Showing 57001 words to 60000 words out of 72723 words

Chapter 20 - AKWAI IRINSU COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Jan 2025

6064

suka gaisa ta dubeshi sosai idanunta cike da tuhuma yaja numfashi yace “Ba laifina bane Maryam ..." Ɗagansa hannu tayi tace “karka damu kanka da son saina yarda Yusuf zanyi mamaki matuka kacemin Bakada masaniya game da abinda ya faru jiya anya Yusuf kodai kaima aiki kakeyi masa?"
Murmushi yayi yana kwanciya a gado yace “Yaushe nasan alaƙarki dashi da zanyi masa aiki kece dai nake tunanin meye alaƙarki dashi da yake shiga rayuwarki kai tsaye haka wannan kutsen yayi yawa abin tambayar ya akayi yasan zakizo gurina?" Da mamaki ta kallesa tace “kai zan tambaya ai “sumarsa ya yamutsa yace “to akwai wani abu dake faruwa ni ina ɗakin dana faɗa Miki naji ana ƙwankwasawa na fito a wanka kenan na bude ina buɗewa naganshi tsaye jikin ƙofar ya janyoni waje yasa wasu ƙaratan sojoji suka ɗaukeni cak suka watsani ɗaki number biyu tazararsa da wannan suka zaunar dani tare da sanyamin budemin wata ƙatuwar leda cike da tsire sai lemuka harda Wine sukace maza naci hannu ya mikamin ya karɓi wayata bazan iya komai ba wlh koshi kaɗai ne bare da wadannan basawan a tare dashi hakanan na bashi ya fita bai jima ba ya dawo ya karamin a kunnena a hannunsa nake lokacin da nakece miki na iso ke nake jira amma ina fuskantar barazana....
Kashe wayar yayi ya fice da ita nikuma suka sani a gaba saina cinye naman nan haka na rinƙa cin naman tun ina masa cin daɗi har na koma yi masa na wahala gumi ya fara karyomin ke har kuka saida nayi musu nidai bansan meye ya faru ba can naji ya kirasu yace su ƙyaleni kuma wayata tana Dakin dana kama Rafi'ah iya abinda na sani kenan"





Girgiza kai tayi tace “Nasan ka samu labarin wani abu game dashi Yusuf Shi Air Marshal Abdulƙadir Ibrahim Barzah tsohon mijina ne kuma uban ƴaƴana mun rabu dashi rabuwar da nakeso ta zama ta har abada amma shi yaƙi rabuwa dani Please mubar duk wani wasa da shashanci Yusuf matanka nawa?"
Bai tsammaci wannan tambayar zatayi masa ba yace “Matata daya yarana uku suna Yola da zama" “Okay Kanada ra'ayin ƙara aure ne ?" Jinjina kai yayi yace “Gsky In so samu ne inason ƙara aure Rafi'ah saboda inason samun matar da zan ajiye anan Lagos kuma wacce zata iyani sosai yanda idan ta dafamin Allah ya shiga lamarina na daina harka da matan waje"
Tashi tayi ta matsa ta riƙe hannunsa tace “Nayi maka?" Da sauri cikin rashin tsammani yace “Raf...fi..." Rufe masa baki tayi tace “Baso nake ka duba matsayina ko sunana ko mahaifina ba kar kaji a ranka Rafi'ah shugabar gamayyar kamfanonin sarrafa magungunan AJSH ce a gabanka a'a Yusuf ka kalleni tsirarata banida rigar komai a wajenka nake nema ka sani a ma'aunin ka kagani zan samu karɓuwa a zuciyarka ma'ana zaka iya aure na?"





Ɗagowa yayi idanunsa sun canza launi ya zuba gwiwowinsa a ƙasa yace “Alhamdulillahi ya Allah na gode maka daka tabbatar da rahmarka da jin ƙanka gareni wlh Rafi'ah tun farkon ganina dake da kika zo min a Maryam ba kallon Karuwa nayi Miki ba nayi mu'amala dake ne zuciyata tana tabbatarmin da baki cancanci haka ba kamata yayi ace mata ce ke inasonki Rafi'ah ko baki da komai kuma zan rayu dake a duk yanda kike"
Murmushi tayi tace “Ok ga compliment card na Daddy na zan gabatar dakai jibi idan naje California domin dama ya nemeni kuma nasan bai wuce issue na aure ba" idan komai ya zama yanda ya dace zanyi maka magana sai ka tura ayi magana amma ka rufe bakinka babu wanda yasan maganar nan dagani saikai sai Munirah"
Tashi yayi yana mata godiya sukayi sallama ya tafi zuciyarsa wasai cike da farin ciki yau ya samu awo daidai ƙirjinsa zaiji daɗi duk ranar daya buɗe ido yaga Rafi'ah ta zama mallakinsa shi kaɗai shi dama baitaɓa mata sha'awar wannan rayuwar ba domin baiga abinda take tsinta a cikinta ba ita ba kuɗi take nema ba ita ba suna take nema ba duk tana dasu an nema mata tun kafin tazo duniya.





Rungume hannunta tayi tana kaiwa da kawowa sai take ganin kamar zaɓin nata baikai ba to amma waye take dashi da zata samo cikin wannan yanayin samanshi. Zama tayi tana tunanin irin makomar da rayuwarta zata samu idan ta yarda tayi aure namiji zata sake yarda dashi kuwa anya namiji zai sake samun zuciyarta to ita meye yasa yasa dole sai tayi auren ne?
Wuntsilawa tayi kan gadon tayi murmushi tace “Badon kaina ba don na ɓacewa ganinka Abdulƙadir kaine kawai matsalata da gaske nakejin tsanarka" a wannan yini babu inda taje tana kwance a gida har dare tana kwance bacci ya fara daukarta taji shigar saƙo wayarta daƙyar takai hannu ta duba Mazajen kuɗaɗe ne suka shiga acct ɗin ta miƙe zaune da sauri tare da ɗaukar waya ta kira Daddy da sauri yana ɗagawa tace “Daddy banida buƙatar kudi fah kullum ina faɗa maka meye yasa kakeson ka rinƙa turomin kudaden da banida abinyi dasu?"




Shiru tayi shikuma ya ɗora da cewa “Bani bane Rafi'ah" cikin mutuwar jiki sukayi sallama tana kashe wayar taga saƙo ya shigo wayarta ta buɗe “Meye na kiran Daddy bayan kinsan nafi Daddy kusanci dake Noor ba wani abu bane fah daɗin da kika jiyar dani jiya bazan iya biyanki ba wannan kawai kyautatawa ce tsakanin zuciya da zuciya" ƙwafa tayi wato Abdulƙadir yana raina mata hankali tashi tayi ta fara haɗa kayanta Nigeria ta fara daukar mata zafi gara ta matsa ko ta samu sa'adar zuci fita tayi bayan ta ɗauki passpost ɗinta jirginta 9:00pm zai tashi zuwa California.
Rayuwarta tayi mata daɗi a kwanakin da tayi a California batada wata damuwa sai guda ɗaya ta kasa gane yanayin jikinta kullum batada lafiya daga ciwon kai sai zazzaɓi haka ta shafe watanni biyu daidai lokacin da takejin lokaci yayi da zatayiwa Daddy maganar Yusuf daidai lokacin ne kuma ya kirata a waya tana kwance a ɗakinta ƙudundune da duvet sanyi na ratsata daƙyar ta tashi taja jacket ta sanya doguwa ta fito parlour suna zaune shida wani matashin magidanci Balarabe kyakkyawane sosai fari sol irin kallon da taga mutumin yanayi mata saida gabanta ya faɗi ta zauna a ƙasa suka gaisa da Daddy tana gyara zama Second Daddy yace “Ummana bakiga bako bane" ɗagowa tayi ta gaisheshi cikin larabci da mamaki ta sake dubanshi jin ya amsa da Hausa cikakkiya murmushi Daddy yayi mata yace.





“Ba Arab bane uwata Buzu ne Wannan shine Shamsunddeen ɗane gurin Alh Badaru Mangal tun shekaru biyar baya mahaifinsa yayimin magana akan Deen yaganki kuma ya nuna shi ke yake da muradin aure, to a lokacin banyi miki magana bane saboda sanin yanda zuciyarki ta ɗauki zafi sai yanzu naga dacewar yi miki magana uwata in so samu ne inason a nunamin iyakar darajata a wannan lokacin idan zai yuwu a karɓeshi matsayin da aka kasa ɗora kowa insha Allahu bazaa kuma kokawa ba kinji"
Tunda second Daddy ya soma maganar taji wani sihirtaccen gumin masifa yana karyo mata ta ɗago manyan idanunta ta saukesu kan Deen da shima ita yake kallo yanason fahimtar yanda ta karɓeshi batakai da yin magana ba taga Daddy ya miƙe yana cewa “Deen ga ƙanwar taka nan ku tattauna saidai kuma kayi hƙr na sanar dakai ƙudurinta duk yanda kukayi mayi magana da Alh Badarun tunda gobe dama munada zama dashi" godiya yayi masa ya miƙe ya iso gabanta ya zauna tare da zare hularsa kyakkyawar sumarsa me kama data larabawa ta sauka a saman fuskarsa ya gyarata yace “Hajiyata Barka da wannan lokacin kiyi haƙuri da Kutse na cikin rayuwarki da soyayyarki nasan komai game dake Rafi'ah tun kafin ke ki sani na soki tun kafin nasan wacece ke saidai na kasa samun dama a wajen mariƙinki hakanne yasani haƙura Mammah na ta samomin mata a danginta nayi aure don inada buƙatarsa shekara takwas kenan da aurena yanzu matata shekararta shida da rasuwa dalilin zata haifamin baby.





_*Oum Hairan*_
[11/17, 7:25 AM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU29....*_



_*Oum Hairan*_



*Alhamdulillahi 💃💃💃💃Meta force yayi anshamu a online business da na cuta da yaudara, Amma meta force yazo yawarkar damu,Meta Force Yafi kowanne crypto project a ynz , inhar kanada qashin arziki zo kusan menene Meta Force kuyi register zakuyita godemin tsawon ryw😃 in kana da rabo acikin wannan tafiya zaka iya zama millionaire ckn kankanin lkc, Alhamdulillahi da zuwan Meta Force alkhairin Allah 💃💃inhar Zaka jajirce 7200 kacal zai iya kaika 1m acikin wata daya kacal👌meyafi wannan, duk Mai Neman Karin bayani ya nemeni_akan wnn number 08141390323*



_Paid book via acct 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank proof of pay 09013718241_




Alfarma ɗaya tak Sarauniya ta don Allah karki kalleni ki duba mahaifinki da baitaɓa neman wata alfarma a wajenki ba kiyi dominsa insha Allahu bazan bashi kunya ba Please kar rashin samun kulawar namiji ɗaya yasa kiyiwa dukkanmu kudin goro ki bani dama..."
Miƙewa tayi da sauri tabar masa parlourn ya bita da kallon mamaki cike da tausayawa irin rayuwar auren da aka bashi labarin tayi har takai da ta tsani auren gabaɗaya a ranta Girgiza kai yayi ya juya ya fita ya shiga motarsa yaja zuwa unguwar da yake zaune anan California a fili yace “Mace baiwar Allah mace abar tausayi mace me rauni mace uwa mace mata mace ɗiya amma wasu mazan sukan ɗauketa kamar baiwa bayan Addinin Musulunci ya bawa mace dama me yawa kuma ya kirata ƙurratul Ayn sannan sanyin zuciya kuma nutsuwa ga mazaje ashe itan dole tana buƙatar kulawa da kuma uzuri saboda rauninta?
Murmushi yayi cikin sanyin yanayinsa na halitta yace “Inasonki Rafi'ah Insha Allahu saina goge miki damuwar data sanya kikewa maza kallon marasa tausayi saina sanya miki jin cewa ashe kinso cutar kanki da kin biyewa dokin zuciya zan jiyar da rayuwarki daɗi kuma zan sanyaki farin cikin da sai kin manta kin taɓa aure kafin Ni"
Yana zuwa gida wanka yayi yayi Sallah ya zauna yana tasbihi ga Ubangiji tare da tura masa zaɓi akan abinda yakesonyi na jihadi ko bayason Rafi'ah ya kamata yayi jahadin cire ta a wannan ƙazamar rayuwar da takeyi bare ya sota tun bata gama sanin kanta ba koda kaddarar manyan ƴaƴanta ba nasa bane shikam yasan harda mariƙinta a taka rawa wajen hanashi power neman aurenta a wancan lokacin da ya ganta a airport zasuje Cairo da Mommy




Kiran Alh Badaru Ali Mangal ne ya katse masa nisan tunanin ya ɗaga da girmamawa yayi gaisuwa ta ban girma irin tasu ta sarakai Alh Badaru yace “Deeni ya akayi ne najika da sanyi" numfashi ya sauke ya tashi zaune yace “Allah ya taimake ka don Allah karta suɓce min da gaske nakeson Rafi'ah kuma kaima ka yarda da ƙudurina Mai martaba a yanayin yarinyar har yanzu da tsoron maza a tattare da ita" dariya sosai Alh Mangal yayi yace “Son kanason Rafi'atu da yawa karka damu insha Allahu zaka sameta da wuri zanyiwa mahaifinta magana yanzu" kashe wayar yayi Deen yaci gaba da kallon wayar yana murmushi so yakeyi ya kirata yana tsoron karta yarfashi hakanan ya kwanta kawai badon yaso ba sai don rashin mafita.
Ita kuwa tana zaune tana tunanin wannan tutsiyen da Daddy yayi mata tana share hawaye tayiwa Yusuf alƙawarin aure meye yasa Daddy be shigo da Deen ba saida ta riga ta tsara komanta? Girgiza kai tayi tasan ko runhu taci bazata iya watsawa Daddy ƙasa a ido ba dolenta ta karɓi wannan zaɓi nasa karon farko da ya nemi wani abu a wajenta ita kuwa wacce irin ɗiya ce mara albarka da zataƙi yin biyayya gareshi?" Komawa tayi ta zauna cikin sallamawa ta ɗauki wayarta dake rurin neman agaji ta ɗaga tare da cewa “Daddy" “Na'am Rafi'ah zo mana" miƙewa tayi ta fito ta buɗe ƙofar ta nufi ƙasan Daddy yana zaune a parlour ya baje system yana dubawa ta zauna ya miƙa mata hannu ta matsa ya shigar da ita jikinsa yana shafa bayanta yace “Bakiyi na'am da zaɓina ba ko Ummana?" Girgiza kai tayi da sauri yace to mene yasaki tashi kika barshi?" Sunkuyar dakai tayi yayi murmushi yace “Addini yabawa zawara damar zaɓen abokin rayuwarta dakanta Rafi'ah nayi miki zaɓi ne don cancanta wlh nagaji da rayuwarki a haka raina tana ciwo da tuna Ubangiji zai tsayar dani ranar da bani da hujjar kare kaina game da rayuwar da kikeyi Rafi'ah ki taimakeni ko bazaki karɓi Deen ba ki fito da wani kiyi aure inason tuhumar Ubangiji tayi sauki gareni..."




Rungumeshi tayi sosai tausayin mahaifin nata yana kwaranya a zuciyarta cikin suɓcewar kalami tace “Na amince da zaɓinka Daddy saidai inajin tsoron..." Ɗago kanta yayi yace “Tsoron me?" Janyewa tayi tace “Ina tsoron na ƙara bada yardata abinda ya faru ya kuma faruwa Daddy" dariya sosai Daddy yayi yace “Shi jini baya ƙarya Rafi'ah na tsorata da butulcin mata tun inada ƙuruciya na kasa sake haɗa rayuwata da wata mace ina rayuwata ni kaɗai tunda Bara'ah ta gujeni nasha wahala Rafi'ah har ciwon hauka nayi kakanki shine yayimin magani gani kuma ina rayuwa rayuwa me inganci karkiyi kallo gareni ni namiji ne kuma na roki Allah ya bani kariya bantaɓa sha'awar aikata zina ba Ummana rabona da aure shakara ashirin da bakwai kenan, ke fah kin samu rauni a ɓangarori da dama kuma idan kika tafi a haka Ubangiji zaiyi fushi dakene ya jarabceki saboda jarabawar da yayi miki ne ma kika lalata rayuwarki"





Girgiza kai tayi da sauri tace “Allah na tuba Daddy...." Rufenta baki yayi yana murmushi yace “Bazan yarda da tuban muzuru ba aure kawai zakiyi na tabbatar da kin tuba" sunne kanta tayi a ƙirjinsa tana dariya shima dariyar yayi yace “Ummana kenan tashi kije ki kwanta zan nemeki" komawa tayi ciki ta kwanta ba bacci tayi ba wayoyine suketa karakainar shigowa wayarta Abdulƙadir Yusuf sai Munirah sannan Mommy duk taƙi dagawane domin tasan kowa meye zaice mata Munirah Zata tambayeta Ina take ne Abdulƙadir shirmensa ne zaiyi mata Yusuf inda maganar aurensu ta kwana zai tambayeta, Mommy kuwa bai wucce ta nemi kuɗi a wajenta ba,
Wayoyin suna gama shigowa ta kashe wayarta gabaɗaya ta kwanta bata kunna ta ba sai washegari shima washegarin Daddy ne yace ta kunna tana buɗewa saƙo ya shigo da wata baƙuwar number hakanan ta kwadaitu da son sanin meye a cikin sakon.
_"Happy maried life My Wife, ina rokon Allah ya bani ikon zamowa mijin da zai zama abin alfahari gareki_
Dirowa tayi daga gadon gabanta ya shiga wani irin lugude zuciyarta na neman barin ƙirjinta kafin zuciyarta ta samu damar tuno mata wani abu kiran Daddy ya shigo ta ɗaga cikin rashin makoma tace “Hello" daga muryarta ya fahimci batada wata nutsuwa yace “kinada baƙo" tashi tayi ta sanya hijjab ɗinta ta fito bata ishe kowa ba sai Daddy a zaune yana duba jarida ta rusuna ya ɗago ya dubeta yace “Mijinki ne ke jiranki a waje zakuje medical test" ta rasa meye yasa a duk lokacin da akayi maganar blood test sai taji faduwar gaba haka ta miƙe Jikinta babu ƙwari ta ɗauki wayarta ta fito yana zaune a motar ƙafafunsa na waje ta isa wajen waya yakeyi da alama kuma wayar ta ɗauke hankalinsa hakan ya bata damar ƙare masa kallo kyakkyawa ajin farko hasken fatarsa har ɗaukar idanu yakeyi....





Kawar da kai tayi lokacin da taga ya juyo ya sakar mata murmushi tare da buɗe mata ƙofa ta zauna a kasalce yaja motar suka tafi sunyi nisa sosai ya rage sautin karatun Alqur'anin da yake tashi a motar yace “barka da yini ƙurrah" kunyarsa ce ta kamata ta sunkuyar da kanta cikin cinyarta batare data amsa ba har yanzu gabanta faɗuwa yakeyi bai kuma ce mata ƙala ba don bayason takurawa rayuwarta da magana shi ba mutum ne me shiru da bakinsa ba Allah yayi masa baiwar magana ita kuma ya lura irin silent nature ɗinnan ce.
Sun isa wani katafaren asibiti yayi parking ya fita bai jima ba ya fito ya tsaya jikin motar yace “Mu shiga ko" zuro ƙafafunta tayi ta fito duk takunta guda ɗaya daidai yake da karin sautin bugun zuciyarta ta rasa meye yasa take tsarge da kanta bata tsoron ciki bata tsoron HIV tasan duk tanada kariya a wannan fannin amma ita kanta tasan ta samu matsalar Infection tun baya data fara bariki daka, wani ɗaki suka shiga me masifar sanyi suka zauna saman kujeru har yanzu ta kasa haɗa idanu da Deen wanda ta lura kallonta yaketa satar yi ta sauke ajiyar zuciya lokacin da likitan ya shigo suka gaisa da Deen ya sake yi masa bayani ya nuna masa wani guri yace ya zaune itadai batasan meye akayi ba taga ya tashi itama ance ta zauna komai Normal kamar yanda ta zata sai abu ɗaya wato sanyi shine babbar matsalarta ita kanta tasan akwaishi donma wai itan babbar ƙwaruwa ce a fannin magani tana bakin ƙoƙarinta, shikam komansa normal bashida wata matsala hatta gwajin ƙwaƙwalwa da akayi musu kowa ya tsallake ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana ayyana yanzu zatayi aure ta haƙiƙance ba mahaukaci zata aura ba duk wani abu da zai biyo baya daga iskanci ne.




Bayan kammaluwar komai ne ya dubeta fuskarsa wasai yace “Zan ɗan ga Dr kiyi haƙuri kaɗan" Lumshe idanunta tayi ta kwantar da kanta jikin mota tana lallatsa wayarta kiran wayar Mommy tayi cike da faɗuwar gaba don batasan me zata faɗa mata game da wannan auren da ake shirin kullawa ba tasan tanason aure saidai batayi zaton shima zaizo mata a bazata irin yau ba sallama tayi ma Mommy ta amsa mata ranta wasai tace “Rafi'atuna Ya Daddyn naki ɗazu munyi waya yake faɗamin ashe aure aka ɗaura Miki ɗazun nan haba da wannan jaraba ta wancan mahaukacin sojan naki ai gara kiyi aurenki kowa ya huta"






Wata ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi tace “Wai Mommy da gaske ne an Ɗaura da Shamsunddeen ɗin" Dariya Mommy tayi tace “Oho ke kikasan sunan mijinki nidai naji daɗi ne kawai da kika yada ƙwallon mangwaro kin huta da ƙuda yaushe ne tariyar kuma?" “Zan kiraki Mommy" ta faɗa tana gimtse wayar daidai lokacin daya ƙaraso wata nurse tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login