Showing 99001 words to 102000 words out of 103712 words

Chapter 34 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7845

cikin kwanciyan hankali da iya gaskiyansa ke nan har kasan ransa baidai kaunar yarinyar nan zeey a rayuwansane.
Cikin tashin hankali da sauri ta dafe kirjinta tana fadin Hafiz kasan me kake fada hakane kuwa yarinyar nan fa yar uwarmuce ta jini ko banza muna alakan da zaisa kasota a ranka.
Yace kwarai kuwa na sani ai sanin da nayi din yasa ban taba jin ina son taba da kowa nata kuma bani fatan wanan ranan ma yazo da zance wai ni hafiz ina son ta
Kai ta sunkuyar kasa tana sauraronsa don tasan akwai wuya yasoni koya nuna kulawa a gareni nan kusa ta dago tana fadin hafiz wai baka hango babban kuskuren da kake kokarin tabkawa rayuwanka nan gaba.
Nifa haba Nafisat ya kira sunanta kai tsaye yana girgiza kai tare da fadin don Allah ki bari inma har kina tsamanin nan gaba yarinyar nan zata zamo wani abu har insota ki sani fa shi so a nan yake ya daki kirjinshi yace ba a goshi ba.
Na fadawa daddy wanan maganan dazun don mun zauna dashi munyi magana sosai yau kuma ya fahinceni don iyakar gaskiyana nafada kema kuma shi nake fada maki yanzu.
Amma ko ka tafka babban kuskure daka fadawa daddy wanan zancen haka kai tsaye don kafi kowa sanin laluranshi ta fada tana mikewa don barin gidan alokacin.
Har anty ta tafima ban sani ba don ni ina daki bansan wainar da suke toyawa ba a lokacin saboda nasa daya fitar suka gani doni nafishi jin duk abinda yake ji a kaina.
Don a rayuwana gaba daya yanzu na tsani in bude ido in ganshi ko inji an ambaci sunansa a gaba don shine mutumin dana fi tsana fiye da kowa a yanzu din.
Jin karan tashin motocinsu ya tabbatar min da sun bar gidan a lokacin kuma hakan na nufin ba mutum daya ya fice da mota ba a lokacin na dan jima kafin na mike na fito falon .
Tsaye nayi ina bin ko ina na falon da kallo kafin nayi ajiyan zuciya na taka na tattara kayam da sukai amfani daahi din saida na gyara tsab na saka kamshi na jawo kofan gidan na rufo da kyau na koma dakina na saka key.
Zan iya cewa na samu sasauci daga hattaranshi a yanzu don kowa harkan gabanshi yakeyi a gidan tsakanina dashi ballema idan na hada mai breakfast tun safe na fita bansan ya yake karasawa ba.
Haka zan dawo in samu gidan kaca,kaca in gyara da yamma ma zanyi abincin in aje masa in shige dakina amma haka zai dawo ya zauna ba kunya yaci ya koshi yabar min kayana a nan saina fito da safe in kwashe in wankesu.
Duk da haka rashin haduwan mu yana min dadi sosai don hakane damuwa da fargabana ya rage min don ko da zaran na fita su hauwa da karatuna zasu dauke min hankali sai idan na dawo kuma gidan zan shiga fargaban kada ya dawo ya sameni a waje.
Wanan yasa nake godewa Anty Nafisa don ina ganin cewa itace ta taimaka min har yake min hakan a yanzu don kafan da ya daga min.
Gashi kamar hadin baki yan uwa bamai zuwa wajena balle kira har baba idan na kirasa a gyrguje zamu gaisa dashi yace yana aikine banda dogon hira dashi balle inyi masa korafi.
Inda na gane bai gari wajen abincin daren dana kawo masane yadda na aje haka na samu abincin nawa na kwashe na gyarawa maigadi nayu masa dumamensa .
Da zan fitane na kula da motarshi baya gurin da yake ajeta maigadi na tambaya shike fada min yana ganin kamar yayi tafiya don ya gansa da yar jakka ya saka a mota.
Hakan yayi min dadi sosai saidana dawo school na bata lokacina na tsaya nayiwa gidan kwal na goge kujerun da ties din kasan har kitchen ga irin watauna don ina ganin kamar ina cikin kayan giyane a zaune.
Rana sati kuma har lokacin bai dawo ba na kara bin gidan nayi mai gyaran gaske saidai da kuskure ban yadda na taba bangaresa ba don gudun sheri irin nasa.
Hankalina kwance nake gudanar da komai don ji nake kamar ancire mun kaya ajikina ga rashin zamansa gidan kira,a na kunna ina zaune falon ga tashan African tv three na aiki a lokacin naji sallaman mum kamar a mafarki.
Da murna na tashi na tareta sai bayan nagama rugumantane kuma na saketa ina fadin mum wallahi nayi fushi mum kamar kin manta kina ya a nan ?
Dariya tayi tana fadin ja,ira kin taba ganin uwar data manta da yarta inba shirmenki ba ko yanzu ai son in ganki yasa yau na roki Alh daya barni inzo in ganki don nasan yau kina gida.
Mum dama daddy ke hana kowa yazo gurina ke nan tace to inya hana ai daidaine tunda mijin ki yana gari yanzu ko da bainan ai kinga nazo da kaina ban aiko kowa ba.
Mum wani miji kuma don Allah ?
Ni ban masan baya nan ba wallahi nidai na daina ganinsa kawai hakan yasa nayi tunanen ya kara gaba ke nan kuma.
Wani irin zance kike fadi mama kina matarsa har yayi tafiya tsawon kwanaki kice baki san baya garin ba wanan wani irin rayuwa kukeyi a gidan naku ?
Shiru nayi don ganin ta kura min ido tana son taji wani abu a gareni hakan yasa na dukar da kaina kasa na daina kallonta.
Tace yanzu shi da zai tafi bai fada maki zaiyi tafiya bane kome toni mum ina ruwana dashi mutumin daya fada gabana ya fada a bayana bai kaunan ya bude ido ya ganni balle a kirani wai da matarsa .
Mama kina son Allah ya konaki ne akan hakkin aure kome ta fada tana lafeni da idanu cikin canza yanayin fuskanta lokaci guda na dan turo baki gaba ina dukar da kaina.
Tace komeya fada ai ruwansa ke dai ki tsare hakkinki duk abinda kikasan mace nayiwa miji kada ki fasa ki masa sai ya saura gareshi amma ba ku taru ku halaka kanku haka ga banza ba .
Mum ina fa girki dashi kuma yana ci ai nayi kokari ban fita gidan nan sai nayi masa girki na aje mai kuma koda zan dawo zan samu yaci haka kuma ina gyara gidan nan sosai ko yaushe,,,
Ke arr rufe min bakinki wurin nan kada inzo in mamareki an fada maki yin girki kiba miji shine kawai abinda mace zatayi ta burge mijinta ?
A gabanki nake shiryawa na wuce dakin Alh kin sani ba baki sani ba zaki min wani zancen girki can da da baki auresa ba an fada maki baya cin anincine kome ?.
Gaskiya kin ban kunya dama nasan harda laifinki cikin wanan abin don da acebkin nuna masa ke mace ce kinsan kanki dole ya sauke wanan iskancin nasa.
Kafin nayi magana saida na daga na kalli kofan dakin nasa kamar zaifito yaji mezan fada a lokacin nace mum cikin shagawaba anty Nafisa bata fada maki furcinnsa a kaina bane wai sai hawaye .
Furucinsa waina banza mama sau nawa akayi irin wanan muna gani kuma ana tare an hayayafa a tsakani idan zaki natsu ki nasu mama ki maida kanki mace tunda ba haka zaki tabbata ba har abada kuna wasan boya a tsakanin ku.
Watanku nawa da aure yanzu na takwasa kuke nemafa ke nan a yadda naji Asiya tsohon cikine da ita niki niki hakama mairo ance cikine itama da ita.
Sai kece zaki zauna haka don baki san ciwon kanki ba kowafa hakkuri yake da auren nan da yaran da manya kuwa duk auren aiba wani dadi garesa ba kowa yasani amma haka ake daurewa da wullakancin dana miji don kowa raminsa yakewa dama.
Sai kawai naga ta mike tsaye a cikin fushi tana fadin inzaki gyara ruwanki mama ni kinga tafiyana tasa kai ficewa daga gidan da sauri na mike ina bin bayanta tare da bata hakkuri kada ta tafi.
Saida muka kai kofan fitane ta juyo tace min saurara kiji muddin kina son mu shirya dake to kibi maganata ko hafiz na dukanki kiyi masa biyayyan aure yadda Allah ya hallata muna yi mu mata kinga tafiyana.
Ta fice ta barni tsaye sororo ina binta da kallo har saida naji tashin motanta na sauke ajiyan zuciya ina tambayan kaina anya mum tana min son gaskiya kuwa ?
Idan ba hakaba tayaya zata umurceni da zuwa wurin wanan kaskantacen da baisan darajan ya mace ba baisan na iyayyenshi ba balle na wani kila dai so take a kwasoni a karye ranan.
Haka kawai naji gaba daya na koma wata kalla nayi tunane iri iri a zuciyana ta ina zan farane da zancen mum kai ni dai gaskiya sai ince banyi dacen zuwa duniya ba a gaskiya.
Kuka sosai nayi ranan don tun ina na zuci har na koma yi na fili ina maganganu ni kadai kamar tababa a cikin gida ko abinci ban iya tashi na girkawa kaina ba.
Monday na shiga school tun haduwan mu da hauwa take korafinnko nayi ciwone during weekend don na fada sosai lokaci guda murmushi kawai na iyayi bancewa kowa kome ba na barwa cikina zancen yana cina.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3?? 2??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Zaune nake nayi tagumi na zurfafa a tunane bayan fitar malam dake daukan daga ajin don cewa da tayi zamu fita practical cikin wanan satin.
Ajin kowa na surutunsa akai ni kuma nayi shiru ina tunanen a zuciyana wanda ya shafi rayuwata a yanzu dama kowa da bukin zuciyasa akace.
Dafani da hauwa tayi yasa na sauke ajiyan zuciya mai dan karfi ina kallonta take fadin kaga manya ba tana can tana tunanen yadda zata fara fida.
Dan murmushi na sauke a saman fuskana ina fadin fidan me kuma anty na tambayeta alaman dai bani tare dasu tace yau ga tsiya me mrs buhari ta fada yanzu kafin ta fita nace ai banjita ba anty .
Banma san tafita ajin ba tace akwai matsala dama na fadi tun Monday yanayinki yake ba daidai ba zainab niko meke damunki hakane har kina batun fita yanayinki lokaci daya?
Lekowan da Rashida tayi tana dan kallon fuskana tace nifa na gane yariniyar nan aure take so ai mata duk kaga yarinyar na irin wanan raman manya sunce aure take so.
Dan wal nayi da ido ina fadin aure kuma Rashida aure na nawa kuma za aimun yanzu lah kinji ko ban fada maku ba ta fada cikin zolaya.
Murmushi nayi ina kawar da kaina gefe daya nace ni ai na dade da aure Rashida ko bakiga alaman aure bane tare dani na fada ina mikewa tsaye don bana son dogon magana a lokacin.
Bangaren mum kuwa a yanzu tana cikin damuwa kan zaman danta Addil da matarsa Aisha wace zamane na zamani mace ke juya miji yadda ranta keso agaban kowa kuwa zata bashi umurni .
Shiko bai dauki hakan komai ba zai bi umurnin nata a ganinsa duk cikin sone da kauna yake hakan gareta wanda su kuma mutane suke ganin ya koma mijin hajiya a lokacin.
Dayawan maza haka suke da sanyin rai amma mutane yan gaza gani zasu fassara hakan da an gama da miji don baida nacewa sai abinda mace ta umuceshi dashi kawai.
Wanda zancen har ya dawo kunnen iyayye ba kunnensu kadai ba don ko a gabansu sunsha ganin hakan sai abin ya fara damun mum don yawan tsegumin da akeyi kan hakan.
Missalin abubuwan kuwa shine agaban kowa zaice su bari adan kara time su tafi zatace No katashi mu tafi yanzu dai sai yabi umurnin ta din ya tashi a lokacin.
Ko kuma yace daga nan zamu wuri kazane sai matar tace ni bazanje yanzu ba hakan kuma zai tabbatan don ba za,aje gurin ba kamar yadda tace abubuwa da dama suke faruwa irin haka wanda su basu daukeshi komai ba a wajen su amma gun mutane hakan ya zama abin magana a garesu.
Sauda yawa hakan yana faruwa tsakanin ma,aurata sai a dauki hakan fin karfine kawai ga matar tashiga gaban mijinta ke nan sai abinda tace za,ayi a gidan .
Don hakane akeson sayawa agaban mutane don hakan ba wayewa bane zubarwa miji mutumcine agaban mutane kome zakiyi kiyishi a tsakanin ku biyu amma matan yanzu basa gane hakan yana ja masu illa ga aurensu sai suyi tunanen kome sukayi sunyi daidaine su.
Amma mutane saisu dauka cewa magani ko asiri matan sukewa mazan su gama dasu sai abinda sukace shine za,ayi duk da akwai dayawa masu hadawa da asirin don su mayar da mazajen nasu haka.
Ita kan Aisha wanan rayuwan yacita don ko babu kauna ko so tsaksninta da yan uwan miji datakewa gani gani a yanzu tana ganin dafisu miji mussanman anty Nafisa da sukasha soyayya dashi a baya na yarinta.
Gashi sun camfata cewa bata son yan uwa su rabesu don zata nuna bataji dadin zuwan dan uwasa garesu ba ko ta nunawa bakon mugun halin da zaisa ya bar gidan ba shiri.
Idan ana irin wanan maganan abin yana konawa mum rai sosai har wani lokaci takan kira dan nata ta fada masa maganganu aka matar nasa wanda baisan dalilin hakan ba.
Abu goma da biyu ya taruwa mum akanta ga zancena da hafiz ga kuma zancen gidan ya Addil dake son yafi karfinsu a yanzu don irin korafin nan yasa yanzu ya dauke kafanshi da kano tun bayan aurena da duka zo sau daya yazo bai kara zuwa ba har wanan lokacin.
Dama ance idan gida yai kyau hakan na samo mafarine daga jajirtatan uwar gida ko mai gida dole sai daya ya jajirce zakiga gida ya kafu har ya tsaya bisa tubali mai kyau.
Dayawa sukan dace da hakan a da zamanin baya namiji zai jajirce ya tsaya a gidansa yayin da mace ita kuma zata tsaya ta kafu ta taimaka masa wajen ganin gidan ta tafiyu a yadda tsarin yake.
Saidai a yanzu zamani yazo da wani nau,in da mata ke mulkin gida da kansu ciki da waje sai abinda mace ta tsayar ne umurni an kaucewa tsarin addini da karfi da yaji saboda boka mata sun koma juya gidajensu ba maza ba.
Wanan yake yawan kawo baraka a cikin al,umma inda dangin miji zasu shigo hakama wani lokacin dangin macen ba za,abarsu abaya ba sai zaman ya koma gashi nan dai agidan ba wani tsari maikyau da za,ai koyi dashi a wani gidan.
Wanda hakan yana cikin abinda ya taimaka wa yawan sakin aure a yanzu zakiga an koma tsarin zaman waje yafi dadi ga ma,auratan an rabu ana son juna bisa kan son zuciya da kaucewa ubangiji akarshe a koma a zaman waje kuma ana yadda badala a cikin al,umma.
Ya ubangijin Allah kasa mufi karfin zuciyar mu mu zauna a saman tsarin addani yadda ubangiji Allah da Annabinsa suka sharada muna muyi damu da zuri,an mu Amin ya Allahu.
To ankai dai inda ba,aso don ko har yakai Dada ta kwashi kafa zuwa gidan ya Addil din dake Abuja da sunan zuwa asibiti saidai ba,asha da dadi ba a zuwan nasu don ko sun sha tarin takaici da bakin ciki a gidan.
Ga rashin kulawa fa kuma yunwa ba zasu karya ba sai shadayan rana lokacin data gama barcin safen ta rafito lokacin zata tsaya girka masu abinci su karya hakama na rana zasu dawo asibiti a wahalce amma ba zasu samu abinci a gidan ba.
Sai dan kayan kwalaman zamani acewanta mijinta baya zama a gida don haka bata girkin rana da dare kuma sai wajajen tara za,a kammala abincin da zasuci.
Wanda suka dawo kano da takaici da bakin ciki wace ta je neman kafiya wani ciwon yunwa kuma yana son kamata a can sun dawo baki na fadi cewa ga abinda akai masu agidan.
Har yakai daddy ya kasa hakkuri ya dauki waya ya kira yaya din yai masa kaca kaca inda ya nuna baisan hakan ya faru ba don shi ba mai zama bane a gida.
Karshe da yaiwa matar magana fada ta hauyi tana fadin wanan yasa bata son yan uwansa suzo don basu zuwa sai sun samu sherin da sukaiwa mutum idan hakane kada wanda ya kara zuwa mata gida tunda gulma ke kawosu gashi yanzu anzo an mata munafuncin da akasaba kulla mata duk kokarinta akansu.
Tas,tas ya kwasheta da mari saida takai ga shirin faduwa a karo na farko daya taba lafiyan jikinta yace ahir dinki wallahi yana fadin ashe baki da mutunci Aisha kakantawace munafuka ko matan babana kike nufi ?
Ashe baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login