Showing 66001 words to 69000 words out of 72723 words

Chapter 23 - AKWAI IRINSU COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Jan 2025

6072

dashi wancan sanadin ganin ya damu ta ware sukaci gaba da harkokinsu.
Kwanci tashi saiga cikinta ya shiga wata na tara tun watanni bakwai ya gano abinda ke cikinta ba ɗaya bane ya shiga tsananin farin ciki yayiwa Allah cikakkiyar godiya da tasbihi sukaci gaba da rainonsa har kawo yanzu da lokacin haihuwa ya matso basu taɓa samun matsala dashi ba kullum yana ƙoƙarin ganin yayi abinda zai sanyata a farin ciki ne sosai ta saki jiki dashi suke rayuwarsu me armashi da kulawa.





Yau juma'a misalin biyu da rabi na dare bayan sunyi al'amuransu sun gama bacci ya gagaresu ciwo kamar bazata kai labari ba tun farkon ciwon yaso su tafi asibiti amma fir taƙi yarda ce masa takeyi zaiyi sauki yaƙi ganin sauƙin a ƙarshe babu shawara ya rakiceta suka tafi asibitin ita ke ciwon shine da azabar don yafita shiga tashin hankali gani yake itama tafiya zatayi ta barshi kamar yanda Rahana ta tafi ta barshi da wannan ya shiga office ɗinsa yayi wasu cike² ya fito daidai lokacin da Gimbiyar Dutse tazo asibitin yake faɗa mata Gimbiya ina ganin aiki kawai zaayiwa Ƙurrah" kallonsa tayi da sauri tace “Akanmi Deeny dama bata haihuwa da kanta ne?" Sharce gumi yayi yace “Haihuwarta ta farko ta bani labarin da tazo da irin wannan jinkirin Cs akayi mata Gimbiya ina tsoron kar itama ta tafi ta barni...."
Fitowar wata nurse ce ta katse masa zancen da cewa “Yallaɓai ta sauka yaranta biyu duk maza" bata gama rufe baki ba tuni shi ya shiga ɗakin ya isa inda take kwance tana mayar da numfashin wahala ya shafa kanta tare da sunkuya yayi kissing goshinta yace “Say alhmdllh Ƙurrah" lumshe idonta tayi wahalar da tasha bata sata jin ɗigo na haushin mijinta ba saima wata sabuwar ƙaunarsa da taji tana mamaye duk wata kusurwa ta jikinta cikin kasalar harshe tace.
“Alhamdulillahi bi ni'imatihi tatimussaliha Zaujh Jann na gode" kama hannunta yayi ya matsa ga yaran suna kwance sai tsotsar hannunsu sukeyi babu wanda yayi kama da ita duka dashi suke kama ƴaƴan buzaye kamar ɗiyan larabawa murmushi yayi yace “Duka nawa ne Ƙurrah?" Gimbiyar Dutse ce data shigo yanzu tace “Aa nawa ne Deeny" Murmushi yayi yana shafa sumarsa yace “Gani nakeyi kamar mafalki Gimbiya" lakace masa hanci tayi tace “Kyautar Allah kenan Deeny ka rasa ɗaya kayi da matarka yanzu ga biyu da matarka an baka" ajiyar zuciya ya sauke tare suka gyara yaran suka shiryasu cikin kayan sanyi suka kwantar dasu Gimbiyar Dutse ta haɗa mata ruwa ta taimaka mata ta gyara jikinta tana fitowa kiran Daddy ya shigo wayarta daƙyar ta ɗaga saboda jirin da takeyi kasantuwar ta zubar da jini sosai ta kara a kunnenta tace “Daddyna" dariya yayi sosai yace “Ina sabbin ƴan Niger?" Murmushi tayi tace “Aa ƴan Nigeria dai ko Daddy"





“Haba yarinya Nigeria da larabawa ne ai saidai Niger ɗin wadannan kyawawan yara haka masha Allah Ubangiji ya ɗorar da lafiya ya bada lafiyar shayarwa ki kula da shan magani sosai Deeny yace kinsha wahala har jini ma da zasu sanya miki shine ya hana saboda gudun matsala"
Godiya tayi masa sukayi sallama ta juya ta kalli Deeny da yaketa juya shayi ya diba a cokali yakai mata bakinta ta karbi cup ɗin tace “Yunwa nakeji Zaujh" saida ta shanye tea ɗin ya duba drip na hannunta yace “Sunci kinyi tear sunyi miki ɗinki ko?" Jinjina kai tayi yace “Ok"
Kwana sukayi a asibitin sai da safe suka tafi gida ƙarfe tara kuwa saiga Mommy da Munirah wannan haihuwar ta zamo mata daban da sauran haihuwarta uku mijinta na tattalinta da kulawa da ita ga mahaifiyarta tare da ita sannan ga ƴaƴanta ababen so ga kowa, kwana ɗaya Mommy taso tayi a gidan taga jikokin ta amma fir Deeny ya hanasu tafiya saida akayi suna saiga Mommy harda gayyatar danginta daga Gombe sukazo suna ƙanwarta da matar yayanta daga Maiduguri ma dangin Daddy sun zo harda Hajiya Nuratu tayita santin yaran tana yabawa da kulawar da Deeny yakewa Rafi'ah “Yanzu kikayi aure Rafi'ah" ta faɗi haka yafi a ƙirga da dare ne da suka keɓe take tambayarta ina su Ablah da Hisham tayi murmushi tace “Hisham Yana United state of America yana karatu Ablah kuma tana gurina ya haƙura ya sallamata da yaga Allah ba wasa ba, kinsan yayi aure matar tace bazata iya zama da ƴaƴansa ba shine ya saketa ya kawo Ablah garemu yaci gaba da zamansa haka"





Bataji daɗin labarin ba ta rasa ya zatayi ta cire lissafin Abdulƙadir cikin rayuwarta shi mutum ne da baya ciruwa a zuciya duk da cewa tasan mijinta yafi kowanne namiji dacewa da zama abokin rayuwarta kuma zaɓinsa alkhairi ne gareta miji ɗaya tamkar da billions samun irinsa a wannan zamanin da maza suka cika da son kansu sai an tona zata zauna dashi ta rayu dashi da gaske da zuciya guda dan yafi kowa cancanta kuma zataci gaba da koyawa zuciyarta sonsa domin yafi dacewa data soshi.
Ranar suna yaran sukaci suna Jamil da Jalal akasha taron suna aka watse kowa ya kama gabansa kwanaki uku dayin suna Deeny ya tafi Canada ya kasance daga ita sai bayin dake hidima a ɓangaren dake duk abinda akace yaji akwai baya zama damuwa idan aka ɗauki yaran aka kai su gurin Gimbiyar Dutse saita manta ma tana da ƙananan yara suke dawowa kullum sukan kasance a chat suna hira soyayyarsa sannu a hankali mamayarta takeyi kafin ta ankara ya jima da huda zuciyarta sannu a hankali har ya cire mata kowa a ranta ita da kanta take ganin wautarta da tayi garajen zaɓi ashe rabon yin ilimi ne gareta tabbas yanzu takejin ta samu abokin rayuwar da bazata iya sakacin ya suɓce mata ba zata riritashi kamar ƙwai zata darajashi fiye da dutse diamond domin duk wani matsayi shiɗin a samansa yake.





Kwanaki sukayita tafiya saida yaranta sukayi watanni biyu sannan ya dawo a Nigeria ya ishesu tunda sukazo yawon arba'in yace tayi zamanta a gidansa na nan kawai basai ta koma ba domin shi kawai yafison zamanta a Abuja, can yaje ya samesu yayi wata guda yace tare zasu koma batayi masa gardama ba domin itama tafison rayuwa kusa dashi suka ɗaga zuwa Canada sukaci gabada rayuwarsu a can cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Ƴan Hausa sukace tafiya sannu sannu kwana nesa shekara kwana sai gashi ta samu shekara goma tare da Deeny lokacin yaransu huɗu Jamal Jalal Hameed da Hameedah suna rayuwarsu cikin soyayya da kulawa wata rashin lafiya da Mai martaba yayi ne yasasu komawa Niger urgent har lokacin Kilishi basa wani ga maciji da Rafi'ah ko guri ɗaya basa zama abin na damunta saidai ta kasa magance matsalar ta rasa meye yasa da surukarta da yan'uwan mijinta da suke daki daya duka basa ƙaunarta Gimbiya Safiyyah ce kawai Zakka a cikinsu itane kawai suke ɗasawa.
Abinda yake bata mamaki ko ganin waɗannan yaran da suke tsakaninta da Deeny sai takega ya kamata koma meye a ransu ya wucce su ɗauketa matsayin tasu domin ko bata tare da Deeny sun riga sun haɗu haihuwa huɗu ba wasa ba.
Watanninsu biyar a Niger wannan karon saida tayi ziyara sosai har Maiduguri sukaje ganin yaranta sunyi murna da ganinta musamman Ablah dake mace kamarta da mahaifiyarta ta fita sosai shikam Hisham sak ubansa ne hutu yazo kwanansa ɗaya da dawowa haka sukayita shige mata Hisham ya ɗebi ƙannensa suka fita sun jima sosai dake ya girma sosai shekara sha tara.
Gidan Daddynsu ya nufa da yaran ya tarar dashi kwance a parlour yana danna waya yana ganinsa ya tashi zaune yace “Son, wow! Masha Allah ina ka samo yaran larabawa?" Zama yayi yace “Ƙannanmu ne Daddy Mommyn mu ce yau ta kawo mana ziyara kamo hannun yaran yayi zuciyarsa na bugawa da ƙarfi yace “Rafi'ah ce tazo ganinku Hisham itan yanzu tana ina?".....



_*Oum Hairan*_
[11/21, 11:41 AM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU....*_



_*Oum Hairan*_




_Me son complete book One 300 via acct 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank proof of pay 09013718241_

*End book One*
_Don Allah karku zargeni da son kai cikin wannan littafin babu wani abu dana canza yanda labarin yake haka yake tafiya rashin lokaci ne yasa yake tafiyar hawainiya._
_Sannan dayawa suna cemin to meye yayi saura Rafi'ah ta auri Deeny har sun haifi yara biyar kuma nace akwai part 2 na labarin to ku sani wannan labarin yanada faɗi zan iya gajarce shi kuma zan iya tafiyar dashi yanda yake duk wanda kuka zaɓa shi zanyi muku, in kunce na gajarceshi shikenan in kuma in tafi dashi yanda yake ne to zaku ƙara payment 300, sannan wannan karon bazanci gaba da VIP ba zan tafi dashi single ne course zanyi wani uzuri shima me cin lokaci kuma shima aikin ƙwaƙwalwa ne,_



_*35*_
Zama yaron yayi yace “Tana gida naji tana anan zata kwana gobe zata wuce Dubai ne" jinjina kai yayi can yace “Ok" daga haka ya koma ya kwanta yana mawa Hameed da Hameedah wasa sune ƙananu don haka dasu ta taho a ransa yana raya wai Rafi'ansa ce ta auri wani bashi ba har ta haifa masa waɗannan kyawawan yaran kuma bayan wadannan ma da wasu?
Zuciyarsa yaji tana neman karyewa ya tashi ya shiga ɗakinsa ya zura kayansa ya fito yana cewa da Hisham “Son kaje gida zan kawosu in mun dawo daga shopping" tsalle Hameedah ta fara tace “Daddy harda sweet zaka suyi mana" murmushi yayi yanajin a ransa dama shine ya saka ƙwan ta ƙyanƙyashe masa yaransa sun girma yana buƙatar ƙari gashi ita tanada shida shi kuwa ya maƙale a biyu.
Fita sukayi ya yawata da yaran ya kuma haɗo musu shop sannan ya wucce dasu gidan lokacin da yaje akace batanan mijinta yazo sun tafi amma akwai driver da zaizo ya ɗauki yaran, zama yayi suna ɗan taɓa hira da Ya Hajja nan ta shiga yi masa nasiha akan aure yaja fasali yace “Hankalina ya koma kansa Zanyi Ya Hajja na rasa irin macen da nakeso ne wlh" murmushi tayi tace bazaka samu wacce zatayi maka daidai da wacce kake hange ba Audu ba'a ɓari a kwashe duka" miƙewa yayi kullum haka take faɗa masa kalamin kashe gwiwa shikam ya haƙura da lissafa waiwayowar Rafi'ah rayuwarsa zai rayu yanda Allah ya tsara masa.





Wani gurin cin abinci ya nufa ya zauna ba don cin abincin ba saidon samun nutsuwar zuciyarsa kawai
Hawayen daya zubo a idanunsa ya ɗauke zahiri Rafi'ah rayuwarsa ce ya kasa samun madadinta tun yana lissafa yini ya koma kwana ya koma wata yanzu shekaru yake lissafawa suma kuma sun fara nauyi alama ta bayyana masa haƙuri da cire matar wani a ransa shine yafi masa alkhairi.
Wayarsa ya ɗauka ya daga kiran Abdallah yace “Mutumin ashe Gimbiya Rafi'ah ta shigo ganin ƴaƴanta wlh yanzu sukazo gidana da mijinta kaga yanda ta zama babbar mace..." Katse shi yayi da cewa “Kana ina kenan Abdallah inason a nemomin mata wlh zan zauce in ban samu me kula dani ba" dariya yayi yace “ya za'ayi na nemo maka mata Abdulƙadir ka aura da kanka ma ka kun kasa fahimtar juna..." Just please Abdallah na shiryu rashin Rayuwata ya bani darasi ta kasa barin raina ita kuma tana rayuwarta da mijinta da yaranta cikin kwanciyar hankali.
Jinjina kai Abdallah yayi yace “Ok kayi addu'a Allah zai baka mafita" godiya yayi sukayi sallama ya tashi da niyyar barin gurin daidai inda zai shiga mota yaga wata arniyar Jeep ta parker ya wani Balarabe ya fito riƙe da jakar mata a hannunsa ya xaga ya bude ɗaya ƙofar wata matashiyar Hajiya ce ta fito da cikinta tsoho idanun Abdulƙadir ya sauka a kanta itama shiɗin take kallo zuciyarsu ta buga da ƙarfi daidai lokacin da Deeny ya kamota yana zuba mata sannu yana cewa “Kinsan dake keɗin ta musamman ce yanzu ma twins zaki yimin Kinga haihuwa uku yara shida ko?" Inda take kallo ya kalla ganin wanda ke tsaye a wajen yasashi sakinta ya taka daidai lokacin da Abdulƙadir ya sauke wata ajiyar zuciya baitaɓa ganin dacewa irin ta Gwanar tasa da mijin nata ba lallai zare yana hawa ne da kalar yadi.




Jikinsa yayi matukar sanyi zuciyarsa ta karye yau kam ya cire rai ya sallama yasan ya rasa kenan da na biyar zata haifa mawa Deeny, a lissafi na gaskiya ko shine akayi masa fatan rabuwa da matar da suka haifi yara har biyar to ya tabbatar ansa son zuciya da buƙatar ruhi amma indai domin Allah za'ayi mai biyu manya shine ya dace da haƙuri ya rungumi hukuncin ubangiji.
Miƙa masa hannu Deeny yayi yana cewa “Barka Marshal munje gidan ai Hajiya tace baka daɗe da fita ba" amsawa yayi yana ƙaƙalo yaƙe yace “Eh wlh nakai yara ya gida da iyali" “Alhmdllh sai godiya dama cewa nayi bai kamata mu tafi bamu gaisa ba" jinjina kai yayi yace “Hakan yayi na gode Allah ya bar zumunci" gaisawa sukayi da Rafi'ah babu yabo babu fallasa domin duk sanda ta ganshi sai yanayinta ya juya ko kaɗan a nesa dashi ne takejin ta cireshi a ranta ƙosawa tayi su tafi fahimtar hakan yasa Deeny takaita gaisawar suka tafi ko a mota saida yanayinta yaso fallasa sirrin da takeson ɓoyewa ya dubeta duba na nutsuwa yace.




“Kinata farin ciki duk inda mukaje amma daga ganin Air Marshal gabaɗaya mode naki ya canza Kodai na ɓata miki rai da ganinsan"
Ajiyar zuciya tayi tace “Please Deeny kayi shiru" murmushi yayi yace “Nayi matar Deeny" daga haka babu wanda ya kuma cewa komai har sukaje hotel ɗin daya kama musu.
Anan suka kwana washegari da wuri suka bar Maiduguri suka ɗauki hanyar birnin Riyadh dake ƙasar Saudi wannan karon anan suka tsara zata haihu kwanansu bakwai ta haifi yarta budurwa sati guda suka dawo Canada rayuwarsu me cike da nutsuwa suke wanzarwa.
Wata ranar Laraba da yamma suna filin motsa jiki su da yaransu Ammy ta kirashi Mai martaba jikinsa ya tashi hakanan kwana biyu suka ɗauki hanyar dawowa suna isa sukaga gidan sarautar maƙare da mutane gabansu dukka saida ya faɗi suka kalli juna yayi saurin cewa Kabir driver “Kabiru wani abu ya faru ne?" Girgiza kai yace “Allah ya taimake ka bikin naɗin sarautar ka akeyi yau ya tabbata kaine Sarkinmu" haɗe rai yayi batare da yace komai ba yace “A juya" da sauri Rafi'ah ta dubeshi tace “Akanme Zaujh?" Baice mata komai ba ya kuma bawa Drivern umarni amma kafin ya juya Fadawa sun zagaye wajen daki kujerar yace.
“Banaso Ƙurrah Ni banason sarautar su wlh indai sai na cika sharaɗinsu ne Gara na rayu matsayin da nake su bawa Deeny second mana shi ai yanaso tunda dama matansa biyu dole saini Please Ƙurrah wlh wannan makircin na Ammy ne saboda tanata kwaɗaitamin nayi aure nace banida ra'ayi shine ta ɓullo min ta bayan gida"





Rungume jaririyar ɗiyarta tayi Hurriyah tana shafa mata sumarta ta haɗiye wani abu me ciwo tace “Saboda karkayimin kishiya shine yasa zaka saki gadonka? Lumshe idonsa yayi tayi murmushi tace “kar ka damu Zaujh idan kayi aure kawai burina ka zama adali idan zuciyata tana tuna uban ƴaƴana adali zan ƙara samun karfin gwiwa bayan haka Zaujh taya za'a tabbatar da nagartar me mace ɗaya, ba'a gane jarumin namiji kuma adali saiya auri mace sama da ɗaya anga yanda ya tafiyar da gidansa Zaujh ina maka fatan nasara"
Tana faɗin haka ta buɗe ta fita zuciyarta na mata wani mugun zugi kishin gado na shuwa Arab ya motsa tunda ta fito aketa yi mata kirari “Gyara kimtsi Giwar Mangal gyara kimtsi larabawan Afrika gyara kimtsi Uwar marayu masu arziƙin gado Takawarki lafiya Uwargida sarautar mata Kofa fitilar gidan sabon Sarki zuciya me motsi jini me kwaranya korama me bada ruwan daɗi, gaba salamun baya salamun uwar marayun Mangal...."
Duk wannan abinda akeyi zuciyarta bata da nutsuwa tana shiga ciki ya biyota daidai lokacin da Jakadiya ta iso da sauri gareta tana cewa “Allah ya taimaki uwar ɗakina jirgin Amaryar Sabon Sarki ya sauka kuma kece me masaukinta sannan har dake za'a tarota a airport..." “Waye ya tsara haka Jakadiya?" Zubewa tayi tana rawar jiki tace “Allah ya taimake ka Wannan tsarin Kilishi ne" cikin hassala yace “Kije kice mata bazataje ba inji ni..." “Aa Zaujh" ta faɗa tana juyawa wa Jakadiya hawayen da take ƙoƙarin shanyewa ya kwaranyo mata tace “Kice mata Ina fitowa da izinin Allah" juyawa tayi ta shiga ɗakinta ta ajiye Hurriyah ta juyo gareshi tace “Don Allah ka daina yimin haka Zaujh duk rintsi ka daina fifita damuwata fiye data Kilishi Allah maɗaukakin sarki yana cewa (Laƙad kalakal insana fih kabadin) aya ce a cikin Kur'aninsa me tsarki yake tabbatar mana cewa “Lallai na halicci Mutune a cikin wahala" Zaujh akanme don nayi farin ciki zaka zaɓi saɓawa mahaifiyar ka Ni wa na saɓawa cikin iyaye na akanka Zaujh ka bari sannan kai kasan Allah yace mana mu bisu akan tafarkin Allah da Manzonsa sannan kar muce dasu uffan don Allah kayiwa Ammy biyayya ba ita ta ɗorawa kanta ƙina ba kamar yanda kaima bakai ka ɗorawa kanka sona ba"





Jikinsa ne yayi matuƙar sanyi yanda take kukan ya firgita yanayinsa ta tsugunna ta riƙe ƙafarsa tace “A wajen mu mutane mutum biyu ne a saman ka Mommy da Daddy a wajen Ubangiji kuma kaine kololuwar daraja a wajena Ka haɗa siffofi da dama a cikin matsayinka guda ɗaya ka amsa aikin Uba, uwa, yaya, ƙani, ƙawa, dangi, sannan gaka miji uban ƴaƴana, Shamsunddeen don Allah karka juyamin baya kamar yanda Abdulƙadir ya juyamin..."
Ɗagota yayi ya haɗata da jikinsa yana shafa bayanta yace “Ina rokon Allah ya ɗauki rayuwata da ganin wannan rana Ƙurrah wlh ina Miki son fansar rayuwa ki yarda dani ki bini mubar ƙasar nan na bar musu sarautarsu bana ra'ayi bata dace dani ba Bazan iya adalci ba wlh koda magani Bazan so wata samanki ba Bazan zauna da Ummi ba Rafi'ah...." Rufe masa baki tayi tana Girgiza masa kai tace “Idan ita alkhairin zuri'armu ce Allah ya kawota da alkhairinta shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login