Showing 39001 words to 42000 words out of 103712 words

Chapter 14 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7833

daddy yace ya faru mana yadda suke so dama in mutum yace iyayye basu isa masa ba shiya iya ai karshensa ke nan wahala.
Sai ya soke kai yace Nafusace dai miji ya sako da ciki dazun shine har uwarta taga wurin fadan shirme yanzu nasu na mata marasa hankali.
Innalillahi ya ambata da sauri yace garin ya haka ya faru kuma yace ba ita tace taji ta gani ba da auren bare ga diyan dangi tako ina duk yawan mu kamar kwaekwata wai ace saita tsalake ta auri bare toga abinda ya biyo baya yanzu ai.
Subbanallahi ya sake ambata ina zaune na soke kai a kasa ina sauraren su na kasa cin komai don daddy dake wajen da ya Addel din.
Mikewa daddy yayi yana fadin abin takaici wai kamar Nafisa miji ya sakota taki fita saiya hada da hukuma an mata koran wullakanci sanan ta fito.
Kai abar zancen yariga ya faru yanzu kuma ai mata uziri don Allah taji da abinda yake damunta yawan surutun nan sai kuma ya kara jefata cikin wani hali.
Ko ance din yana maganine yanzu tunda saki ukune ba gyara subbahanallah wanan wani irin wawane shi da zai saki mace da ciki har saki uku ya Addel ya fada rai bace.
Kaddarace kawai amma tun farko mutumin nan yana da matsala ga duk wanda ya kallesa yasan kuma dacewa amma sam Nafisa bata dace dashi ba gaskita abu daine baya faduwa a lokacin aga bakinka ga banza.
Har daddy yakai kofa da ledanshi a hannu ya juyo yace ai yanzu dai ta kare tunda ba gyara kuma yasa kai ya fice daga dakin yana dan lalabawa.
Ajiyan zuciya na sauke a daidai lokacin da mum ke fadin ai abi ke nan in ce mutum ya bari suce bai waye ba toga wayen nan mungani yanzu Allah dai ya sauwaka Nafisa kan yanzu ta zama abin tausayi ga ciki dole a lalabata.
Shiru nayi ina kara nazari kalami kowansu a raina shima bai dadeba ya tashi ya fita yana tajan tsoki nasan abin ya taba mashi zuciya sosai a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/3, 07:47] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FAKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

1?? 4??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Sosai naji dadin fruits din nako bude ciki na dirka naci naman don bambcin da yake dashi da wanda mukeci saboda wanan dai gadashi akayi dan ruwan kazan na ainihi na jikinsa wancam kuma nagida ai soyashi mukeyi wanan ne vamvamci da mutane ke daukin cin nama kasassa wani lokaci saidai da yake ra,ayi ya bambamta wani lokaci kowa da abinda ransa keso.
Mun danyi kallo don da alaman Mun ta samu sauki tun shan magani da kuma mai dana shafa mata banji ta kara korafin wanan ciwon kan nata ba kuma don so dayawa yana damunta gaskiya zakiji ta kwanta tace kai na mata ciwo.
Saura na dauka nasa a fridge kada ya lalace na rufo ko ina muka kwanta don yanzu a daki daya muke kwana tun bayan barin halimatu wajenta.
Da yake washegari ba school hakan ya bani daman samun yin batcin safe sai karfe takwas da rabi na tashi na soma yan aiyukan gida da nasan ni zanyi don nikan gaskiya ba sai an tuna min aikina ba.
Kafin goma da rabi har wanka nayi na dauki kayan karin Dada da muke kai mata irin wanam raman nakaiwa Dada din kamar yadda muka saba duk weelend idan muna gida.
Sai lokacin na tuna da zancen anty Nafisa din na shiga wajenta zaune take bakin gado ta kurawa kasa ido tana tunane idamuwanta har lokacin sunyi hulu hulu dasu wanda ke nuna alaman bata bar kuka ba.
Gaida ita nayi ta dan dago a sanyayye tana amsa min kafin in samu waje a gefenta nakai zaune kasa na dago na kalleta nace.
Anty kiyi hakkuri nasan akwai zafi hakan don anzalunceki amma inkinyi hakkuri kin barwa Allah lamarin sai ya saka maki kan zaluncin da akai maki din daga baya don kukan nan illane yanzu a gareki halin nan da kike ciki.
Cikin dan tausa murya nake kallonta ina fadin hakan sai naga ta fara sauke wasu hawaye masu zafi a fuskanta nima bansan lokacin da hawayen yazo min ba na fashe da kuka.
Ajiyan zuciya naji ta sauke kafin tace dani haba dai sis ke kuma da nake jin dadin kasancewa dake kin dora da kuka ya kike son inyi ni kuma yanzu ?
Jin hakan yasa na dan tsagaita ina hadiyan zuciya tace min a sake alaman ta dan fara saukowa lokacin tace kina jina sis nace gyada mata kai don ban iya bude baki a lokacin.
Tace can you trust me as i can trust you nan ma da sauri na sake daga mata kai alaman ehh ba tare da nadago kai mun hada ido da ita ba lokacin.
Good sis dake kadai na yarda kaf gidan nan kuma kalaman ki gareni da kike tunatar dani komawa ga Allah yasa nake jin dan sauki a zuciyana tun jiya ba wanda ya bani magana mai dadi irinki gidan nan gashi yanzu kuma kinzo kin kara min wani haske.
Tabbas Habbib ya cuceni ba karami ba koda yake laifinane don sonsa ya makatar dani a lokacin har na kasa gane illan abinda yake yawan fada min din sai yanzu nake tuno komai.
Don gaskiya yasha fadain hakan don yaji dadin rayuwansa dani yasa yake ya aureni yasha fada min hakan amma sai ban daukeshi komai ba idan ya fada min wannan lokacin.
Na yarda dake sister dari bisa dari donke din tayuwanki na dabane kin samu tarbiya daya dace ace mun samu tundaga tasowan amma mummy ta kasa gane abinda daddy ke nufi sai son ranmu take bi.
Don da ace tayi tsa AQye ta hanani auren habib da wanan abin duk bai faru dani ba yanzu akwai wullakanci kamar wanan cikin yau in haifeshi sister ba tare da ubansa ba duk akwai wullakancin daya kai wanan.
Anty kiyi hakkuri hakan na cikin jerabawa daga ubangiji ki daukeshi hakan don Allah ki dinga istigifar da haila sai kiji sanyi a zuciyan ki haka malama mu na islamiya suke fada muna sai tayi murmushi donjin abinda na fada din gareta.
Mummy ne ta fado dakin ta bimu da kallo gani ina sharan hawaye tace ita kuma wanan me take nema a nan anty Nafisa tace wurina tazo mana mummy tunda kin ganta tare ta wani daure fuska na mike ina fadin anty zanje in karasa aiki tace ki dawo fa sis nace insha Allah.
Ina mikewa naji mummy na fadin ta dawo tayi maki me kuma kidai baku da zuciya wallahi ina ke ina wanan karamar yarinya kuma har kina jaddada mata wai ta dawo fa tayi maki uwar me a nan din.
Kilama an aikota leken asirine kike wani cewa taje ta dawo to banson hakana kai mummy do lalacewa mai wanan zata zolayeni dashi kuma ?
Ni natsuwan yarinyar nake jin dadinsa kuma haka Allah ya dora min kaunata a zuciyana don Allah ki barmu karkice zaki saka ido ga abinda mukeyi ni banson haka tunda ba yarinya nake ba yanzu dai.
Na dai fada maki kiyi hankali da yarinyar nan don sani da kikai mata don yanzu an lalatata da makirci in kin kashi kikaganta zauna a ciki indai wanan yarce.
Nikan ko wajen Dada ban tsaya ba part din mu na shiga a falo suke ya Addel yana karyawa a sake na gaidashi da ina kwana yaya duk da nasan ba lalai bane ya amsa min amma sai nayi sa,a ya amsa a lokacin.
Ina kika tsaya kuma nace ina wajen anty Nafisace dama jiya tace in dawo ban samu zuwa ba sai yau ba koma sai naga mum tayi min wani kallo kafin muryan yaya ya katseta ga abinda tayi niyar fadi yace OK ta tashine jiya nashiga ance tana barci.
Caraf nace barci kuwa andai fada ma hakane amma ita kan tana nan tana aikin kuka zancen mukeyi da ita saiga hjy ta shigo nafito ke mama ni dai kibi a hankali don Allah.
Ban sanki da jaye jayen magana ba dai kinsan halin uwarsu dai yanzu ba sai na fada maki ba dai don haka ki kula don Allah.
Yanzu mum harda yara za,a hana mu,amula da junansu kema kinsan halin Nafisa ai in bata yarda da ita ba aiko kusa gareta bataga wajen zuwa ba ai ki barsu kawai suyi abinsu ita wanan bata taba yarda da mutum dama idan ba jininta ba.
Kaida bari in tsawata mata ko banza nasu baizo daya da mama ba nasan ko tunda tana wajena ta dauki tsana ta saka mata don ni itama ta iya badon iya ba ko ganinta batayi part dinta yanzu kuma ga Nafisa.
Kai ya dago ya kalloni yana fadin kisan yadda zakibi dasu a zauna lafiya na amsa da to da sauri ina mamaki ashe yana magana mai tsayi irin haka.
Saida ya gama ya mike zuwa wajenta sun dade suna magana a tsakanin su yana bata shawara a karshe take fadin wallahi daga kai sai zainab kuka ban shawara mai dadi a gidan nan.
Yace wace zainab fa tace zainab din mum mana yarinyar nan dake zama da mum ina jin dadin kalamin yarinyar zakace wata babbace idan tana bawa mutum magana.
Kai haba wanan meta sani banda shirme Allah yarinyar nada hankali sosai ta fada kafin mummy ta fado dakin kamar yadda tayi min haka shima tayi masa amma bai kulata ba don bai tashi ba cigaba sukayi da hiransu kan aiki ta gaji da zama ta mike ta fita wai tana amsa waya.
Halin rayuwa irin na mummy sai a barta irin mutanen nan ne da basu da yarda ko kansu basu yarda dashi ba balle wani ga korafi da cin zarafi ga dan abu kadan idan ya hadaka da ita idon ta zai rufe ta yankewa mutum kauna nan take.
Yanzu kan ko banje gun anty Nafisa ba ita zatazo har part din mu ta sameni ta zauna nan abu ga mai ciki tace wanan take so wancan takeso a kawo mata.
Mum bata faye zama damu ba a irin wanan zaman don ta kula duk tazo sai an turo yan leken asiri azo aga me takeyi a part din zakiga kwana biyu ta dauke kafanta kwana biyu kuma ta dawo muna.
Idan ta dauke kafanta nima nakan da jaye mata a lokacin sai kuma ta aiko a kirani ranan a gaban yan uwa take fadin kai zainab nifa wanan zaman naki ba waya ya fara isata haka .
Ko mutum yana son kiyi masa abu sai ya aiko ko yazo gashini yanzu nayi nauyi tashima yana zama min wuya wani lokaci don haka ina da karamar waya zan baki ki rika yafi mun sauki hakan.
Wani waya anty badai iPhone din nan naki nada ba Asiya ta tambaya cikin kashe yar nasu da idanu tace meye in shine ba nawa bane kuma zan bata.
Ta mike da kyat ta dauko min wayan a dakinta tabani nan na kama murna da jin dadi taban kuma dubu biyu tace nasayi sim nasa da kati nayi ta mata godiya sosai.
Washegarine muna zaune da Mum falo saiga hjy mummy kamar an jefo muna ita falon ina kusa da Mum na mane mata don dadin da uwata bata ban ba na tajani a jiki yanzu ina samu a wuri mum gaskiya.
Lafiya mum ta tambaya a yadda ta ganta ta fado yace gun yarki nazo ina wayan da Nafisa ta baki jiya nace yana daki dauko ki kawo min ta fada a hasale tana gimtse fuska nace to a daidai lokacin da mum ke fadin jeki ki dauko mata.
Kafin in dawo na samu suna cacan baki a tsakanin su mum na fadin kaiyya dadin abidai badai sata tayi ba bata akayi ke kuna jakkadiyan shedan kin hana yar ki alheri.
Zance kike so ni dai waya nake son a bani ba wani abu ba kiji dadin zuwa kulla min sherin da kika saba to van fada ba waya nace ta miko min kawai ba wani abu ba.
Ina mika mata ta fisge a hannuna kamar mai shirim kwata tafice tana fadin haka kawai ni ba a kawo min iskanci ai ke kuma kinci bashi don nasan nayi kike nema yanzu tana fadawa mum din tace tafican mara ta ido kawai.
Ta dawo gareni tana fadin ke kuma kingani ai saida na fada maki kibi sannu da mutanen banzan nan kina ganin kamar ina son in rabaki da yan uwankine togashi kin gani da idanun ki.
Har kuka sai da nayi don waya akwai shiga rai sosai dan kwana dayan da nayi da ita har na fara sabawa da wayan tun lokacin kuma zancen ya fice min a raina.
Ban kuma nunawa anty Nafisa komai ba kan wayan zata sakani aiki in mata ta kuma shigo wajen mu nan wajen mum tayi yadda takeso ta tafi abinta.
Bayan kamar sati biyu sai gata tunda safe su ya suna zaune suna karyawa ta shigo bayan sun gaisa take fadin ina zeey tana ciki mum ta fada ta nufi ciki sai gani muka juyo zuwa falon da ita.
Nan take fadin wai ashe mommy tazo ta karbi waya a hannun ki ban sani ba kuma baki fada min ba akan me kika bata tunda ba ita ta baki waya ba watace fa don me zata karba taba Asiya Asiya ta fiki garenine ko me ?
To nan tazo muna da tashin hankali a bata waya ni kuma nace ta dauko mata ta bata ta fita tana zage zage ba wanda ya kula tana kallon mum din kafin ta juya wajen yan uwarta tace .
Wai me yasa mummy take hakane for god sake bana son irin wanan abin ta sani daddy ma baya so to ba zan ba Asiya wayar ba tunda ba wani ya saya min ba.
No ki bar mata ita ta bari zan sayo mata waya idan na fita shike nan don Allah abar zancen ya tafi a haka please tayar da zancen yana iya kawo matsala kuma a gidan nan yanzu.
Kinji dan uwanki yace abar zancen nima ban faye son ta rike wayan nan ba yanzu tunda karatu takeyi gaskiya no bari dai a saya mata tunda duk yan uwanta suna da waya itama a saya mata din ya fada.
Sai ta juya ta fita ya juyo gareni yace wani irin wayane mummy ta karba nace ko iPhone nawa karama daice naji su halima na fadi mum tace kaji wata shegiya nan halimatu din nan bansan me kika tare mata ba a gidan nan.
Anyi hakan koda zai dawo sai gashi da waya ya kawo min ina falo ya jefo min ledan saman jikina yace kardai ki biyewa waya ki bar karatu mum tace nina sagartaki da waya ya juya ya fita.
Ihun murna na sake jiki na rawa na fada jikin mum ina rawa tace ohh abin naki ya zama shegantaka yanzu na karbe wayan naga tsiya kuma nan na shiga rokonta murna ya hana bakina rufuwa a lokacin caji nakai na saka wayan.
Anyi hakan da kwana daya saiga mahaifiyar halimatu wai tazo ganin uwarta Dada har part din naje na tareta amsawan da tayi min ba yadda muka saba da ita bane.
Zuwa yamma da mum tashiga saiga mace ta fara yankar kauna tana fadin dama da biyu tazo garin nan ke kubura ki fada min tsakanin Zainab da Halimatu wayafi galihu a gidan nan wajen ku.
Ina dai zariya daya muka fito nida mai gidan nan mum tace hakama aida uban zainab ko don banga bambamci a tsakanin ku ba kai har mu tace ato uwa daya dai ta haifomu dashi ko don haka banga dalilin da za a saka min ya gaba da bakin kishi ba.
Zainab don ta iya makirci da kisisina tabi ta kammale ku babba da yaro kun mayar min da ya saniyar ware a gidan shine nazo in kafa sheda don ku sani ita ma dai nan gidan kawuntane ehh,hey.
Au da kice don ni kikazo ashe tace bake daya ba wallahi dan kowa nazo ke can kin koreta saboda taki yarda ta zamo boyi boyin ki nan kuma data dawo suma sun tasa min ita agaba.
Au abinda ta fada maki ke nan dama to inkin dauka haka din ne saidai ki sani ni ban dogara ga aikin yaro ba gasu nan ki tambayesu kiji mamace dai wanan kamar yadda kika fada kuma nima inada iko da abina.
Jin hayaniyarsu yasa hankalin mutanen gidan ya dawo gunsu har Dada dake waje tana gugan goro da zata watsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login