Showing 30001 words to 33000 words out of 103712 words

Chapter 11 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7836

zan yarda inje lahira in tashi da barin jiki shanyayye a na nunani ana fadin ga wanda mace ta halaka a duniya to ba zan yarda takaini can ba donta hakan ya faru dani.
Hakan ma ba zai faru ba insha Allahu Alh kowa yasan kai mutumin kirkine a cikin yan uwa bamu fatan hakan ya faru dakai insha Allahu wani dan uwan hjy malka din daga cikin iyayyemu ya fada.
Nan sai aka kirasu har Dada da hjy Mum sukazo a zatonsu sallama zasuyi da bakin gida din zasu koma sai bayan sunzone sukaji sabanin hakan ga bakin baba sani.
Indaya zaiyano abubuwan garesu cikin hikima amma kafin yakai hjy malka tareshi da fadin shi Alh din ya fada maku hakan ko wani dan game game ya tsayar daku ya fadi hakan a kaina don makirci.
Tunda wanan zancen nasan gun yar bakin cikin nan zai fito tunda ba kauna takeyi ba ta kallo inda hjy Mum din take zaune a falon gefen Dada.
Au wai dama dani kikeyi hjy malka niki sani baku cikin zancena don nina dogara da turban da iyayyena suka dorani tun farko nasha tmTabara nasha Yasin sai gani sai hange a wajen ki duk wani sherikin a yanzu ni baya girgizani tunda ba kallan sherin ki daban sani kuma ba hjy Malka.
Haka dai kikace fadi a baki Annabi a baki zuciya fir,auna waye bai san abinda kema kikeyi in kina takama kinsan na wani.
Saidai zargi irin haka din don ba zan biyewa sherinki mu lalace a tare ba saboda duniyan nan me karewa ga bawa.
Kina ganin akwai wani abinda zakiyi koki fada yanzu da zai firgitani kuma nasan irin ku shedanun mutane masu kai mutum ga halaka to bani cikinsu kin sani.
Ku dakata don Allah ba mun taraku a nan bane kuyi muna irin wanan haukan yanzu mun tarakune don mu sulhuntaku mu gyara tsakanin ku kun tsaya kuna muna hauka.
Mune ma mahaukata yau Garba don samun waje wai tsaya kina nufin Garba din ma baida daraja a idonki ke nan kome ta kallo baba na kano dayai maganan yace kun gani da ku barni da ita in nuna mata iyakarta.
Nan dai akai ta magana aka taru wajen aka bata rashin gaskiya tare da ja masu kunne kan zaman nasu kamar kananun yara dasu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[1/28, 09:55] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

1?? 1??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Da ace nashiryane aida mun sauka gida a yau din nan muma Dada ta fada daga inda take tana mikewa tsaye don tagaji da jin irin jayayyan da akeyi da hjy marka ana tausanta a wajen.
A,a mama ku dai bari ku kara dan kwana biyumana kafin ku koma gida zaifi ai tunda dama ba tare da sauran yan uwa kukazo ba babana ya fada.
Dama baka tsaya fada ba don a nan zatayi muna azumi ko zata shigo katsina killa sai ubangiji ya kai muna rai bayan babban sallah in Allah ya yarda.
Wace Dada di badai wanan ba idan na zauna yaran fa dana kwaso zan barsu su koma su kadai ne gida lokacin baban kano ya kara fadin yara waisu mamana kike magana.
Aisu sunzo ke nan garin nan ba zasu koma katsina ba koda ke zaki tafi su anan za a barmin su don har na yanke shawaran makarantan da zan sakasu ana gama buki nan insha Allahu.
Wani kallo Dada tayi wa babana daya soke kansa lokaci daya don jin abinda abokin haihuwansa ya fada akaina gashi ba wurin gardama bane balle yaja a gaban kowa.
Lokaci daya zancen na shiga masa kunne yaji gaba daya gabobin jikinshi sun daina aiki sun bada wani sauti kamar sun tashi aiki lokaci guda.
Shiko Babana kano din yaci gaba da magana yana fadin zanso zamansu a nan don su kara fahintar abubuwa saidai ita wanan dayan da kamar banda iko da ita ya kallo Dada yana nufin halimatu ke nan.
Yace ita idan zata koma ko yaune zatabi yan uwa tana iya tafiya ita idan tace bata zama a nan damu tunda banda karfin ikon akanta kamar yadda nake dashi ga mama.
Amma ita mama nagama yanke shawarana akanta ni zan karasa rike uwata kafin na aurar da ita ga mijin dana zaba mata don na riga da nayi mata miji ko a nan din gaban babana ya kara faduwa har yakai dan muskutawa yana gyara zama alokacin.
Yawan kallon da Dada kewa mahaifina aduk lokacin da baba din ya fida harafinsa yana jin kamar ana daka masa guduma akai lokacin hakan yasa babana kano fahintar shi take kallo don haka a gaban kowa yace da mahaifina Garba ko kana daja da hukuncin dana zantar ne ?
Da kyat baba dake dana sanin zuwana kano din tun bayan tafiyan mu da Dada har zuwa yau yace nina isa Alh dakai da kafa ai duk mallakan wuyace don Abbu yarkace ai halal malak don haka kana iya zatar da hukuncin komai akanta ai kamar yadda nima nake da iko da iyalinka.
To shina gani naga kamar akwai maganane don irin kallon da Dada ke maka a yanzu din yana nuna kamar akwai matsala ga hukuncin dana zatar ga yarshi.
Haba dai shiya isa ya musanta hakan kan yarsa don ka yanke hukunci akanta tunda dakai dashi duk daya kuke a wajen ta duk da kowa yasan dole abin ya daki Garba dubaga irin rikon taka tsantsan da yakewa yaransa gaskiya.
Nasan da wanan shiyasama na zabi zamanta da hjy kubura wanda dama kamar Allah ya hada abinsane don tun zuwanta tana hannunta dama kaga ka kwantar da hankalinka idai gun kuburah insha Allahu kamar yarka tana hannunkane.
Kuma nayi hakanne don yan uwa su tuna da abinda mahaifan mu sukeyi a baya na kai baka isa ka rike diyanka a hannunka ba sai dai na wani dan uwa da zaran an yayye za,a kada a wani zariyan saboda karfin zumuncin su kowa nan yasani kuma.
Da biyu da uku na dawo da rikon mama yanzu a hannu na na farko har kasan raina har yau banyi wani abinda zan iya rama irin rikon da hjy mamana tayi min ba kowa nan yasani a cikinku.
Yau duk abinda na zama ban taba mantawa itace dalilin zamana hakan a duniya agaban kowa mamana ta sayar da jeren dakinta lokacin dasu malam sukace babu kudin da zanzo kano karatu har abin ya zamo rigima akarshe tsakaninsu da malam ke Dada kin sani ai.
Dada ta dan gyara tana fadin kwarai kuwa wanan ne kuma mussababin barinta katsina ta koma can kauyensu da zama har shi Garba a karshe ya bita suka zauna a can din.
To Alhamdullahi yau Allah ya ban ikon fitar da wanan maganan daya dade yana damuna don hakane nima nake son mama tasan tabar baya a duniya batayiwa banza ba.
Shago na nan a kasa dani ina ginawa da sunan Garba insha Allahu idan an kammala an saka kaya nasane halak malak akwai kuma gida nan bayan mu kadan wanda na tanada donshi da iyalinsa da zasu zauna a ciki shima nasane nasaye da sunansa ga takardun gidan ya tura hannu cikin aljihun riga ya zaro takardun yaci gaba da fadin.
Ko yau kaga daman dawowa kano ka zauna kana da ikon hakan na fada a gaban kowa don ku sheda wanan nayine sadakatul jariya zuga ga uwata mama data rikeni da zuciya daya har na zamo hakan a yanzu.
Amma ai yaya mama tayimane da zuciya daya basai ka wahal da kanka wurin cewa zaka rama abinda tayima ba ta hanyan kyautatamin da iyalina.
Shin Garba kana son ka hanani alherine nima in samu lada da ake samu ta hanyar zumunci babana kano din ya tari numfashin babana da fadin hakan.
Mahaifina ya girgiza kansa yana fadin ko daya wallahi yaya ni maison kayi fiye da yadda kakeyi din nan ne ma wallahi yace to ka barni haka na tsara haka kuma zai tafi.
Sai kuma yan uwa kai sani naga kafi karfi ga wanan sana,an naka na yashi don haka mota nan zata shigo gobe katsina insha Allahu da sunanka halak malak na saya makashi.
Kai Amadu dakafi karfi a fannin gina kuma shagona ma bakin layi nace a gyara ina fatan kagani ana gyaransa suka amsa da ehh kwarai kuwa yace to kai akewa gyaran za,a zuba maka kayan gina aciki kana juyawa.
Gaba dayansu kaf falon saida yayiwa kowa alheri kwatabkwacin aikin da mutum keyi ya habbakashi ta yadda ba zai koma cima zaune a cikin dangi ba kuma kowa nada abin yi ke nan a cikinsu.
Ranan anyi farin ciki sosai inka debe babana da abin bai masa dadi ba don yana ganin dawowa kano a wajenshi komawa bayane haka kuma rabashi da yarsa tankar dabawa cikinsa yuka yake jin abin har yakai an fahinci rashin walwalanshi a motan baba haruna dake kusa dashi shiba mai yawan surutu bane kamar saura ya dafa baba din yana fadin.
Da nan katsina da kano duk dayane a wajen Allah iyaka bawa yayi hamdallah ga duk abu yadda yazo mashi kasa a ranka hakan ya zamo maka alheri nan gaba.
Gyara dan zama baba yayi yace hakan nake fata tun dazu don bada wani zabi dayafi ba ubangijina haka kuma ba zanso na zama tushen rusu ginan zumunci da Alh ke kokarin yi a tsakanin mu ba dashi don wanan wani hikimace dashi ya barwa kansa sanin dalilin hakan kayi tunane maikyau anan garba Allah yasa hakan yafi zama muna alheri ga baki daya ya amsa da amin.
Lokacin da labarin hukuncin da baba ya yanke akai yazo min kuka na saka ina fadin wallahi ni banzama gida zan koma kuka sosai nayi amma haka baisa inna ta kulani ba duk da itama daurewa tayi ta cije kada aga kasawanta don ba yadda ta iya da hukuncin iyayyena.
Hakana inaji ina gani duk iyayyena suka tafi suka barni zamana a kano wajen su baba da mommy ya tabbata ke nan a kaina yanzu don dole ko naso in zauna a hannun hjy mum din.
Wanan yasa zazzabi mai karfi ya kamani zuwa marance dama kuma jikin nawa akwai gajiya sai abin ya taru ya hade min ya saukar min da wanan zazzabin daya kaini kwance lokaci guda.
Ban fadawa kowa halinda nake ciki ba a lokacin har yamma da hjy Mum tazo kirana take fadin daddy yana son ganina ta fita har takai kofa ta juyo tana fadin mama nine baki son zama dani ko kuma muga baki dayan mu yan gidan nan ne bakya son zama tare damu.
Shiru nayi ina hawaye taja kafanta ta fice daga dakin don ba zata iya jure kallon hawayen da nake sakewa ba saidana tsaya na gyara kaina na nufi fallon wajen daddy din inda tace min yake.
Kusan tare muka shigo da hjy Mum din falo inda ta zauna na zauna a kasa gefen kafanta ina gaida daddy din cikin raunin murya dake da alaman maishi yayi kuka sosai a lokacin yayin da Dada da hjy malka dake zuba mai zuma a kofin shayin dake hannunsa yana fidda tururin hayaki take tsaye a kusa dashi.
A,a mamana wai da gaske ko kukan kikeyi har yanzu na dauka ai kina da wayau da zaki san nan ma gidane nima ubankine kamar Garba.
Idona runtse da hadiyan wasu busasshen yuwu da suka tsaya min a baki suke damuna kamar zan hade kaya a lokacin sam bani cikin hayacina a lokacin amma su basu farga da hakan ba gareni dama da kyat na iya takowa zuwa falon amsa kiran daddy din.
Dago kai da daddy yayi yaji shirun da nayi ban bashi amsa ba ya fara ganin halinda nake ciki anan yake furta ya subbahanallah wanan kalman ce yazo min a kunnena karshe.
Bansan tsawon minti nawa na dauka a hakan ba saidai sama sama na dinga jiyo muryoyinsu yayin da nake kokarin bude idanuwana cikin karfin hali duk suna kewaye a kaina lokacin cikin wani yanayi daba zan iya fassarashi ba a halinda nake din.
Muryan Dada naji tana fadin dama nasan za a aika hakan yadda yarinyar nan take da iyayyenta kamar cingan da rana tsaka ace za,a raba zamansu zaiyi wuya gaskiya hakan.
Itako hjy Mummy na fadin abu daine irin na Alh ma da kuma an zugashi don me zai dauko yarinya haka da girmanta yace ta dawo nan da zama dole don wani ra,ayi.
Kokarin dagowa nayi sai lokacin naji ashe a jikin hjy Mum nake kwance murya take fadin kankine yake ciwo mama ?
Da kyat na iya daga kan nayi mata alaman ehh tace asibiti ya kamata mu kaita duba yadda jijiyoyin goshinta sukai wani radau suna harbawa.
Da sauri nace ban zawa asibiti Mum abani magani zazzabi nakeji da??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ma a cikin raunin murya dauko panadol a daki ku bata tasha hjy Mum dake rike dani tayi kokarin ajeni ta mike don hjy Mummy ko gezau batayi ba lokacin balle taje dauko maganin.
Cikin tsawa daddu yace kije mana malka sai ta mike ta tafi ta dauko gami da goran ruwa a hannunta ta bare ta miko min duk da halin da nake ciki dana karba zan hadiya saidana furta nagode a gareta.
Da kyat na hadiye nakoma na lafe a jikin Mum din ina sauke numfashi wai dama bata da lafiyane Mum tace ina zato don kwance na sameta kuma ai dole hakan ya faru da ita tun safe take abu guda baya tafiyan yan gida.
Batune dai bai faduwa amma a maida yarinyar nan gun iyayyenta shiyafi don me za a mayar da ita ko tana can ciwo yazo bayi zatayi ba halan banson irin wanan kalamin daga yanzu naji zancen a mayar da ita zan sabawa maishi a gidan nan kowaye.
Nikan ina jin kan nawa ya fara lafawa na yunkura na tashi zaune nabar jikin hjy mum din dake rike dani lokacin tana dan min tofi a jikina duka.
Ina zaki na juyo ina kallo daddy din a raunane nace daki zanje in kwanta yace kubura kaita dakin ta kwanta ta amsa da toh Alh muje mama ta fada ta rikeni na mike duk da ina dan iyawa a lokacin.
A cikin bargo na kudundume don sanyin da nake ji a jikina gami da runtse idanuna ina jin wani zazzabi mai karfi yana son kamani ina dan rawan dari aciki.
Muryan mum naji tana fadin haba mama dama baki da lafiya baki fada min ba aisai a dauka tun yanzu ban iya kula dakene yanzu bari na kawo maki ruwan shayi kisha ko zazzabin zai sauka tunda baki son asibiti kamar daddynku kike.
Duk sai naji tausayin hjy Mum din ya kamani lokaci guda don ita din dai me kaunatace gaskiya don tunzuwa gidan ta nuna min so da kauna irin ta jini duk da naji Dada tace min dukkansu zaman gwaggonina suke don jininsu daya da ubana dukansu.
Barci barawo ina wanan tunanen yayi awon gaba dani da har bansan dawowanta ba dakin ban falka ba sai tsakan dare kuma naji garau ina yankan zufa a jikina.
Kokarin yaye bargon nayi lokacin naji muryan hjy mum dake gefena zaune ta kafa glass din idanu tana karatu tace
Ya mama wani abu kike sone ya jikin naki ko yunwa kikejine ta jefo min wanan tambayoyin lokaci guda don haka na rasa wani zan amsa mata sai cewa nayi kewayawa zanyi inyi sallah.
Kaita girgiza tana kokarin mikewa tace zaki iya tashine nace naji sauki mum zan iya na samu na mike zaune ina jin jikina wani iri alaman jikin dai ya tabu a ranan.
Hanyan fita daga dakin na nufa don fahintar danayi a dakinta nake naji muryata tana fadin ina zaki yanzufa karfi biyu da rabi na dare ki kewaya a nan mana .
Alwala na dauro na gabatar da sallalolin dake kaina tun daga la,asar duk da hijjab din Mum din kana na mika kukana ga ubangiji Allah wanda yafi kowa sanin daidai ga bawansa zamana a gidan nan yasa alherine a gareni kamar yadda yan uwa suka tafi suna fada min har hakan yasani kuka a lokacin.
Wanda a yanzu ya haifar min da wanan zazzabin da nake ciki komawa nayi na kwanta har lokacin mum na zaune saman gadonta tana karatun Al,kur ani mai girma cikin dan murya.
Banyi barci ba nima har zuwa lokacin data gama ta kwanta duk ina jinta sai zuwa asuba barci ya dan saceni saida ta tayar dani nayi sallahn asubahin ranan.
A gaskiya zance a dan kwana biyun nan naga canji sosai ga kowa na gidan har hjy malka da yaranta don wuni suke suna shigowa part din hjy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login