Showing 45001 words to 48000 words out of 103712 words

Chapter 16 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7834

Nayi murnan jin hakan da suka fada din sosai don haka na samu waje na zauna a nan din tunda Dada ma bata nan tare suka tafi da ita donshi na zauna a nan din ina mai mata adduan sauka lafiya a zuciya.
Don nasan hakan tun ina karama a kauye da baffa Ado yayi aure wajen haihuwan farko amaryan nasa mai kyau da ita ta mutu abin ya tsaya min azuciyana don na kasa mantawa da hakan.
Ajiyan zuciya na sauke kafin na mike na fada dakin anty Nafisa anty Nafisa badai kazanta ba kan na fada a raina don dakin ga komai nan a yashe kasa ko ina ka duba kayane datayi amfani dasu ta kasa daukewa zuwa muhallinsu.
Tsab na gyaro dakin har bandaki da ko ina sau daya Asiya ta dan lekoni don jin motsina datayi a dakin taga ko waye a ciki take fadin au kece ashe kina da aiki kuwa indai dakin nan ne .
Don har pant sai kinci karo dashi a dakin nan indai Anty Nafisace zaki ganta a waje tsab amma a gida kuma kazan kazan da ita bata daga hammata ki shaka wanan ya san ban dariya ta fita tana tabe baki wai kazanta ance gwano baya jin warin kansa tunda kusan duk haka suke.
Don basu koyi ko kawar da kara da kansu ba yan aiki ke masu a baya saida fitinan mummy yayi yawa daddy yace ba zai kara daukan masu yar aiki ba kuma kowa ta sallami masu aikinta.
Da farko suna ganin ai hjy mumce zata sha wahalan haka sai gashi sule wahala a yanzu son ko basu saba ba don haka basa iya kula koda muhalinsu a yanzu.
Sunkai awa uku sai gasu sundawo da ita wai ruwa aka kara mata malaria ke damunta ashe haka muka kewayeta a falon mummy muna mata sannu tana amsawa da kyat.
Yayin data yunkura da kyat tana tashi gwanin tausayi ta nufi kofan dakinta duk muka bita da kallo lokacin hjy mum kece min ai ina can ina tunanenki don nasan yanzu kun dawo daga school din zaki samu kofa a rufe.
Nan nazo na bata amsa yayin dana gusa ina karban ledan hannuta wanda lemune ne a cikinsa mai yawa ta sayo don naga an aje wani a part din su anty Nafisa din hakan yasa na juya da zuman in karbi na hannun mum din.
Sister kin shigo dakin nan ko muryan anty Nafisa ke fadan haka nace ehh na zata ai haihuce zakiyi don shi na gyaro dakin kada baby yazo ya samu dakin a haka .
Wai kekan kina da bakin iyayi wallahi kamar tashin kaka duk wani zance da iya fada a bakinki ake jinsa mairo ta fada tana jan tsuki a,a yanzu kuma meya kawo?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? wanan maganan .
Idan ta iya fada a cikin hikima ba kacaba irin daku kuka gada don ku kome yazo a bakin ku haka zaku iya fadawa mutum shi a lokacin.
Don ta gyarawa yar uwarku daki haka kuma laifine ashe don baku raina abin wullakaci ku ko yaushe kuna gadara ana zaune gidan ubanku to uban naku bai iya raba daya biyu ba kamar yadda kuka iya.
Dadace data kai kofa take fadan hakan ga mairo itama kai tsaye nan mairon ke fadin gawa muka gaji hakan agunki ko cikin jin haushin abinda Dada ta fada mata.
Haba don Allah baku bari wanan zancen meyasa kuke hakane ta kallo inda nake tana fadin mujemu kiyi min abu ni dai muka fice muka barsu a nan har Dada don tana gaban mu muna bayanta muka fita daga part din.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/14, 11:11] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

1?? 7??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Alhamdullahi yanzu dan dawowan mummy din nan zance don ta rage tsiwa da jiji da kai din nan nata a yanzu sosai don haka fitina da yawan tashin hankali ya ragu a gidan yanzu sosai.
Yadda na lura ayanzu hjy mummy din bata da wani power yanzu kamar da datake shimfida ikonta da mulki iya son ranta kamar sunanta Malka.
Don a yanzu daddy kamar bai damu da ita ba a gidan ta zama powerless ga komai yanzu haka zaliki a yanzu na kula komai kamar da hajiya mum yakeyin shawaransa saiko ya,yansa.
Don ko yana kasuwa kan ya dawo zaiyi waya da hjy mum yafi a kirga kan abinda ya shafi rayuwansa na gida dana kasuwa ranan ma ina zaune inawa hjy kitso ya bugo hakan baisa ta tashi don kada inji me zasu fada ba.
Complain yake mata a cikin tashin hankali cewa kaninsa dake Enugu ana fadan kabila a can yanzu haka suna kulle a cikin gidajensu kwana biyu ke nan basu fita ba har iyalansu.
Nan mum kebada shawaran su samu hanya su dawo arewa kawai yafi masu sauki da zaman dar dar a can kullun daddy yace nima haka nagani zan kirasa yanzu na fada mai shawaran dana yanke akai din.
Saidai yayi warning kada abar Dada taji wanan zancen don kada hankalinta ya tashi takuma dagawa mutane hankali ana cikin wanan kuma naji mum tace ina fa ai gara ta gansu kawai sun iso shine kwanciyan hankali a yanzu garemu sukai adduan Allah ya fito dasu lafiya har nima dake tsaye bayanta ina kai tsoron kintson na amsa da amin lokacin.
Kingani ko shiyasa zama a cikin kabilu wani lokaci badai dadi mutum at list ya bar rabin iyalinsa anan arewa rabi kuma na can komai zai faru sai yazowa mutum da sauki amma irin wanan ina dadi duk suna can har shi cikin halin hau,ilahi hannu a gaba.
Washegari kuwa naga an fara gyaran part din dake gefen Dada nasan ko a nan zasu zauna ke nan sai a lokacin nagane hikimar masu kudi da suke gina babban gida ka rasa me mutum zaiyi a cikin katon gida yanzu na fahinci hikimarsu nayin hakan sai kamar bayan kwana hudu suka iso kano.
Alokacin duk su daddy har matansa sun gama rudewa da halinda dan uwa ke ciki can lokaci lokaci mahaifina zaizo koda safe koda yamma su dade da daddy din nasan suna shirya yadda dan uwan nasu zai fito ne da iyalin nasa.
Allah ya taimaka suka fito lafiya tare da matansa biyu da yayayensu sun iso kano a wahalce gidan daddy din duk sun fice hayacinsu suna bada labari a firgice na irin tashin hankalin da suka gani a can din.
Ni ina school saida muka dawone muka samesu sun iso suna falon mum zaune sunci abinci sun bata waje suna hayaniya da yaransu a sanyaye nayi sallama nashigo.
Duk suka juyo suna kallona gaidasu nayi kafin namike zuwa ciki don in sauya kayan jikina muryan watace ke fadin wanan a nan gidan take itama ?
Ehh diyar Garbace dayazo dazun mana nan take zaune a wajen mai shiyan nan matar tafadawa yar uwarta dake zaune ishishire kasa saman ties din falon mum da alama a gajiye suke lokacin.
Nidai nayi ciki jin motsina da mum tayi yasa ta fito tana fadin kin dawo mama sai kuma kika samemu da baki nace wallahi fa nagansu a falo ai tace matan babangi Ahmed ne dake Enugu sun samu sun fito.
Allah sarki wai munyi barka da suka fito lafiya na fada na shige dakina Allah yagani na debo gajiya sosai ga yunwa a lokacin don haka yasa banson komai ko wani dogon hira a lokacin.
Saida na shiga na tube mafito don in debe abinci inci saidai babu komai duk sun cinye haka yasa na koma ina fadawa hjy mum ban samu abinci ba.
Take fadin abincina yana nan cikin farin kula ta dora sama na koma duk na burkuce kayan kitchen din banga abincin ba na koma na fadawa mum tana jan tsuki da fada ina son na hanata hutawa kawai.
Tana zuwa idon ta yakai wajen abinci yace daukeni inda kika aje salati mum ta saka tana fadin yanzu wayiwa yarinyat nan haka don Allah ko abinci nace za a dafa mata yanzu kafin ya dafu ai wani aikine kuma.
Hjy abu kuke nemane dayan matar baba da sukazo yau ta tambaya sai mum ne ta juyo tana fadi wallahi abincin yar nan dana aje shine ban gani ba.
Au ko shine shamsiya ta dauko a kitchen dazun da tace bata koshi ba kinsan mun jima ba wani cima mai kyau a cikin mu na tsawon kwanaki.
To amma ai da sai ku tambayeni tunda sai kuma tayi shiru ta juyo gareni tana fadin kinga muje ki samu abinda zakici a daki nabi bayanta daidai ina shiga wayata dake dakin mum aje yafara kara na dauka.
Anty Nafisace ke magana tana fadin tana nemana don Allah yanzu a part dinsu nace ganinan zuwa nake fadin antyce ke nemana wai inzo yanzu don Allah.
Kije ba tare da kin samu abinda kikaci ba nace barin dawo mum nafada ina fita daga dakin nata na nufi wajen kiran da ake min din tana zaune a falonsu ta mike kafa kodana shigo tace yauwa sister don Allah magani nake son ki karbo min tafada a kasalance.
Magani wani kala anty dauko min bag dina a daki in baki kudin tun dazun nake neman mai sayo min maganin nan ban samu ba, bag din dana dauko mika mata karba tana budewa yan naira dubu ta miko min tare da kwalin maganin.
Bayan na karba na juyo naji muryanta tana fadin sister meya faru naga kamar ranki a bace mana ba komai anty banci abinci bane abincin da Mum ta aje min wanan bakin wai sun dauka sunci.
Haba dai is undead kashe ki suke son yine don Allah ya zasu daukar maki abinci zo zo nan ta fada tana mika hannu gareni ga cikinta da yai wani kato a gabanta nace cikin yar murya No barshi kawai inje na sayo maki ai.
Ban jima ba na dawo daga sayen maganin har canji na mika mata lokacin kuma yaron dake dan zirga zirga ya dawo daga aiken da tayi mai don bata da aiki sai faman aike da kashin kudi shiyasa bata shiri da kannenta ko kadan a yanzu.
Mika mata Allah yasa dai ki iyaci ta fada tana kokarin bude ledan maganin dana sayo mata din tasha kaina girgiza ina fadin ki barshi No kefa nasa ya sayowa shi dama.
Lokacin na dago kai ina fadin nagode na juya zan tafi take fadin idan kinje can zasu bari kici kuwa don haka suke dama kamar yan yunwasu balle wanan abin ya faru zan shiga daki naci na fada ina juyawa na fice.
Banci ba saidana biya wajen mum na nuna mata tare da mata bayani ta danyi shiru kafin tace jekici ai Nafisa bata da wani manufan sheri akan mutum ita.
Wani lokaci idan Hjy Mum tana irin zancen nan nakanji haushin hakan a zuciyana sai in dauka dukkansu dai suna da bakin kishi a zukatansu kome basu da yarda a kan dan uwa dukkansu din.
Ta ya daga ban abinci zata furta rashin yarda alhalin tana kwance a inda na barta ita bataje nema min abinda zanci ba an ban kuma tace wai tana zargin abincin bayan a gaban idona aka sayoshi ina kallo ko karban ledan take away din batayi ba.
Haka gidan ya koma family house don saida suka share kusan kwana uku a tare damu kafin su koma part din da aka gyara masu din da zama suka barmu da aikin gyaran waje.
Saida hakan ya dan sani zazzabi kwana biyu don komai dagani sai mum keyi daga su har iyayyensu suna zaune suna kallo ko hira kafa mike abinsu.
Munyi barka komawansu wajensu din don yanzu ko hayaniya da koke koke yai muna sauki ko haka kawai zakiga danbe ya kicime a tsakaninsu zakice su din diyan yarene ba hausawa ba wallahi.
Don dabi,unsu sam baiyi kama dana dan bahaushe ba gasu a tsatsaye koga iyyayansu wanan yasa na kara nisa dasu din don ko hjy mum da taga zasu shige min yanzune zata kirani ta sakani wani aikin da zai dauke min hankali.
Don yaro ya zagi uwarshi ko kuma yace yayi fushi yana kaiwa uwa duka itako tana dariya adole ga yaro su iyayyen basu dauki hakan komai a wajensu ba.
Gasu dai tsab a ido amma kan gaskiya halin ba kyau ko kadan suna da saurin fita ran mutane don wanan halin nasu naba kwabo a garesu .
Ranan da suka koma din wuni mukayu muna gyaran part din mu wani abin kn saidai hjy mum din tayi hakkuri dashi don sun halaka mata kaya ko yaro ya dauki abu zai barnata uwa bata iya tsawata mashi sai idan yayi barnan kaji ana fadin kai dan nema kawai zan dukeka/ki fa.
Da yake weekend ne mun gama na dan kwanta don in huta sai barci gashi kuma nayi wanka a lokacin sai kawai kasala ya sauka min shine na buge da barci nayi sa,a kuma hjy mum bata tayar dani ba a lokacin kodan tasan na debi gajiyane ta barni oho ?
Karfe biyar na tashi a gagauce ina duban lokaci a dan zabure na mike ganin lokacin danayi na nufi bandaki na dauro alwala sallah na tayar ranan ba zancen zuwa islamiya awajena.
Falo na fito na leka mum bata ciki hakan yasa na nufi kitchen nan ban ganta ba sai na tuno ranan itace zatayi girkin daddy watakila tana part dinshi kuma tana gyara ga girki dai ta dora amma bata nan cikin part din namu.
Tsayawa nayi saidana tuka tuwon tare da hada miya lokacin tashigo a gajiye tana fadin yar albarka kingani na gama wanan na dan shiga wai in rage aiki bakiga uban aikin dana sama ba kuma a can din.
Taja tsuki tana bude kulan dana kwashe abinci zuwa lokacin ledan yayi sutum sutum ciki ya dauki zafi ga tuwon na kwasheshi yan madaidaita daidai cin mutum daya.
Mama ke kan kin huta mijinki baya shan wahalan abinci da gyaran gida komai da akeson ya mace ta iya kingama iyasa Allah ya baki miji dan albarka irin ki sai na turo mata baki hakan nakanyi a duk lokacin da tayi min zance irin hakan.
Niga nawa watauna na tsani aure ayanzu tun akan abinda ya samu anty Nafisa yadda naga suna soyayya da mijinta amma a karshe suka kuma rabu rabuwa mai muni a tsakaninsu.
Hakan yasa a yanzu nake jin na tsani zancen aure ban ma taba kawowa kaina wani zancen aure ba can balle har naji ina son yinsa din a kaina.
Mun karasa kafin magariba don haka a nan baya na dauro alwala nashige ciki ban kuma sake fitowa ba don nasan ranan kwana ni kadai zanyi a part din tunda Mum kila part din daddy zata kwana.
Kwance nake falon ina kallo sai wayana dake gefe ya dauki kara na dan dago ina dubawa Anty Nafisace don wani lokaci takan kirani hakan tace inzo in karbi wani abu a part dinsu.
Nasan kuma ranan bamu hadu ba ko donshi zata iya kirana a lokacib tayi min korafin hakan tace na manta da ita ko naki zuwa inga lafiyanta.
Na mika hannu nayi receiving ina fadin Ayya anty Nafisa wallahi yanzun nake zancen ki a raina yau aik,,,,, muryanta naji cikin wani yanayi hadi sauke numfashi guda guda tana fadin da kyar.
Sister kina inane kizo yanzu don Allah ki sameni a dakina sai naji ta kashe mikewa nayi tsaye da sauri na dauki wayan na nufi hanyan kofa sai kuma na tuna babu kowa a part din mu a lokacin.
Hakan yasa na tsaya na jawo kofan mum dake bude nasaka key na jawo kofan na nufi hanyan part dinsu sauri nake jikina na rawa ina dan hada hanya don sauri.
Ina tafe inawa kaina tambayoyi barkatai na meya sameta naji muryanta a hakane ina mutanen part din nasu suka tafi kuma da wana tambayan har na isa part din nasu nayi sa,a babu kowa a falon hakan ya ban daman shigewa dakinta kai tsaye.
Ina tura kofan na hangota kasa tayi gurfane ta dafa gado ta dukar da kanta kasa da gani tana a cikin wani hali mai muni a lokacin hakan yasa na karasa da sauri dakin ina fadin Anty meya faru meya sameki kuma ?
Ta samu ta dago kai da kyat ta kalloni yanayinta gaba daya ya sauyawa sanin da nayi mata son lokaci guda naga hallittan ta ya canza min ga gani hakanlina ya kara tashi da gagawa na karasa gab da ita ina kiran sunanta.
Dafata nayi ina maimaita tambaya anty meyake damun ki hakane sai naji ta dan sauke ajiyan zuciya a wahalce t dago kai wani uban zufa naga tayi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login