Showing 36001 words to 39000 words out of 72723 words
zame tace “Meye amfanin na ci gaba da son maso wani meye amfanin soyayyar da baasan inayi ba Abdulƙadir zai zamana nayi zuwan shantun duduwa duniya banji daɗin gidan iyaye ba banji na gidan miji ba nikam na gaji da wannan auren naka banyi maka komai ba kayimin hukuncin da kai kanka bazaka iya rantse wa akan laifin da ka hukuntani akansa ba Abdulƙadir ka barni nace ka barni wlh bazan koma gidanka ba ka zauna da ƙanwarka kawai ka barni zan nemawa rayuwata mafita...."
Duk da firgicin daya shiga jikinta na irin mugun kallon da yake watsa mata hakan baisata yin shiru ba saida ta gama ta mike tare da juyawa zata bar masa wajen ya kira sunanta.
Ƙin juyowa tayi har Saida ya kuma kiran sunanta yace “Indai akan ɗakin ki ne yanzu kizo mu shiga zata fita tabar miki ɗakinki hakan yayi miki?" Da sauri ta juyo tace masa “Aa Abdulƙadir a'a hakan baiyi min ba" duk jikinsa yayi sanyi idanunsa sun kawo ruwa ya tsani yayiwa mutum laifi yace ya barshi da Allah shi gara ka rama yaji a ransa ka rama gashi ita kuma batace masa komai ba akan dukan da yayi mata amma ta haɗashi da wanda idan ya tashi hukuntashi baisan da wacce siga zai hukuntashi ba wato Allah.
“Ƙwallar idanunsa ya goge yace “Ok meye kikeso Rafi'ah" kamar me jiran jewarsa tace “Ka fita daga rayuwata ka barni naje na samu irin mijin daya dace dani mijin da zaiji tausayina ya fuskanci naƙasuna ya zama adali a gareni wanda zaike min hukunci daidai da laifina ba irinka ba wanda yake hukunci da son zuciyarsa wlh na tsanek...."
Saki rufe mata baki yayi yace “karki ƙara cewa kin tsaneni bazan iya control kaina ba a karo na uku Rafi'ah ki juya mu koma gida saiki zaɓi wani abun banda wannan bazan iya ba wlh bazan iya yi miki abinda kikeso ba, Noor ko kin daina sona ni ina sonki"
*ASALIN LABARIN MU*
Ƙwanƙwasa ƙofar da taji anyi ne ya dawo da ita daga duniyar tunani ta share hawayen da yake zuba a idanunta ta miƙe tana gyara gashinta tace “Waye?" Can ƙasa taji ance “Raffy Nice" Wata ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi ta buɗe ƙofar suka rungume juna tace “Munirah kin tafi kin barni cikin bala'i tsayin wata shida na kasa samun nutsuwa don Allah ki bani mafita banason Abdulƙadir yaci gaba da bibiyar rayuwata don Allah"
Dafata tayi tace “Abinda ya dawo dani kenan nasan duk inda kike zaki buƙaci kasancewa dani yanzu ke me kike ganin ya dace muyi Ni inason sanin Meye yaci gaba da faruwa ne da ya sanyaki yankewa rayuwarki da masoyinki wannan tsattsauran hukuncin har kikejin daki ƙara rayuwa a kusa da inda zai iya ganinki ma gara ki mutu kowa ya huta, Ruffy Ni na amsa kira ɗazu ina shigowa Nigeria muka gaisa yake cemin na gane waye ke magana nake cewa a'a shine yacemin “Air Marshal Abdulƙadir Ibrahim Barzah ne akan layi" nasan sunan a wajenki amma jin muryarsa Saida tasa nutsuwar jikina saisaita ina shirin yin magana yacemin “Munirah kece ɗaya da zan tambaya labari akan matata ina nufin Rafi'ah ki hanzarta sanar dani inda zan ganta yau a faɗin duniyar nan, Please ban sanar dake sharaɗi na ba baamin ƙarya kuma ba'a min alaye idan na fahimci ƙarya a zancenki daga inda nake zan fasa kanki da bindiga babu abinda aka isa ayi saboda haka inajin ki"
Ji nayi bazan iya yi masa ƙaryar ba koda ace baima faɗamin sharaɗinsa ba take na sanar dashi inda kike kawai ya kashe waya can ya kuma kirana yace na turo masa International number ki na tura masa ban matsa daga inda nake ba naji alert na 3 millions nifa kaina ya kulle don Allah me yayi miki da ya kasa gogewa a ranki har haka"
Share hawaye tayi ta miƙe tace “Munifa da zuciya da ruhi na tsani Abdulƙadir wlh tallahi duk da ni ba jahila bace amma inajin abu ɗaya ya rage da zanyi idan yaci gaba da bibiyata Kinsan menene?" Girgiza kai Munirah tayi juyowa Rafi'ah tayi ta kama hannun Munirah tayi ƙasa da murya tace “Kisa Munirah!...."
Cikin kaɗuwa tace “What ubanwa zaki kashe Ruffy?" “Kaina Munirah na rantse miki Indai Air Marshal Abdulƙadir Ibrahim Barzah bai daina bibiyata ba zan kashe kaina ya huta nima na huta...."
“Girgiza mata kai Munirah tayi tace “Aa Ruffy haramun ne hakan don Allah ki daina faɗa" murmushin yaƙe tayi tace “Meye bai zama sila ba Munirah haramun nawa na aikata ta dalilinsa? Mafi munin haramun zina yasani nayita inama kan yinta Munirah bantaɓa bawa wani namiji kaina banyi kuka ba wlh bantaɓa bawa wani namiji jikina banyiwa Abdulƙadir Allah ya isa ba, to meye yasa bazan kashe kaina ba idan yaci gaba da bibiyata?"
Buɗe baki Munirah tayi zatayi magana ta daganta hannu tace “kiyi shiru bazan fahimceki ba idan kika takura min zan yanke alaƙa dake tunda kema ya fara biyanki don kiyi masa aiki akaina Munirah na rabu da mutane da yawa Sabodashi na ɓoye miki shi ne don inasonki saidai shi yayi nufin shiga tsakaninmu shiyasa ya sakaki a cikin lamarinsa yake kallonki matsayin wadda zata iya yi masa wani ƙoƙari"
Zama sukayi Munirah taja numfashi wayarta ta fara ruri ta duba “Air Marshal ta gani ta kalli Rafi'ah tayi murmushi tace “Ki ɗaga mana ai kwangila kika karɓa" Kin ɗagawa tayi har wayar ta katse ya kuma kira bata ɗaga ba can ya turo sako ta buɗe sakon.
_“Nasan kuna tare da ita yanzu haka ki faɗa mata Allah yayiwa Gana Hajja rasuwa ɗazun nan yanzu haka ina shirin tafiya Nigeria in zata tayi hƙr ta buɗe wayarta iya yanzu inason magana da ita"_
Girgiza kai ta soma yi tana furta “innanillahi wa inna ilaihir raji'un!" Miƙewa tayi ta lalubo wayarta ta buɗe tana buɗewa kiransa ya shigo ta ɗaga muryarsa a shaƙe yace “Zan jiraki a airport na gama shirya komai harda Munirah zaku taho" kashe wayar tayi ta ɗauki jakar hannunta tayi rolling ta dubi Munirah tace “Muje" “Ina?" Munirah ta tambaya" idanunta dake kan agogon hannunta tace Nigeria Maiduguri Munirah Gana Hajja tayimin gatan da Mommy na batayimin ba Indai zan tsaya kan gawar Mommy to shakka babu Gana Hajja tafi cancanta"
_Paid book nrml 300 VIP 600 special 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar first bank proof of payment 09013718241_
_*Oum Hairan*_
[11/17, 7:25 AM] OUM HAIRAN: _*AKWAI IRINSU...18*_
BHUZUWA EMPIRE
BHUZUWA EMPIRE
BHUZUWA EMPIRE.
Assalamu alaikum Al'ummar musulmi baki daya.
Kamar yanda ku kasani nice *buxuwa empire* wanda nake kawo maku kalolin mallaka da dama ga duk wacce take da wata damuwa ko matsala da take ciki tana iya bina ta private ko ta kira ta waya ..... Aikin mu babu kauce hanya da sirrorin Alƙur'ani mai girma muke duk wani Ayyukan mu .
*AYYUKAN BUXUWA EMPIRE*
1.munayin aikin bakar mallaka wacce muke kira bita zai zai , amma sai mun yi istihara mun bin cika Zuciyar ki .
2. Munayin aikin haihuwa ga wacce bata samun haihuwa inshallah da kinzo taskar empire za'a haske da buwaya na mai sama'u .
3. Munayin aikin bakar firraku wacce duk wacce a kai mashi sun rabu kenan har abada.
4. Munayin aikin da idan mijinki na biye biyen mata kina iya kimasa mallakar gabansa ki gama dashi , shi da wata mace sai ido. Wannan mazinata ake yi mawa ,idan kin san kina da kishiya da cutarwa . Na iya wanda mazan su ke bin matan banza a waje ake mawa .
5. Munayin aikin dafa'i na zallar Ayar ALLAH .
6. Munayin aikin farin jini a duk inda kk ko kuma na samari .
7. Munayin mallakar wajen a aikinku ko na office wannan na ma'aikata ne .
8. Munayin aikin aljannu musanman wanda aljani ya takura masa ko ya hanashi aure ko samun samari ko saurayin da yazo yau gobe ba zai dawo ba. Ko ya hana zaman gidan Aure .
9. Munayin aikin budi akan kasuwanci .
10. Munayin aiki a kan miji idan baya maka kyauta ko baya kula da kai da yara tare da ɗaukar hidimar ka . Maza taho Taskar empire kisha mamaki .
Sannan duk macen da takeso a zautar mata da mijin ta a kanta a mallake mata shi sai yanda tayi to akwai wani aiki da nasomayinsa wanda nake aikawa da turaren gari garii idan ki kayi amfani dashi komai nashi sai kinsani haka kuma komeye kike so sai ya baki. Amma sai mun duba zuciyar ki idan babu cutarwa .
*WhatsApp or call*
*08139762831*
Mata masu bukatar kaya da'a wato mgnn mata masu aiki da rubutu ko wanda ba mai aiki ba available maza ku garzayo gurin *Buxuwa empire* domin jin dadinku ma'aurata akan number ta dai wanda kuka sani gashi *08139762831*
Masu bukatar shuumin humra komai ya haɗa subhanallah wannan humra tayi wlh wlh wlh duk wacce tayi amfani da wannan humra mijinta wata ya mace ta burgesa an gma kuma, sannan da na farin jini mai kyau gaske wanda ake haska tauraronki mata ku garzayo wajen buzuwa empire domin kuji dadinku kuma godiya ga Allah
*BHUZUWA EMPIRE*
*08139762831*
_*18*_
Bin bayanta Munirah tayi taxi suka hau har airport ɗin suka shiga reception a zaune suka taddashi yana wasa da hannun Ablah Hisham ya kwantar da kansa a jikinsa suna hangota yaran suka miƙe suna tsalle Ablah ta nufota da gudu ta rirriƙe mata ƙafafu tana cewa “Mommy na inason zama a gurinki bazan sake zuwa wajen Daddy ba" Munirah ce tasa hannu ta ɗauki yarinyar tace “Fine girl ya sunanki" kwantar da kanta tayi tace “Nana Hauwa'u Abdulƙadir Ibrahim Barzah" idanunsa dake kan Rafi'ah tunda suka shigo ya janye ya miƙe yaja hannun Hisham sukayi gaba ita da Munirah suka bisu a baya nesa dasu ta tsaya har aka gama komai aka fara shiga jirgin Saida ya shiga Munirah ta shiga sannan itama ta shiga nesa dashi ta zauna batare da ko arzikin kallo ya samu ba ta ɗauki wayarta tana daddanawa ba komai take da ita ba kawai bazata jure yawan kallon idanunsa bane domin duk sanda ta ɗago idanunsa akanta suke batason nacin kallo musamman a wajensa.
Sunyi shigar dare sosai lokacin da suka shiga Abuja biyu saura hakan ne yasashi yanke shawarar suje gidanshi su kwana da safe sai su wucce Maiduguri nan taja turjiya tace a'a sun gode zasu nemi hotel, bai bata amsa ba sai umarni daya bawa drivern na tafiya dasu inda yace sudai basusan meye yace da drivern daya daukesu ba saida suka shiga unguwar Katampe Extension bata kawo komai ba kasancewar unguwar babba abinda ta kawo wani gurin hutawar ne Saida suka buga horn a wani arnen get taga an wangameshi baki daya gidan ya cika da haske lokaci guda duk da cewa daren me duhune kasancewar wata yayi nisa amma zaka ɗauka rana ce.
Parking motocin sukayi a gurin aje motocin suka ganin yanda sojoji suka kewaye motar ne yasasu kallon juna ita da Munirah daidai lokacin da Ablah ta buɗe idanunta tace “Wow! Mommy munzo gida" “Gida?" Ta furta a hargitse yarinyar tace “Yes mana Mommy Daddy yace daga yau bazaki ƙara zuwa ko ina ba zaki zauna mu rayu tare" da sauri tace “ƙarya yake muku Ablah Ni banida wata alaƙa daku Daddynku zai iya shine yace zai iya..." Buɗe musu motar akayi suka fito dukkansu suna kallon kallo ya tako cikin takunsa na isa ya miƙa hannu zai karɓi jakarta ta janye yayi murmushi yace “Har ƙarshen rayuwa bazaki ƙara fita daga da'irata ba Rafi'ah dama ɗaya tak nake buƙata ki bani kuskure na nakeson gyarawa"
Juyawa tayi zata fice ya riƙota tare da janyota jikinsa ta durƙurshe tare da cewa “Zan keta martabar ka idan ka Kuma taɓani Abdulƙadir ba don kai na baro uzururruka na na dawo Nigeria ba idan kuma dama ra'ayinka ka faɗa don cika wani burinka Please ka sanar dani inada abinda yafi haka muhimmanci"
Ya lura tsaf Rafi'ah zata tara masa sojojin dake kai kawo a gidan shine dalilin da yasa ya cillawa John key yace “Ka buɗe musu wancan part ɗin ɗaukar key ɗin yayi ya nufi part ɗin shikuma ya juya ya nufi ɗayan bangaren zuciyarsa a cunkushe yake damuwa neman sanya ƙoƙarinsa gazawa takeyi yanajin zuciyarsa tayi masa nauyi kamar shirin bugawa takeyi yana shiga ya faɗa gadon ko takalmi bai iya cirewa ba yayi flat yana hasaso rayuwarsu ta shekarar farko ta aurensu meye yasa bata dore a haka bane"
Daƙyar Munirah ta tausheta suka shiga ciki shimfiɗe Ablah Munirah tayi a ƙaton gadon dake daya cikin ɗakunan suka kalli juna sosai Munirah tace “Wato dole guy ɗinnan ya tsula tsiyarsa ya take ƙasa jibi wannan katafaren gida saikace a Turai dubi iyayen sojojin da suke karakaina don tsare lafiyarsa anya Rafi'ah mutumin nan bazaki dubeshi ba ki tsaya kiji dame yazo….."
Tsawar data daka mata ce ta sanyata haɗiye maganar tace “Karki kuma Munirah shiɗin waye ne wai me zai nunamin ne wannan yar ƙididdigaggiyar dukiyar da batafi wani sashi na dukiyar mahaifina ba ko kuwa kyawun da yake ruɗar ƙadangarun bariki dashi da yaza silar rasa farin cikina a lokacin da farin cikin nawa ya ta'allaka dashi? Munirah ko kuma Isa da kuma shaharar da yake ganin ta isheshi komai zata iya bashi damar take kowa kuma zata hanashi gane masoyin gaskiya Munirah ita ko nace su ɗin da suka hanani samun kulawa da nutsuwa a lokacin da nakejin banida wani daya dace da yazama mahaɗin rayuwata saishi da gaske bana ƙaunarsa wlh zan iya raba kaina da rayuwa akan na haɗata da Abdulƙadir ki bari karki sanyawa zuciyata kokwanto akanki ke bafa shi kaɗai ba dukkan maza na tsana"
Tana faɗin haka ta haura gadon ta kwanta Saida tayi addu'a ta tofawa kanta da Ablah sannan ta rintse idanunta tana tuno irin ƙuncin da Abdulƙadir ya ɗanɗanawa rayuwarta.
Washegari tun asuba data tashi sukayi sallah ta zauna tana azkar ɗinta bayan ta gama ne taji wayarta tana ruri ta tashi ta ɗauko number batada ita hakan ne yasata karawa a kunnenta “Muna jiranku" iya abinda ya furta kenan ya kashe wayar ta mike tana cewa da Munirah muna iya tafiya" dama dake Ablah tun asuba ta tafi wajen Maman yara.
Airport aka kai su suka hau jirgin Maiduguri motar haya suka ɗauka har gidansu kasancewar Abba shine gwamnan jihar na yanzu tun daga farkon shiga gidan ta fara haɗuwa da idanun sani yaran ƙannesa da suka santa suka fara rugowa suna ga Aunty Rafi'ah ga Aunty Rafi'ah" murmushi tayi musu tana rungumesu yaran duk sun girma taja kumatun Zahra tace “Yar lukata ta kin girma" turo baki tayi ta nufi ciki tana bubbuga ƙafa tana cewa “Ni Ni Mom Hisham har yanzu kinƙi ki daina cemin ƴar lukuta bayan duk na rame"
A harabar gidan suka ishe Abba suka gaisheshi tare dayi masa ta'aziyyah yace “Rafi'ah dama ana ganinki tunda kika gujemu shikenan saidai muganki a labaran magunguna ƙasa tayi da kanta tana wasa da ƙasa “Ai Abba insha Allahu ta dawo garemu kenan...." Wani mugun kallo data watsa masa shine yasashi haɗiye maganar ta miƙe suka nufi cikin gidan.
Saida suka gama yiwa mutane ta'aziyyah sannan suka nufi part ɗin Ya Hajja kowa mamaki yanda ta zama babbar mace yakeyi ashe da gaske dama zatayi ƙiba guri ne bata samu ba kai wasu ma basa ganeta sai sunganta da Ablah da Hisham yaran sun maƙale mata sunƙi barinta duk inda tayi suna biye da ita.
Sun gaisa da Ya Hajja ta zubanta idanu tace “Rafi'ah anya bazaki yiwa kanki faɗa ba nikam na rufe ido banga kyawun makanta ba ace da mutuwar aurenki shekara biyar har yanzu kin kasa tsayar da mijin aure shin tsoron me kikeyi bayan ba duka mazan ne iri ɗaya ba"
Murmushi tayi tace “Ya Hajja kenan ai komi lokaci ne" “Eh nasan lokaci ne amma akwai sawa a rai Rafi'ah ko kin ɗauka bansan yanda kika mayar da kanki bane wallahi nasan komai kuma ina takaici ina baƙin ciki daya zama sanadin Audu ne da nasan Audu da gaske bazai iya riƙe ki ba da tun farko ban bari anyi auren nan ba koda yake babu makawa sai anyi ko don zuwan Hisham da Ablah duniya.
Yanzu Ni kiyimin wata alfarma ɗaya don Allah Indai da gaske ne abinda kike faɗa Rafi'ah kiyimin alƙawarin daina karuwanci ko bazakiyi aure ba ki kame kanki ko don ƴaƴanki wannan abu yana damuna yana damu Audu duk sanda yaron nan yazo Indai zaiyi zance naki ne yakance shi dama mutuwa yayi da wannan baƙin cikin da yake neman yi masa kisan mummuƙe matarka mafi soyuwa a ranka uwar ƴaƴanka wai yau ita ce karuwar ƙasa da ƙasa kuma ka zama kaine sanadi...."
Numfashi ta sauke me ƙarfi tace “Nima ba farin ciki nakeyi da hakan ba Ya Hajja na zaɓi haka ne saboda haka na taso na gani na fahimci ashe nice na zalunci kaina da na horar da zuciyata kan cewa aure yafimin komai ashe aure yana zama komai ne idan kaso aka soka kuma ka sadaukar aka sadaukar maka Ya Hajja rayuwar yanci da Mommy tayita nunamin kenan na kasa fahimtar ta har nake ganinta matsayin wata mara makoma ashe nice mara makoma Ya Hajja....."
Ɗaga mata hannu tayi tace “shikenan Rafi'ah Kinsan dai nafi kowa murna a lokacin da Audu ya sakeki saidai yanzu ni nasan haƙƙin ki ne yake wahalar dashi ya kasa aure ya kasa zama guri ɗaya yau yana wannan ƙasar gobe yana waccan ya kasa barin yaran nan su rayu a waje ɗaya kullum shi kenan a canza musu gari da me kula dasu ya kasa nutsuwa bare ya samawa wani nutsuwa Rafi'ah Abdulƙadir yayi nadama ko bazaki dawo gidansa ba ki yafe masa"
Ɗagowa tayi idanunta cike da ruwa tace “Ya Hajja Ni dama ban riƙe Daddyn Ablah a raina ba tunda dai na samu na kuɓta asirina ya rufu amma kiyi hƙr Wlh bazan iya kuma rayuwa a ƙasan Daddyn Ablah ba har abada insha Allahu na gama aure ba nashi ba na kowa ma"
Bazata fahimceta ba shiyasa tace “Shikenan Allah yayi mana