Showing 60001 words to 63000 words out of 103712 words

Chapter 21 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7861

yar uwarshi kukan zuci mai yawa.
Albarka yasha shi wurin kowa wanda bakin mummy ya mutu mutus da ganin kayan idan ba dan gida ba yadda kowa ke fadi idan yashigo yaga kayan zasu tambaya wanan kayan sunane ace masu ehh.
Zakiji sunce gaskiya yayi kokari haka akai suna kowa na farin ciki da yamma akai walima anci ansha an raba abubuwa kamar ko wani suna aka watse.
Da daren kuma wanan budurwan nasa ta zowa jariri da nata gudun mawan shake da leda don ko Pampers har hudu nagani a cikin kayan.
Ranan kuma bata tafi ba saida tabi su mum ta gaidasu taba kowa turmi daya daya har Dada wai na fitan suna wanda kowa yasan aiki ya Addil ne hakan.
Sani mum bata so yasa hjy mummy kama zancen kamar da gaske wai danta yayi dace da mace ta gari gaskiya wanda kowa yasan bana Allah takeyi ba hakan da takeyi dayan biyune.
Ko dai don rufawa yarta asirine da yayi ko kuma akwai abinda take kokarin kullawa gareshi nan gaba don danin halin mummy din da kowa yayi.
Mun dora abubuwan shagalin sunan da akayi wanda har ita maijegon ta dora hakan yasa shi uban dan gani a status dinta har yabi bayan kwana kamar ukku da suna saiga yan gidansu sunzo.
Da nasu kayan suna wanda ba wani abin azo agani ciki kuma wai sunan da Sani sunan kakansa Dada ko ta hausu tace su dauki kayansu su tafi yaro ya rigada yaci sunanshi dama mohammadu daga iyayyensa masu kaunarshi.
Mum ce tasaka baki har suka danji sanyi aka karbi kayan da sukazo dashi din daga bangarensu suka tafi tsomai tsomai dasu da kunyan da dan uwansu yaja masu.
Haihuwan nan na anty Nafisa yasa innan mu zuwa gidan akai akai wanda zuwanta kusan uku duban maijego da danta bayan suna kuma suka dauke kafafun su don gudun magana.
Ganin angama shagalin buki lafiya yasa na mayar da hankalina kan karatu na da yanzu saura kiris mu kare gaba daya mu fada wani matakin a yadda nakewa kaina fata nan gaba.
Don ganin yadda su Mairo suka maimaita shekara yasa ko ysushe ina addua Allah ya taimakeni inketare nawa ba tare da tabgardan komai ba

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/17, 08:02] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2?? 0??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Alhamdullahi zance a yanzu don duk wani challenges din rayuwa da nake samu a gidan daddy hakan bai hana in tsaya inyi karatu ba don ko naga abubuwa kuma naji da kunnuwa amma haka na daure na fuskanci karatuna.
Sai gashi Allah ya taimakeni na fito da sakamako maikyau da har daddy din ke alfahari dani akan hakan wanda wanan abin a wani bangare yayi min dadi wani bangaren kuma baimun dadi ba.
Don ko yaja min bakin jini a cikin gidan sai bangaren mune kuma suke nuna min farin ciki sosai a kan hakan suna yabawa.
Mun gama da sati biyu lokacin akai bukin auren ya Addel wanda asha kwama cala a lokacin bukin don hjy malka ta dauka cewa daddy ne ke masa hidima wanda hakan har ya kaisu da zama da manya akan bata yarda da abinda Alh yakeyi ba tunda shima yana diyan daya haifa da cikinsa.
Hjy malka bata da kunya ta ido Daddy baiyi magana ba saida yace a kira hjy mum don abune daya shafi family tazo dashi don haka suka bukaci da mum tazo falon a zauna da ita.
Bayan mum da Dada sun shigo daddy ya kalleta yace hjy kubura ina son ki fadi tsakanin ki da Allah ya mukayi da Aliyu kan zancen aurensa daya nace sai wanan yarinyar .
Kallonshi tayi cikin mamaki tunda abin sirine daya shafi ahalinta a lokacin yace maimaita don Allah mum din ta dan gyara zama tace ehh to kace ba ruwanka da zancen auren iya sadaki zaka biya masa tund yaki bin akidarku na gida sanan bayan hakan yasani zaka kara mai mata muddin ana raye yar gida kamar yadda yake ga al,adan nan gida lokacin zakai masa naka auren kamar kowa .
Hannu ya daga yace ya isa haka kunji ko bayan wanan me suke shiryawa me suka hada wallahi ban sani ba kayama da kike zance nasan akansane ga hjy kubura ta gaya min nazo nagani sungama hadawa nace sukai Allah bada sa,a koba haka akayi ba ke kubura ?
Allah da Annabinsa sunyi gaskiya da sukace zato zunubi koda ya zamo gaskiya a wajen bawa kin daiji hjy malka ba hannun Alh a wanan zancen ashe .
Daddy ya dauka da fadin jiyan nan yazo yana fada min cewa yasai gida a Nasarawa nima da mamakin hakan na kwana a raina.
Saidai banyi mamaki ba duba ga inda yake aiki yanzu a matatan mai na kasa koda yayi hakan zai iya yin fiye da hakan ma idan yaso.
Wani gwauron ajiyan zuciya mummy ta sauke dayan babansu yace ai a haifi da arziki yafi a mutu abarmai gado wanan gaskiyane kowa nan ya sani.
To amma waya dorashi a hanyan hakan ai kaine dai Alh kana da daman yadda ka samu nashi aiki a nan wurin samu suma sauran ka sama masu ai kamar yadda shima kai masa hanyar.
To ban samoba din don bansan inda ake samuwa ba ko kina nufin sai kin jefawa diyana kiyayyana dana dan uwansu a kanmune kwadan ki zai fada.
Bansan ya yayi ya samu abinsa ba illa takarda daya zo muna dashi gidan nan na aikinsa danki dana samuwa aiki ai rainaw kukayi ashe hangen nesa kuke masa wayasan na samuwa hafiz aiki a gidan nan bayan ke ?
Ko ita kuburan bata da dan dana haifa da itane da yake son aiki baga Nasir nan zaune a gida ba shima ya gama nasa karatun ?
Yanzun dai abar zancen tunda angano gaskiyan yadda lamarin take kowa yasan yadda zuciya take bata da kashi ke hjy malka kinyi kuskure ai kafin ki taramu nan yakamata ki tambayi mijin ki yai maki bayanin komai.
Kona tambayesa aiba fada min gaskiya zaiyi ba don haka na kiraku a nan hjy mummy ta fada cikin jin nauyi da kunya da batayi tsamanin zai koma a kanta ba lokacin.
Ba zan fada ba tunda ita yar uwar zaman naki bata taba tsareni kan harkuku tasani a gaba ba duk da tasan ina tauye ta wani lokacin ta barmu ga Allah dani dake.
Baba kun gama dani in tafine mum ta fada tana mikewa don takaicin daya rufe mata idanu lokacin Dada tayi magana tace ina zaki ai ki tsaya kisha labarin irin cin zalinki da sukeyi a gefe daya tunda yau ranan tonon sili a garesu.
Murmushi Mum din tayi tana fadin niga Allah na dogara don shine gatan mu nida yaran nawa duka tana fadin hakan ta juya ta fita nan yan uwa dasu Dada suka hau kan mummy din da fada akan bata kyauta ba tana hassada da dan yar uwarta kan duniya.
Akarshe dai dole taba daddy din hakkuri su babanane suka samu mum a part dinta suka bata hakkuri akan abubuwan da ake mata gidan ana danne mata hakkinta din.
Inda daddy Enugu yake cewa ai gashi duk sukayi sai abin ya koma tsakaninsu duniya tajisu akai ga tonawa juna asiri da sukeyi akarshe kowa yajisu.
Yanzu kan da buki yazo suga irin hidimar da akeyi a part din hjy mum sai bacin ran ya yawalta daga ita har yaranta suna nuna bakin ciki kan abindake faruwa agidan suna kallo.
Saboda basu taba zato ko tsamanin hakan ba daga bangaren hjy kancewa wani daga part din cikin yayanta zaizo ya shayar dasu mamki tun ba,aje ko ina ba a rayuwa.
Allah ke nan kadogara dashi ya jarebaka ta nau,in rayuwa a hanyoyi daban daban akarshe inkayi mai imani da yarda da kaddarace sai ya sakama a ta hanyar da baka zataba haka ubangiji yake lamarinsa a inda yaso.
Abu namu maganin a kwabemu bukin mune bukin part din mu gaskiya ko a sanka wajen daya ashe asalne mai kyau sanina a yar mum kwara daya datakeji dani na zamo kamar igenta inji hausawa yasa min farin jini ga masoyanta dama kowa mai kaunarsu ita da diyanta.
Wanan daman ya haskani a idon mutanensu na arziki inda wasu ke dauka koni din ma diyar cikintane ai wanda suka sani kuma suke daukata da daraja a idanunsu na zamana a wajenta.
Haka zama din ya kulla wani halaka mi girma tsakanin mum da mahaifiyata da yanzu shawaransu guda kasancewan su gari daya da aka fito.
Hakan yana taba zuciyan hjy malka da har yakai tanawa inna tuhumar dabai dace ba kindai san yadda kishiya kan zargi duk wata wace ke tare da kishiyanta koda kuwa tasan ba wani abin asha suke gudanarwa ba ga amintakan amma wanan kishin yakan koma ga aminiyar kishiyan a hada da ita.
Buki yayi kyau sosai anyi program kamar na sauran buki anci ansha an koshi a taron baki sunzo daga gida anyi kara ga hjy mum da mijinta marigayi daya rasu har na da bangaren daddy kowa ya koma gidansa lafiya aka bar amarya da ango da halaiyansu da zasu fahinta a zama yanzu tunda an zama daya.
Kamar yadda manya kance so ya kare sai zaman hakkuri duk wace tayi aure sai an rakata da wanan kalman walau a ciki musulmi ko kirista kalman dai dayace da ake fada kan a zauna lafiya kosu shi aka fada akansu.
Dan anty Nafisa yayi wayau sosai haka yasa ta fara neman aiki da zata dan fara kafin abubuwa su koma mata daidai arayuwa.
Inda tayi sa,a inda ta fara aiki a B U K suka kara daukanta aiki karo na biyu don tana da hazaka sosai akanta lokacin ilimi ake nema ba nasaba ba kamar yanzu donshine bata sha wani wahala wajen komawa aikin ba.
Hakan yasa tunda muna gida bamu fara karatu ba renon danta Amir ya dawo kaina da farko mummy ta hana hakan sai daga baya data kula ana bar mata da a wahalce ta daukoshi take kawo muna part din mu inda bai fita sai idan ta dawo da yamma an masa wanka akai mata abinta washe gari haka kuma idan zata fita zata kawo munashi.
Ni da mum ke faman dawainiya da yaron da yanzu yayi kyau sosai saboda kulan da yake samu a wajen mu din.
Inda yakai har yaron yana neman ya yaye kansa daga nono don ko uwar ta dawo daga aiki bai damu da nono ba tunda yana da koshi hakan yasa itama take neman yayeshi din lokacin.
Nan kuma mummy ta kawo tsurkun cewa a daina dura masa abinci abarshi yasha nononsa ya koshi sai a kama karamin yaro ana dinkira masa abinci har yazo yai masa illa kuma a karshe.
Zance wasa wasa har yakaisu gaban daddy don mum tayi fushi da kalamin hjy malka inda tace daga yau idan anty zata fita ta barshibgun hjy malka din don kada a kashe mata yaro a nan din wajen mu.
Fafir ranane taki karbanshi ta kuma hanenima karbansa tunda kona karbeshi ai dole a part din tae zan zauna dashi ganin irin rikincin da uwar keson jefata ciki yasa kai tsaye ta samu daddy afalonsa ta fada mai abinda ke faruwa ranan.
Baiyi kasa a gwiwa ba ya kirasu suka sameta tsugune da yaron gabanta da alaman har kuka tayi a gaban daddy din kan abinda ke faruwa dasu nan ya bukaci ta kara fada mai matsalan ta kara maimaitawa a gaban nasu.
Kafin takai karshe uwarta cabe zancen da fadin kalai kan angama dake baby ta yarda baki iya fita inbaki arziki ba nan gabama kina iya cewa ni ba uwarki bace.
Zancen banza ke nan ana magana zaki dauko muna wani zance can ki jefo cikin magana ita zancen danta da hjy kubura tace basu karba tazoyi ke kuma kina kawo muna wani zance a nan.
To Alh banda haka tunda tace basu karbanshi ita bata da uwace ko ba masu daukanshi a wajena idan ni banda lokacin hakan yace ballema kina da lokacin me zai hana ki kula da dan yarki kuma.
Tunda kin rai karan da ake masa can sai lokacin ta gano ba goyon bayanta daddy yakeyi ba ashe magana ya fada mata a dunkule ashe .
Yace ke kin gaza masu kula dashi kuma kina kokarin zarga masu sherin ki da kika iya akansu ko nine aiba zan karbeshi ba ko kin manta lokacin da take bar maku yarin kuka tashi illanta matashi ?
To baby abinda kike nema kin samu a tozartani gaban kowa yanzu kin samu ai saiki zuba ruwa kasa kisha ke nan kanki aka fara haihuwane da baki da kunya ko kadan akan danki ?
Ai bata yar ba don tarbiyan data samu ke nan gara itama tana kara da har ta amince tana kaishi wajen su kubura ko kin mantane in fada maki yanzu ?
Abar zancen nan ke Nafisa kiyi hakkuri kibi zancen mahaifiyarki a zauna lafiya nidai Allah ya gani ko ina sheri banga abinda zai kaini cutawa wanan da mala,ikan Allah ba don Amir har meya sani.
Jin mum din ta kira sunansa yasa yaron yasake nonon dayake sha ya taso zuwa wajen mum din ya haye jikinta daddy ya kwashe da dariya yana fadin duba yanzu ki gani don Allah.
Don Allah Dad aba mum hakkuri ina lantti zuwa wajen aiki tayi hakkuri subar zancen nan a karban manshi tunda dasu ya saba anty Nafisa din ta fada tana kallon mahaifin nata.
Ni banda matsala kin sani abin zargi ko tuhumane banso a rayuwana in bashi ba mai zai hana in karbi Amir to ki karbeshi tatafi gun aikinta daddy ya fada a cikin bata umurni a lokacin.
Yace mika mata kayanshi ki tashi ki tafi hakan tayi kamar yadda daddy ya fada din ta mike tana masu saita dawo yaron bai ko kulaba yana jikin mum kamar yadda ya saba yana wasanshi.
Bayan fitan anty Nafisa daddyn ya kallesu yace waike malka sai yaushe ne zaki barmu a zauna lafiya a gidan nan ko sai ranan da hafiz yayi aure kikaga kin kai ga sarakuwa zaki daina hakan .
Ai ba gatse don yadda kowa yayi aure shima din yi zaiyi insha Allahu balle aso fada min magana a fakaice haka niko nasan yi zaiyi tunda nike da dana da ikonsa sai ta kalloshi.
Mun na ganin haka ta mike da yaron tana fadin muje in kaika wajen uwarka ni islamiya zan tafi yanzu bata tsaya jinsu ba tafice abinta nan sukayiwa juna kwal suka kuma shirya.
Nikan ina barci nake jin alaman ana tabani don daga kwanciyan da nayi na boyewa anty Nafisa kar in dauki yaron sai barci yayi gaba dani a dakin mum din.
Na dinga jin ana dan tabani sama sama ga nauyi da dadin barcin safen daya daukeni haka na kama tsinkayo gwalancin yaron a gefena.
Idona na bude da kyat ina fadin kai kuma ina ka fito nan mum dake tsaye tana saka hijab tace dani gashi nan dai maki ai uwarsa bata yarda ba ai takai karab mu wajen daddyn kune.
Da yake uwarta bata da kan gado can na barta tana babatu nafito don kada shirmensu da bai karewa kullum yasa in makara ban fita ba tara ya kusa yanzu.
Zaune na mike ina kamo yaron zuwa jikina nace kai matsalan mum harda yaro duk wanan wahalan ita bata gani sai kuma zargi da sheri ya biyo baya.
In batayi ba ai bata jin dadi munta fada tana daukan jakkar hannunta bata da kunya ko yanzu a falo sai shirme da rashin kunyavtake zuba min wanan ina tausayawa wanda zai zauna da ita wallahi.
Shiru nayi na dan lokaci kafin tace sani nina fita abincin ki yana falo yau dan wake nakecson in mun dawo muyi akwai komai na tanada jiya na sayo kayan hadinsa a islamiya.
Sai kin dawo za,ayi din na tambayeta tace ehh to ai ina zaki iya kwabinsa ko karki manta ki saka kuka dan madaidaici da zai isa saiki kwaba ki bashi madaransa a daina bashi abinci tunda shine basu so.
Kallon yaron nayi ina shafo kansa nace wanan aiko ban bashi ba shi zai saka hannu yaci da kansa indai abincine wanan madaran yanzu bai masa ai sai an hada mai da abinci.
Ai gaku nan dai ta fada ina mata adawo lafiya shima yaron ya daga hannu alaman bey bey a gareta na kamo hannunsa ina dariya tarw da rungumesa a jikina ina jin son yaron yana shiga zuciyana.
Falo muka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login