Showing 27001 words to 30000 words out of 103712 words

Chapter 10 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7863

Ance kaso kanka duniya taki ka haka kaki kanka sai duniya ta soka nako sheda wanan karin maganan don ko nagani ga halima da hjy mum din don sai tayi min abu kiri kiri tabar halimatu din.
Tun zuwan mu na sance jiki nakoma wajen su halimatun dake min wani kallon mamaki don bata sanni da wanan kayan ba gashi kuma ta ganesu a jikina.
Nan ta fara fadin kaji yan kyashan na mane da sarki banda wanan basu iya daukaka rayuwan mutum sai idan yana masu bauta ni ina zan iya wanan don ragar banza.
Duk da irin maganan ya bata min rai amma ban tsaya kulata ba saboda nasan halinta akwai kyashi da nuna hassada bata iya boye hassadanta ko ta hade kowa yasanta da wanan mugun halin.
Amsa daya nasan na bata shine ko hakan iyawane don wasu sun gwada sun kasa ko kuma hakan laifine kayiwa dan uwaka tsakani da Allah kuma yanzu ya zama laifi.
Hakana a dunkule mukai maganan hjy mum bata tashi burgeni ba sai da aka kirata tayi bayani a matsayinta na uwa irin addua da nasiha mai kashe jiki datayi ta watsowa mutane hakan sai ta burgeni har kasan zuciyata.
A haka dai taro ya watse bayan ansha bidia da sauran abubuwa a wajen tun kan a tashi ta nemoni muka dawo gida do makulin part din yana wajena.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[1/27, 20:17] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FOKON ,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

1?? 0??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Mun dawo da wuri gida inda halimatu ta lake muka dawo da ita nan din ma ba zama mukayi ba don hjy mum din ta turamu makwabta mukai mata sakon hadin sinasir da zataiwa baki na karyawa da safe don hjy mum bata yarda tayi sanyi da bakin part din nata ba lokacin itama don tana iya nata kokarin gaskiya.
A hanyan dawowane kawai mukaga gari ya hade da hadari lokaci guda nakali halima nace kinga ikon Allah ko halimatu wai hadari aka shirya yanzu kuma .
Tace nima haka nagani Allah ya taimaka mun bar wajen taron nan da yaya zamuyi mu dawo gida yanzu garama ke hjy mum taje dake niko badon nayi dubaraba duba ga yadda mukaje na biyoki da bansan ya zamu kare a wancan wajen ba.
Sai ta kara daga kai ta kalli saman tana fadin da alaman amaryan nan zata shiga a sa,a irin wanan hadarin hakan inama yau za a kaita gidan miji aida ta more.
Ta more dame ruwan kome na tambayeta tace ke banson shakiyancin tambaya baki taba jin inza akai amarya akai ruwa ace tayi sa,an tafiya ba komai ?
Nikan ban taba ji ba sai yau a bakinki kuma wanan ruwan wata kila iskane kawai ke nuna alaman damana zai sako haka har kina wani dogon fassara haka.
Bamu ankara ba mukaji wani irin iska kamar guguwa ya taso lokaci guda tuni wuri ya turnike da kura cikin sauri muka daga kafa don akwai dan taraza da gidansu hjy mum din da gidan da muka fito.
Wata motace tazo ta wuce mu lokacin muna kokarin mannewa junan mu don iskan yayi yawa a lokacin sosai har yana shiga ido hakan yasa sosai na tsorata da yanayin.
Sannu a hankali motar ke dawowa da baya wajen mu ke wancan motar fa kamar wajen mu yayo ta fada nace kewa kika sani garin nan da zai tsaya maki cikin wanan yanayin yanzu.
Motar ta dan tsaya gaban mu kadan tace kingani ko na fada maki ai don mu ya tsaya donki dai nikan tun kan nabar gida baba sunja min kunne da garin nan .
Ahankali ya dan sauke glass din motan yana fadin kuzo na karasa daku mana ina kuka fito haka cikin iskan nan muryan dan gidan hjy mum din nan a gaban motan.
Ganeshin da mukayi da sauri muka kutsa cikin motan daya bud muka shiga wani sanyi da kamshi ya dakemu lokaci guda saina raina wancan iskan mai kuran da muka fito cikinsa.
Bai kara magana ba muma bamu tanka masa ba dan tafiya kadan sai gamu a gidan nasu saida yayi packing ya bude muna muka fito.
Zuwa lokacin iskan ya dan tsagaita sai wani iri iskace mai tattare da kamshin ruwa irin na farkon damina din nan da alama andan sake ruwa a wasu wuraren garin ke nan lokacin.
Cikin gidan muka nufa da saurin mu don iska da yanayin duk sharaban mu yana baiyana sarari saboda karfin iskan dake kadawa a lokacin.
Wani irin ajiyan zuciya na sauke don kin dumin part din hjy mum din daya dakemu a lokacin gashi kuma NEPA sun dauke wuta sai wajen ya dayi duhu sai masu hasken waya ke amfani dashi.
Hjy mum da hankalinta bai kwanta ba da rashin ganin mu tana jin muryan halima ta ambaci sunan ta tana fadin halimatu kun dawo ke nan ina nan na damu har nayi waya take fada min aikun fito ko nasan a hanya iskan zai tsura daku.
Ina zainab ta tambaya na amsa gani nan ai halimatu ke fadin badon wanan yayan na wajenki ba daya gan mu ya dauko mu aida bamu dawo ba har yanzu ga gari yayi duhu kuma.
Wanan ai yasa hankalina tashi gara wa yan can ba,a rasa motar da zai kwasosu ai tunda wajen har yanzu akwai yan gida amma wasu sun dawo daga cikin su sunce sauran na hanya tafe.
Kizo zainab ga ummanki sun iso ai bansan lokacin dana daka wani uban tsale gami da ihu ba na nufi inda take nuna min din.
Ke tsaya daga can kada ki fado muna inna ta fada tana bawa karamin danta abinci don dashi tazo kawai kallon inna nayi ina fadin ina su habiba tace suna gida banzo dasu ba.
Hjy munce ke fadin ashe motace ta lalace masu a hanya har suka bata lokaci haka basu karaso da wuri ba hannu nakai ina kokarin taba kanina din sai naga yaki ya make yana harin jikin inna din.
Kai bashar badai wai har ka manta dani ba zakace sai kawai nakai hannu na daukeshi don dole ai dole ya manta dake kin zama yar kano yanzu mana hjy ta fada.
Nan zuwan inna din ya dan dauke min hankali duk da inna na kogeni irin na yar fari a gaban mutane hakan baisa na barsu ba jin sauran mutane sun dawone yasa na mike naje na gyarawa inna din waje inda zasu faku don anyi yawa a part din .
Ko wani dan katsina yazo a nan part din ake turoshi nan zai zauna wai yasa wajen ya cunkushe muna gashi anzo da yawa don yana bukin su na farko a lokacin kowa ke kwadayin zuwa don baba na kano mai kula da dangine shi don shi da yawa sukazo masa kara.
Sau biyu ina jin hjy tana kwala min kira ban taba jin haushin hakan ba sai wanan lokacin data kasa barina da uwata in gansu lokacin kan naji haushin hakan gaskiya.
Innace ke fadin wai bake hjy ke kira bane na amsa daga ciki ina fadin gani zuwa mum na mike na fita daga kofa take fadin kinga jeki muje kitchen a kawowa mutane abinci don Allah.
Na amsa da to muka nufi kitchen din ban huta ba saida naba kowa abinci yaro da babba a daidai lokacin kuma aka gwauce da wani irin ruwan sama mai karfi a garin kamar ba ruwan farkon damana bane yadda ruwan yazo ranan.
Ranan nagaji iya gajiya muna wajen inna hjy mum ta leko dakin tana fadin zainab kizo dakina ku kwana keda halima don nan din ba waje nagani.
Dan lokaci na kara nayi masu saida safe saboda gajiya na nufi dakin mum din don in kwanta da sallama na shiga azatona ita kadaice ciki amma sai naga sabanin hakan.
Tana zaune ita da yaran nan nata maza ukku da sukazo kamar suna magana da sauri na juya da nufin komawa baya naji takirani tana fadin shigo mana abinki zainab nida yan uwankine ai a dakin.
Sallama nayi na shigo a darare dakin ina dan gaidasu kafin hjy mum ta juyo tana fadin mama ya akayine ko har zaki kwanta ke nan na amsa da ehh cikin kada kaina gareta.
Dole don kugaji da yawa da badon zuwan ku ba aini da bansan yadda zanyi da wanan taro ba haka sai karamin ke fadin muma mun fadi haka ai mun dazun muka gama zancen nan da Bros nake fadin gaskiya yarinyar nan tana da kokari da mun shigo zata tambaya a baka abincine yaya kuma cikin ladabi.
Dayan yace zuwansu ai sunyi kokari wallahi don ko big brother yana iya cin abincinsu don tsabta kinsan ko tunda yaci ai akwai tsaba banda abincinki da inya dafa bai tsayawa yaci abincin kowa har yanzu amma jiya naga yaci wanda ta bashi saidai ba sosai ba ya fada yana dan dariyan shakiyanci.
Tsam ya mike tsaye don barin dakin nidai ina tsaye daga kofa ina binsu da kallon kasan ido kai kuma ana zance zaka tafi mana Bros ba wanan bane a gabana ya fada har yakai kofa.
Uwartace wanda ke gabanka din aina fadama yadda za,ayi shine ka samu Alh da kanka da zancen don bansan yadda zanje masa da wanan zance bani yaji dadin nike daure maka dama gashi har kaiga dauko bare bayan kansan yadda tsarin iyayyenka yake tun farko.
Baice komai ba yasa kai yafice daga dakin saidai kafin sauran su fitane saida suka dan tsaya sukai dan zance da mahaifiyar taso inda na kara fahintar akan aure suke magana.
Ko bayan fitansu din hjy mum din fada takeyi dashi wai zai ja mata matsala tana zaune kalau ya dauko mata magana wurin Alh ni dai ban amsata ba don zancen yafi karfina.
Irin wanan bani kan tanka mata dan dama dama abinda ya shafi aikin kitchen dana cikin part din ta amma wanda ya shafi rayuwanta gaskiya ya girmewa tunanena nikan duk dako wani lokaci ko damuwane ke saka tayin zancen dani ban sani ba.
Shigowan halimatu dakin ya dakatar da ita ga fadin komai ta kallo halimatu din dake fadin ashe kin min wayau kin shigo nan ko nima wallahi wurin kwanci nake nema inna ke fada min ai kina nan.
Gashiko dama ke nake jira ki shigo in aikeku nan bayan layi gaki kuma kina fadin kin gaji saita kallo hjy mum din dake shiri tana magana tace ehh aiken ku zanyi yanzun nan kuwa.
Nima na kalli mum din dake magana ba alaman wasa a gareta ganin nima na yarda da abinda take fadi yasa mum din cewa wasa nake mata mamana har wani aiki tayu datake fadin wai tagaji haka ina karfin aikin uwatace tayisa ai.
Wai da sai ince yanzu ga wayanda aka bari wurin buki dazun suna fadin yadda gari yayi duhu mukan da aka kunna inji ai kinga bamu san wanan ba nan muka dauko hiran bukin tana dai shirinta sai lokaci lokaci take bamu amsa.
Zata fitane take fadin idan kun tashi don Allah mamana ki fita ki rufe kofan nan na cikin gida kada ku kwana a sake na amsa da to tayi muna saida safe ta tafi wurin mijinta.
Mun dan jima muna hira kafin namike don jin part din yayi shiru nafito don in rufe wajen ganin mutane sun dan rage zirga zirga a lokacin don haka zan rufe gidan kamar yadda ta umurceni dayi din.
Kodana fito mutanene har corridor din hjy mum din don dama nasan za,a rina don ba karamin mutane sukazo yiwa baban kano din kara ba sabodashi mutum ne maiyi ga zumunci da kula yan uwa sosai irin mutanen nan da kudinsu bai rufe masu idanunsu ba.
Haka na tsatsalakasu don wurin a gyare yake ko yaushe ties ne malale masa har karshe kuma babu wani datti don hakane basuji kyaman kwanciya a wajen ba.
A yadda naji suna dan tsegumin cewa da mutum yaje part din hjy malka za,a koroshi ace ga wajen yan katsina can wanan abin yai masu zafi sosai don sunata magana akan hakan nasan ko dama za,a rina dasu din.
Don ance wata gwaggon mu saida sukaso fada da hjy malka din take fadin malka ki tuna ba rawa kikayi gaban Allah ya baki wanan matsayin ba ya barmu duk da kika ganmu nan saboda ku mukazo wajen nan balle kita koran mu kauyawa.
Itama hjy mum din tace ke kika sani dai haka nace ku koma shiyan hjy kubura don can akai maku masauki matar tace don tana yar kauye yar uwarmu ko to ai zamu koma kuwa inda aka san mutuncin mu din.
Jin karan rufe kofa yasa dayan tambayan waye na amsa da nice gwaggo ina rufe kofanne nasa sakata tana gyara kwanciya tace hakan ma yafi sannu kinji nayi masu saida safe nashige ciki.
Washegari ban bari an tayar dani ba na tashi kitchen naje na kunna wuta kafin na koma bin daki daki ina kunna heater don a rage wahalan ruwan zafin wanka.
Gamu katsina duk yadda kayi da bakatsinem mutum bai yarda yayi wanka da ruwan da baida zafi koda kuwa dan dumi sukayi basuyi zafi sosai ba basu iya wanka dashi.
Tun wanan ranan muka samu sauki a part din don hjy mum bayar da aikin tayi ana dafowa ana kawo muna anan saidai muce wahalan rabone muba mutane shine kadai wahalan mu gashi kuma wasu sun karban muna aikin don haka muka samu akai sha,anin bukin damu babu takura.
Kamar ko wani gida suma wanan gidan suna da nasu a boye wanda dama sai mutum daya ya kwanta irin hakan har mutane kan zata akwai zaman lafiya a tsakani.
Don a zahiri dai hjy mum ce a gidan nan ta kwanta ake takanta iya son rai wanda har mai hankali zai iya gane hakan shigar a farkonshi gidan.
Saidai hakan baiyiwa hjy malka ba son ita burinta kawai tabar ganin a gidan ga baki daya shine muradinta a kullum cikin irin hakanne ta samu mijin nasu da wani zance daya bata mashi rai.
Har tayi ta kare bai tanka mata ba saidai bata sanda wanan karon takaishi makura ba don ya gama fahintar idan ta dosa dai a yanzu har yan uwashi na kud da kud duk hjy malka bata kaunan kowa dashi to me hakan yake nufi ke nan ?
Da yake daurin auren ranane sai ranan dauri aure iyayyenmu maza sukazo daga katsina ciki ko har da babana saidai baizo da kannena ba ya barsu a can gida wajen wata kanwarsu baba musa da keda tsohon ciki ita bata samu zuwa bukin ba.
Yayi murna sosai yadda yaga na koma a dan zuwan nan namu kano din sai washe baki yake ya kasa boye farin cikinsa a lokacin gareni na tambayeshi kannena yace suna gida tare da gwaggon mu a can ya barsu da zaizo ninayi ta dawainiyar kawo masu abinci da abinsha da aka tanada donsu dama.
Sai bayan daurin aure da sukaso tafiyane baba na kano ya hanasu tafiya ranan sam basuso hakan ba don tafiyan nasu bana kwana sukai niyar yi ba a ranan suzo daurin aure idan angama su juyane sukazo sai gashi yace yana da magana dasu kada su tafi.
Dole suka dagata da tafiyan sai washegari da safe aka hade a wajen nan akaita dawainiyar kai masu abin karya kummalo bayan sunci sunshane Alh ya dauko masu zancen ya fara da sallama tare da godiya kafin ya danja lokaci irin ta manya yace.
Dalilin dayasa na tsayar daku a nan shine kan matsalana da iyalina shine ma musassabin tsayar daku din da nayi din ina son in kafa sheda daku don ku sani na kusa rabuwa da malka a matsayin matata na sunna don ba zan yarda ta konani ba saboda son zuciya irin nata.
Nan suka dauki fadin subbahanallahi meyayi zafi haka Alh yace hakane donshi na tsayar daku don kafa sheda don kada kuji zancen kuce ban kyautawa iyayye ba ko wani abu a gaskiya nagaji yanzu.
Don nasan bayan wanan bukin akwai gagarumin fitina da zamuyi da ita wanda zai biyo baya tsakanina da ita don haka ku sani wanan karon zan dauki mataki akanta.
Baikai can ba Alh ka bari abi komai a sannu zamu zauna da ita din akira muna ita yanzu basai mun tafi ba nan ya fayece masu irin zaman da sukeyi dashi yace kowan ku nan yasan yadda na auri malka.
Takuma shigo gidana ta samu kullu da kubura har tayi sanadin fitan kullu data biye mata a lokacin sukai ta tashin hankali har yakai saki ya shiga tsakanin mu.
To hakan takeson yanzu a maimaita kan Kubura kuma ya kasance an barta gidan ita kadai daga ita sai yayanta a gidan nan tana yadda take so wanda ko hakan ba zai taba yuyuwa a gareni ba.
Don ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login