Showing 3001 words to 6000 words out of 103712 words

Chapter 2 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7844

dadi a gidan mucishi man shanu dai ne baka raba baba dashi a gidan mu don hurda da fulani da baba ke yawanyi a daji wajen aikinsa idan yaje yake dawowa da nama da man shanu mai yawa ayi amfani dashi.
Amma baikai ko ina duk matan babban gida zasu kwasheshi wajen roko har sai sunga karshen kwano sanan zasu huta zuwa tambaya yanzu ko da bamu nan nasan saidai idan mutum ya saya din zaiciwa bakinsa

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[1/7, 21:41] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FOKON BIRI

ZAINAB IDRIS MAKAWA



GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

2??

Zauren gidan namu sabo shine daga farko sai idan kashigo daga ciki kuma zaka fara cin karo da rijiya sai dakin farko wanda babane a cikinsa.
Sai tsakiya dake zaman inna na karshe kuma mune da kannena a cikinsa da shimfidan mu na tsohuwar katifan inna da take yar muna dashi kasa muke kwamciya tun a kauye.
Tsakar gidan da simiti tako ina sai kitchen daga gefen dakin namu sai kuma wani dan daki baikai sauran dakunan girma ba shi kuma sauran tarkacen mune a cikinsa da yan akuyoyina da aka saka a cikinsa.
Ban gajiya da kallon Gidan don abin yana burgeni ko yaushe ina waje ina bin ko ina da kallo sai ina ganin kamar munzo bakuntane zamu koma.
Inama ace su mama tambai zasuzo suga gidan nan namu da bakin ciki saiya kashesu don nasan zasu koma kauye da labarin bakina fadi tsuliya na fada na abinda suka gani a katsina din.
Saida muka kwana biyu ranan muka shirya da safe muka shiga gaida Dada daga nan ta turamu da wata jikanta taikai iyalan Audullahi gidan yan uwa su san mu mu sansu.
Matashiyar itace take fada muna alakan mu da inda muke shiga din wanda maganan babane duk yan uwane saboda yanayin inna muka dawo gida badon mun gama zaga dangin Ruma ba a lokacin.
Gashi yadda baban mu keda kalangu a gefen fuskanshi duka biyu haka suma nake ganin hakan a fuskansu har dayara a wani gidan muka dawo gida ina wanan tunanen ni kadai a raina.
Wanan abin kamar a mafalki saiga baba yana muna zancen makaranta nayi murna nayi murna sosai islamiya aka fara kai mu a nan kasan unguwa har uniform aka dinka muna.
Muka saje da sauran yan uwa wanda duk yawanci diyan dangine a wajen a gaskiya duk wanda iyayyensa ke da ilimi ko uwa ko uba ya godewa Allah don za a bashi tarbiyan da ba zai wahala ba a duniya sai idan shiya jefa kansa cikin wahalan.
Don hakane garemu don ko na sheda hakanne saboda ban wahala basakamakon tarbiyan da baba ya doramu a kai tun a kauye, sai sajewa dasu nan bai zamo min wahala ba ina dai kokarin kafa kafa da yan kannena a lokacin duk inda nake idona nakai gashi suna kiran mu da sunan yan bararo.
Saboda hasken mu da zubin mu daya huda jinin mu na uwa da muke kama da bararo din wajen kama ga tsabta koda yaushe kafan mu da kumshi na lalle har hannuwa inna ke kumshe muna don ta saba da hakan tunna kauye itama hakanne ko yaushe a cikin kumshi take gata fara sai abin yake muna kyau daga mu har ita din indan anyi.
Baba yai shawara da yan uwanshi kan bokon mu suka bashi shawara ya jefani secondary kawai zaifi don ya mace make girman diya mace baida wahala a yanzu.
Aka kaini makarantar yan mata na jeka ka dawo inda yawancin yan gidan namu suke karatu an min uniform da safa da jakkan tare da littafai guda goma sha biyu nayi murna ranan barcima banyisa sosai ba don daukim in gani school din.
Washegari aka kaini aji daya aka ajeni a kauye kuma ina aji hudu ne na daina don ba daukan karatun da wani ma,ana mukayi ba a can talla ko aikin gida yafi karatu muhinmanci a wajen iyayyen mu mata damu.
Allah ya gani ina da ra,ayin yin boko a rayuwana saidai daukan da akewa wanda ke boko a kauyen mu yasa nima na bar zuwa bokon don da waka nake zuwa dashi nake dawow ga yara kamar mahaukaciya wanan yasa na tattara na daina bokon ina zaman gida tare da inna.
Ashe ina da rabo sai gashi nice ranan zaune a aji cikin yan bokon da nake mafalkin ganina a cikinsu yau gani garesu muna cudanya atare dasu a cikin aji.
Nayi kamar sati da farawa suma Aiaha aka kaisu boko suka fara zuwa tare muke tafiya dasu dawowane baba yake zuwa ya daukosu donsuyi kankanta da bin hanya.
Yawan shiga gidan Dada ina kai mata abinci yasa shakuwa ya shiga tsakanina da ita don muddin na shiga zan tsaya indan mata aiki diban ruwa shara da dan wanke wanken kayan ta daba wani yaw bane dasu kayanta kuma in dauko in kawowa inna ta wanke mata in an gam na wanke in kai matasu a nade kamar an goge.
Wanan yasa muka yi wani sabo da tsohuwan na sosai har yakai ta roki baba in dawo da zama a wajenta amma baba yasawa idonshi tankwa ya hana hakan .
Ya fake da cewa itace idon gidan Dada uwar tayi nauyi a yanzu ita ke taimaka mata da wasu aiyukan Dada tace gaskiyane kuma fa da can da nan ai kamar dayane tunda tana shigowa kullum .
A haka maganan ya shashance amma inna cewa tayi aida baba ya badani din ba komai ta dingayi da kanta gasu Aisha sai suna kama mata ai.
Baba yace ke dai bari fake min baya jiran biri abu ga hannun maishi shine abinsa zamani yanzu ya lalace gidan Dada gidan kowane ni ko shigan nan ba kasafai nake sonshi ba kinsan zainab ba wai ta gama wayewa bane haka.
Yarinyace har yanzu tunda ko goma bata idda rufewa ba barta a nan inda muke ganin abin mu yafi muna alheri a wanan zamanin inna tace hakane kumafa.
A haka har ubangiji ya sauke inna lafiya ta haifi danta kyakyawa mai zubin mahaifinmu sak nan yan barka suke ta shigowa gidan mu don Dada ta aikawa kowa a unguwa sun samu labarin haihuwan.
Dada mutumiyar arzikine sosai zakice itace ta haifi baban mu da cikinta yadda take manu nan ko kishiyar uwace matar mahaifinsane shima baba ya rileta tankar uwa a gareshi.
Nan a gidan mu tayi waya da wani danta da take kira da Alh ta sheda mashi zancen haihuwan ya saka albarka bayan haka da kwana biyu saiga baba ya shigo yana fadawa inna yayansa dake kaduna zaune ya tura masa da dubu hamsin yayi hidimar suna har ragon sunna.
Ranan muyi murna sosai haihuwan nan na mama ya jawo muna arziki a gidan mu zance don ta dalilin haihuwan baba ya gyarawa mama dakinta aka sayo mata saitin gado da mirror har da wardrobe a gidan dillaliya aka kafa haka yasa koda yan kauyen mu sukazo sun sha mamaki sosai a gidan.
Ganin waje lafiyeyayye mai kyau da daukan ido mama tambai sai kallon ikon Allah takeyi zancen baba Ado yana dawowa a zuciyar ta da yace kaiya ai kin masu silan takewa ke nan a rayuwansu don wani hassada takine ga mai rabo gashi ko ta gani.
Don yau innace zaune a gidan simiti da bugon kwano sun zama yan birni janta ya kara fitowa hakama yaranta sai wanan abin ya kashe mata jiki dama gulma ya kawosu katsina suka fake da sunan zuwa suna don suga kwam.
Ko haihuwan farko macen kauye tayi bata taba samun wanan abin arzikin da gatan da inna ta samu haka a kauye da wanan bakin cikin suka koma gida kowa na fadin albarkacin bakinsa a wajen.
Aikuwa wayen garin dawowansu labari har yabi gari sun kwaso karya da gaskiya suna bada labari a gari kowa da abinda yake fadi a bakinsa don sun kwaso saida suka cika akori kuran fam zuwa suna sunzo da sunan kwana baba ya hada baki da driver yace ba zai kwana ba jin hakan dole suka mike ba shiri suka bishi suka isa a cikin dare sosai garin.
Anyi suna lafiya an watse lafiya aka barmu mu kadai a gidan namu sai yayun inna su biyu don ba tafiyansu daya da tawagan kauyen mu ba zasu tsaya su dan kwana biyuwa inna a nan su kara ganin inda muke.
Don haka koda aka watse bansha wahala ba don aikin komai su sukayisa karshema gidan Dada naje sai yamma lis na dawo gidan na dan kama masu shara dana sama dayansu tanayi.
Akwai school don haka washe gari na shirya nida yan kannena muka nufi school bamu dawo ba sai biyu da yab mintuna na shigo gida tun daga nisa na hango mota a kofan gidan mu haka na shiga gida ina kallon motan dake sheki a cikin rana.
Tun daga soro nake jin wani kamshin turare har nayi sallama na shiga gidan a dan innuwan gidan na samu su baba da bakonshi saman sabon tabarman inna an shimfida masu suna zaune a kai.
Har kasa na gurfana na gaidasu sai naji mutumin na fadin kai yar tawa ke nan ashe ta girmane haka gaskiya Abdullahi kasa ka cutawa rayuwan yaran nan a kauye.
Wa yan nan kyawawan yaran masu kyau zaka aje a kauye ka cuci rayuwansu gaskiya da haka ya faru ba zamu yafewa kan mu ba ga hakan Allah ya taimakemu dai mun samu kun dawo garin nan gaba daya.
Ni dai na mike na nufi ciki na gaidasu inna nan na nufi dakina na kwabe uniform ganin bako a gidan yasa ban fito yadda na sababa don na wanke muna uniform din mu.
Muryan wanan bakon dan uwan baba naji tare da babana yana kwala min kira da zainab baba kuma yana fadin zainabu ke zainabu daga dakin na amsa da na,am baba da sauri na mike na nufo waje naji baba na fadin kizo baban ku zai tafi yana neman ki.
Kamar farko yadda na gaishesu ko wanan karon haka na zube a kasa gabansu ina fadin gani baba bakon yace yata zan tafi nace kizo muyi sallama ina sauran yan uwan nakine ?
Ya tambaya nace suna cin abinci nan ya fara magana yana fadin na fadawa babanki ki maida hankali ga karatu tunda ance kina da kokari don wata rana mukai ga babban likita mace ko wata babban office a cikin zurian anmu amma fa kinsan hakan bai samuwa saikin dage da karatu kada a yi wasa maison wanan matakin baya wasa da cikar burinsa sai ya dage.
Kaina fara dagawa kafin na bude baki da kyar nace to baba yana sa hannu a aljihunsa yace ina son muyi alfahari daku cikon yayan da zasu daga muna sunan wanan gidannamu ko bayan ranmune kamar yadda muma a yanzu muke alfahari da bazar namu mahaifin daya rasu.
Insha Allahu baba yace daga gefen shi yace ungo karbi wanan ki sayi duk wani abinda baki dashi a gidan nan na karatun ki ga babanku nan na fada masa duk wani abinda za ace za a bukata gun karatun ki ya sanar dani tunda nan kaduna nake zaune.
Kudi ya ban masu yawa saina kada kai alaman ya barshi akul naji yace dani ni babankine idan baki sani ba uban mu daya dashi tare kuma mukai karatu dashi zaria shiyasa kikaga munfi shakuwa dashi a cikin dangi kaf ni ashi haka muke kamar aminai ba zakice mu din wa da kani bane idan muna tare.
Jin hakan ga kuma baba a gefe yana wani irin murmushi yasa na mika hannu na karbi kudin daga hannun dan uwan baba din tare da fadin nagode baba cikin yar murya yace babu komai aike din diyatace halak malak ba godiya a tsakanin mu.
Jeki baba yace har lokacin fuskanshi yana dauke da murmushi na mike da sauri nabar wajen na shige gun inna dake daki da bakinta ganin sunanan dakin yasa na dunkule hannuna ban nuna mata kudin ba a lokacin.
Bayan kujeran inna na labe banda sakin jiki idan muna da bakon fuska a gidan mu har nakan kagara bako ya wuce ya barmu mu kadai wani lokacin don nakan ji na takura dayawa.
Inna taje sunyi sallama ta dawo dauke da dan jajiririnta a hannu wanda kayan jikinsa bani gajiya da kallonsu saboda kyau yadda aka saka kayan sabanin sakan mu na kauye dana saba gani ana sakawa yara acan.
Kwanan bakin biyu suka juya suka koma ba wasu dangin can bane ga inna kawai dai don sun fito nahiya dayane suke zumuntawa junansu a nan abin gwanin ban sha,awa idan ka gansu tare.
Gidan Dada na koma da zama da suke nan sai yamma nakan dawo nan gida in zauna don ban yarda kafe shidda yayi ina waje hakan yasa muka dayi sabo da yan matan dake yawan shigowa gidan Dada din hira da samun abin tabawa don baka raba gidanta da dan abinda diyanta suke aiko mata.
Wanan yasa yanzu da bakowa a gidan mu kona dawo daga school ina gida zaune ina dan aiyukan gida sai suka fara dan shigowa gidan namu wurina muna hira a nan ina aiyukana kuma.
Zasu girme min sa,adatuce sai Nabila amma haka muke kawancen namu dasu har yakai ko islamiya ko boko tare dasu muke jerawa mu tafi a wajen su nake jin komai daya shafi family wanda ni ban ma gama sanin yan uwa ba sai yanzune nake sanin wasu.
Nan nake jin ashe yawa garemu akwai wa yanda basu zaune a garin amma sukanzo gida jefi jefi tare da iyalansu lokacin sallah ko wani buki haka idan ya taso a family.
Zaman mu a nan cikinsu yanzu bazance zaman dadi bane yadda nake fadin su a,a zama daine yanzu wanda yafi muna na baya cikin yanci da sallama babu tsana babu tsangwaman kowa akan mu.
Zama na kasanni na sanka zama na cin gashin kan kai abinda kowa ya samu bakinsa saidai babu saka ido irin na kauye na lungun su wance kaza akeci ko kaza aka dafa yau.
Ko saka ido akan mu,amulan miji da mata don zaman babban gida irin wanda muka baro a baya zamane na kai mutum wuta idan bawa baiyi taka tsatsan da duniya ba a wanan zaman .
Gashi zamane na shagala kamar ba gobe sam ba mai kawo mutuwa a rayuwansa yace wai a,a bari nabar kaza a kwai mutuwa ko wani lokaci zata iya riskana saidai shagala da duniya ana dukar daji da kafafu.
Ban daki wurin wanka da bahaya daya ko biyu ansan tashin wace ansan sunyi sunna da mijinta mai kishiya akwai yan tayata gani suna saka mata ido a kishiyanta su zasu fada mata sunga tayi wankan tsarki ko sunga mijin yayi wankan asuba.
Duk damu da baba ya dan kebewa inna wuri bata tsira da hakan ba don sai kiga mace ta fado mata wai a san mata waje ta kewaya don gulma har yara suke turawa yin wanan laccan ga junansu.
Saidai ni dana dan tasa a cikinsu Allah ya kareni ga hakan don iyayyena basu yarda insha cikinsu ballema a koya min wanan akidan na babban gida babban bala,i.
Don da zaran aka fahinci mijinki yayi wankan tsarki baiyi a dakin kishiyarki ba aiki ya samu a gidan yanzu zancen boka da malam zai tashi aje kuma a zageki tsakar gida sai kin tsargi kanki da kanki kan hakan.
Idan kuma ke kadaine gun mijinki tofa nan ma ba,a barki ba za a sakaki gaba dasherin cewa kullun kina mane a kafadan namiji kin hanasa ya karo maki kishiya kin mallakesa kin hana wata tashigo itama taci arziki.
Wanan jahar su inna ke nan su akewa irin shaguben nan don duk ranan da aka ganta da sabon kaya zakiji an fara dama hakan take so taci ita kadai daga ita sai yayanta bata son wata tazo aci tare.
Saida baba ya tsaya tsakar gida ranan yai fada kan kewayawan da suke zuwa yi sashen mu sanan muka samu sauki saidai baiwai sun bar zuwan bane sukan faki idonshi s shigo su kewaya din don gulma.
Kai gaskiya zaman babban gida a kauye ba karamin fitina bana yasa ko baki da baki idan kin shigo dole bakin zai bude sai kiga yar karamar yarinya tana ciwa tsohuwa mutunci a tsakar gida gaban yayanta da kowa.
Nikan nayi barka naji dadi da Allah ya kadarta iyayyena suka taso dani don da karshensa a gidan aure zai kamani ace anyi auren hadi tsakanina da wani can a dangi.


ZAINB IDRIS MAKAWA
[1/16, 12:13] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FOKON BIRI

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login