Showing 30001 words to 33000 words out of 72723 words
durƙushe ta riƙe bayanta da mararta tana wani irin nishi na masifa shi kuwa takaici ne yasashi miƙewa zai shiga bathroom ta riƙo ƙafarsa tace “Innanillahi wa inna ilaihir raji'un Abdulƙadir marata bayana wayyoh Allah ya hayyu ya ƙayyumu...." Tureta yayi ya fusge ƙafarsa zuciyar ƴan maza ta motsa ya argajeta ya shige bathroom ji yake kamar ya haɗiyi zuciya tsabar ƙuncin data shaƙa masa.
Yana jiyo nishinta amma bai ko saurareta ba yayi wankansa ya fito ya wucceta daƙyar ta iya ɗago kanta idanunta na tsiyayar hawaye tace “Meyesa baka tausayina AbNoor bantaɓa maka ƙarya ba amma baka yarda dani idan da ni maƙaryaciya ce da tuni ka fahimta inajin ciwon da yayi kama dana datsar rayuwa idan kai bazaka iya taimakona ba ka kiramin Ya Hajja ko Gana Hajja...." Tsawa ya daka mata cikin bala'i yace “Uwarki ce ita Ya Hajjan da zan kira miki badai ciwo kike gayyatowa kanki ba kije kiyitayi haƙƙina ne kije Allah ya isa zanje na nemawa kaina mafita" sakai yayi zai fita ta bisa da kallo cikin mawuyacin hali tace “Don Allah Abdulƙadir karka aikata zina Indai da gaske zuciyarka bata yarda da halin da nake ciki ba kazo na rantse ko zai zama matakin ajali na zan jure....."
Bata gama rufe bakinta ba yayi ficewarsa ya barta a halin rai kwakwai mutu kwakwai daƙyar daƙyar ta iya ɗauko wayarta dake ƙasa a yashe kusa da ita itanma ring ɗinta taji ta samu ciwon ya ɗan sauka kaɗan har ta samu hayyacin ɗaukar wayar “Mommy!" Tagani kan sensor ɗin ta sauke wata ajiyar zuciya me ƙarfi duk da mawuyacin halin da take ciki ta kara a kunnenta tace “Way...yohhh Mum... Mommy don Allah wayyy innanillahi Mommy mutuwa zanyi ki...kema kina fushi dani shima yana fushi dani Mommy ke ki...." Jifa tayi da wayar taci gaba da murƙususunta tana maimaita kalmar shahada da duk addu'ar da tazo bakinta tanajin Mommy nata maimaita “Rafi'ah ya sallam Rafi'atuh meye ya sameki ina mijin naki waye a tare dake bashi waya???" Tambayoyi barkatai saidai batada ikon amsawa a karon farko a rayuwar aurenta watanni goma kenan da sukayi waya da mahaifiyarta cikin mawuyacin halin daya zaune a zuciyar Mommy.
*Oum Hairan*
[10/16, 11:58 AM] OUM HAIRAN: *AKWAI IRINSU....*
_(Emotional Eroctic romance and bad destiny)_
_*Oum Hairan*_
_Paid book nrml 300 VIP 600 special 1k Email post 2k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank evidence 09013718241_
_*Last free page 15*_
Bazata iya cewa ga yanda akayi ba ita dai taji an banko kofar an shigo tun daganan bata kuma gane wani abu ba sai bayan ta farka a asibiti ashe jini ne ya ɓalle mata da Abdallah da Nasiba sune suka daukota suka kawota asibiti a ranar duk yanda Abdallah yaso samun wayar Abdulƙadir bai samu ba a kashe ake faɗa masa lokacin da likitocin suka bashi tabbacin wannan cikin saidai a cireshi domin tunda dama watan haihuwar ya shiga shidai kasa cewa komai yayi Saida Nasiba ta bashi shawarar ya kira can Maiduguri ya sanar dasu halin da ake ciki.
Bayason tonawa abokin nasa asiri wannan abu ne me girma kasan Kanada me tsohon ciki har ka iya ficewa ka barta kuma a halin lalura ma domin sojan dake gadi a daren ya faɗa masa bai daɗe da fita a gidan ba kuma da alama da fushi ya fita, haka don bashi da wata mafita ya sake kiran Ya Hajja ya sanar da ita halin da ake ciki ta sanar da Abba shi Abba ne ya bashi umarnin tunda ba'a san inda za'a nemo Abdulƙadir ɗin ba yasa hannu kawai ayi mata aikin amma ya ɗan jira ya sanar da mahaifinta"
Babu jimawa Second Daddy ya kira Abdallah ya bashi umarnin yasa hannu nan take ya cike takarda aka shiga da ita Emergency theater tsayin awa biyu suka fito cikin nasara Allah ya basu ikon ciro mata ɗanta namiji ƙarfe uku na dare lokacin Abdallah ya amshi Yaron a hannun Nasiba tunda dama harda ita a aikin domin asibitin da take aikine kuma tana cikin manyan likitocin wajen.
Kurawa yaron idanu yayi kyakkyawa masha Allah sak fuskar sa ta mahaifinsa gashi ƙato masha Allah, daidai lokacin ne kuma wayar Abdulƙadir ta samu shiga ya ɗaga muryarsa a gajiye Abdallah bai jira cewar sa ba yace “Yanzu haka kana ina?" Cikin ƙosawa yace “Ina hanyar komawa gida" iska ya furzar me zafi yace “Me zakayi a gidan?" Jim yayi saboda in ya lura Muryar Abdallah akwai wani abu saɓanin abinda yake furtawa “Tuhuma?" Ya tambayi kansa yana taka birki a daidai parking space na gidan ya shiga ciki da sauri yana kiran sunanta ƙasa yayi da kansa yanabin jinin daya bushe a parlourn da kallo yace “Jini.... Meye ya kawo jini parlourn nan Samuel?"Ɗakin Rafi'ah ya nufa da gudu ya buɗe babu wata alama da take nuna anshiga dakin a yau ma hakan ce ta sashi nufar nasa da sauri ya banka ƙofar iya kofar ya tsaya saboda ganin jinin da yayi duk ya fara bushewa a ƙasan gadon ya isa da sauri ya tsugunna tare da sanya hannu ya dangwali jinin yakai hancinsa da gaske jini ne ya miƙe cikin wani yanayin tashin hankali ya fito ya ishe Samuel da Abdulkarim a parlourn suka sara masa ya dubesu yace “Ina Rafi'ah?" Ƙasa Samuel da Daniel sukayi da kansu Abdulkarim ne yayi ƙarfin halin cewa “Sir Madam ta shiga mawuyacin hali ne shine Lieutenant Abdallah yazo ya ɗauketa a mota shida Madam ɗinsa da alama asibiti suka tafi da ita domin naji matarsa tana cewa haihuwa zatayi...."
“Haihuwa!? A'a cikinta baikai haihuwa ba" waya ya ɗauka ya kira Abdallah kira ɗaya ya ɗaga yace.
“Nou'emh hospital" iyakar abinda ya faɗa masa kenan ya kashe wayar ya shiga motar a hargitse yajata yabar gidan bai samu wata doka ba domin da ID card ɗinsa a jikinsa ya isa har asibitin yana zuwa suka fara kallon kallo da Abba da second Daddy da kuma Ya Hajja dake zaune ɗauke da babyn naɗe cikin towel mamakin yanda akayi wannan mutanen suka haɗu a wannan lokacin ya hanashi magana da kuma lissafin yanda akayi Rafi'ah ta haihu a daidai wannan lokacin bayan lissafin wata bakwai sukeyi, toma wai cikakken ɗa ne ɗan wata tara ko kuwa bakwaini?"
Cikin tsananin sanyin jiki yace “Kuyi hƙr Daddy..." Ɗaga masa hannu Abba yayi yace “Yanayin aiki ba yanda baya kamawa Audu masha Allah Ubangiji ya sanyawa Abdulkarim Albarka..." Saurin kallon Abdallah yayi Abdallah ya kawar da kansa yace “Banyi tunanin dawowarku a wannan lokacin ba ashe da wuri ma zaku shigo"
Ajiyar zuciya ya sauke karo na farko da ya aminta aka ɓoye laifinsa kuma yaji daɗi har cikin ransa yasani don ta Rafi'ah komai zai zama me sauƙi tunda akwai so da ƙauna zatayi saurin fahimtarsa amma iyayensa musamman Ya Hajja da suka ɗebota tun farkon cikin bazata taɓa yi masa uzuri ba.
To waishi wanne irin ma abune yasashi aikata wannan ɗanyen hukuncin akan Rafi'ah in bai manta ba ta sanar dashi tana cikin mawuyacin hali amma ya kasa tausa zuciyarsa ya saurareta yayi mata hukuncin da inda wannan haihuwar tazo da ƙarar kwana bazata iya yafe masa ba domin shine sanadi" shidai duk da cewa baiga alamun tuhuma a fuskar kowa ba amma ya kasa matsar Ya Hajja domin wani irin kallo takeyi masa daya rasa da me yake masa kama.
Zargi ko tuhuma? Bai samo wannan amsar ba ya jiyo muryarta tace “Ga ɗanka Audu Allah ya kawo shi" daƙyar ya iya takawa ya karɓi jaririn ya sanya hannu ya buɗe fuskar handsome boy ɗin ya saki wata ajiyar zuciya me ƙarfi soyayyar yaron tana kwaranya a zuciyarsa yanajin wani baƙon yanayi na musamman yana shigarsa ya sauke ajiyar zuciya ya ɗago ya motsa bakinsa daƙyar yace “Ina Noor ɗin Ya Hajja?" Tana miƙewa tace “Tana ɗakin hutu kasan dake aiki akayi mata jinin daya zubar ta galaɓaita bazata iya haihuwa da kanta ba shiyasa tun zuwanka Maiduguri nace ka taho mata da Nasira saboda gudun irin wannan matsalar yanzu badon Allah yasa mahaifiyarta ta kira ba da saidai ƴar mutane ta mutu babu wanda ya sani"
“Ta kira?" Ya faɗa yana kallon Ya Hajja nandanan ya canza yanayi ya miƙe yana cewa “Nasiba zan iya ganin Noor?"
Yanayin fuskarsa ya tabbatar mata da bazai mata uzuri ba tayi ƙasa da kanta tace “Eh a'a Yallaɓai" da sauri yace “Tana cikin critical conditions ne?" Girgiza kai tayi tace “Bata ciki saidai har yanzu Allurar da akayi mata kafin theater bata saketa ba Yallaɓai in so samu ne tanason cikakken nutsuwa" ɗaga mata hannu yayi yace “Don Allah cewa nayi zan iya ganinta ba abinda zai yuwu na tambayeki" kallon Abdallah tayi ta ɗaga mata kai tayi gaba tace “Ok muje Yallaɓai" binta yayi a baya yana dauke da jaririn suka shiga rest room ɗin tana lulluɓe da wani mayafi fuskarta ce kawai a buɗe ya ƙarasa ya zuba mata ido shi kansa yasan ta rame tun a baya ba kamar yanda ya ɗaukota gaban mahaifiyarta ba amma yau yafi ganin ramarta fiye da kullum.
Kallonta yakeyi yana kallon Babyn hannunsa yana murmushi tare da shafa sumar yaron da yaketa bacci hankali kwance yace “Inasonku kaida mahaifiyarka ɗana...." “A hakan?" Yaji an faɗa ya juyo da sauri yana sauke injin idanunsa kan Abdallah da Mommy dake shigowa Isa tayi gaban gadon ta ɗage rigar Rafi'ah ta fara dubata sosai tare da sauke idanunta kan Rafi'ah sosai taja numfashi tare da murmushi tace “Zaɓin da kikayiwa kanki kenan da nake nuna miki aibin hakan gani kike tsanarki nayi, ki rayu cikin aminci keda iyalinki Ɗiyata Allah yaci gaba da baki kariya"
Juyawa tayi ta fice ba tare da ta ko kalli Abdulƙadir ba domin da gaske takejin haushinsa ita ta kasa yarda baya gari ne domin kalmomin Rafi'ah kafin ta rasa hayyaci sun nuna yasan halin da take ciki ya kasa bata gudummawa, bayan fitar Mommy ne Abdallah ya dafashi yace “Shiyasa nake yawan tuna maka zuciyar ɗa da mahaifi sarrafuwar ubangiji ce jini ne ya jiyar da baiwar Allan nan halin da ƴarta take ciki harta bibiyi abarta da babu ita a rayuwarta da tuni ba wannan zancen akeyi ba tabbas uwa uwa ce amma fah wata uwar tafi wata duk da saɓanin ra'ayi bai hana Mommy jin ƴarta a jininta ba so kayi taking care"
“Abdallah!" Ya faɗa da ƙaraji idanunsa na canza launi yaci gaba da cewa “Akwai abinda ya faru ne da gazawata ta bayyana hakan yau ne ko yanzu Rafi'ah takemin ƙaryar ciwo kawai don batada ra'ayin sauke haƙƙina dake kanta Abdallah na fara gajiya da tuhumar nan da kukemin kaida Ya Hajja akan Rafi'ah wai ku kuka ɗaukomin ita ne ko fina sonta kukayi da kuke ɗora zargi a kaina Please ku bari banason zanyi rashin mutunci akan hakan wlh" yana gama faɗin haka ya juya yayi ficewarsa yaron ya kaima Ya Hajja ya tambayeta meye ake buƙata ta sanar dashi ya fita ya nufi gida ya fara haɗo masu kayan sai yanzu asuba tayi babu shaguna a buɗe shiyasa ya ɗebi iya abinda ke a gida ya juya ya fita ko a motar tunani ne barkatai a cikin kwakwalwarsa lumshe idanunsa yayi yana ajiyar zuciya a baya yayi neman mata amma tunda yayi aure sai yakejin bazai kuma ba zai daina to meye kuma yanzun yake neman mai dashi ruwa? Rashin kulawar matarsa ko meye?
Gari ya fara wayewa lokacin daya koma asibitin daidai lokacin ne kuma Rafi'ah ta samu farkawa da kalmar shahada ta tashi ta zubawa ɗakin idanu dadai sa'ar da likitan ya turo ƙofar ya shigo idanunta a kansa har ya ƙaraso yayi mata sannu tare da fara duba jinin dake maƙale a jikinta ya cireshi ya ɗauki wata ledar ya saka mata ya juya gareta yace.
“Da wani abu da kike buƙata ne?" Lumshe idanunta tayi tace “Ina Mijina" kallon nurse yayi yace “Zaifi ki tambayeni abinda kika haifa" bata kuma cewa komai ba ta kawar dakai ya fice daga ɗakin babu jimawa kuma saiga Abdulƙadir ya shigo yana ɗauke da babyn daya karɓa a gurin Ya Hajja domin itama ta samu ta watsa ruwa.
Tunda ya shigo suke kallon kallo har ya ida ƙarasowa ya zauna a kujerar dake gefenta cikin Muryar lalura ta buɗe baki tace “Abnoor nasan ni me laifi ce a wajenka saidai banyi tunanin girman laifin dana aikata a gaɓar lalura yakai kayimin wannan mummunan hukuncin ba don Allah kayi hƙr...."
Shigowar Ya Hajja ce tasashi saurin murmushi yace “Zuciyata ce ta kasa samun nutsuwa ba'a tashi daga taron ba na taho amma dai yanzu kinajin karfin jikinki ko?"jinjina masa kai tayi ajiyar zuciya Ya Hajja taji daɗi a ranta daya tabbata ba halin rashin tausayin nasa ya nuna mata ba ita dai tanason yarinyar kuma tana jiye mata tsoron halin Abdulƙadir da turjiya da kafiya akan ra'ayi"
A takaice Saida suka kwana uku a asibitin sannan aka sallamesu suka tafi gida Gana Hajja ce ta taho Ya Hajja ta koma ita ta rinƙa kula da Rafi'ah wani abu daya dawo musu da matsalarsu sabuwa tunda suka dawo gida kwanansu biyu da dawowa ya shigo dakin nata da dare tana zaune tana bawa yaron nono ya zauna a gefenta yana kallon yanda take feeding na yaron abin yana burgeshi yakai hannu ya gyara mata riƙon yaron yace “Kwana nawa yau da haihuwar nan?" Batare data ɗago ba tace “biyar" jinjina kai yayi yace “Addini ne yace “Idan mace ta haihu ta raba shimfiɗa da mijinta?" Girgiza masa kai tayi yaja ajiyar zuciya ya miƙe yace “Ok al'ada ce kenan? To ni ban yarda da wannan al'adar ba nasan daidai Rafi'ah saidai bazan iya aikata daidai a daidai gaɓar da aka yimin badaidai ba Please kiyimin daidai nayi miki daidai ki dawo shimfiɗata ki tallafeni yafi sauƙi akan abinda zai iya biyo baya Noor inashan wahala da sanyi inason ɗuminki a kusa dani"
Gana Hajja dake fitowa a bathroom ce ta cafe da cewa “ka kunna room Hit bazatazo ba anya kuwa Audu kai ba hariji bane to in banda haka yarinya daga haihuwarta ko sati bata rufa ba ka fara kafa mata sharraɗin komawa turaka ubanme zatayi maka tana fama da kanta" idanunsa kan Rafi'ah da tayi ƙasa da kanta baka iya gane asalin yanayin da take ciki yace “Ba hariji bane Ni saidai Ni namiji ne me son kulawa abinda na faɗa miki kenan Rafi'ah saura ya rage gareki"
Ficewa yayi abinsa ta ɗago idanunta da suka ciko da hawaye Gana Hajja tace “Taɓ ah yarinya dole ki rame wannan fitina haka to ubansa zakiyi masa" batada abin cewa shiyasa ta kulle bakinta kawai ta kwantar da Hisham itama ta kwanta ƙasan zuciyarta ji take yi kamar ta tashi taje taji me yake buƙata to inma taji ɗin tanada maganin matsalarsa ne?
Dole ta kwanta tanata juyi can cikin dare taji tashin motarsa ta tashi tayi kasaƙe tanason tashi saidai batada ikon mikewa a daidai lokacin gabaɗaya zuciyarta ta ƙuntata da wannan sabbin ɗabi'u da yaketa fito dasu itadai bata sake rintsawa ba har garin Allah ya waye suka gama abinda zasuyi bai shigo gidan ba a takaice har washegari bai shigo ba kuma bai kira ba saida Gana Hajja ta gaji ta kirasa yake faɗa mata ya yi tafiya ne kuma zai iya ɗaukar sati biyu kafin ya dawo"
*Oum Hairan*
[11/17, 7:25 AM] OUM HAIRAN: _*16*_
Mamaki ne ya cika Gana Hajja ta juyo ta kalli Rafi'ah da Salmah tace “dama yana tafiya bai sanar ba?" Ɗagowa tayi tayi murmushi me haɗe da yaƙe tace “Aa Kinsan dai yanayin aikin nasu maybe wani abu ne ya ɗauke masa hankali" masifa Gana Hajja ta rinƙayi tana cewa ”wannan ai wulaƙanci ne ko yabar komai a gida wadatacce sallama yayin tafiya addini ce"
Ajiyar zuciya tayi itadai batace komai ba har ta gaji tayi shiru can dare wajajen sha biyu na dare wayarsa ta shigo ta ɗauki wayar ta ɗaga tayi masa sallama.
Muryarsa can ƙasa ya amsa yayi shiru itama tayi shiru tsayin kusan 2 minutes yace “Bazakice komai ba Noor?" Hawaye ne ya kwaranyo daga idanunta ya zigayo har kan pillow taja numfashi ta kuma yin shiru yayi murmushi yace “Bazaki ce komai ba ko?"
Cikin muryarta me rauni tace “To me zance maka AbNoor na rasa yaushe zan zama mara laifi a wajenka kana yankemin hukunce hukuncen da suka girmi tunanina wlh bansan a ya kakeso mu rayu ba idan har da haka zaka horani a daidai lokacin da nafi buƙatarka ko badon kaina ba don tarbiyyar ɗanmu muna buƙatar fahimtar juna...."
“Ya isa Noor Ya Hajja ce ta kirani wai zaku tafi da Gana Hajja jibi ke meye ra'ayin ki?" “Ra'ayin ka" ta faɗa tana tashi zaune yaja ajiyar zuciya yace “ok zan bari su tafi dake saboda bananan idan na dawo sai nazo mu taho"
Jinjina kai tayi nan ya rinƙa lissafa mata laifukanta da takeyi masa musu gardama fifita wani abu saɓanin abinda yakeso da rashin bashi lokacin da yake buƙata, ita dai ta kasa gane sanda hakan ke faruwa saidai dole haka ta karɓa sukayi sallama ta kwanta washegari aka tashi da hidimar suna dake ma babu wasu mutane sosai lallai surukanta sunyi ƙoƙari saida suka haɗa akwati shidda na kayan Barka dukkan babu ƙaramar sutura Abba kam harda mukullin mota ya bata shikuwa second Daddy kayan takwarar da yayiwa Hisham abin Saida ya zama abin mamakantawa ga kowa harda kyautar wani babban gidan gonarsa dake Maiduguri yayiwa jaririn kar uban gayya yaji labari shi nasa kayan harda rashin lafiya don abin Saida ya bawa Gana Hajja tsoro sai kace za'a buɗe kanti.
Washegari ko da wuri suka ɗauki hanyar Maiduguri gidan iyayensa aka wucce da ita kulawa kam in tana yawa tayi mata tun ranar da taje aketa zuwa mata sannu kowa ta gani banda Billy ta tambayi ya Hajja ina Billy Ya Hajja tace “Billy watanta huɗu a garinku ai nice na hanata zuwa gidanku don nasan zuwanta bazai haifar da ɗa me ido