Showing 81001 words to 84000 words out of 103712 words

Chapter 28 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7857

banzane ke nan tunda har take iya zaton daddy ya hada muna dacin hanci don a zauna dashi ko ?
Da yamma muna zaune ana hira gida ya cika saiga Dada ita ta saka min lale ta shammaceni banyi aune ba ta zuba min akafa har zuwa sawayena da hannayena tana guda.
Wani irin zabura nayi ina hawaye tare da furta ta faru ta kare ke nan na dai tabbata matar hafiz ke nan na fada a zuciyana na mike zuwa babdaki.
Kuka nayi sosai kafin nabawa kaina hakkuri na wanke nafito don kada mum ta gane cewa kuka naje nayi saboda nayi alkawarin ban sake yarda inyi kuka kuma kan auren.
Nan buki ya fara ga jama,a ko sai zuwa sukeyi daga garuruwa don su sheda kawai su nunawa iyayyena farin cikin ganin wanan lokacin kamar yadda yake a al,adance.
Kamar ko wani buki kuma ko wani gida aka hada bukin yayan daki biyu ake samun yan tsegumi da gulmace gulmace wanan ma namun hakan aka samu.
Hakan yafi faruwane kuma abangaren mummy din hakane ma a asirce mum taba da girki da za a dinga yo mata daga wani gida ana kawo mata nan gidan kawai saidai aga ana shigowa da manyan kuloli na abinci apart dinta.
Sai hakan kuma ya tsonewa mummy ido sai gasu har gaban Alh wai bata yarda da tsarin da mum ta dauko din ba nan daddy yake fadin baki yarda ba sai kije kiyi yadda tayi din mana kema.
Ni dai nasan Kubura bata tambayeni kudi wai zatayi girki ba haka kuma nima ban dauki kudi na taimaka mata tayi girkin nan ba ina duk abinda tayi tayine da sunan taimaka muna dai a cikin sha,anin nan .
Tunda dani dake keda bukin nan ba dole bane sai kubura tayi wani abin bajinta da har zai tsone maki ido idan kina da tunane mu tayi wa wanan karan ai a nan.
Duk da haka mummy bata fahinta ba don bata yarda ba kishi ya rufe mata idanu a lokacin sai cewa tayi dama ai bakinsu hadene gashi ita din dake cewa mum tana da rowa .
Itace irin halittan nan ne da komai sai sunci riba dashi kudin ba bata samu bane wajen miji bata dai iya fitarwa ne akashewa jama,a ta zata daddy zaicewa mum a hada a dinga kawowa ko wani part ga nata wautan.
Sai daren da za a daura aure hafiz din dasu yaya Addil daya shawo kansa suka iso garin cikin dare sosai bayan mum tayi ta korafin rashin zuwan nasu akan lokaci.
Tana cewa rashin zuwan matarsa da wuri yaci mata rai ace tana bukin kanwarsa amma ace wai ba matar Addil a wajen don tana yar rainin wayau.
Wanan yasa washegari da sukazo mum din taki tsayawa ta basu lokacinta tana nuna masu fushinta ga hakan da sukayi na basu kyauta mata ba son gaba su gyara.
Amma sai gashi itama Aishan wai tayi fushi don mum bata nuna tana da muhinmanci ba a wajen ta ga idon jama,a din haka ta sulale ta fice daga gidan ba tare da kowa ya sani ba.
Saida mum tace akirata tana kitchen shine ake fadin ai bata nan a zaton mun ta shiga wani part na gidan ne sai gashi ana fadin anga fita ai tabar gidan.
Ita kuma mum nata matsala ke nan daya fara bullo mata shine matar danta bata da mutunci balle kirki don sam bata da tarbiyan bin nagabanta uwar miji da take tankat uwarka ga me tunane amma ita ko gaban dan sai ta nemi ciwa nasa mutunci.
Don hakanema gaba daya gidan ba wani mai dogon shiri da ita baya ga gaisuwa da za a tsaya a danyi sama sama don gani take ta girmi wayewan kowa a gidan don haka babu sa,anta take daukankai
Sai dai ita a wajenta kuma gani takeyi kawai dai ba,a sontane don hakane bata nemi hanyan gyarawa ba sai iskanci da takeyiwa mutane tana kara bata kanta a zuciyan yan gidan mijin nata.
Don ko hakan datayi ba wanda baiji wanan labarin ba kowa na tir da halinta a cikin taron nace kinga bone kowa ya zageki Allah yasa mu gane gaskiya mu gyara ba sai ana son mu zamu kyautatawa uwar miji da yan uwan miji ba halinmu zai muna alkalanci a gidajen auren mu mata.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

[2/28, 06:27] Maman K: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2?? 6??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Duk wanan badakalan da akeyi iyayyena basuce uffan ba duk ko da zagi da cin mutuncin da mummy keyi kamar a gabansu take fadinsa don komai sunaji amma sun taushe zuciyarsu saboda zumunci.
Akwai sauran imanin zumuci a lokacin dan uwa na iya bugun gaba da dan uwashi ako wani lokaci ya yanke hukunci akansa ba tare daka daga kai kace don me akayi hakan ba.
Duk dadai har duniya ta nade akwai masu imanin gaskiya da biyayya bisa ga tsarin musulunci don sai ince duk yawancin al,adun malam bahaushe kadan ne yake tsarin al,ada duk koyine da addini bahaushe yake abinsa.
In banda yanzu da boko ya sauya wasu suke ganin tsarin na farko ba tsari bane akwai tauyewa acikinsa yasa karfin zumunci da bahaushe yake girmamawa ya rage a zukatan mutanen yanzu sosai bisa ga mutanen baya da suka kwanta dama.
Allah ubangiji ya jikansu da rahama ya gafarta masu albarkan kalman shahadan da suka rike a bakunansu Allahuma amin.
A kwana a tashi hasaran rayuwa inji malam bahaushe buki dai ya karato kowani bangare sai shiri akeyi inda hjy mum gwaggona uwar dakina itama ba,a barta a baya ba wajen shirya yarta da zata kai aure watau ni ke nan.
Don ko wani tsimi wani gunba wani hayakin jiki dana tsuguno da siracin irin na shuwa duk nashashi a wajen hjy mum don sai dare yayi kafa ya dauke zata tasani agaba da wa yanan abubuwan tun ina sha ina amai har ya fara zama min aciki saidai idan nasha zuciyana ya dinga tashi inyi ta barci.
Sai yanzu nake tuna abubuwan nan don tun ina karama muke shiga daji debo wasu ganyewa matan gidan mu na kauye wani lokacin muke hada masu kafin yan sari suzo daga birni suna saya.
Wanda sai na mahaifiyata ya kare kafin saura su samu shigar da nasu don ita tasam hadi don hakanema nima na koyi hadin ina taimaka mata wajen hada abubuwa.
Sai yanzu tunanen hadin yake dawo min arai naga ai nima nasan dame dame ake hadawa ya zama gumba ko hayaki ko gari da sai sauran haki irin na yar mai ganye .
Tabbas sudin ne don na tuna da dandanonsu hakan yasa na fara tuhumar wasu daga ciki sun fito hannun mahaifiyata ke nan.
Saboda nasu hadin na El,sutura daban ne dana saura ba irin hadin neman kudi bane kawai hadine na sahihi da masana tasirin ganye a jikin dan adam suke hadawa mata don amfaninsu.
Hadine mai inganci dake saukarwa mace da ni,ima da gyaran jiki ki koma abin sha,awa agun kowa duk wanda yasan asalin yar mai ganye yasan yadda maganinsu yake da kyau da tasiri agun manya da yara don ita yar mai ganyen asali bata tsaya iya gyaran mace ba kadai har yara da masu lalura tana taimakawa da magani cikin yardan ubangiji kuma a dace harma da maza wani lokacin suna dace idan sun samu yar asalin yar maiganyen na ainihi.
EL,SUTURA TANA SOKOTO YANZU HAKA ZAUNE GA DUK MAI BUKATAN MAGANIN TA NA AINIHI HAR GOBE AKWASHI KU GARZAYO KUSHA MAMAKI DA IKON ALLAH .
Saura kwana hudu bukine anty Nafisa ta turasasa min binta zuwa wajen gyaran jiki inda ta kaini wani shagon gyara na mata suka fara gyara min jiki tun daga kaina zuwa tafin kafana basu barshi a baya ba .
Don bayan dilka ga kitso ga kumshi ga kuma turaren jiki bayan wanda hjy mum ke banka min din itama ta dora nata akai don hakane duk inda nazo na tsaya zan bar wajen da kamshi.
Duk da ba fita nakeyi ba ina dakina ko dakin mum in kafa ya dauke kuma a falonmu .
Saidai hakan bai hana halimatu yawo da sunana wajen classmates din mu da sunan raba chewegun din buki tana tallana cewa auren hadi za,amin ai.
Mijin baisona amma ni sai rawan kai nakeyi dan naga dan maikudine tun yanzu na dara dagawa mutane kai shine ita tace bari tazo ta kawo masu IV don kar,a manta juna.
Wanan dalilin yasa Anty Nafisa daukana kowa bai sani ba gidan takaini wajen gyaran jiki don ta fahinci irin makircin da sukeyi suna son bambanta sha,anin da wani manufa.
Sai gashi suna ganin gyaran da akai min sai kuma ya koma tsone masu ido ni ina ta kaina su kuma suna hassada dani bansan dalilin wanan abin ba nasu akaina koda yake ba abin mamaki bane don mummyce uwarsu fa.
Hakama kawayen da halimatu ta gayato sai sunzo zasuga aiba gaskiya ta fadaba don yadda suke samuna cikin rashin dadin rai a lokacin zasu fita suna gulma nan dai Allah zai wankeni akan zargin su gane gaskiya a take.
Nida kaina na fadawa wayanda muke courses tare yanzu gaskiyan abindake faru dani sun kuma tausaya min jin zanyi aure da fara karatun mu ta hanyansu suka kara walwalewa kawayen namu gaskiyan al,amarin sabanin abinda halimatu ta fada masu kaina.
Ban taba ganin mahaifina ya shigo wurin hjy mum ba harsu kebe su dade suna magana sai a yau da ya saura kwana biyu daurin aurena da yaya Hafiz ba alamansa nasan wanan maganan kodai wani daya shafi rayuwanane ya kawo baba wajen hjy mum din har suka dade irin haka suna tataunawa a falonta dashi.
Daddy ko ance kallo daya zakai mai kagane hankalinsa ba a kwance yake ba don ance ya fada sosai don tashin hankalin abinda dansa keson yimasa na bashi kunya ga yan uwa da mutanen arzikinsa ga kowa sunan hafiz ya sani a cikin yayansa don haka sunajin auren Hafiz ne ai zakiji mutum yace insha Allahu muna nan zuwa damu za a daura auren.
Wanan ganin da nayiwa baba da mum ya kara daga min hankali sosai da har na kasa fitowa washegari ina kwance a daki sai da mum ta leko tana fadin wai ke lafiya kin shige daki tun safe baki leko ba.
Zaune nakena mike kafa saman gado dake nuna alaman lafyata kalau illa da dumuwa kawai ke damun zuciyana lokacin na dan dago da zuman kallonta saiga hawaye ta ko ina idona sunyi hulu hulu saboda kuka da naci.
Kai haba mama yanzu kuma don Allah damuwa ko kukan nan meye kikeyi hakane don kawai ki tonawa kanki damu asiri mama.
Ya kamata ace kinsawa zuciyanki dangana game da zancen nan don kin gani a zahiri tun ainda aka fito har kawo yau din nan babu alaman canji ko gezau ga Alh gareku.
Aiya kamata ki dauki hakan a matsayin kaddara ki yarda ki amince da hakan kaddarakice mama yin biyaya zaisa kiga Allah ya sakawa rayuwanki ba zaki taba tabewa aduniyan nan ba insha Allahu.
A hankali na iya dago kai na kalli mum din ina fadin mum badon wanan nake kuka ba ni ko waye daddy zai ban ya bani amma ba ya hafiz mashayi dangiya da,,,,
Haba mama kul na sake jin wanan kalamin a bakinki kin taba jin inda hannunka ya rube ka yanke kayar wanan dalilin na cikin nacin auren ku da Alh keyi don yasan irin tarbiyanki yana fatan ta dalilinki hafiz ya shiryu nan gaba.
Mum ta ya ni zan iya shiryashi bayan Allah daya haliceshi yakewa sabo ga kuma daddy da mummy aisu ya kamata ace sun gyara abinsu bani ba ni har wani hikima nake dashi da zan gyarasa.
Addinin ki da tarbiyanki mama dasu zakiyi amfani ki gyara dan uwanki dashi ke dai kawai banda garaje kinsan halin hafiz sai kin bisa a sannu.
Ba kuma ance da zuwanki ki fara masa zancen shaye shayenshi ba a,a cikin hikima da basira da saka wa,azi da kuma addua idan da rabo sai kiga kinyi babban jahadi kin kwatoshi daga wanan mumunan dabi,an.
Ki tashi maza ki wanka ki gyara jikinki kamar kowa don gida ya fara cika da baki ko tun yanzu don yan katsina na nan sun fara isowa kuma suna tambayan ina kike ki kuma adana duk wani abinda kikeso cikin wardrobe dinki ki kulle ki miko min key din na rike a hannuna tana kaiwa nan ta juya ta fita daga dakin.
Jin hakan dole natashi nashiga bayi nayi wanka na fito na samu wani yadin material da akaiwa dogon riga na saka a jikina.
Mum ce ta kwala min kira daga dakinta na amsa nashiga take fadin in dauki abinci inci itama shi takeci a lokacin ban jaba na dan diba a plate nan na zauna ina tsakura saiga anty Nafisa ta fado dakin.
Lah ke kina nan zaune a daki ba zaki je wajen event din naku ba kai na dukar kasa kafin nayi magana mum tace bamu tsara wani event ba don walima kawai.
zamuyi a bangaren mu.
Haba mum ina tare da yan uwa zatayi komai ko ?
No Nafisa kinsan halin yaran nan don Allah barshi a yadda muka tsara zamuyi walima hade dana saukarta shike nan itama idan mijinta nason suyi event idan ya iso saisu tsara abinsu amma barsu can suyi abinsu don Allah mun ta kakabe zancen.
Ta danyi shiru kafin ta juya tana fadin Allah kyauta mum don dai kinkine amma ina wajen ai waya isa yai mata wani abin bayan gani wajen a dai bar zancen har mijinta ya iso garin.
Mum kina ganin wai hafiz zaizo garin nan ko bakiji irin kwasan rikicin da sukeyi da daddy bane tun shekarajiya kan zance guda.
Ban tsamani zai shigo don ko mum yau naji ta kirashi da safe tayi masa kaca kaca ko zaiji yazo ban sani ba dai ni har mamaki yake ban wallahi waima baki san wani abuba mum ?
Mum din ta kalleta tayi mata signal da ido ta daina zancen a gabana saita juya tana fadin barin dawo mum yanzu ina sauri sister mum ta hanaki zuwa ko ?
Dan murmushi nayi bayan fitan ta mun ta juyo tana fadin nasansu yaran banzane basu da kwabo sai kunje wajen taron nan su nemi su wullakantaki a can gara dai ki zauna gida kawai.
Mum nima ba zanje ba don ban ra,ayin wanan event din da zasuyi yau ai yanzu dai na fada mata taje can ta sanar dasu na hanaki duk wani program nasu da zasuyi.
Washegari yan katsina suka shigo kusan mota uku na mata bada maza ba wai wasu suna baya tafe ashe yan uwan inna ma sun shigo a ranan su da yan kauyen mahaifin mu baba.
Wanan kauyen da muka fara zama a cikinsa suma sunyo gaiya sunzo don sheda aure da za,aimin a lokacin suyi kokari sosai gaskiya yadda suka kashe lokacin su zuwa har kano wurin bukina din.
Saidai duk a gidan iyayyena suka sauka basu sauka a gidan daddy din ba don haka ko gidan mu basu huta da jama,a ba don an taru a can din ma.
Daddy da kansa ya sauke abinci a can duk dako mahaifina yayi nasa kokarin ya tanadi abinda zasuci har su koma amma duk da hakan saida daddy yayi nasa kokarin.
Washegaru mum ta tura akaje akai min jere duk da daddy yai muna komai amma kuma saida tayi nata na fannin uwa a waje an gyara gidan tson kowa ya dawo yana yaba kyawonsa da tsari.
Yayin da bangaren mummy sunje su tun saura sati daya buki sunyi nasu gyaran dakin wa diyansu acan garuruwan da za,a kaisu din .
Don sun fara tsegumi akan mum wai dama ai sunsan ba zata taba yimin wani abin kwarai a rayuwanta ba tunda bata da alheri bautar dani kawai tayi.
Balle ba zata kai min abin kwarai ba ai tunda tasan hafiz zan aura don kawai tana bakin ciki da hassada dashi yana dan mummy haka dai suke ta tseguminsu .
Sai gashi sunji cewa mum ta tura an gyara mun daki aka shiga lissafo irin abin arzikin da tayi min mummy sai baki ya mutu kuma ta koma fadin ai dole tayi min hakan.
Dama ta rikenine don ganin iyakar mummy din don ta nunawa duniya ita ba kowa bane san nan ai sun san komai duk abinda aka gani daddy ne ya bada kudi a boye akaimin shi son kawai ya farauta muna rai.
Niko nace ashe mummy tasan dan nata abin banzane ke nan tunda har take iya zaton daddy ya hada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login