Showing 63001 words to 66000 words out of 72723 words

Chapter 22 - AKWAI IRINSU COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Jan 2025

6066

abinda zan basu Noor kamar ni ina raye zai zama abin kunya ƴaƴana suyi agolanci amma alfarma ɗaya rak" kallon Deeny tayi da yake shigowa ya miƙa mata hannu ta miƙe ta matsa jikinsa ya rungumeta daidai lokacin da Abdu yace “Komai daɗewa inaji a jikina zaki dawo gareni Rafi'ah da wani kika aura ba Deeny ba to ki tabbata mazanki zasu zama biyu saidai bazan iya wasa a wannan gonar ba na haƙura na sallama badon na cire rai ba saidon rungumar zanen ƙaddara don Allah ki hana kanki haihuwa banason mu cuɗanya yaranmu da wasu...."





Ƙit Deeny ya kashe wayar ya ɗago fuskarta tayi saurin rufe idanunta ya ɗora lips ɗinsa a goshinta yayi perk nata yana ssuke ajiyar zuciya yace “Kiban aron yinin ki masoyiyata niko na baki kwana.... Badaban ganin ido ba habibiya dakin ganni tunda rana...."
Dariya tayi ta buɗe idanunta tana lakace masa dogon hancinsa tace “Wai kai baka fushi ne?" Murmushi yayi ya ɗagata cak yace “Inayi mana bari kiga kalar nawa fushin" sauketa yayi saman gadon ya bita ya turmushe suka kama kokawa daƙyar tana zillewa tana masa magiya ta samu ya sarsra mata yana mayar da numfashi yayi ƙasa da muryarsa daidai kunnenta yace “Daɗine dake Ƙurrah"
Tureshi tayi tana mita tana bubbuga ƙafa ta shiga bathroom ta gyara jikinta ta fito ta isheshi yayi bacci ta tasheshi shima yayi wanka suka koma bacci.
Wata ni'imtaccciyar rayuwa suka fara shimfiɗawa me ban sha'awa da burge kowa sun kwashe wata biyu da sati biyu a California sannan jirginsu ya daga zuwa Nigeria sunyi kwanaki biyar a Nigeria ana jibi zasu tafi Niger ne yace ta shirya suje su gaisar da Mommy, mamaki ya cikata da tunanin hali irin na Deeny, iyakar rayuwarta da Abdulƙadir baitaɓa bata damar zuwa ta gaisar da mahaifiyarta ba hassali ma idan ta nuna masa sha'awarta da hakan ransa ɓaci yake har ya faɗa mata maganar da zata sosa zuciyarta amma shi Deeny gashi shine yake bata umarnin ta shirya suje su gaishe da Mommy, lallai ta yarda maza iri² ne kowanne da irinsa.





Wannan ya ƙarawa Deeny martaba a gurinta ta shirya sukaje suka gaisa da Mommy Mommy ta nutsu sosai ta tarɓesu tare da sanyawa aurensu albarka har tana cewa yanzu ne Ƴartata ta samu irin mijin da takeyi mata fatan samu itadai kallonsa kawai takeyi da suka tashi tafiya yayiwa Mommy kyauta ta girma da daraja amma fir Mommy taƙi karɓa abinda take faɗa masa ita dai burinta a zauna lafiya a riƙe amanar juna sai ajiyewa yayi suka tafi a hanya yake cewa da ita.
“Akwai Gimbiya Zabba ƙanwar Mai martaba ce tana auren Ɗan Sarkin Bauchi kuma anan Ƴankaba gidansu yake ko muje mu gaisa ne Ƙurrah" murmushi tayi tace “Yanda kace mana Allah ya taimake ka" kalmar tayi masa daɗi yace “Shikenan bari mu ƙarasa mu gaisa tanada kirki sosai halinta halin Mai martaba sunada kara da girmama ɗan adam da ace Mai martaba ne Kilishi wato Ammy da kinji daɗi kuma kin shaida kin mori suruka amma yanzu saidai ko kiyi haƙuri Ƙurrah muma data haifa hakuri mukeyi da ita musamman ni saukinta ma ba'a gari muke tare da ita ba"
Horn yayi jikin wani ƙaton gida zubin na sarauta aka leƙo tare da wangame masa get ya sunna hancin motar yayi parking masu hidimar gidan sunata gaisheshi yana daga musu hannu tare dayi musu alkhairi me gwaɓi har suka shiga ɓangaren Gimbiya Zabba ya kirata ya sanar da ita zuwansu ta fito tana dariya tana cewa “Ni babu ruwana dakai Deeny shine zan samu ƙarin ɗiya ko ka sanar dani saida naje Niamey nakejin ashe ka daura aure" shafa sumarsa yayi yace “Affuwan Uwata maganin kukana ku daina zargina auren ne yazo a haka dagani har Ƙurrah babu wanda ya shirya kawai labarin daura sa mukaji"





Kamo Rafi'ah tayi ta zaunar da ita tace “Ai naje Niamey Kilishi tananan ta haɗiya tana jiranka" murmushi yayi ya zauna yana cewa “To wai ita me take buƙata ne duk abinda Allah ya shirya shine zai faru burinta nayi aure kuma nayi Gimbiya yaushe ne Kilishi zata daina yi min kallon yaro ne" murmushi tayi tace “Sai ranar da taga ka cika gda da yara dagwai dagwai tana shigowa suna harɗeta" idanunsa ya sauke kan Rafi'ah tun ranar da sukayi waya da Abdulƙadir yaji yana rokonta karta bari ta haihu ya ɗora ayar tambaya akanta baiyi mata magana bane yana jiran yaga abinda lokaci zai nuna amma da gaske yake buƙatar shima ganin babynsa shima dagwai dagwai a gabansa.




_*Oum Hairan*_
[11/17, 7:25 AM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU....*_



_*Oum Hairan*_



*Alhamdulillahi 💃💃💃💃Meta force yayi anshamu a online business da na cuta da yaudara, Amma meta force yazo yawarkar damu,Meta Force Yafi kowanne crypto project a ynz , inhar kanada qashin arziki zo kusan menene Meta Force kuyi register zakuyita godemin tsawon ryw😃 in kana da rabo acikin wannan tafiya zaka iya zama millionaire ckn kankanin lkc, Alhamdulillahi da zuwan Meta Force alkhairin Allah 💃💃inhar Zaka jajirce 7200 kacal zai iya kaika 1m acikin wata daya kacal👌meyafi wannan, duk Mai Neman Karin bayani ya nemeni_akan wnn number 08141390323*



_Paid book via acct 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank proof of pay 09013718241_



Yana jinsu suna gaisawa Gimbiya Zabba nata jan Rafi'ah da hira shikam wani sabon shauƙi ne ya ɗarsu a zuciyarsa da ya fara tunanin faruwarsa kowanne lokaci, miƙewa yayi yana cewa da Rafi'ah zanje na dawo ku gama gaisawa fatan alheri tayi masa ya fice sukaci gaba da hirarsu Gimbiya Zabba nata bata labarin yanda takejin Deeny a ranta har tana sanar da ita ashe ma kusan a wajenta ya girma batayi mamaki ba domin yanayin kararsu da mutumtakarsu yayi kamanceceniya dama anan ta yini bai shigo gidan ba sai yamma likis yana zuwa yace ta tashi su tafi Gimbiya Zabba nace masa ya tsaya yaci abinci amma ta lura hankalinsa yayi gaba haka ya ɗauke matarsa suka tafi.
Kai tsaye ba gida sukayi ba ganin inda ya kawo su ne yasata kallonsa da sauri shima kallonta yayi yayi murmushi yayi parking kana ya kalleta yace “Inason baby Ƙurrah kawai naji zuciyata bata aminta da zamanmu haka ba yana da kyau a bincika lafiyarmu ta wannan fannin shin zama mu iya samar da ɗa a tsakaninmu" sosai tsji gumi ya karyo mata tayi saurin cewa “Amma Deeny idan muka jira jira ma lokaci zai nuna kansa ai" girgiza kai yayi yace “Hakane saidai bincikawar yana da amfani" bata kuma cewa komai ba suka shiga asibitin shikam yau ma bashida wata matsala kuma zai iya bawa kowacce mace ciki abinda likitan yace kenan da yazo kanta ne ya ɗago ya dubeta yace “Madam mahaifarki a ɗaure take kinsan da haka?" Jinjina kai tayi tace “Na sani" cigaba yayi da bincikensa ya jima sannan yayi rubuce²nsa ya fita itama ta tashi tabi bayansa office suka shiga suka ishe Deeny zaune yana danna wayarsa ya aje wayar yana kallonsu dukkansu likitan ne yace “Itama Madam batada wata matsala babba kawai dai mahaifarta a ɗaure take ne ranka ya daɗe in anason a samu abinda akeso saidai ayi aiki a kwance ta"





“To ayi mana Dr..." “Aa Deeny don Allah..." Kallonta yayi da tsananin mamaki yace “Aa fa kikace Ƙurrah why?" Ƙasa tayi da kanta tana matsar hawaye yaja ajiyar zuciya yace “Ok shikenan sai yaushe" yanda yayi maganar muryarsa na rawa kai dagaji kasan ƙoƙarin danne dukan da maganar tayi masa yakeyi saida ya bata tausayi tayi ƙarfin halin cewa “Ba abinda kake tunani bane Deeny inashan wahala shiyasa na haƙura da haihuwa" saukowa yayi gabanta ya kama hannunta yace “Ko ɗaya ne don Allah Ƙurrah da gaske inason baby kar kiyimin wasa da damar da nake da ita har lokacina ya ƙure Please...." Zatayi magana ya miƙe yace “Bazanyi miki dole ba Ƙurrah amma dai ki sani inason baby" daga haka ya fice.
Miƙewa tayi tabi bayansa a jikin mota ta tarar dashi ya kifa kansa a samanta ta rungumeshi ta baya tace “Na amince indai zakayi farin ciki Zaujh jannah" wata runguma yayi mata ya ɗagata cak yace “Na gode Ƙurrah ina zuwa" komawa cikin asibitin yayi bai jima sosai ba ya dawo ya shiga motar itama ta shiga yaja suka tafi.




Bayan sunje gida sunyi wanka sunyi dinner yake nuna mata magungunan da Dr Aleem ya bashi yace “Ya faɗamin idan kikayi amfani dasu Insha Allahu za'a samu abinda ake nema saboda dama zaren da aka ɗaure mahaifar yayi rauni" itadai jinsa kawai takeyi da kunne domin ba wani murna tayi da hakan ba.
Maganin ya ɓalla ya bata tare dayi mata bayanin kowanne ta karɓa tasha suka kwanta washegari suka ɗauki hanyar Niger suna sauka airport Sarkin mota yazo ya ɗebesu suka isa gidan sarautar gidane babban gaske me matuƙar ƙayatarwa ta kalli gidan ta kuma kallonsa ashe shiɗin daga babban gida na sarauta ya fito haka? Lallai Allah shine yake halittarsa yanda yakeso shi daya kamata yaji izza da girman kai bai ɗorawa kansa ba shikuwa Abdulƙadir ya ara ya yafa.
Wani babban ɓangare a gidan suka shiga ɓangaren Hajiya Kilishi suka fara zuwa da gaske ta amsa Kilishin domin yanda take amsa gaisuwarsu tana yatsina tana batsewa yasa jikin Rafi'ah sanyi ya dubeta yace “Ƙurrah Mahaifiyata kenan ina fatan zaki jita a ranki kamar yanda nake jinta" sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsunta Ya miƙe yace “Zanje na gaisa da Mai martaba ina dawowa" fatan alkhairi tayi masa har yanzu Kilishi batace komai ba ya fice bai jima da fita ba Kilishi ta mike ta nufi wata ƙofa tace da barorinta su kawo mata komanta can itadai Rafi'ah ta cika da mamakin rashin darajar matar dake amsa sunan suruka a wajenta haka ta wanzu a wajen kusan 1 hour sannan ya shigo duk ta ƙosa da zaman wannan dalilin ne yasata miƙewa ya dubeta yace “Ina Kilishin take Ƙurrah?" Murmushin yaƙe tayi ta nuna masa inda ta shiga.
Wata hadima da tazo wuccewa ya kira gefe ya tambayeta yaushe Kilishi tabar gurin ta sanar dashi ta jima da tashi ya jinjina kai ransa ya sosu sosai baisan meye yasa Kilishi batason kwanciyar hankali ba yanzu meye aibin zaɓinsa da zata fara nunawa Rafi'ah ƙiyayya bayyane?
Kiranta yasa hadimar tayi ta fito yana tsaye jikin mota kallo ɗaya tayiwa fuskarsa ta fahimci yau ran mazan ya sosu tayi ƙasa da kanta yace “muje" da sauri tace “Kace Ammy su uku ne a gidan kuma naga bamuje sauran part ɗinba" juyowa yayi ya zubanta manyan idanunsa da kusan ba kowa yake gane yanadasu ba saboda lumshewarsu yace “Zuciyata tafasa takeyi Ƙurrah kizo kawai muje gida in na samu nutsuwa ma dawo"





Ba ɗabi'arta bane musu shine kawai dalilin da yasa ta shiga motar yaja suka koma ɓangarensa saboda girman gidan kusan tafiyar ta zama me ɗan tsayi suna parking ya fito ya buɗe mata ta fito barorin gidan sunata kwasar gaisuwa suka shiga ciki a daidai kofar shiga asalin inda ɗakunan suke yace “Ok Jakadiya ina buƙatar a samo masu hidima amintattu da zasu rinƙa yiwa Gimbiya hidima" amsawa tayi da “Godiya nake Ranka shi daɗe anyi an gama a huta lafiya santali masgaye gaba salamun baya salamun..."
Shigewa yayi ciki Rafi'ah tafi bayansa ta mayar da ƙofar ta rufe ta juyo zatayi magana ya riƙota ya zaunar da ita ya tsugunna a ƙasanta ya tallafo fuskarta yace “Kiyi haƙuri da Ammy Ƙurrah itaɗin murɗaɗɗen hali gareta Sogiji tafita daɗin azanci ita da Gimbiyar Dutse" shafa sajensa tayi tayi masa farr da ido tace “Meye zaisa a rinƙa bani hƙr akan abinda yake rayuwata meye Mahaifiyata zatayi min da zaisa a rinƙa jin laifi ne Deeny nifa in kaci gaba da yimin haka zakasa zuciyata a kokwanto"




Mamakinta ya cika shi sosai ya Girgiza kai ya janyota jikinsa ta kwanta luf a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya Deeny yaci gaba da shafa sumarta ta janye ta shiga bathroom ta haɗa ruwan wanka tazo ta fara cire masa kayan jikinsa ta jashi sukayi wanka tun kafin gama wankan ya fara rikice mata tayi masa murmushi tace “Kaifa ko" “Jarababbe ko?" Rufe fuskarta tayi da hannunta tana dariya shima dariyar ya tayata suka zube a gadon suka fara bawa shukarsu ruwa.
Tundaga wannan rana rayuwar ta fara canza musu Hajiya Kilishi bata ƙaunar ganin Rafi'ah a da'irarta amma Gimbiyar Dutse da take ita ce mace ta biyu a gidan mugun ƙauna take nunawa Rafi'ah hakan ya sanya mata daraja gurin Deeny watansu biyu a Niamey ciwon bacci ya sarƙi Rafi'ah basu kawo komai ba sukaci gabada rayuwarsu a haka sau dayawa takan fara aiki taji bacci ya kamata ta yanda bazata iya ƙarasawa ba hakanan zata kwanta lokuta da dama saidai idan ya shigo yayi murmushi ya gyara mata kwanciya ya sanya a ƙarasa mata ko ya ƙarasa.
Da wannan yace ya ɗauke mata girki ta daina saboda tsaron lafiyarta.
Bashi ba ita kanta bata kawo komai ba haka saida suka ɗauki tsayin watanni biyar wata rana Yayarsa Safiyyah tazo gidan dake bata ƙasar suka dawo tunda tazo Rafi'ah ta fito suka gaisa ta kishingide suna hira sai bacci ya tashi yana cewa Gimbiya sai haƙuri ƙanwar taki ciwon bacci ya sameta ba'a doguwar hira da ita" murmushi tayi tace.




“Ai dama ana samun irin haka wani laulayin kashe jiki da bacci yake sawa saidai fatan Allah ya inganta ya raba lafiya" fasa tafiya yayi ya zauna yace “Wai da gaske Gimbiya Sofsy cikine da Ƙurrah?" Kallonsa tayi da mamaki tace “Au kai nan baka fahimta ba kakeso kacemin Deeny matsayinka na likitan ƙasa da ƙasa kuma naji ance itama Pharmacy Dactor ce" zubawa Rafi'ah idanu yayi so yake ya fahimci abinda zuciyarsa take raya masa gaskiya ne ko ƙarya amma ya kasa hakanan ya miƙe yace “Na fahimci sauye² da yawa a jikinta da yanayin halittarta Gimbiya abinda yasa ban kawo cikina ke jikinta ba saboda tace tanashan wahala sosai amma bari yanzu nasa a bincika ta.
Duk abinda akeyi bata sani ba domin baccin nata da nauyi yake ɗaukarta.
Tashi tayi zaune yace “Unguwa zamu je yanzu zamu dawo" ƙara narkewa tayi tace “Unguwa Zaujh jannah Allah jikina duk a mace yake banjin ƙarfi" “Daure yanzu zamu dawo ba daɗewa zamuyi ba" tashi tayi dake dama da hijjab a jikinta Gimbiya Safiyyah tace “Ato nikam tafiya zanyi Allah ya inganta" sauketa sukayi a gidanta sannan suka wucce asibitin hoto yasa akayi mata abin mamakin da baitaɓa kawowa a yanzu ba Ƙurratul Ayn ɗinsa ciki gareta ya zarce watanni biyar ya shiga na shida tsabar farin ciki baisan sanda yayiwa Ubangiji sujjada ba yana zuba masa kirari tare da tasbihi gareshi buwayi gagara misali gwani Sarkin hikima ashe zai kuma jin irin wannan farin cikin da yaji a shekaru bakwai baya? Miƙewa yayi ya matsa inda take zaune ta kifa kanta a cinyarta yace.





“Na gode Ƙurrah kinga hikima ta Ubangiji ko zaki haifamin baby nima ina mutum zaiyi da rabon wani a hannunsa wannan rabon shi kadai ya isa hana kwanciyar hankali...."
Maganarsa ce ta katse lokacin daya ɗago fuskarta yaga yanda take hawaye kuka da gaske ya shiga mugun mamaki da tashin hankali tare da tunanin dalilin kukan nata yace “Innanillahi Ƙurrah me nayi miki" zamewa tayi ta kwanta a jikinsa ta rungumeshi tana shassheƙar kuka tace “Zaujh Jann ciki fah yanzu kaima saika fara wulaƙantani da juyamin baya akan hakan...."
Rufe mata baki yayi ya sakar mata murmushin ƙarfafa gwiwa yayi kissing nata yace “Allah ya kasheni kafin zuwan wannan rana da zanyi butulci ga kyautar da banida ikon yiwa kaina Ƙurrah mafi alkhairin duniya samun mata ta ƙwarai ta haifa maka ƴaƴa nagartattu ku basu tarbiyyar addini ta yanda ko bayan ranka zasu kasance masu yi maka addu'a yana cikin ayyukan ɗan adam masu gudana ko bayan baya numfashi, don Allah Ƙurrah ki daina munanamin zato ko iya zaman nan namu na wata takwas ya kamata ki fahimci suna ne kawai mukayi tarayya da tsohon mijinki wato maza amma kowa halinsa daban Ni inason yara sosai Ƙurrah don Allah kiyita haifamin masu kama dake kinji"




_*Oum Hairan*_
[11/17, 7:25 AM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU....*_



_*Oum Hairan*_




_Paid book via acct 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank proof of pay 09013718241_


Shafa bayanta yaci gaba dayi har saida tayi shiru sannan ya fita ya ɗauko musu magunguna suka tafi gida suna zuwa gida ta zube a kujera tace “wlh bacci nakeji" murmushi yayi yace “Ki kwanta kiyita bacci daganan har ranar da babyna zai buƙaci zuwa duniya bakida matsala kinji" lumshe idonta tayi ya shiga kitchen ya haɗo mata tea me kauri domin ya daɗe da fahimtar shi takeso dakansa ya rinƙa bata Saida tasha isasshe sannan ya fita ita kuma ta kama baccinta.
Daƙyar take tashi tayi sallah ta koma dake ta samu daurin gindi tun kafin yasan matsalarta ya hanata komi saida ya shigo bayan Isha ya ɗagata cak tun shigowarsa tajisa bata buɗe idanunta ba sai bayan ta sanya hannu ta saƙalo wuyansa ta sauke masa wani mayen kiss ta fara lasar wuyansa tana shafa ƙirjinsa cikin Muryar raɗa tace “Yau kayi dare Zaujh Jann ina ka shiga" sauketa yayi a gadon yabita ya danne yana lalubar bakinta ta riƙeshi tare da kanne masa ido tace “Aa Zaujh muje kayi wanka ka huta mana" noƙe kafaɗa yayi yana kama fatun kunnenta ya fara lasa.




Lumshe idonta tayi tana karɓar saƙon nasa saida ya gama abinda zaiyi tana tayashi sannan sukayi wanka tare duk jikinta yayi laushi daƙyar ta ciyar dashi yanacin abincin yana zubanta santi tare da bata labarin yanda suka kwashe da Ammy lokacin dayaje don sanar da ita alkhairin daya sameshi sosai bataji daɗin irin abinda yace tayi masa ba duk da cewa abubuwa da yawa baya sanar da ita abu ɗaya daya sani kawai ya kangeta daga zuwa wajen Ammy ko gidan sukaje baya barta ta daɗe zaice ta tashi su tafi amma a ɓangaren Gimbiyar Dutse yakan barta ta jima sosai.
Yaso fahimtar ta damu da abinda ya sanar da ita saidai tafisa dabara ganin yana shirin ganota ta hanyar tambayoyinsa yasata riƙe ciki tana cewa “Ahhh Zaujh marata" yowa kanta yayi da sauri yana tambayarta meye damuwar me i sameta da wannan ta mantar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login