Showing 72001 words to 75000 words out of 103712 words

Chapter 25 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7835

Ban tsamanin shi yake kallo anty amsan dana san na bata ke nan kada tayi ta zuba ita kadai ba tare dana dan tanka mata ba sao naga ta dan girgiza kai tana dukan sitiyarin motan tace.
Baki san waye daddy ba ke nan yadda mukai mai banga da auren habbib shine yanzu yake son ya rama akan yan uwana ya rike zancen a ransa tun farko kuma nasan hakan zai iya faruwa tunda abin nan ya faru tsakanina da habbib din nake fargaban hakan amma ban dauka yan uwana zai shafa ba.
Mun shiga haraban makarantan ta samu waje tayi parking din motan sai lokacin ta kalloni tace nasan kina cikin wani yanayi a yanzu ki daure ki tsaya ki dage da karatun nan shi zai kwato maki rayuwa a nan gaba insha Allahu kin dai gani yanzu a gareni.
Kusan tare mukai komai don bata barni nayi wani wahala ni kadai ba sai wajajen biyu nagama don samun taimakonta da nayi na zama daliba ke nan a yanzu nima .
Don gata yai min komai bansha wani wahala da sauran dalibai suke samu ba yayin cike ciken form dinsu saboda ita don tana aiki a tare dasu wajen.
Karfe hudu duk ina gida part din mu na nufo kai tsaye sai dai ban samu mum ba don haka na nufi daki in rage tufafin jikina har kuma nafito falo mum bata shigo ba hakan ya ban mamaki fitanta tabar part din abude .
Cikin gida na dosa in tambaya ko ta fitane a tsaye na samu matan daddy enugu suna magana suna ganina kuma sukayi shiru gaidasu nayi nake tambayan mum din.
Amaryan ke fadin tana ciki dasu Alh tun safe yau bai fita ba yana gidan nan suna rigima da hjy Malka akan zancen auren yayanta Allah dai ya sauwaka tashin hankali baida dadi wallahi shi kuma Alh ya kafe sai yayi abinda yayi niyar yi.
Hafiz ma yazo dazun nan duk suna ciki suna magana tare da wasu yan uwa da sukazo daga katsina a raina nace Allah yasa a wargaza zancen nan.
Saidai a fili juyawa nayi na koma ciki na kwanta a saman dogon kujera ina faman tunanen abinda zaije ya dawo akan zancen.
Don nasan mahaifina ba zai taba budan baki suyi magana kan hukuncin da daddy ya yanke a kaina ba sai dai Allah kadai zai kwatoni ga hakan.
Na dade wajen sai ga mum ta shigo tayi mamakin ganina a falon zaune take fadin kin dawo ashe na amsa da ehh tun dazun nashigo .
Muna can yau gaba daya abin baiyi dadi a gidan nan ba wallahi badon zuwan su yaya ba da Allah ya gyara gaakiya yau da ban san inda fitinan nan zai tsaya ba gidan nan.
Don abin ya kaisu har da duka da rotse rotse da girman su suna aikin yara ga hafiz yazo shima da nasa haukan shikan ai ban raga masa ba don mahaifi mahaifine ko ya yake kuwa.
Allah dai ya gyara Allah yasa kuma iya fitinan ke nan don gaba akewa gudu tunda abu har yakai ga hukuma ai zance baiyi dadi ba.
Haka tayi ta koro jawabi a gajarce ta yadda ba zan fahinci meya faru ba don dukule zancen da tayi ill takardun resit dana mika mata ta karba sama sama ta duba take fadin anyi komai ke nan na amsa da ehh .
Tace Allah ya bada sa,a yasa ki amfana damu duka da sauran al,umma baki daya wanan yasa ban damuwa sosai don karatun nan da zakiyi din.
Baga Nafisa ba yanzu karatunta ya taimaka mata ga komai har takan manta da abinda ya sameta a baya karatun yana da amfani sosai ga mutum idan ka dage kayisa Allah ya taimaka yaba sa,a na amsa da amin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/21, 21:53] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2?? 4??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Me karatu nasan zakiyi mamaki da al,ajabin yin shiruna haka lokaci guda ba tare dana nuna wani bori ko botsewa zancen daddy ba alokacin .
Hakane kwarai hakan kuma ya samo asaline bisa ga gargadin dana samu daga mahaifana dakuma hjy mum dita da sukai min cikin kakausan murya kan yiwa iyayye biyayya don baba ya gargadeni da cewa duk yaji wani rashin mutunci ya fito a bakina in tabbatar dana nemi wani uban bashi a duniya.
Amma ke kina ganina kinsan ina cikin tashin hankalin tsaka mai wuyan fita a rayuwana gashi ansano yin shiru koda kuwa ana min habaici ko cin fuska dole nake jan bakina inyi shiru.
Saidai yanzu gaba daya na daina fita ko ina daga makarant dana fara a yanzu sai zaman part din mu wanda ya zamo sabon hali agareni yanzu din.
Ban shigo ko wajen Dada balle part din hjy mummy da yanzu a kusan haukace ta da kowa agidan don ganin laifin kowa takeyi yanzu mutakat ka zaune a karkashin daddy don tace hadin baki akayi ai mata hakan don aga iyakanta.
Tana zaton da bakin mum cikin wanan shawaran kamar yadda nima na zata fa farko koda saninta akai min haka djn daddy ya rasa wanda zai hadi aure sai hafiz dan hjy malka.
Matar da bata kaunan ko jin sunana a bakin wani balle ace wai nice a matsayin sarkuwarta kan danta data kwallafawa rai a duniya fiye da kowa da komai nata sai gashi haka ya faru yanzu.
Ni kaina nakan zauna wani lokaci inyi tunanen ko meye dalilin daddy na zabana yaba ya hafiz a matsayin mata ko hakan na cikin karin zumuncin da yake ikirarin yanayi da mahaifina ke nan.
Duk rikicin nan ban taba sakashi a idanuna ba saidai inji a bakin mum cewa yazo koya tafi cikin zance don dama ba gwanin shigowa part din bane ya gaida mum shi sai lokaci lokacin daba,a rasa ba can ko wani abu kwakwara ya shigo dashi part din mum din.
Safiyace sauri nake kada in makara don yanzu tafiyan mu bai daidai da anty Nafisa don ita takan dan jima a gida yasa nake rigata fita a yanzu din.
Sauri nake nafito daga cikin gida inata kokuwan gyara hijjab din jikina kamar ance in dago kai ya hafiz nagani tsaye gaban motanshi daga shi sai gajeren wandon maza da taba a hannunsa yana zuka.
Ya harde kafa daya cikin daya yana waya kuma tare da zubo min muggan idanunwans dake daga min hankaki da kallonsu take naji kafafuwana suna hardewa haka na daure na sawa kaina kwazo ko kara kallonwa banyi ba nasa kai nafice daga haraban gidan.
Break muka fito kamar yadda muka saba fitowa don yan lalurorin mu na yau da kullun ban kokaiga fitowa wayan anty ya shigo wayana na dauka.
Take tambayana da ina inane munfito break na amsa da ehh take fadin kizo yanzu ina jiranki office dina na amsa da gani nan zuwa.
Gashi akwai nisa sosai tsakanin department din mu dasu haka na taka ga yunwa dake cina a lokacin har addua nake azuciyana da Allah sa wani abinci zata bani inci alokacin.
Ina isa jerin office din na tsaya tare da nocking naji muryanta tana amsawa da shigo nasa kai zuwa ciki ina mata sallama ji nayi lokaci guda kamar in juya don ya hafiz din da nagani zaune gabata.
Lalai kiran nan yayi sa,a har kin karaso shigo ki zauna dama ga wanda yazo ganin ki ni barin dan je in dawo kafin ku gama kar in zauna ace min surikar zamani kuma.
Tafita tana dariya sam bata kula da yanayin da nashiga ba a lokacin shiko ya hade rai kamar yaga mugun abu a lokacin fuskar nan nasa a tanke kamar kullun duk da yana son kama da daddy ga zubin hallita rashin fara,arshi kamar daddy yasa kaman nasu yana dushewa.
Don daddy mutum ne mai fara,a da son mutane ga sakin fuska ga kowa daya sani komu da muke yaransa yana sake muna fuska wani lokaci daine idan ransa ya baci zaka hadu da fushinsa.
Dan lokaci mai tsawo yaja ina tsaye ina saurarensa yana cike da haushi da takaicin zubar mai da mutuncin da daddy ke shirin masa akaina.
In ba abin daddy na kauyenci ba da wanan karamar yarinyar da bata gama ko fetan majinan yara ba daddy zai hadashi a raina masa wayau kawai.
Iska mai karfi naji ya furzo da iska dakyar maganan ya fito masa yace well, koda yake ba sai kin zauna ba dan baki da darajan da ina zaune kina zaune a guna.
Ina son ki saurareni kiji me zan fada dama shi ya kawoni nan ba wani abu ba don karki dauka ko donki nazo nazo nayi maki kashedine a kaina.
Nima ban fatan ace irin ka yazo zance wurina na tsunci kaina da bashi amsa don raina ya gama baci sosai dashi don yadda yake min maganan da kuma kalamin daya fara fada.
Sai naji yace really yarinya ashe show din zaiba da cita tunda kina ja abin yayi min daidai kuwa toki saurara kiji idan kina son kanki da lafiya ina mai shawaratanki da kiyi gagawan samun iyayyenki ki fada masu baki da baki da baki kaunata kema kamar yadda ban kaunarki.
Wani shu,umin murmushi irin na wullakanci ya subbuce min a lokacin na kallesa a wullakance bandaiyi magana ba yace kwarai abinda nake son kije kiyi ke nan a wajensu.
Don ke kanki kinsani niba sa,an aurenki bane don kawai ajawa mutum abin kunya yasa mahaifinki ya likewa daddy ashe don kawai a manna mani ke in kaiki ina dubeki don Allah ?
Wata kala mace tsaye haka kimkam kamar muciya ko fasali da ma,ana babu irin na mata don zalama nan ma saida kuka biyomu don kwadayi.
Wani malalacin murmushin mai karawa mutum haushi da takaici na sakar masa ina cewa.
Au ashe naku zargin ke nan dama akan mahaifina ya mannewa daddy ko daddy ya manne masa ?
Yadda ya dahewa baba din yana cin riba dashi aimu aka cuta da sunan zumunci akaci amanar mu baku ba.
Ke ni sa,ankine ya taso min kamar zai kaureni kome ya tuna kuma naga yaja baya yana fadin kin daiji menace dake kiyi gagawan zuwa ki sanar dasu tunkan rana yai maki dare a zancen nan.
Au kai baka san hanyar yin hakan bane saini zaka zowa da wanan zancen donnka daukeni sakarai mara tarbiya da bansan darajan iyayyena ba ko to kasani niba hakan nake ba.
Nasan zafin da darajan iyayyena fiye da kowa a duniyan nan saboda nasan zafinsu da darajansu don shine ma kaji nayi shiru tunda aka fara zancen nan daidai da rana daya bani fatan su kwana da bakin cikina a zuciyarsu don haka bani da ja a duk hukuncin da suka yanke akaina koda kuwa nasan abin zai cuta min.
Common ki rufe min wanan bakin naki a nan tun ban masgeki ba ya mike ya nufoni yana zare min ido nace .
Oho dai kaika sani na juya da sauri dama a kofa nake tsaye tunbshigowana tun kan ya karasa fitowa daga cikin kujeran da yake zaune yakai gareni nafice daga office din.
Anty dake tsaye da wani abokin aikintane taga fitowana a office din kira take kwala min ko juyo banyi ba nasa kai na wuce ina share kwallan da yazo min a lokacin.
Ina jin kira a wayata nasan itace banbi ta kan wayan ba na nufi school mosque kai tsaye don gabatar da sallah azahar ko zuciyana zai min dan sanyi alokacin yadda nakeji.
Office din ta koma ta sameshi yana huci a ciki shi kadai tunda ta shigo take fadin hafiz me kaiwa yarinyar nan meyasa kai baka jin maganane don Allah ?
Kaki ka bari abi abin nan sannu kowa ya huta sai kara jagula lamarin kakeyi ga baki daya yanzu me kai mata don Allah nasan halinka da saurin hannu wallahi ?
Lalai yarinyar nan tana da ja meta daukeni da zata tsaya gabana tana mayar min da magana haka watau nine dan iska mara tarbiya take nufi kome ?
Wallahi nama fasa ja akan zancen nan yanzun zan aureta din in koya mata hankali ita da wa yanda ke daure mata gindin badai igiyar auren nasu a hannuna yake ba ya buge table da karfi jin hakan yar uwar nasa tace .
Me kake nufi da wanan kalamin naka hafiz ?
Ya jefo mata wani kallo na bacin rai kafin ya kuta yasa kai ya fice daga office din kiransa yakeyi da karfi bai tsaya ya kallota ba yafice abinsa.
Kai ta dafe tana fadin oho my god me yaron nan yazo yayi a nan yanzu Allah dai yasa ba dukan yar mutane yazo yayi a nan ba yaja min aiki .
Waya ta kara lakuban layina saidai wayan akashe yake lokacin don haka takai zaune tana shawara a zuciyarta kafin dabaran kiran mummy yazo mata ta danna mata kira kai tsaye.
Mummy na dauka tace mummy yanzu abinda hafiz yazo yai min ya kyauta ke nan don Allah nan yazo gun aikina ya sameni yace yana son don Allah nasa a kira masa zeey yana son magana da ita.
Mummy ina ganin fa dukar ta yayi yadda naga ta fito tana hawaye bata ko saurareni ba ,,,,,,,
Ke dakata don Allah nina dauka wata tsiyan ya shuka kuma har hankalina ya tashi inya doketa ai ya duki banza dama haka sukeso ai ita da iyayyenta ki bari in kirasa inji meya ya faru tsakaninsu ?
Sai kuma ta koma fadin ina ma ruwansa da itane wai da zai bita school ya ja maki fitina acan nima mummy abinda ya daga min hankali ke nan ai.
Wai harda ce min yama fasa yanzu aurenta zaiyi yaga iya gudunsu badai auren a hannunshi yake ba ai shike nan yasan maganin su tunda abin tsiyace.
Barshi zai shigo ai ya sameni don shine mani yanzu banson zuwanshi garin nan don inyazo kara caza min kai yakeyi ba kwantar min da hankali ba.
Ina fitowa mosque din kai tsaye gida na nufo dan nasan anty Nafisa zata iya zuwa nemana a lokacin don haka na nufo gida ban koma ajin ba kuma.
Nayi sa,a mum tana falo na shigo bata kula da yanayi na ba sai cewa takeyi yau da wuri kuka dawo haka amma dai kunyi saurin tashi yau din sai sheshekan kukana taji da sauri ta dago tana fadin subbahanallahi meya faru kuma ?
Da sauri ta mike ta karaso gareni tana fadin wai meya farune kin zauna haka kina min kuka ki fada min abindaya faru mana ?
Nace mum ina kamo hannuta don Allah ku taimakeni ku raba aurena da wanan azzalumin mutumin don ba dai kaunar juna mukeyi dashi ba mum.
Wai hafiz meya faru ina kika gansa nace school ya bine office din anty nafisa nan na kwashe komai ban boye mata ba na fada mata tace.
Lalai hafiz yakai dan iska dama wanan zargin sukewa yaya Garba ashe haba gaskiya dai habaici ke zuwa yana dawowa ashe da yaya sukeyi manufansu ke nan dama.
To wallahi bari Alh ya dawo dolene yaji zancen nan kuwa don ba jaka za,a kai masa ba da zai kama ki tin waje yana duka da zagi harda cin zarafin iyayye haka dole ayi wani abin gaskiya akan zancen nan.
Don wanan zancen ba karamin magana bane dole iyayye maza su sani su tsawata mashi tun wuri yanzu waya saura aure da dukan mace kuma ?
Nan dai ta lalasheni da kalami masu dadi tana kwantar min da hankali da kara ban shawara kan yadda zan kiyayyeshi .
Anty Nafisa na dawowa nan part din mu ta dira take tambayan mum ni tace ina ciki dakina ta nufo zaune nake saman gado na mike kafafuna da takardan karatuna a hannu ina faman tunane.
Jin shigowanta yasa na dago kai gareta ina kallonta na samu na bude baki da kyar ina fadin sannu da dawowa anty itako sai wani kallo take min na kinganki ko din nan.
Tace watau shine kika kashe min waya don kinsan zan kiraki kuma kika kama hanya kika dawo gida tun ba,a tashi da kika dawo gidan karatun naki fa sister ?
Kada ki bari kiyi wasa da karatun ki gaki kinsan course din ku bana wasa bane meyayi maki kika fito kina kuka ina dai ba dukanki yayi ba ko ?
Ta fada tana kallona don son jin amsan da zan bata a lokacin hawayene suka fara fito min kafin nace da ita meye ma bai mun ba anty ya dakeni ya zagi iyayyena yaci masu mutunci ya kirasu da yan maula.
Don shi suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login