Showing 9001 words to 12000 words out of 72723 words

Chapter 4 - AKWAI IRINSU COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Jan 2025

6062

ƙofar ɗakin nata ta tashi tana share hawayenta ta buɗe ƙofar Alh Habibu ta gani tsaye wanda yake uba a gareta yayi mata murmushi tare da lakace mata hanci yace “My Daughter kina lfy?" Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta ya lura da hakan shine yasashi cewa “Yauma kun fafata da Mommy kenan, kema Daughter kina da shiga abinda babu ruwanki ki ƙyale kowa ya rayu yanda ya zaɓa am kinga kizo dakina inason magana dake"




Nufar sama yayi ita kuma ta juya ta nufi kitchen ta ɗauko masa lemo da ruwa wannan aikine da yake a kanta tun batasan kanta ba Mommy batada lokacin mijinta sai ya zamana duk wani abu da yake aikin Mommy ita keyi saman ta shiga yana zaune da waya a kunnensa ta tsugunna ta ajiye masa tace “Daddy gani" ajiye wayar yayi yace “Waye Abdulƙadir Ibrahim Barzah?" Tunanin inda tasan sunan takeyi can ta tuna compliment ɗin da aka bata ɗazu ta zaroshi cikin aljihun rigarta ta mikawa Daddy tace “Bansanshi ba saidai ɗazu wani me makamancin wannan sunan ya bani wannan katin" numfashi ya sauke take fuskarsa tayi cuɗu² fara'arsa ta ɗauke tace “Shine ɗazu Barrister Ibrahim Barzah ya kirani yake fadamin yana nemawa ɗansa izinin neman aurenki idan baayi miki miji ba, so a zahiri banyi miki miji ba amma nace masa nayi miki miji saboda haka wannan alaƙar a yanketa tun kafin tayi nisa gidansu yaronnan ba ƙananun mutane bane Barrister Ibrahim Barzah shine Deputy governor na jihar Sokoto na yanzu Maryam indai na isa fah dole ki dakatar da yaron nan"





Bata iya tuna meye ya faru ba itakam Abdulƙadir yayi mata tun batasan da abinda yazo mata ba taji tanason kasancewa dashi “Kinyi shiru Daughter" cikin sanyin jiki tace “To Daddy" dafa kanta yayi yace “Dakyau ƴar lele Allah yayi miki albarka yanzu zanyi baƙuwa in tazo ki nuna mata inda nake" idanunta ne ya kawo ruwa ta ɗaga masa kai ta tashi ta fice yabita da kallo yana murmushi tare da lasar lips ɗinsa yama za'ayi bayan gama gininsa shekaru kusan goma sha tara kwatsam rana tsaka baici gajiyar abinba wani yazo yace zai yi wuf da ita kuma daga haduwa ɗazu shi har ya sanar da mahaifinsa ina lefin ma yazo suyi rayuwa da ita ko ta waye ta daina kallonsu daban shida Mommynta murmushi yayi yace “Maryam kenan baiwar Allah" tana saukowa ta ishe wata mace a kasan ta wucceta tayi shigewarta ɗakin ta kwanta tare da ɗaukar wayarta 5 miscall ta gani da wata baƙuwar special number tunanin ta ya tafi ga manufar mahaifinta na cewa da mahaifin Abdulƙadir yayi mata miji.
Wani kiran ne ya shigo ta danna ta kara a kunnenta tayi sallama, ajiyar zuciya taji an sauke tsayin few minutes taji yace “Nakasa gane asalin sunanki Rafi'ah ko Maryam wanne a ciki?" Koda ba doguwar magana sukayi ɗazun ba ta gane muryarsa domin har gizo ta rinƙa yi mata a kunne ɗazu.





“Kinyi shiru" a sanyaye tace “Mommy na tana kirana da Rafi'ah shine jikin duk wasu takarduna amma Dad ɗina da Maryam yake kirana" “Owkey da gaske anyi miki miji?" Shiru ta ratsa na dogon lokaci can ya nisa yace “Da gaske nakeyi Rafi'ah kuma aurenki zanyi don Allah ki fadamin gaskiya...."
Cikin sanyin jiki tace “Aa" da sauri yace “Da gaske bakida alƙawarin kowa a kanki?" Jinjina masa kai tayi tare da cewa “Inma akwai Ni bansani ba amma Dad yace nace maka yayimin miji" murmushi yayi yace “To me yasa yace hakan?" Noƙe kafaɗa tayi tace “Shine abinda nake tambayar kaina nima" “Ok yace kawai yace “Ni kinyi min zan so kuma zanyi farin cikin samun nutsattsiyar mace kamarki matsayin uwar ƴaƴana amma bansan komai game da zuciyarki akan wannan bawan Allan Abdulƙadir ba don Allah kiyimin adalci wajen yanke hukuncin karɓar tayin soyayyata ko akasinsa bazan miki dole ba burina na auri macen da take tsananin sona ta yanda zata bani kariya da kulawa"
Da mamaki tace “Ko baka sonta?" Murmushi yayi yace “karshen so gani yabawa kulawa da aje duk wani iko isa da sarauta wajen furtawa Rafi'ah ta ina zan fara rayuwa da macen da banaso kamar ni? Kema kinsan banyi kama da wanda hakan zai faru dashi ba ki shirya karɓar baƙunci na Rafi'ah zan aureki kwana kusa indai kin amince"........
[10/16, 11:58 AM] OUM HAIRAN: *AKWAI IRINSU....*
(Eroctic romance and bad destiny)




_Free page 6_




_Oum Hairan_




_Paid book nrml 300 VIP 600 special 1k Email post 2k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank evidence 09013718241_



Murmushi tayi cike da jin daɗi tace “Okay Allah ya tabbatar da abinda yake alkhairi cikin rayuwarmu baki ɗaya nikam zanyi istihara kamar yanda Sheikh Muhammad ya koya mana in har alkhairi ne tarayyata dakai zanyi kuma zan baka kariya koda zan wahala, Ni kaga bantaɓa soyayya ba duk da yawan mutanen da suke nuna sha'awar su gareni daga Dad har Mommy babu wanda suke karɓa Bama sa bari maganar ta iso gareni suke datseta"
Cikin lokaci kaɗan sai gashi sun saki jiki da juna sunata hirarsu nan yake bata labarin aikinsa yake sanar da ita shi kanal ne na soja sannan ɗan kasuwa ne shi kuma Mahaifinsa shine Mataimakin gwamnan jihar Borno na yanzu asalin mahaifinsa kanuri ne mahaifiyarsa shuwa'arab ta jinjina tace “Mommy na bafulatanar Gombe ce Daddy na kuma haifaffen Kano ne amma...." Shiru ce ta ratsa yana jiran cewar ta yaji batace ba har saida ya magantu yace “Amma me?" Ajiyar zuciya tayi tace “idan kazo mayi maganar"
Jinjina kai yayi yace “Okay Noor Ki kasance da farin ciki nidai yau ko ango bazai kaini farin ciki ba dama Abdullahi yana yawan fadamin yanda nake gudun soyayya duk ranar dana afka bazan karɓu ta daɗi ba to yau dai ga jarumar tayi ram da zuciyata" ƴar ƙaramar dariya tayi yayi kissing din wayar tare da ce mata ki kwanta zamuyi magana da safe kinji" amsawa tayi da “to" ta aje wayar cike da shauƙin kauna zuciyarta wasai da sahihin farin ciki “ashe haka so yake da sanya nishaɗi" ranar kwana tayi tana mafarkin farin cikin da zata kasance a ciki idan ta samu wannan nagartaccen ingarman namijin ya zama mallakinta zata samu sururi zatayi rayuwa me ƴanci ba irin wannan rayuwar ta ƙila wa ƙala ba har addu'a ta rinƙayi Allah yasa kamar yanda yace da wuri ya kasance da wurin domin tanajin fargaba ta kasancewarta a wannan gurɓataccen gida a ganinta da tunanin ta idan tayi aure zata samu kariya daga dukkan sharri.




Cikin lokaci ƙanƙani suka samu wata muguwar shaƙuwa soyayyarsu ta bazu ta yaɗu ga dukkan dangi hatta a skyline da Rafi'ah take karatu duk wani classmate nata yasan Abdulƙadir masu son su kai mata caffa duk saida suka sha jinin jikinsu saboda basu ga alamun gurin da zasu kawo wasa bane mutumin da wani lokacin idan zaizo come boys yake yowa na sojoji yazo susha soyayyarsu ya tafi.
Lamarin ya fara samun tasgaro ne lokacin da Iyayenta suka gano ɓoyayyiyar soyayyar da suke yi ranar bata mantawa taje wani practical a AKTH ta dawo ta gaji sosai don haka tana shigowa bata saurari kowa ba ta nufi ɗakinta ta cire kayanta ta nufi bathroom tayi wanka tana fitowa kiran Daddy ya shigo ta ɗaga yace yanason ganinta a sama ta amsa ta ajiye wayar kenan tana sanya rigarta kiran Abdulƙadir ya shigo ta ɗaga tace masa “Noor Daddy ke son magana dani zan kiraka idan na dawo" ajiyar zuciya yayi yace “Okay nasan dalilin kiran amma jeki dawo" kashe wayar tayi ta fita ta haura saman gabanta ta tsinta da faɗuwa a parlourn ta tarar da Daddy da Mommy Daddy yana zaune itako Mommy kaiwa da kawowa taketayi a parlourn haka ta dake tayi sallama bata samu arziƙin amsawa ba sai wani uban mari daya ɗauke mata ganinta na tsayin minti guda da taji ya sauka a kuncinta.
Ɗagowa tayi cikin mamaki tace “Me nayi miki Mommy..." Ta kuma daga hannu zata mareta Daddy yace “Bari mana Bara'ah dukan maganin menene babu abinda zai maganta ki bari muyi magana Ni da ita dama ni tayiwa alƙawarin barin soyayyar kuma ni ta karyawa ba keba"





Durƙushewa tayi cikin kuka tace “Wlh Daddy sonsa ya shigeni tun farkon haduwa ta dashi na kasa cireshi a raina bazan iya ba ku barni na sameshi Daddy yaudara kuke gudu shi kuma da gaske yakeyi kuma yana sona shima..." Tsawa Mommy ta daka mata tace “Waye yace miki yaudara muke gudu inma yaudarar taki zai yi yayi abinda zai yi yayi gaba ai da sauki amma aure... Haba Rafi'ah tayaya zan yarda kiyi aure to wlh tallahi kinji na rantse ko zaki aure ba yanzu ba abinda nake da ra'ayin kiyi shi zakiyi"
Mikewa Daddy yayi ya matso gabanta ya kama hannunta ta miƙe ta kwantar da kanta a jikinsa cikin kuka me kashe zuciya tace “Daddy ya zanyi ne ku taimakeni wlh inason Abdulkadir..." Rufe mata baki yayi yace “Bawai muna gudun aurenki dashi bane don wani abu Maryam muna gudun aurenku ne don tseratar dake daga faɗawa wahala kinga ni in kinyi hƙr da kaina zanyi miki miji Alh Saddiq yana son kasancewa dake yanzu haka mun gama magana dashi Dala dari uku da hamsin zai baki in kika yarda dashi just 1 kawai ki amince ki samu yanke talauci meye zaki samu a wajensa suna kike nema kome? So kike in anganki a rinƙa cewa ga matar Ɗan Mataimakin gwamnan jihar Borno ne kome? Duk abinda kike nema idan kika samu kuɗi zaki sameshi in baki da kuɗi kuwa shima bazai darajaki ba"





“Girgiza kai tayi tace “Aa Daddy Ni banason kuɗin shi kawai nakeso Daddy na tsani zina wlh bana sonta da nayita Gara na mutu a ƙone gawata tun a duniya Dad ku taimakeni tsira da mutumcina...." Ashar Mommy ta kwaɗa mata tace “Kuma wlh ko bazaki karɓi kuɗin ba mu zamu karɓa mu badaki kyauta Yayi duk abinda yakeso dake" cikin tashin hankali tace “Aa Mommy kar kiyimin haka anya ku kuka haifeni Mommy kullum abinda kuke fadamin life is freedom banason halinku daga ke har Dad amma na haƙura ina kallonku don rayuwarku ce toni meye yasa kukewa tawa rayuwar kutse?"
Shaƙota Mommy tayi ta haɗa kanta da bango tana surfa mata ruwan bala'i tana cewa “Na haifeki a cikina Rafi'ah ki zaɓi namiji akaina nice fah na ɗauki cikinki wata tara ko ruwa nasha saiya dawo Ban isa cin abinci ba saidai naci garin kwaki ubanki ya gudu ya barni karshe ya aikomin da takardar saki nazo haihuwarki akayimin Cs na ɗauki wata huɗu ban warke ba nazo na shayar dake da nonona wanda ake tacewa ta cikin jinina a sarrafashi ya zama abincinki barta ni tunda na haifeki babu yanda zanyi dake shifa wannan bawan Allan daya karɓeki ya riƙeki fiye da ƴar cikinsa domin shi bai ma haifa ba ke yakewa kallon tasa, ya tsayawa rayuwarki cinki shanki iliminki lafiyarki walwalarki komanki ya zama shine yakeyi yake nunawa duniya ke matsayin ƴarsa amma Rafi'ah irin sakayyar da zakiyi masa kenan ashe butulu ce ke bansani ba butulu na haifa da cikina ni Bara'ah...."




Rugawa tayi da gudu ta rungume Mommy tana girgiza mata kai tana cewa “Sorry Mom wallahi ba butulci nakeson yi muku ba so nake ku fita kunyar Ubangiji akan amanata daya baku Mommy Ubangiji madaukakin Sarki ya kiramu dukka makiwata (kullukum ra'iy wakullukum mas'ulati arra'iyatihi) don Allah ku barni nayi aure wlh zan iya shiga wani hali zamana tsakaninku tunda bazan iya canzaku ba nisanta kaina daku zai bani damar samun sauƙin abinda ke damun zuciyata game da wannan rayuwar da mukeyi a gidannan"
Ta fahimci ƴar tata bazata taɓa fahimtar abinda take jiye mata ba shine dalilin da yasa ta janye ta tace “Nikam banason yaron nan baimin ba ki nemo wani amma banda Abdulkadir"
Taɗan samu sauƙi da wannan kalmar ta ɗago tace “Mommy dama Daddy ba shine mahaifina ba?" Harara ta watsa mata tace “Amma ai yafi mahaifin naki da ya wofintar dake tun kina cikin mahaifa" shiko Daddy takaici ma bai iya barinsa magana ba ta matsa gareshi tace “Nasan zuciyarka tana nadamar abubuwa da yawa a kaina Daddy kayi haƙuri bansan ta yanda zan iya cire shi a raina ba inasonshi matsayin miji kuma shi ɗin yanada nagarta wlh baitaɓa furtamin ko kalma ɗaya ta banza ba shi na musamman ne..." Nuna mata hanya yayi yace.





“Naji Maryam tashi ki bani guri nace miki kice nayi miki miji kin faɗa masa baki da baikon kowa a kanki kin mayar dani maƙaryaci babu komi Maryam kije kiyi aure amma ki sani na cire hannuna akan aurenki tun daga farkonsa har ƙarshensa kar a sakani a ciki Bara'ah ki nemi ubanta ki turata can ya daura mata aure"
Kuka ta saka me ban tausayi tana bawa Daddy hƙr amma bai saurareta ba yayi shigewarsa ɗakinsa Mommy ta rufa masa baya suka barta a gurin ta miƙe a kasalance ta nufi ɗakinta tana shiga wayarsa na shigowa ta ɗaga tace “Noor kuma bazamu haƙura ba?" Cikin ƙaraji yace “akan me Rafi'ah?" Kuka ta saka masa tace “Parent ɗina sunyi fushi dani saboda kai sunata jawa aurena dakai mugayen alkaba'i inajin tsoron yin dana sani da gujewa gara na faɗawa zago Noor kaine kaɗai zaka zama gatana a lokacin da iyayena suka juyamin baya kasan komai akaina bazanso ace wata matsala da zata sani jin nadamar zaɓar sunnah ta giftawa rayuwata dakai ba and end Noor sanadinka ne yau nasan cewa Daddy ba mahaifina bane yace da Mommy na duk yanda zatayi tayi ta nemi mahaifina ya dauramin aure amma shi bazai daura ba, wai duk meye ya kawo wannan ne Noor?"




Numfashi yaja me ƙarfi tare da murmushi yace “don kinƙi yarda kiyi rayuwar da suke so kiyi ne Noor karki damu da zarar anyi auren komai zakiga ya saitu Daddy ya turawa da Abba address na mahaifinki a Lagos yanzu haka Abba ya tura ƙaninsa da amininsa gurinsa tunda sun kirashi ya sanar dasu ya shigo Lagos daga Austaralia jiya yanzu kamar sati nawa kike ganin zaasa nifa wlh na matsu ayi a wucce wajen ƙiyayyar da Mommy take nunamin ta fara taɓa zuciyata da gaske idan aka cika ɗaukar lokaci haƙurina zai iya karewa idan hƙr na ya ƙare kuma komai zai iya faruwa"
Shiru tayi masa batace komai ba yaci gaba da bata labarin irin farin cikin da zai kasance duk ranar daya ganta a gidan shi matsayin mata.
Sun jima sosai sannan sukayi sallama washegari kuwa tana zaune a ɗakinta tana chat taga number Dad ya kirata ta ɗaga muryarsa babu wani sukuni yace “Kizo parlourn baƙi" saida taji saukar wani sinadari tun daga cikin kwanyarta har zuwa yatsanta ta jima tanason mikewa amma ta kasa saida Mommy ta turo ƙofar ta ganta a zaune tace “Bakiji kiran da akeyi miki bane?" Tashi tayi ta zura hijjab ɗinta ta fito ta nufi ɗakin baƙin tayi sallamar da bata karasa fitowa ba saboda idanun da taga duk ya dawo kanta magidanta ne guda uku sai wasu dattijan mata guda biyu gefe kuma Abdulkadir ne da Abdullahi zaune tunda ta shigo idanunsa ke kanta fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi.




Ƙasa tayi da idanunta ta rusuna gefen Daddy tare da cewa “Dad... Daddy gani" dafa kanta yayi yace “To komai sauri ai agaida ango ko kowa bazai samu gaisuwar ba" ɗagowa tayi idanunta ya sauka kan fuskar wani farin mutum kyakkyawa gabanta ya fadi duk da cewa ance mutum baya gane kamarsa amma ita fah taga tsananin kamarta da wannan mutum na zaune kamar kuwa ya lura da kallon da takeyi masa ya yafitota da hannunsa ta tsinci kanta da kallon Daddy ya ɗaganta gira ta miƙe ta nufi inda mutumin yake zaune ta zauna kusa dashi ya kamo hannunta idanunsa suka kawo ruwa ya buɗe baki yace “Mamana tun shekaru goma da suka wucce dana samu labarinki naketa bibiyar yanda zanyi na ganki abin ya faskara sai yanzu dalilin aurenki haƙiƙa nayi farin ciki da zuwan Abdulkadir sanadinsa gani gaki ina godewa Ubangiji Sarkin da yake sanya sanadi da sila a kowacce rayuwa tashi kije ki gaisa da surukanki ga kuma mijinki can shima ki gaisheshi"
Kallon kowa takeyi batare da fahimtar abinda mutumin yake faɗa ba. Ɗaya cikin dattijan matan ce ta taso ta iso ta ɗagota tace “Tashi kije ku gaisa da Abbanku ɗiyata kowanne ɗa na gari albarka yake nema a sabuwar rayuwar da zai tunkara kije su sanya miki albarka kamar yanda suka sanyawa mijinki durkusar da ita tayi gaban wani dattijo ya dafa kanta yana murmushi yace “Wannan suruka tawa akwaita da kunya muna farin cikin zuwanki Barzah Family alkhairin dake tattare dake Allah ya tabbatar mana dashi akasinsa Allah ya tsaremu dashi baki ɗaya" haka ta rinƙa zagayawa tsakanin mutanen dake parlourn a ƙarshe ne aka tsugunar da ita gaban Abdulƙadir daidai lokacin da kukan da take ta son makalewa ya kwace mata ya sanya hannunsa ya kamo yatsunta Hajiya Nana ta buɗe wani akwati ta zaro wani zoben gold ta miƙa masa ya karɓa ya zura mata a hannunta gabaɗaya ɗakin suka ɗauki kabbara daidai lokacin daya rungume ta a jikinsa ta kwantar da kanta luf a ƙirjinsa tana sakin sautin kukan da yake ƙara karfin bugun zuciyarsa ya lalubo kunnenta ya ɗora harshensa akai yana lasa a hankali wata kasala na saukar mata yanda ya lumshe idanunsa ne ya tabbatarwa da Abdullahi ya manta a ina suke shine dalilin da yasanyashi jan rigarsa yayi saurin dawowa hayyacinsa ya raɗa mata “Bazan hanaki kuka ba don nasan na farin ciki ne amma ki bari muje gidanmu kisani a gaba kiyimin Ni kaɗai nayita kallo".......
[10/16, 11:58 AM] OUM HAIRAN: *AKWAI IRINSU....*
(Eroctic romance and bad destiny)




_Free page 7_




_Oum Hairan_




_Paid book nrml 300 VIP 600 special 1k Email post 2k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank evidence 09013718241_




Dariya dukka manyan dake parlourn sukayi amma banda Dad da Mommy da fuskarsu take kamar anyi musu wahayin mutuwa gobe Daddy ne ya fara mikewa Mommy tayi saurin cewa “To me kuma yayi saura ne Abdulkarim ka nunawa duniya salon naka butulcin kwai kawai ka saka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login