Showing 87001 words to 90000 words out of 103712 words

Chapter 30 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7851

sai dare zan dan nemi abin da zanci in kwanta sai hankan ya fara kwantar min da hankali.
Kwatsam saiga mummy da kawayenta wani safiya wai sunzo ganin amarya don basu samu zuwa ba saboda gajiyan buki suna wani dan yatsune yatsune da mede baki kamar sunga kashi.
A cikin ladabi na taresu na kawo masu ruwa don shi ke gareni gidan lokacin to ba maigidan balle ya sawo min wani abu ko ruwan nice naba maigadi kudi ya sayo min bag biyar na ruwan don masu zuwa ganin amarya duk daba wasu jama,a ke zuwa ba sai in wuni ma wani bai shigo gidan ba ranan.
Yo ga tsiya mune zaki tara da ruwan leda ko haka uwar naki kikaga tana taron baki inda kika baro ?
Koda yake ba mamaki hudubar da tayi maki ke nan kike gwadawa a yanzu ai in ba rashin tarbiya ba munyi maki kama da masu shan ruwan yaku bayine a nan.
Sai naji dayan matar tace ki barta muko takawo ba zamu shaba ai ruwa na gida mun bari ke dai yarinya dauke ruwanki a nan dama mu ganin gidan dan mu mukazo muyi ba wani abu ba.
A take idona ya kawo kwalla dakyar na iy furta kuyi hakkuri mummy shi kadai nake dashi a gidan nan bansan zakuzo ba danayi maku tanadi ai.
Lah yar nan ke kuma da sherin da kikazo ke nan batawa dan mu suna kan bai kula dake kome ?
Rudewa nayi lokaci guda ina basu hakkuri daba haka nake nufi ba iya gaskiyata na fada amma suyi hakkuri don Allah sai naji mummy din taja wani uban tsuki ta mike tana fadin.
Kunga irin abinda nake fada maku ko dama nasan yarinyar nan ba karamin makirci aka kulla mata ba da zatazo tayiwa mutane gashi ko tun ba,aje ko ina ba har ta fara.
Don Allah ku tashi muje da wanan abin haushin da muke gani a,a hjy malka ba,a hakana yanzu me yarinyar nan tayi kuma wata daga cikinsu ta fada .
Ku tashi muje don Allah da wanan bakin takaicin da muke gani a nan din dama abinda Alh ke so ke nan inga bakin ciki ya dauko wanan yar tsiyar ya mannawa hafiz don bakin ciki ya kasheni gashi kuwa .
Ai hafiz din zai dawo koshi yaji wanan rainin wayau da kikai muna ba zai kyale ba ai mune zaki wani tara da ruwan leda kamar kinga gayyan yan kauye.
Da kuka na kira mum ina fada mata ashe lokacin suna tare dasu Dada har da anty Nafisa hakkuri mum din ta ban tace wanan shine auren ai mama.
Mun fada maki sai kinyi hakkuri ina jin muryan anty Nafisa tana tambaya meya ya faru mum din tace ba komai ta dai ban magana muka kashe waya .
Halan mummy ko don naji suna waya dasu hjy Ramatu yau zasuje gidan suga gida na mantane wallahi in kira ta in fada mata zuwansu din nan mum ta labarta masu abunda ya faru tsakanin mu.
Anty nafisa tace sai tayiwa mummy din magana hakan nan dai sukace ta barta dama sai an samu haka ai tsakanin mu kafin a shirya take fadin don me mummy zataje gidan yarinya suci mata mutunci.
Toke Nafisa aiyin maganan naki zai kara rura wutan abin tsakaninsu kawai dai kije kikaga mama din ki bata magana in ma wani abune dole ta kyale akan cewa zatayiwa mummy din magana da tayi niyar yi da farko.
Ita ko mummy hafiz din ta kira inda take shiga ba nan take fita ba ta kwashi karya da gaskiya ta fada mashi ya hau yana batsewa yana fadin i can't mummy ba zan iya zama da wanan yarinyar ba gaskiya.
Kece wai har yarinyar nan zatayiwa wullakanci tace ba dole tayi min ba tunda tana ganin Alh ya daure mata gindi zama da kai dolene ko bamu so ai dole tai muna haka taga gidan mike kafa a dole.
Wani shu,umin murmushi yayi kafin yace a ina fa mummy kawai ta bari inzo in sameta gida zata raina kanta wallahi mutane kamar mayu duk wanan bai isheta ba sai ta gwadawa mutane ita yar dajine ko zanzo zanyi maganin yar iska ai.
Hutun mu har ya kare na sati uku don hakane ranan na bugawa daddy waya ina sheda mashi ya danyi shiru kafin yace dani to uwata ba zan tauyeki ba a gida in hanaki zuwa abinda zai fisheki ki shirya kawai ki koma school din ki kici gaba da karatun ki tunda shi haka yaga yafi mai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/2, 21:07] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: [3/1, 07:51] +234 706 511 1949: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2?? 8??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Zaune take a falon tana katatun littafin da take kai a Islamiyansu yayi sallama ya shigo falon nata ta dago daga karatun tana amsa mashi.
Kallo daya tayi mai ta fahinci akwai matsala koda bai fadi ba tasan akwai matsala a wani bangare hakan yasa ta rufe littafin da take duba din ta fuskanceshi.
Zaune yakai har tsawon wani dan lokaci kafin ya dago yace zancen hafiz ne dai yake damuna don ban fahinci me yake nufi da yar mutanen dake gidanshi zaune ba da muka tauye.
Dazun ina shago ta bugo min tana fada min cewa hutunsu ya kare tana son ta koma karatun ta watau hakan ke nan yana nufin bai waya da ita tun tafiyansa ?
Dan murmushi mum ta sake a fuskanta kafin tace ai kaima ka sani Alh ban tsamanin cewa hafiz nada number mama a wayarshi.
Kuma hafiz bai yarda ya karbi auren mama ba kamar yadda kake zaton ka shawo kansa daga baya har ya yarda ya amince nina sani saidai sanin baida amfani a gareni .
Tunda banda power din da zan dauki mataki alokacin da nasan haka din wayar yarinyar nan samira dake hannun mama din a cikinsa mukaga irin yankar kaunar da yai mata ranan da kuka kaita kuka fita.
Mikewa ta tashi tayi ta dauko wayanta data tura ta kunna mashi yayi shiru yana sauraren rashin mutuncin da yake shuka min a lokacin har lokacin da aka fara nocking kofa ya fita da dan hiran mu dasu Anty da suka shigo take fadin har yanzu kukan rabuwa da mum nakeyi ne ?
Nisawa daddy yayi kafin ya dago kai ya kallo mum da idanuwansa da sukai ja jajir dasu yace lalai yaron nan yakai dan banza yana ganin banda sauran amfani a garesa yanzu ko ?
Tunda nagama masa wahala ya girma yana ganin yanzu kafansa shi sun kama kasa sakaiyan da zai mun ke nan kafin ta kiraka ni ta fara kira ai mum ta katse mashi magana don luran da tayi ya fara fita hankalinshi lokacin.
Cikin hikima ta fara canza zancen da fadin tana kirana ta fada min wai tana jin tsoron fadama shine nace dole saika sani ai wanan yasa ta kiraka.
Alhamdullahi ai tunda ita yarinyar bata bijire muna ba har yanzu tasan a karkashin iyayye take tana kuma biyayya ka kyaleshi kawai shida kansa zaizo ya gane cewa yayi kuskure abinda yakeyi a yanzu.
Yin shirun ka shi zaidaga masu hankali zasu shiga tashin hankali don basu san me shirun ka yake nufi dasu ba amma idan kai magana abinda suke nema ke nan dama rayuka sukai ga baci a yanzu ka kyalesu kawai ka saka masu ido zaifi.
Illa iyaka ita mama mu saka ido akan al,amuranta a bata kula yadda ya dace ta yadda damuwan hakan bazai dameta ba ni shawarana ke nan .
Ya shafo kai yana fadin neman maganane nina sani kuma da hadin bakin uwarsa yake hakan duk abinda hafiz keyi malka tana da labari don hakan shawaran ki ya kawo min mafita a cikin zancen nan yanzu ya mike ya fito daga dakin nata .
Ranan monday da safe bayan na shirya naji horn direban dake kaimu school ne yazo daukata shiya kaini makaranta a ranan da aka tashi kuma yazo ya daukeni .
Anty nafisa bata san da cewa nashigo ba don bamu hadu ba ban kuma nemeta ba don banba office dinta ba har na dawo gida don a yanzu ko waya bamayi da ita tunda aka kawoni gidan dan uwanta halakar mu ya danyi rauni tsakanin mu.
Bansan dalilin hakan ba amma tun lokacin buki ta fito da wasu abubuwa gareni mum tace a shareta kawai nikan badon mum ba gaskiya da bansan ya rayuwana zai kasance ba a cikinsu.
Hankalina kwance nake karatuna ban sakawa zuciyana komai ba inci mai kyau insha maikyau ba abinda ya dameni saboda kurciya har mantawa nake da nayi aure a lokacin don wauta.
Sai wata ranane malam isah ya daukoni zamu dawo gida muka hade da ita a daidai get tabi motan da kallo don sanin motar gidansuce wanan .
Sai lokacin ta ganni ciki zaune a baya malam Isah yana jana zai mayar dani gida mamakine ya rufeta a lokacin tabimu da kallo har muka bace mata.
Malam isah din ke fadin ga hjy Nafisa can ko mu tsaya ne nace a,a mu wuce kawai illa iyaka ya danyi mata horn ta mayar masa itama muka tafi.
Mamaki tayi sosai har takai inda zata kafin ta dauki waya ta kira mummy tana tambaya dama ashe yarinyat nan tana zuwa makarantane mummy yanzu naga malam isah ya daukota zai mayar da ita gida.
Wace yarinya ke nan mummy ta sake tambayanta tace Zeey mana ta nan gidan matar hafiz ta fada kai tsaye sai uwar tace kika ganta ina tace school mana mummy na dauka aitamooiu n dainane yanzu don auren nan.
Kima daina zancen nan don Allah bari nakira hafiz din inji sai yar ta katseta da fadin to meye mummy idan taje school tunda dama tana karatunta ba sai a barta tayi ta zuwa ba.
Wai meyasa ke baki gane abinda ake nufine baby wanan fa anyi hakanne da wani manufa sai yanzu nake gane nufin dan iskan yaron nan me dadin bakin tsiya da har ya bada shawara kan taje karatu zaifi.
Watau ita tayi karatu su mairo ko suna gida zaune wai suna aure ba damuwansu bane su kinga abinda nake sha fada maki ke nan baby amma kin kasa fahintana dake ke nan suke son jayayya a gidan nan tunda hjy kubrah bata da diya mace sai wanan yarinyar.
Haba mummy ni kuma Zainab fa har yaushe zainab zata iya kaini balle su tsaya kwatantawa dani don Allah sai dai idan suna da wata manufa dai ta daban akan karatun nata dai.
Shiko hafiz din data kirashi bai dauki waya a lokacin ba sai data masa da dare ya dauki wayan suka gaisa ta fara fadin kai ka umurci yarinyar nan da tafita zuwa school ?
Wace yarinya ke nan mum ya tambaya tace matarka mana zeey dazun baby ke fada min ta ganta malam isah driver ya daukota daga makaranta.
Mummy akan zancen yarinyar nan kika kirani don Allah kibar kirana kanta mummy don banson ai min zancen wanan yar iska don nabarwa daddy ita shida ya matsa sai anyi auren nan to anyi din ban bashi kunya ba sai su zauna da ita din mugani.
Wai dama har yanzu tana gidan a matsayinane kota koma gida tace kai hafiz ka natsu ka saurareni kaji me zan fada maka akanta.
Don na rarasheka ka yarda ka aureta hakan ba yana nufin ka fita zancenta yadda kayi din nan gaba daya bane don akan zancen nan na tabbatar da Alh zai iya saba muna gaba dayan mu daku.
Koma yayane akala ka dan kula da ita a matsayin matarka kana dan zuwa baka share haka ba har ana neman kwasan wata baka leko ba me hakan da kayi yake nufi ke nan ?
Gaskiya mummy i can't ban taba jin wani feeling akan yarinyar nan ba kwata kwata wallahi mum banko son in ganta a rayuwana wallahi kai kadakata da wanan shirmen ka saurareni kaji me zan fada ma.
Nan dai ta koma lurar dashi abinda ya dace yayi har ya fahinceta don a yanzu ta fahinci Daddy ya juya mata baya itama duk da bata san dalilin hakan ba saidai ta fahinci akan zancen dan natane da yake ganin bakinsu daya ya kawo sauyin nan tsakaninsu.
Don yanzu iyakan daddy da ita ina kwana ya amsa mata a daure ko kuma inta kawo abinci daga part dinta zai zauna ya danci wani lokacin wani lokacin kuma ko kallon abincin baiyi zai barshi a wajen.
Bata saba da irin wanan rayuwan ba sai abin yazamo mata sabon ak,amari don hakane tayi shawaran cewa dole sai tasa dan nata ya natsu kafin ta fahinci inda Alh ya dosa da ita.
Bawai tana nufin ya zauna dani dole bane a,a suyi nasu irin takon suma su nunawa Alh din ai suna tare dashi da hakane zata fahinci me yake nufi da canzawabshi.
Duk da dai bai sake mata magana ba akan dan nata amma tasan shirun shi a yanzuma din maganane bawai ya kyale zancen bane akan a tafi a haka hakan na nufin shima da nasa shirin akansu ke nan.
Anty nafisa bata dadara ba saida ta dauki waya ta kirani bayan sjn gama waya da mummy tana fadin sis ashe kina shigowa school shine baki taba nemana ba sai yau dana ganku din nan ?
Ina zuwa anty iyakaya department din mune kada nayi wani laifi kuma ace ina yawo donshine ban zuwa ko ina idan nashigo amma kiyi hakkuri don Allah na fada a karshe.
A,a aiba komai nafahince ki amma ki sani dake da hafiz din dukkan ku kanne nane don kinzo waje na bashi zaisa a jefiki da wani zargi ba sai dai idan dama kina da wani manufa akaina.
Na danyi murmushi na sake fadin anty kiyi hakkuri ba haka bane na fada maki gaskiya kawai don ki fahinceni bayaga school a yanzu babu inda nake zuwa kuma.
Gidan na bude nashiga ina sauke ajiyan zuciya tare da zama ina bin ko ina na gidan da kallo kafin in sauke ajiyan zuciya ina lumshe idona na fada bayan kujera na fara tunane.
Wayana dake aje gefena dana aje yake dan haske alaman kira yana shigo min a lokacin na dauka ina kallo number kasar wajece Canada na gani a rubuce.
Na sake maimaita sunan garin har kiran ya tsunke ban daga ba don ina tsoro banda kowa dake kasan waje da zai kirani nayi tunane a zuciyana lokaci guda.
Saiga kiran ya kara shigowa again nayi karfin hali na dauka na kara a kunnena ba tare da nayi magana ba sai naji muryanshi yana fadin.
Keda wullakanci ana kiran waya kina share mutane me kike daukan kankine wai ko kin dauka kina da wani matsayin da za,a kirakine wai ?
Muryanshine ba tare da sallama ba yatareni da fadin hakan daga daukan wayana kafin ya koma fadin ke ina kika fita kikaje ba tare da sanina ba ?
Wai waye hakane don Allah kamar ba musulmi ba daga daukan waya sai bakar magana kamar mara hankali to wrong number naja tsuki na kashe waya kai tsaye.
Ina jin yana fadin kika kuskura kika kashe min waya wallahi dip na kashe wayan ga baki daya ina jan tsuki nace wawa dab giya kawai kafin in koma fadin.
Lalai mum tayi gaskiya da takece min na kula da Anty Nafisa don yanzu a matsayin yar miji take a gurina watau dan ganin nan da tayi min har ta buga masa waya kai lalai mutum abin tsorone duniya.
Wasu zafafan hawayene suka zo min lokaci guda suna sintiri a fuskana har sai yaushe wanan zai fahinci iyayyenmune na tambayi kaina ina runtse idanuwana a cikin takaici.
Wanan kila ya kora tsiyar nasane yake son ya karanto min hauka daga kawai fita zuwa school inba abin dan giya ba zaka kirani kana zagina.
Na dade zaune a wajen kafin na mike zuwa dakina na sauya kayan jikina zuwa na shan iskan gida banso yin girki ba amma dole nayi saboda maigadina tun lokacin da yace min shi bakone daga kauye yazo neman abinci kano ya samu gadi nake tausayinsa.
Dadina guda shine Allah baiyini da yawan magana ba don haka ban fadawa kowa abinda ya faru ba balle a ban shawaran na dakata da karatuna dana kwallafawa rai.
Don hakane washegari na shirya na nufi school duk da zancen ya tsaya min a raina ni kadai nake hade abina tunda banda abokin shawara a lokacin.
Ina nan zaune da yake ina fashin sallah naji sallama a gefena na dago ina amsawa watace tsaye a gefena take fadin ko zan iya zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login