki saidai batasan hanyar da ya kamata tabi ba, Gimbiyar Dutse ce ta faɗo mata ta ɗauki waya da sauri ta kirata kira ɗaya ta daga tace “Rafi'ah ina kika shiga kika barmu da tashin hankali?"
Zuciya taja tace “Ina Zaujh Gimbiya ya tashi hope yana lfy na kira wayarsa a kashe" Numfashi taja tace “Wanne lfy jiki ya rikice ai tunda ya farka ya nemeki Kilishi ta sanar dashi kin tafi tun daren jiya shikenan ya sake rikicewa wlh yana cikin yanayin da duk me imani saiya tausaya masa likitoci ma sun tabbatar da cewa zuciyarsa ta samu matsala fiye da ko yaushe ki dawo cikin iyalanki Rafi'ah yafi miki alkhairi mijinki yana sonki kiyi domin Allah ki duba halin da yake ciki ke kaɗai yakeson gani" shiru tayi na tsayin lokaci can ta ajiye wayar ta tsunduma duniyar tunanin abinda ya dace wata special number taga an kirata da ita ta ɗaga da sallamarta jin Muryar babban mutum yasata nutsuwa “Rafi'atu kin gane wake kan layi?" Numfashi ta sauke tace “Lahh Mai Martaba Barka da wannan lokaci" murmushi yayi yace “Sannu Rafi'atu ya haƙurin rayuwa kuma, yanzu kina ina?" Shiru tayi kafin tace “Ina California Allah ya taimake ka" shiru yayi can yace “Yanzu babu yanda za'ayi ki dawo kenan
_*Oum Hairan*_
[11/25, 8:03 PM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU...*_
_*Oum Hairan*_
Shiru tayi ranta yana kai kawo a ƙirjinta bazata iya cewa da Mai Martaba a'a ba domin itama tana on sanin halin da Deenya yake ciki “Bakice komai ba Rafi'atu mijinki yana buƙatar kulawar ki jikinsa ya rikice kamar komai zai iya faruwa Yakamata in ya rasa kulawar uwa ya samu ta matarsa Rafi'ah nake Kilishi ke ƙi ba mijinki take ƙi domin ba ita ta haifeshi ba shiyasa take faɗa da duk abinda yakeso karki raba kanki da mijinki domin yafi kowa dacewa da zama jagoranki shiɗin uban ƴaƴanki ne" numfashi ta sauke cike da tausayin kanta da kuma na Deeny ya jima yana faɗa mata meye yasa Kilishi batason farin cikinsa ya jima yana cewa shi baitaɓa ganin uwa irin tasa ba duk wani abu da yake alkhairi gareshi bata ƙaunarsa shin ya zaiji lokacin daya fahimci ashe Kilishi ba ita ta haifeshi ba ya zaiji duk lokacin da ya tuna irin karfa ƙarfar data rinƙa yi masa da baya? Kaico da uwa irin wannan lallai ne zata komawa mijinta tunda yana sonta abu ɗaya dake karyar mata gwiwa Kilishi tayiwa aurensu rauni to wai shin ma saki nawa yayi mata ne?" Miƙewa tayi ta fita tana cewa “zan shigo Mai Martaba" aje wayar tayi ta nufi ɓangaren Daddy tana shiga yana fitowa ta tsaya tace “Niamey zan tafi Daddy" kallonta yayi kallo na nutsuwa yace “Jikin Deenyn ne?" Ƙasa tayi da kanta tace “Bayan hakan ma inason komawa daki na" murmushi yayi yace “Akwai uzuri na dole dake faruwa a Nigeria nima yanzu shirin tafiya nakeyi ki shirya saimu tafi gabaɗaya" taji daɗin hakan duk da cewa batayi tunanin samun matsala dashi ba dama.
Yini daya suka ƙara ya nema musu urgent flight suka tashi zuwa Nigeria taso a yau ta kwana a Niger amma abin ya faskara saboda Daddy ne yace tayi hƙr suje Maiduguri tukunna, tunda ya ambaci Maiduguri gabanta yake faɗuwa hakanan jiki duk sanyi suka tafi tafiya ce ta kurame saidai lokaci zuwa lokaci takanga Daddy ya duba agogo suna isa Filin jirgin saman Borno suka fito drivern Daddy har ya hallara ya ɗebesu a motar ne taji Daddy yana waya yana cewa “Sun iso an kawo gawar?" Gabanta ya yanke ya faɗi jin yace “Ai a America ya rasu" ta sake shiga ruɗu tuni zuciyarta ta soye ta damƙi hannun Daddy tace “Hisham ne ya rasu Daddy dama bashi lafiya ba'a faɗamin ba..." Ganin yanda ta ruɗe ne yasa Daddy kwantar da kanta a cinyarsa yace “Kullu nafsin za'iƙatul maut Ummana babu wata rai da zata gocewa wannan lokaci shi tashi ma tayi kyau yayi kyakkyawar cikawa saidai fatan Allah yasa kwanciyarsa ta zama hutunsa"
Galala take kallon Daddy har ya ida fadar abinda zai faɗa daidai lokacin da sukayi parking gaban wani Arnen gida na uban babansun Kofar gidan maƙil yake da motocin sojoji sai zagaye sukeyi haka suka kurɗa suka shiga ciki suna shiga taga wata ƙatuwar akwati a harabar gidan rubutun dake jikin akwatin ta kalla (R.I.P AIR MARSHAL ABDULƘADIR IBRAHIM BARZAH)..... Wata ƙara ta saki tayi zaman ƴan bori a gurin jikinta na rawa tace “Abnoor innanillahi wa inna ilaihir raji'un a'a bashi bane ya mutu don Allah karku cemin Abdulƙadir ya mutu burinsa bai cika ba...."
Ji tayi an kwanta a jikinta an rushe da kuka daya bangaren ma an kwanto mata ɗagowa tayi juwa na ɗibanta a zaune ta dubi ƴaƴan nata Hisham da Ablah ta rungumesu suka rushe da kuka a tare Hisham yace “Mommy ya mutu shikenan mun rasa Daddynmu mun rasa soyayyar sa...." “Mommy meye yasa Daddy zai mutu a daidai lokacin da muka fi buƙatarsa yanzu waye zai bamu kulawa Mommy shikenan babu ke babu Daddy mun rasaku dukka..." Sake rungume yaran ta kuma yi tana kuka me tsuma zuciya ta ji tayi an dafata ta ɗago idanunta ganin Alh Ibrahim Barzah yasata miƙewa yace “Ku shiga gida" shiga sukayi suka zauna kusa da Ya Hajja data haɗe kai da gwiwa ɗagowa tayi suka kalli juna suka sake fashewa da kuka sun jima a haka sannan akazo aka kira Iyalinsa domin suyi masa bankwana bata tashi ba saida Hajiya ta riƙo hannunta tare suka tafi suka shiga dakin da akayi masa sutura yana kwance sunkif cikin likkafani ta tsugunna gabansa tana kuka me tsuma zuciya abubuwa da dama da suka faru a baya tsakaninsu sunata dawo mata hawayenta yaƙi tsayawa daƙyar ta iya yi masa addu'a yaran sunata kukan rashin mahaifinsu ɗaukarshi akayi Hisham yabi bayansu zuwa gidansa na gaskiya.
Sai lokacin ne suka gaisa da Ya Hajja tare da yiwa juna gaisuwa itadai Rafi'ah banda kuka babu abinda takeyi bata taɓa jin mutuwar data Girgiza duniyar ta kamar wannan mutuwa ba shikenan manyan ƴaƴanta sun zama marayu tana zaune ne bayan an dawo daga kai Abdulƙadir makwancinsa Alh Ibrahim Barzah ya shigo ya kirata ta miƙe ta fita zuwa wani daki dake cikin parlourn mamaki ya cikata ganin Mai Martaba da Deeny da Abdullah ga kuma Daddynta sai Hisham duk a zaune kallon kallo sukeyi tsakaninta da Deeny yana mata kallo me cike da ƙauna da tausayawa ita kuma tanayi masa kallon tausayin irin ramar da yayi zama tayi a gefe Mommy ta shigo Ya Hajja ma ta shigo suka zauna.
Mai Martaba ne ya buɗe taron da addu'a akayiwa Marigayi Abdulƙadir addu'a sannan taron ya fara da cewa “Muna masu miƙo saƙon gaisuwa ga wannan ahli musamman ma iyayen Abdulƙadir da ƴaƴansa bayan haka Alh wata magana mukazo da ita kuma Alfarma ce da zakuyi mana muma don musamu ladan maraici duba da Mahaifiyar waɗannan yara tana hannunmu karkashin kulawar mu wannan dalili yasa Sarkinmu kuma mijin mahaifiyar waɗannan marayu yake neman alfarmar a bashi waɗannan yara su koma karƙashin kulawarsa da mahaifiyarsu. In hakan yayi muku to mu a shirye muke da tafiya dasu bayan