Showing 93001 words to 96000 words out of 103712 words

Chapter 32 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7860

zubo da kunnu ayyah mai dadi na hada nasa a basket sai gida da anty Nafisa na fara haduwa wani kallo take min zakice ranan ta fara ganina muka gaisa na shige part din hjy mum.
Ashe fasa fita tayi taje tana fadawa mummy shigowana dani da basket din ban ko zauna ba mum ta daukeni takaini falon daddy mu gaisa dashi muka gaisa ya nuna jin dadi da ganina din ba cikin mugun kama ba da sukayi zaton ina ciki.
Mun dan dade dashi muna hira kafin na mike don yafita don ba komai bane illa nasiha da saka min albarka kan biyayyan da nayi masu da suke min shida mum din har ya bada basket din yace a kaimai a mota kafin ya fito shida abokansa zasuci a kasuwa.
Yanawa mum sheri da cewa saidai ajin kamshin wanan hadin amma ba mai lasawa a gidan nan tunda diyana tayo min part din mum muka koma a can muke hiran karatuna da mum kafin na mike ina fadin mum bari nashiga nagaida mutanen gida.
Part din Dada na fara shiga inda na sameta a zaune ita kadai tana kallon tv na fado dakin ina fadin halan kina jin abinda suke fadane kin kurawa tv ido haka ?
Saida ta dago ta kalleni da kyau tace ja,ira yau kece a gidan namu ko angon naki ya dawone kuka shigo na kai zaune ina fadin ai kunfi kusa idan ya dawo kece zaki fara sani ai.
Watau Dada harke kika shareni kuka barni ni kadai kamar banda kowa ina rayuwa agida kamar manya kiri,kiri kikaki zuwa mu zauna tare ?
Tace bari yar nan karma kiyi magana don Allah nasan kaf gidan nan mu masu laifine a gareki ai amma don Allah ki yafe muna .
Da sauri na tareta da fadin haba Dada kin taba jin inda iyayye sukaiwa yarsu laifi kome kukai min ai a cikin gatane wata rana sai labari insha Allahu.
Allah dai yai maki albarka yau da ace ba jinin Abu kike ba watace da ba,asan yadda rayuka zasu baci ba da zancen nan lalai hakurima da kawaici gadonsa akeyi na yarda da hakan akanki.
Don kin nuna muna ke jinin Abuce da malam na cikin gida yadda suke kiran kakan mu dashi ke nan lokacinsu dan muskutawa nayi ina murmushi.
Tace yau abin nan da badon ke da iyayyenki masu hangen nisa bane bansan iya inda zancen nan zai tsaya ba ja,iri dan banza zai gama haukansa ya dawo hanya ai.
Bayace wai course ya tsayar dashi ba to wata shidda yanzu ai ya cika sai mugani wanan dan anyi la,anane a cikin zurian mu wallahi duk halin su Marka ya dauko babu halin zariya da dan nan ya dauko namu.
Bari na gaida mummy in dawo Dada na fada ina mikewa tsaye tare da gyara mayafin kaina da kyau na fice daga wajen Dada din.
Har nakai kofa na tuna da halimatu da ban ganta ba na juyo ina fadin wai halimatu fa Dada tace ke dai bari wata yar banza ke nan ai.
Tana katsina kusan wata ukku ke nan yanzu daga zuwa ta dubo iyayyenta taje can ta samu waje ta zauna ni banmasan ko sun rike abinsu bane can.
Sallama nayi har sau biyu ba a amsa min ba hakan yasa na zata basu falon a lokacin sai nasa kai nashiga amma sai ganin mummy nayi zaune tana cin abinci hankali kwance sai anty Nafisa dake fitowa daga daki.
Ban daddaraba na sake sallama a gareta ta amsa min a dakile na zube kasa ina gaida da ita kamar ba zata amsa min ba tadai amsa din tana fadin .
Ashe ina da darajan da zaki shigo gaidani na dauka ai ba za a barki ma kizo ki gaidani ba tunda nina haifi hafiz ai da sauri na dago na dan kalleta daga inda anty Nafisa take tsaye tana sauraron mu tace haba mummy haka ba kyau fa.
Ke ki min shiru don Allah ko yanzu ta shigo gidan nan watau ni banda darajan da zata fara zuwa wajena ta gaidani sai kubura ko don bata daukeni da muhinmanci ba a rayuwanta.
Koda yake ai dolene kiyi hakan tunda yadda akeso ba,a samu ba kinga ko dole ki hakan ina dai duke ban dago ba a yadda nake.
Taso sis ya exam anty Nafisa ta fada tana kama hannuna zuwa part din dakunan su mummy data bini da kallo taja uban tsoki tana hade rai tare da kawar da idanunta kaina.
Hijjab na rufawa mata asiri don haka hijjab din dake jikina ya hana mummy ta fahinci yadda na koma a lokacin sai take ganin ina nan yadda nake ai ban karu da komai ba sai bakin ciki da takaici kawai.
Na kasa sakin jiki da ita duk yadda take dan jana da hira akan exam din mu wai idan ina da matsala in fada mata tabi min case din nan na nuna mata banda matsalan komai ga karatuna ban jima ba na koma part din mum.
Kwatsam muna zaune muna hirane sai ganin mummy mukayi kamar an jefota tana shigowa take fadin hjy kubura yanzu ma din da zainab take matsayin sarakuwa a gareni ba zaki bari mu zauna lafiya da ita ba ?
Dan abinda ta kawo kin karbe kin tura daki koda yake ba mamaki ai don kinyi hakan dama donshi kikai dumu dumu a cikin rayuwanta ai.
Kaiya Allah waddan naka ya lalace inba lalacewa da rashin sanin ciwon kai ba har yaushe zakizo nan ki tsaya kina fada akan abinda mama ta shigo dashi gidan nan.
Au to haka kikace kina da wani manufa ke nan ashe watau lalacewane don na nemi sanin hakkina don yanzu mama a matsayin karkashin dana take ba karkashin ki ba ko wani a gidan nan.
Amma tunda hakane shike nan zan gwada maki baki da wani power yanzu akan yarinyar nan ke kuma makira zaki gane cewa kina wullakantani baki daukeni matsayin uwar mijinki ba ko kadan ko ?
Na dukar da kaina banyi maganan komai ba har tagama fadin maganganunta ta juya ta fita ban jima ba mum tace in tashi in koma gida wunin da banyi ba ke nan a gidan kuma.
Nayi niyar inje gidan mu sai na tuna da sharadin mahaifina akaina daya haneni da zuwa gida in dubasu sai idan mijina ya dawo yace inzo zanzo gidansu.
Wai ashe hakan bayan na tafi mummy bata bar fitinan akan zabcen zuwan nawa ba , acewanta wai nazo masu da abu mum ta boye a part dinta ita kadai don zalama.
Dole har gaban daddy dake zaune saida ya gama sauraron korafin mummy din ya dauki waya ya kira malam isah yace ya bude boot din motan ya dauko kayan nan da mama tazo mashi dashi da safe.
Nan mummy ta fara wiki wiki da idanu kafin malam isah ya shigo da kayan yana fadin Alh ayi hakkuri na manta inshigo dasune yace ya aje nan gabansu ya aje ya fita.
Lokacin daddy ya kalli mummy din yace bayan wanan tazo da wasu kayane gidan nan ina tace ani tayowa cake din da abinsha na kumace ba zan ba kowa ba a cikin ku na fita dashi kasuwa mukaci koba haka ba hjy kubura ?
To ni me zance Alh mum ta fada tana dan murmushi amma ai kasan ba,a kyauta min ba ta yaya yarinyar nan zatazo da abu gidan nan amma ba zan sani ba.
Ke Malka kada ki manta har yanzu ba dan nakine ke ciyar min da ita ba saiki bari duk ranan da dan naki yazo ya dauki abinda mukai masa da muhinmanci sai kiyi wana barazanan naki a kanta.
Ya dai tawace nike da iko da abina kuma ta nunawa duniya na isa da ita ni yarinyar ta gama min komai a duniyan nan don haka ki dauki zancen ki na shirme ki nade ke yanzu bakiji kunyan fadan wanan maganan ba.
Lalai mlka baki da kunya da har kikazo fada kan wanan abin don da kinada kunya da bakiko daga kai kin kalli wanan abin ba.
Ni dama nasan don a cuta muna akai wanan hadin bawani abu ba yaron nan yace baison hadin nan amma ka nace akan hakan yanzu kuma nayi magana kace ina na fito ?
Ta mike ta fice ta barsu zaune a wajen kowa imani ya kashe masa zuciya sai mum ne tayi karfin halin fadin inba shirme ba keda kika iya wanab kika gazaki saka danki yaiwa mahaifinshi biyayya.
Ta mike itama ta fice don lokacin har mijin nasu takaicinshi take ji ganin ya gaza daukan mataki akan iya shegen da matar nasa da danshi sukeyi ya zuba ido kawai ya kasa magana.
Tun rana kuma ban koma gida ba haka na hakkura na zauna gida ni kadai don in maida kaina busy na fara karatu a lokacin kan abinda mukayi a baya ko kuma in kuna kallo ina bin episode.
Har hutun mu ya kare muka koma makaranta nan karatun mu yaci gaba bani marmarin zuwa gida saboda fahintar da nayi cewa zuwan nawa yana haddasa masu fitina.
Don Allah ya gani a lokacin ba, zan iya zama part din mummy na tsayin wani lokaci ba saboda ban saba hakan ba a rayuwana zama a part dinta don bata da dadi ko kadan.
Karatu muke babu kama hannun yaro don haka inna fita tun safe ban dawowa sai yamma lis cikin irin hakane ranan na dawo a gaji bakin get nake sauka don ban shigo ciki don kada in wahal da malam isah din.
Sai dai idan ina da kayane zai shigo dani ciki in sauke sai ya tafi duk da umurnine na daddy nima akwai kyautatawa a tsakanin mu don ina mutunta dattijon sosai saboda ya dan girmewa mahaifina ga shekaru.
Ina turo get din gidan na shigo na hango mutum zaune saman mota ya kurawa kofan idanu ga karan sigari a hannusa sai hayaki ke tashi a wajen baiko gudan yaja matsala wuta ya tashi.
Gabanane ya fadi rasa don ban taba kawo zuwanshi ba sai ganin nan da nayi masa da alama ya dan dade a wajen zaune don guntayen taban da nagani a warwatse a wajen.
Cikin karfin hali na karaso ina furta sannu da zuwa makin ya amsa min sai dirowa da yayi daga kan motan yana jan tsuki tare da kakabe hannayesa.
A zuciyana nace kazamin banza Allah ya kara nisantaka dani mugu kawai azzalumi na nufi hanyar kofan falo na dauko key ina budewa.
A daidai lokacin wani mugun warin taba ya shiga hancina saida na zabura na dan juya shine ke hawowa step din daidai inda nake fuskan nan murtuk dashi kamar abin tsoro.
Gashi yayi baki ya dushe gashi kuma kananan kaya ya saka a jikinshi rigace mai dan hannu daya fito masa da damtsen hannusa waje sai wando jeans na maza dark blue ni bama idona ke mun gizo ba sai ince harda wani katon sarka da yan iskan maza ke sakawa idan sun kosa da iskanci a wuyansa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[3/5, 08:43] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3?? 0??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Da kyat na samu kallaman sannu da zuwa ya sake fito min daga bakina don kaina daya fara juyawa a lokacin ina jin kamar zan amaye yan hanjin cikina lokaci guda.
Hasaran rayuwa ko kana da rai baiyi ba wallahi don ga mutum har mutum tsayayye a zahiri amma ga idanuna bai cika mutum ba a wajena don raunin shi dana rifa na sani na boye.
Don hakane bani iya kallonsa da kima ko daraja a wajena yadda na taso da tsanar mashayin giya tun ina fuciciyata sanin da mukayiwa yan giya shine irin fulanin daji din nan dakan fara tambadewa suke shan giya a cikin garin.
Zasu biyo hanya suna tambele suna faduwa suna fitsari a wando da amai yara nabinsu da jifa suna masu waka sunyi marisa sunsha kwaya .
Sam ban taba dauka akwai yan birni dake wanan rayuwan hasaran ba ashe abin badaga nan yake ba kowa da tasa kalan kaddara a rayuwa abin masiface in Allah ya nufa kana ciki zaka tsunci kanka a cikinsu din din gani nima yau abin ya shafi rayuwata.
Shine zama da dan giya dan giyan kuma miji a gareni kuma dan uwana kaiconi da wanan rayuwan dana tsunta a kaina na fada cikin abinda baifi second ba na gama wanan tunanen lokaci guda.
Key na murda hannuna rawa na mude gidan ban ko tsaya juyawa ba na shige ciki kai tsaye Allah ya taimaka akwai wutan Nepa a lokacin da sauri nayi dabaran zuwa wurin fanka na kunna don ya kore abinda nake ji kafin na juya zuwa dakina.
Jakka na aje ina kaiwa zaune bakin gado dan tunane nayi dashi din akwai hakkin aure atsakanin fa kada Allah ya kamani da laifin hakan akaina wanan tsakaninsane da ubangijinsa.
Da sauri na daga daga wajen na fito na nufi kitchen din mu ruwan roba na dauko mai sanyi tare da cup na dora saman wani dan ture na nufi falon dashi.
Haba warin taba sigarine daya kunna still ya tareni a lokacin hakana daure har kafana na hardewa a waje daya don rudewa na nufi ida yake zaune ya mike kafa yana waya yana zukan taban a cikin harshen turanci.
Dago kai yayi ya jefeni da wani kallo mai kama da muguwar harara wanda hakan ya janyo min faduwan gaba, gaba daya sai naji na rude a wajen lokaci guda.
Wani irin tsorone da fargananshi suka ziyarci zuciyana jikina har rawavya dan somayi na aje cikin karfin hali ina fadim ga ruwanan cikin wani kyarman murya da ban taba sanin ina dashi ba a rayuwana.
Na juya da sauri don in bar falon ai bankai ga dagawan ba naji tsukin shi yana fadin uban wa zai sha maki wanan abin da kika aje ko nayi maki kama da kazaimai ne wai ?
Maza ki kwashe kayan tsiyarki a nan jaka kazama kidahumar banza kawai wai ku wasu irin dabbobine da baku da zuciya hakane ?
Shin wai auren nan dolene kome da zaku nacein kamar ni kadaine a cikin dangi inba kwadayi ba da naci irin naku nagado ke baki zuciya ki koma gidan ubankine wai ?
Ko ina kwadayin mace sai a rasa wace za a hadani da ita saike kucaka haka mutum da zubi kamar kara koda yake ba laifinki bane naci gadansa kikayi ai don haka ba abin mamaki bane idan kinyi.
To ki sani akai kasuwa idan nine badai hafiz ba mata masu ajima ban kalla ba balle ke din nan da banga abin gani a wajenki ba har aba ko kun zata wanan farin naki zai iya rudanane wai ?
To fararen suna can suna mutuwa akaina saina zaba make hole rayuwana dasu ba banza irin ki ba ya karasa da sakar min wani uban tsuki.
Kada ki dauka donki nazo garin nan nazo don uwata da munafukin ubanki ke son kashewa aurene don in kwatar mata incinta ga kowa ba zuwan mutunci nayi ba da kika ganni nan a yau don haka na fara dake din kafin,,,,,
Ina tsaye na bashi baya kamar an dasani a wajen a fusace na juyo kafin yakai karshe nasan zagin mahaifina da suka dafawa laifin hakan akansa zai komayi kafin nace.
Ina sakin wani murmushin takaici a fuskana mai nuna takaici ga kalaminsa nace aikin banza dama hausawa sunce gwano bayajin warin kansa ai.
Ni da ka ganni na tsagwaron biyayya ga iyayye ya zaunar dani gidan nan don in nuna masu sun haifi diyar da suka isa iko da ita a duniya kuma ako ina.
Har ina abin kwadayi ga mai mumunan rayuwa irin naka a nan kadubeka ka dubeni in ba fin karfin iyayye ba nayi maka kama da zama da dan giya ?
Wani zabura naga yayi dayasani ja da baya kadan don ganin bai taso ba naci gaba da fadin babu hayar jirgi data mota wanan dai uban nawa daka raina kuka mayar dashi asuwakin bankiku saboda daukan alhaki ya gama maka komai a duniya ai tunda har ya haifeni nakuma zamo matarka a yau kowa ya sheda hakan .
Ba mamaki kila lokacin kana a cikin mayenka koda hakan ya faru amma wani gyatumin ya daura hakan don da son ran mune ba hadin kifi da kaska ko a hanya kuwa.
Wani zabura yayi yana nufo ni tare da fadin ke kina nufin ubana shine wani gyatumin nace ashe ka gane ina kaiwa dakin na rufo kofa da karfi na saka key ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login