Showing 12001 words to 15000 words out of 72723 words

Chapter 5 - AKWAI IRINSU COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Jan 2025

6080

bayan ƙinƙisarsa Habibu ne yaci gaba da ɗawainiya har girma amma yanzu ka nuna masa iko ka ɗaurawa ƴarka aure da wanda bai zama zaɓin zuciyarmu ba hakane dama haka ɗan Adam yake butulu ka nuna ƙarfin ikonka akan Rafi'ah ga Rafi'ah nan ga zaɓinta saidai kafin ku tafi inaso dakai da Rafi'ah da Abdulƙadir dama duk wanda yake nan ku sani ni Bara'ah na cire hannuna akan duk wani abu daya shafe ta muddin tana gidan sa domin akansa ne Rafi'ah ta fara bijire mana akansa ne ta fara karya dokarmu kuma akansa ne ta nuna mana bamu isaba stil akansa ne tayi fito na fito damu har ta shirya guduwa ta barni don ban amince da auren su ba kije Rafi'ah na barwa Abdulƙadir ke saidai inaso ko gaba kikayi ki rinƙa tuna namiji silar rabani dake kuma shine na farkon wanda zai farayi miki butulci"
Da gaske kalamanta suka yiwa Abdulƙadir zafi a zuciya musamman yanda yaga Rafi'ah ta zame a jikinsa ta nufi Mommy tana kuka tana kiran sunanta amma ko kallon tsiya bata samu ba bare na arziki Mommy tayi ficewarta tana shirin fita Alh Abdulkarim ya riƙo hannunta ya ɗago kanta ya sanya hannu yana share mata hawaye tace “Daddy kabarni na fasa auren zanyi mata biyayya" girgiza mata kai yayi yace “Yafi dacewa da kiyiwa Allah biyayya Mamana babu biyayya ga bawa wajen saɓawa Ubangiji bansan ya mijinki yake ba amma mahaifansa mutanen kirki ne shima ina masa fatan kasancewa a haka muje ɗiyata da kaina zai kaiki gidanki kuma duk abinda akewa ɗiya ta fannin uwa da uba da dangi duka Ni kaɗai gayya ne zanyi miki"





Hajiya Nuratu ce tayi ajiyar zuciya ta ɗauke idanunta akan Rafi'ah ta mayar dashi kan Abdulƙadir da keta danna waya hankalinsa kwance tausayin Rafi'ah ya sanya jikinta duk ya mutu ita ta haifi Abdulƙadir amma tana tantamarsa akan riƙon amanar yarinyar nan dama Abdullateef ne da zai iya zuciya da saurin fushin Abdulƙadir sunyi yawan da ba kowanne irin screenning yake iya tsallakewa ba shi mutum ne me tsananin son kansa da kin bawa rayuwa uzuri abu ƙanƙani zai sa yanzu yaci mutumcin mutum koda kuwa zai yi nadama a gaba.
Alh Ibrahim Barzah ne ya tashi ya kamo hannun Rafi'ah yace “Daina kuka ƴar lelena insha Allahu bazaki ƙara kuka ba zaki rayu cikin farin cikin da sai kinji dama tun farko a haka kika faro rayuwa mu Bama ƙin ɗan adam don wani aibi dake tattare da rayuwarsa zamuyi ƙoƙarin jansa a jika da bashi kariya ta hanyar dawo dashi kan hanya daidaitacciya muje mun fasa barki anan gara mu tafi dake ayi bikin a Maiduguri in an gama kin tare a gidanki" girgiza kai ta farayi ta ɗago sai yau takejin ashe da hauka takeyi da takejin cikin sauƙi zata har Mommy ba tare data damu ba, bata ankara da sun fito ba saida taji an sanyata a mota ta ɗago da gigitaccen sauri tace “Banyiwa Mommy sallama ba batayimin nasihar da kowacce uwa kewa ƴarta a wannan ranar ba sannan ban dauko wayata da kayana ba" murmushi Alh Ibrahim Barzah yayi ya kalli Abdulƙadir da duk zuciyarsa ta damu da kukan da matar tasa takeyi a ganinsa a yanzu babu wani mutum daya kamata tayi kukan rabuwa dashi kawai don zata koma gidansa gidan da kullum sukayi waya mafarkinta gata a cikinsa tana shimfiɗa kyakkyawar rayuwa me ƴanci da walwala me wadataccen farin ciki" kwafa yayi lokacin da Abba yace “Alh Abdulkarim ka karɓo mata wayar kaya kuwa akwai wasu acan" girgiza kai Second Daddy yayi yace “muje kawai Alh duk uwar duniya sawa takeyi a nemo mata ƴarta ta sanar da ita yanda zata rayu a gidan mijinta ba ƴa ce take kai kanta ba babu buƙatar sai Mamana tayi sallama da Bara'ah tunda itama bata buƙata ba"





Tana kuka tana komai suka ɗauki hanyar birnin Maiduguri tafiyar ta mota ce shiyasa duk ta gaji domin a tarihin rayuwarta bazata iya tuna lokacin da tayi tafiya me tsayin haka ba, ƙarfe biyar motarsu taci birki a unguwar .......... ..... Jerin gidajen gwamnatin jihar ɓangaren mataimakin gwamna suka shiga motocin suka parker a rumfar ajiye motoci direbobin motocin suka fara buɗewa Hajiya Nana da Hajiya Nuratu sukazo suka sanya Rafi'ah a tsakiya tuni Sanƙirar gidan ya fara baza magana fadi yake “Godiya ta tabbata ga Allah yau ga ta iso garemu ƴar Alh Abdulkarim Babagana ta shigo ahlin Alh Ibrahim Barzah matsayin suruka tabbas wannan hadi yin Ubangiji ne bana mutum ba uba na ƙwarai kenan gashi ma dakansa ya kawota" nandanan kowa dake gidan tun daga ma'aikata har zuwa yan siyasar da suke jiran dawowar Alh Ibrahim duk suka fito ganin wannan amarya bansan mijina ɗan gata bane sai a wannan rana tuni na samu karɓuwa wajen kowa a gidan shiko sai washe baki yakeyi yanata gaisawa da mutane da fara'a saɓanin halinsa na kullum shariya da miskilanci.
Wannan rana duk wanda yayi katarin isowa gareshi kyautar ban girma yakeyi masa a wannan rana ta tabbatar ta dace mijinta ba ƙaramin kaunarta yakeyi ba ashe da gaske ne da yake ce mata bazata gane matsayinta a zuciyarsa ba sai ranar data zama mallakinsa nan ta rinƙa hawaye biyu na farin ciki dana tunanin irin rabuwar da sukayi da mahaifiyarta.




Ɓangaren Hajiya Nana aka shigar da ita bisa al'ada bazata zauna a sashin surukarta ba shine dalilin da yasa aka kaita ɓangaren abokinyar zaman surukar tata karamcinsu ya tsuma zuciyarta ta karɓi sabon sauyin rayuwar ashe AKWAI IRINSU dama a wannan duniyar dangin mijinta mutanen kirki ne.
Tun a daren Hajiya Nana ta fara yi mata gyara irin nasu na barebari a cewar ta angon nasu ɗan gatane dole amaryarsa ta zama ta musamman gyaran jiki aka farayi mata basu kwanta ba sai biyu na dare dake babu waya a hannunta bata samu takurar kiransa ba dama kuma batayi tunanin samu ba tunda shi ɗin ba mutum ne me son takurawa ba





Hajiya Nana ce ta takura saita kwanta tana fita ta tashi ta shiga bathroom ta dauro alwala ta tayar da Sallah tana hawaye tana godewa Allah daya mallaka mata muradinta Abdulƙadir shine farin cikinta rayuwarta ta cika da haske dalilin shigowarsa cikinta ta jima tana zaune tana ganawa da ubangiji tana kai masa bukatunta sai uku da rabi sannan ta haƙura ta kwanta bacci kuwa me nauyi ya ɗauke ta badon Hajiya Nana ta tasheta ba da asuba zata iya makara ashe su bisa al'adar gidan kowa masallaci yake zuwa har mata to itama hakan ce ta faru gareta Hajiya Nana ta bata doguwar riga sabuwa dal da hijjab sai casbaha irin ta dannawar nan da ƙur'ani mai tsarki suka fita ɓangaren mata suka shiga saida sukayi nafila sannan liman ya shigo sukayi sallah bayan idarwa ne kuma Abba ya shigo shi da Abdulƙadir da Abdullateef suka fara karɓar haddar kowa ita dake gefe tana sauraron Tajwidin kowa wasu tanajin gyara a furucinsu wasu kuma tana yabawa ƙoƙarinsu taji an kira sunanta ta ɗago da sauri domin ta shagala da sauraron zanjen Allah karatun Kur'ani yana sanyaya mata zuciya ko ba ita takeyinsa.





Sauke idanunta tayi kan Abba ta miƙe a hankali ta isa gabansa ta rusuna da ladabi tace “Sabahul khair Abba" murmushi yayi ya mayar mata da raddi da “Sabahul Noor ƴata ya kika kwana ya kwanan baƙunta yau kinyi kwanan garinku ko garin da aka bar dake tun kina ɗan tayi a cikin mahaifa baki ƙara shigoshi ba sai da aure ya dawo dake" idanu ta sauke kan Abdulƙadir da yake ta zungurinta da ƙafa.
Ɗaga mata gira yayi tayi masa murmushi tare da cewa “Ina kwana" noƙe kafaɗa yayi yace “Ba haka ake gaisawa da miji ba bari ki gani" saukowa yayi ya zauna kusa da ita yasa hannu ya kama kanta ya ɗago fuskarta kawai batayi aune ba taji bakinsa cikin nata gurin ya ɗauki tafi Abba yace “Dakyau Son kai malami ne na kwarai Gara akeyi mata practis zatafi saurin hadda" kunya kamar ta nutse gabaɗaya ta tura kanta cikin cinyarta ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige.
Hajiya Nuratu ce tace “Haba ranka shi daɗe ka biyewa shirmen Abdul duba yanda kuka sata cikin kunya" dariya Abdulƙadir yayi yace “Ya Hajja ya ina ta fara jin kunya bayan bata fara yawo da tumbi a gaba ba yana rinjayarta" jifansa Ya Hajja tayi yayi murmushi yace “saura ƙiris yanzu dai Abba muyi magana ta gaskiya yaushe zaku bani matata Allah jiya kwanan wahala nayi fah inajin inada mata amma na kwana ina hugging pillow"




Harararsa Ya Hajja tayi tana miƙewa tace “Da Abba yake cewa sati biyu ayi biki wlh babu ruwana wannan jarababben ɗan naka zakuyi biki amarya da ciki kuwa" sake ɗago kan Rafi'ah yayi yace “Wai haka ƴar matata" tsam ta miƙe ta rufawa Ya Hajja baya Ya Hajja tayi murmushi tace “Haka nake fama da Audu bashida kunya saidai kiyi hƙr ya samu daurin gindin Abbanku baya masa faɗa komai yayi daidai ne" ƙas tayi da kanta tana wasa da zayyanar ƙur'anin dake hannunta tace “Amma Ya Hajja Mommy na zatazo ta ga gidana?" Dafata Ya Hajja tayi tana share mata hawayen tace “Audu bayason kuka Rafi'ah ki daina Mommy bazata zo yanzu ba domin tana kan zafi amma dole wataran da kanta zatazo inda kike don kinakan gaskiyarki aure shine darajar duk wata ɗiya mace sannan ma'aiki (S.A.W) yace “Idan mutum na ƙwarai yazo neman aure gurinku ku bashi" kinga ashe mai'aiki yaa tafi cancanta da mu kyautatawa fiye da kanmu da iyayenmu surukata ina alfahari da samun ki kema kiyi alfahari da zamowa ɓangare na zuri'ata kuma kiyi biyayya mu kanuri munason mace me biyayyar aure tana samun girma da martaba da kaina zan tayaki saita rayuwarki tunda ke ɗin kin kasance farin cikin ɗana"




Kama hannunta tayi saida ta kaita har dakin da aka bata na part ɗin Hajja Nana sannan ta fito ita kuma ta cire hijjab ɗinta ta kwanta bacci mai daɗi ya ɗauke ta saida taji ana taɓa pillow nata sannan ta buɗe idanunta ganinsa tsaye yasata saurin tashi zaune tana gyara rigarta data lura idanunsa kan tantsa tantsan nononta suke tace “Yaushe ka shigo?" Zama yayi yana sauke numfashi yace “na jima ina kallon baiwa da kyautar da ubangiji yayimin na zuƙeƙiyar mace kamarki tsintar dami a kala Noor wai ya akayi duk alhazawan nan na Kano suka kasa yin ram dake har saida nazo na ɗaukeki" ƙasa tayi da kanta ya miƙe yace “Ok zaki bani amsa a Special night" da haka ya ajiye mata sabuwar waya ƙirar Iphone ya fice abinsa ta bisa da kallo kamar ta kirasa amma miskilancinta ya hanata har ya fice ta ɗauki wayar tana dubawa dake irin tata ce amma wannan babbar tata ce batasha wahalar sanin kanta ba ta shiga wajen saƙo ta fara rubutu kamar haka.
_“Tabbas godiya jinjina da karramawa sun tabbata ga Allah daya ƙaddaramin ganina a da'irarka matsayin matarka ta sunnah ina fatan Ubangiji ya bani ikon yi maka biyayya kamar Sayyadatuna Rabi'atul adawiyyah"_
[10/16, 11:58 AM] OUM HAIRAN: *AKWAI IRINSU....*
(Eroctic romance and bad destiny)




_Free page 8_




_Oum Hairan_




_Paid book nrml 300 VIP 600 special 1k Email post 2k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank evidence 09013718241_




Argazo ƙofar da akayi ne yasata miƙewa da sauri tana jiran taga waye wannan yake abu kamar taɓaɓɓe wata matashiyar kyakkyawar budurwa ce sanyi da ƙananun kaya riga top iya cibiya da wando three quater daya kama jikinta sosai tsaye take jikin ƙofa idanunta na tsiyayar hawaye tace.
“Tabbas rai yakanyi motsi a lokacin da zuciya ta gamu da irin mafarkinta Rafi'ah ƴar karuwa haƙiƙa kin shammaci rayuwata kin sanyani cikin taskun rashin masoyi bansan shirinki yakai haka ba saida na tsinci labarin wai an daura aurenki da Abdulƙadir matashin guy ɗin da na shafe tsayin rayuwata ina yiwa ƙaunarsa hidima da biyayya ashe kece takobin yanke farin cikina"
Takawa tayi zuwa cikin ɗakin ta isa gabanta tare da dafa kafadar Rafi'ah tayi murmushi tace “Ban karaya ba kamar yanda kema da kika ƙetaro gonata banga alamun rauni ko karaya daga yanayinki ba Rafi'ah zan shayar dake mamaki kuma zan tabbatarwa da mijinki na wucce wulaƙancin ɗa namiji bare yaci amanata in yazo ki sanar dashi Billy tazo tayaku murnar aure "Tana ida furucinta ta fice Rafi'ah na binta da kallo kalmomin da tayi amfani dasu duk sun taɓa zuciyarta saidai kalma ɗaya tafi kowacce dukan ruhinta Rafi'ah ƴar karuwa.... Ya akayi ta sani? Tambaya mara amsa shine dalilin da yasa ta koma ta kwanta tare da harɗe hannunta a ƙirjinta bayan ɗan lokaci ne masu hidimar abinci suka fara shigowa dashi Hajiya Nana na biye dasu ta zauna suka ƙara gaisawa tace “Nasan zaki iya yi mana baƙunta shiyasa na biyosu in kuma kinƙi na kira mijinki yazo ya ciyar dake"
Ƙasa tayi da kanta kamar ta haɗiye maganar ta amma ta kasa ta dake tace “Gana Hajja wace Billy meke alaƙarta da Noor?"




Daga yanayin Gana Hajja ta fahimci bataso tasan wani abu tsakanin Billy da Abdulƙadir ba amma dake kanuri babu ƙarya nan ta gyara zama tana haɗa mata abin karyawar tace “Billy batajin magana wato duk irin kashedin da Ya Hajja tayi mata shine saida tazo tayi abinda zaki fahimta to zan sanarwa Solder kuwa zata gane kurenta, kinga kar wani tsakaninsu ya dameki itaɗin ƴar ƙanwar Ya Hajja ce mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama shine Ya Hajja ke riƙonta ta daɗe tana nunawa Audu soyayya shikam bata gabansa ƙarshe²n nan ne ma da ta sanar da Ya Hajja ita kuma ta faɗa masa ya kamata yayi mata mugun duka yace uba me zai yi da ita ragowar masu gadi har yana cewa idan aka ƙara masa maganarta in ya koma gurin aiki sai ya ɗauki shekara goma bai dawo ba tun wannan lokacin Abba yace to ya nemo mata a hakan an ɗauki wajen shekara biyu ganin ya koma yana ɗan kulata sai tayi tunanin ko ta fara samun karɓuwa ne kwatsam sai yazo da maganar aurenki ranar yini tayi tana kuka lokacin da taji iyayenki sunyi miki miji har party tayi kuma babu zato Alh Gana ya kiramu yake sanar damu sunje Lagos gurin mahaifinki sai suka ishe ashe classmate ɗinsu ne da sukayi karatu tare kuma abokinsa Abdulkarim da ya ɓata shekaru baya, dukkanmu munsan Abdulkarim Abba yafi kowa jin daɗi domin shi dama babbar damuwarsa kar Audu ya ɗauko ƴar ƙananun mutane, koda ya sanar da Alh Jafar ya aminta da auren tunda kinaso amma yana neman alfarmar indai an shirya a daura aure in yaso daga baya ayi biki a kaiki gidanki domin shi ba zaman ƙasar nan yakeyi ba yafi Zama a Austaralia shine batare da sanin kowa ba aka daura aure hatta Audu bai sani ba sai bayan an daura Abba ya kirashi yake sanar dashi to shine fa taketa hauka bansan zata shigo miki nan ba domin mijinki ya kafa mata doka jine batayi ba"





Kasa kawai tayi da kanta tana cakalar breakfast ɗin dake dama ita ba ma'abociyar yawan cin abinci bace bayan kammalawarta ne Gana Hajja ta fita tana cewa “Ki gama shirinki yanzu Manguru zata iso" batasan wace hakan ba shine yasata komawa ta kwanta kawai wajajen 12:00pm Aka buɗe ƙofar aka shigo Gana Hajja ce da Ya Hajja da Wata mata suka zauna saman gadon Ya Hajja tace “Wannan Amaryar Army ce da aka dauro aure jiya to kinsan dama auren yazo da ƙura shiyasa ba'a samu an shiryata muka taho da ita don Allah kiyi mata gyara ciki da waje fiye da yanda kikayiwa Amina da Salmah domin su fitar dasu mukayi muka bawa wasu Ita kuwa tamu ce amfanin namune" jinjina kai Manguru tayi tace “Bakida matsala Ya Hajja Army namune dole sai munyi babban aiki akan Amaryarsa" da wannan Ya Hajja ta fice ta barsu dirji can goge can jiƙa wancan karkada wannan turara wannan yi tsarki da wannan saida aka kwashe kwanaki goma anayi cikin kwana goman nan tsakanin Abdulƙadir da Rafi'ah babu wanda yaga juna yayi nacin har ya gaji ya hƙr ya daina kira.




Yau tun safe suka fita da Gana Hajja basu suka shigo gidan ba sai Magrib tare suke da Salmah wajen lalle sukaje dake ranar juma'a zasu fara biki Lahadi akai amarya ɗakinta suna shiga harabar gidan suka ganta cike da motocin airforce gabanta ya faɗi domin dukkan shirinsu ban nuna zama sukazo yiba zagaye kawai suke yi a gidan ƙarasa parking sukayi suka fara fitowa idanunta na kallon inda ta hangeshi naɗe da hannu cikin kakinsu na sojoji fuskar nan babu alamun wasa.
Duk da tana yawan ganinsa a hoto cikin uniform yau sai taga yayi mata wani mugun kwarjini da saida taji ƙirjinta ya buga, kuma ta lura duk da cewa akwai glass a idanunsa gabaɗaya hankalinsa akan motar tasu yake batasan an buɗe mata ba saida taji Salmah na cewa “Aunty Rafi'ah ki fito mana da alamun akwai ƙura a gidannan naga Boss ya kasa ya tsare" Fitowa tayi cikin yangar yanayinta na halitta idanunta a kansa ya zare Glass na idanunsa ya sake saita injinsu akanta tayi ƙasa da nata Ya Hajja ta fito da sauri tana cewa.
“Dama ka tafi ka barta yafi maka sauƙi Abdulƙadir bazaka tafi da yarinyar nan ba in ka samu hutu ka dawo ka ganta haba yaushe ma zan yarda ka tafi da ita ka wahalar da ƴar mutane kai ba rarrashi ka iyaba ita mace a wannan matakin kulawa takeso"





Tana maganar tanajan hannun Rafi'ah daidai lokacin daya iso garesu har yanzu idanunsa akanta yake ya buɗe hannunsa tare da buɗe bakinsa yace “Come on My Wife!" Yayi maganar muryarsa a shaƙe alamar da take nuna yana cikin matsanancin bacin rai, haka kawai ta samu kanta da kasa musa masa ta cire hannunta daga na Ya Hajja ta faɗa jikinsa hannunsa yasa ya rungumeta sosai yana sunsunar jikinta kamshin turaren gafgaf da aka shafe kwanaki ana turarata dashi yana ratsa kwanyarsa yana sake shigar dashi yanayin daya shafe shekaru yana ciki.
Da murya me rauni yace “Ya Hajja bari na buɗe miki maganar nan ki fahimci yadda take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login