Showing 42001 words to 45000 words out of 103712 words

Chapter 15 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7831

a bakinta tana fadin me nake gani nake kuma ji hakane ke Atika ?
Barta hjy tace da biyu tazo gidan nan saboda mu don mun saka mata ya a gaba da wullakanci ehh haka nace ba,ayi hakan bane dama ta fada a gadarance.
Atika ki daiyi da mai kalan diya mata amma bani ba don nawa da Allah ya ban sun isheni tinkaho a ko ina a garin nan don ba sai naje ina karamin murya kwaso wasu diyan ba .
Sai fadan ya rikice masu tsakaninsu su uku kuma Dada tayi rabo har ta gaji ta fashe da kuka sai anty Nafisa ta daga waya ta kira daddy a kasuwa ta fada mai sai gashi yazo rai bace.
Bai tsaya tambaya ba don Nafisa ta fada mai abinda ya kawo rikicin don haka yana zuwa yace Atika ki tattara kayan ki da yarki ku bar min gidana a yau din nan basai gobe ba.
Nan kuma Dada tasa mashi kuka tana fadin sai dai suje tare ina zasu da daren nan ga yara dole ya barsu akan washe gari zasu tafi har halimatu di dake ta kuka wai bata zuwa saboda rashin zuciya.
Ni dai ina part din mu tunda ba abin kallo bane nan aka zauna bayan sallah isha,i daddy ya tambayi ba,asi mum ta mayar mai da komai tun farko tunda itace babba a cikinsu.
Ya juyo kan halimatu yace yau ga ranan magana tunda kikazo gidan nan Kubura ta taba koranki a part din ta ki fadi yau ta girgiza kai yace ba kai nake son ki girgiza min ba ki bude baki kiyi magana.
Tace bata taba ba to meyasa kibar part din bayan kinsan nan na ajeku wurinta yar uwarku ta tsaya ke kuma kika canza sheka dama irin wanan rana nake jira yazo ai .
Sai ta dukar da kanta kasa yace magana zakiyi ko gobe tunda safe in sakaku motar katsina daga ke har uwarki wallahi jin ya ambaci wallahi yasa ta dago kai ta kalleshi tana dan kokarin budan baki tare da fadin dama dama naga tafi son zeey ne yasa kawai nabar part din.
Dole inso mama tunda ke,,,, dakata don Allah banzo gareki ba ya fada sai mum din tayi shiru tanawa yar uwarki wani abune ke batayi maki ba ?
Ta girgiza kai to ya kika gane tafi son mamana dake nan ma shiru tayi to tunda baki da amsa kuma ba koranki akayi ba akan me zakije wurin uwarki kiyi hadi ?
Nifa yaya bashi ba gidan nan kaf an saka mata Ido sai a gaban idon ka ake nuna anasonta har satan nama da kudi da tufafi saida malka da yaranta suka dafawa yarinyar nan.
Gashi kullun hjy malka da yaranta komai zasuci ko susha itake dafa masu amma hakan baisa sun ganewa yarinyar nan ba.
Kutuma wace yarinya ke muna wanan aikin wazaici girkinta ko jagwalgwale amma kin rainawa mutane wayau watau kinzo fada daine akan yarki.
Meya rabata da part din hjy kubura idan ba son jiki da munafunci da kika koya mata bandashi bata iya komai ba a rayuwanta.
Idan kince hakan gaskiya kika fada nazo nan da biyu kai kuyi min shiru gobe ki shirya keda yarki ku koma gida ta huta yiwa mutane bauta a nan shike nan daddy ya fada masu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/9, 09:51] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

1?? 5??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

An samu an sulhuta da kyat bayan yan kokekoken daya biyo baya tsakaninsu kan cewa zata zauna tare da Dada a part dinsu tunda dama a wajen Dada take zaune din.
Don Dadan ta nuna cewa tashin tashinta idan ya kori Halima din da a yanzu nida Dada muka saura kiranta da halima ita Dada sai tace halimatu din nan niko ina fada ta dinga fada dani ke nan wai ina bata mata suna.
Don yanzu ta koma amsa Sadiya a school su kuma yan gidan daddy din yan gayu suna kiranta da Sady cool sunan da takeso ke nan fiye da wanda ake kiranta dashi da baya.
Ga karyan tsiya tana nuna ita din diyar cikin daddy ce ta dinga shara karyan arziki saidai azo a tambayeni ince ehh hakane din amma kowa yasan ni iyayyena suna katsina don ko a hausa na suna gane cewa lalai daga katsinan na fito.
Saboda hausan namu ya dan bambanta da nasu kanawa kamar yadda hausan kowani dan state ake saurin gane jaharshi don harshe da dabi,u yakan bambanta.
A cikin wanan dan takin mahaifana suka dawo kano da zama a cikin gidan da daddy din ya gina masu wanda wasu yan uwa manya sukayo masu rakiya har zuwa kano din.
Naji dadin wanan abin duk da dai ba,a wajensu zan zauna ba amma munje nida hjy Mum mun dan dade a gidan tare dasu naga kannena sun kara min girma sosai yayin da baba bai boye jin dadin ganin yadda na koma ba yanzu a hannun Hjy Mum dake rikona.
Don nazama wata babba dani komai ina yinsa cikin hankali da wayewa wanan yasa iyayyen nawa jin dadin ganina din da sukayi a lokacin.
Ana sallah azahar nice ma na matsawa Mum da mutafi saboda ranan mum ce zata bawa daddy abincin dare don haka muna da aiki da zamuyi idan mun koma din.
A bakin Hjy Mum da suke zance da diyata naji irin rikicin da akayi da hjy Mommy da daddy akan dukiyan da daddy din ya warewa mahaifinmu da sunan ya bashi su halal malak har gaban Allah.
Wanda hakan ya tunzurata ta shiga ballawa daddy din miyagun magana marasa daddy har abin ya kaisu ga saki a tsakaninsu sakin ma kuma na tijara da har yasa ta bar masa gida wanda sai a lokacin nasan ashe mommy din wai bata gidan na daddy.
Allah shedata banji dadin jin wanan maganan ba duk da ba,a kan baba kawai ya faru ba amma kusan hakan shine sanadin faruwan komai a tsakaninsu din.
Nan na barsu suna hira na dauki abincin Dada don in kai mata don ina son in dawo in wanke uniform dina da ban wanke ba a ranan kafin dare yayi sosai duk da ina da wanda zan saka a jikina din.
Tunda na doso part din nake jin muryan Dada yana dan tashi da alaman fada takeyi da wani a lokacin har na karasa na kai abincin can ta baya dakunan da su Dada din suke zaune wanda aka gyara mata shi don an saka komai irin su kujeru tv capet da sauran abubuwa wanda a takaice dai daddy ya dauko gyatumanshi ya dawo da zamanta yanzu a kusa dashi ke nan ba zancem komawa katsina kuma a wajen Dada din .
Duk wanan yana cikin tashin hankalinda mommy din tayi da daddy har yaja mata saki a cewan bakunan su wai mommy tace don daddy yaga baida lafiya shine yake rabar da dukiyanshi ga yan uwa don yai masu keta su iyalanshi yana kwasan dukiyanshi yana bawa yan uwanshi da sunan taimako.
Idan ba aikin asiri ba wani mai hankali zaiyi wanan abinda daddy din keyi don haka ita wallahi bata yarda da wanan tsarin daya dauko yi ba.
Saidai in hakane ita ma yayanta ya ware masu nasu kason ya basu tun yanzu kowa ya rike a hannunsa mamaki kwarai daddy din yayi da kalamanta din gareshi.
Har ya dago yana fadin waiko malka kina cikin hankalinki kuwa ko so kikeyi ki konani da gaske ki hana min lahirana a sanadin ki ranta ya baci tace ina ruwanta da lahiranshi ita su dai ya basu dukiyansu kafin asiri ya kara kan mashi ya kwashe komai ya rabar.
Wanan kalman ya harzuka daddy din da ita har yace ke malka kije dai yau na sakeki tunda nagane badon Allah kike zaune dani ba dai.
Dama kowa yasani an fada kuma tunda kika aureni cewa don dukiyana kika aureni tunda da farko aida banda komai kina kikayi sai daga baya dana dan fara dagowa kuka shiga kuka fita har na aureki keda iyayyenki.
Ita kuma tace dashi dadin abin dai ba ita kadaice iyayyenta suka iya shige da fice ba wajen malamai shima nasa iyayyen ai sun iya don suna mata kuma tasan komai kan hakan.
Yanzu ma mommy dince ta shigo gidan ta tayar da zancen tana surfawa daddy din zagi shi da yan uwa da mugun kalamai wanda ran Dada din ya baci na yadda tazo tana aibanta mata zuria har yakai ta tunzura ta biyewa kalaman nata sun rikice.
Ban shiga ba ina ajewa na juya zuwa part dinmu koda naje ban fada ba sai da ta jiyo hayaniya ta fito ta samesu ida Dada ke fadin ko an raba an baki kason nawa zaki samu marka ?
Mai yaya maza a gida ta kyale taja bakinta tayi shiru saike mai gayar yaya mata saboda kwadayi zakice sai an raba dukiya anbaki kar ya kare.
Su yaya matan ba mutane bane Dada diyan suka fada nan dai suka tararwa Dada din da yake ta iya ta biye masu suna maida kalamai a tsakaninsu din.
Anty Nafisa ta fito da tsohon cikinta daga daki tana fadin haba mummy wanan abin kunya da kike ja muna fa daddy fa hakkin zumunci yake kokarin fitarwa yan uwansa .
Ina dai kudin nan nasane shiya nemi abinsa don haka ki kyaleshi kisa masa ido ko duka zai raba masu kudinsane ai mommy.
Kuma ya fada min cewa kwangila yayi mai tsoka ya samu alheri ya roki Allah ya yayi mai mafita dasu har dabaran yin hakan yazo masa.
Don Allah mommy ke ba mai taimaka masa bane wajen yada wanan manufan nasa na alheri a garesu tunda kema harda yan uwanki aikaiwa alherin nan bafa nasa kadai yabawa ba kudin nan har naki yan uwan.
Don daddy yaiwa yan uwansa hidama da dukiyarsa a yanzu shine zai rage dukiyansa kome har kuke wanan abin kunyan kuma a yanzu bakuyi saki a tsakanin kuba a da sai yanzu yanzun ma din ace akan alheri mum kada abinda yan uwa ke fada a kanki ya zamo gaskiya fa.
To uwata imun fada keda kika san gaskiya har kike fada ni kinsan bansan wanan ba ai saikin fada a yanzu zan sani tunda dama yan uwana fadi a kaina .
Ayai kiyi hakkuri mommy ban fada don ranki ya baci ba ai don Allah ku bar wanan abin na zauna yau da safe da daddy akan yayi hakkuri ya barki ki dawo dakinki ki zauna yanzu kuma ki shigo kina wanan masifan ai kinsan ba zaiji dadin hakan ba har ya hakkura din.
Kallon hjy mum tayi datake tsaye yar ke wanan kalamin a gabata sataji haushin hakan nan take ranta ya kara baci ita ko Nafisa din ganinta bai hanata fadan abinda take fadawa uwar ba don hakane uwar taji mugun haushi tayi cikin diyan da zumar dukanta sai muryan danta mukaji yana fadin kada ki tabata mana mommy.
Kinsan dai anty Nafisa ba zata fada maki karya akan daddy ba nima na sameshi ya fada min sun zauna da ita don shi kikaji na kyale zancen hakan .
Alokacin hjy mum ke bawa Dada hakkuri ta fita part din ta koma nata don Allah abar zancen a sasanta a tsakani tunda yara har sunsa baki a zancen.
Wani juyowa da yayi ya watso muna harara hakan yasa da sauri na labe a bayan hjy mum dake kusa dani tsaye ina satan kallonshi ta bayanta.
Ku,kuma me kuka tsaya saurare ya fada a cikin tsawa yana zare idanunsa garemu hakan yasa hjy mum fadin kubar wurin nan na juya da sauri na riga kowan mu fita daga part din ni dai har nakai ina jin muryan mommy a lokacin .
Barcine ya daukeni a fslon hjy mum din ban sani ba wanda har suka shigo suna dan hayani hakan ya tayar dani daga barcin dana samu inayi din a lokacin.
Saidai ban motsa ba illa ido dana bude yayin da nake gane da yaranta take wanan zancen a lokacin don muryoyin su da nake ji na gane hakan tana fadin lalai yanzu na yarda hjy malka akwai jahilci a lamarinta sosai.
Mum ki daina biyewa wanan macen kin dai ji yau metake fada da bakinta yau din ma ni sai naga kamar bata cikin hankalinta babban ya fada yana kallonsu.
Ba dole ta koma haka ba tunda tana ganin hakan ba zai taba faruwa ba kuma ya faru yanzu zata karasa halaka kanta wajen yan bori da yan tsubu tana ganin wani ya saka hakan ya faru gareta.
Ba,abinda zai sameki mum tunda baki mata ba ya fada yana mikewa lokacin wayana yayi kara na mika hannu ina dauka duk suka kalloni danna dauka nayi ina fadin inna ina wuni ta amsa min sai kuma na sake fadan gata na mike ina mikawa hjy mum din wayana.
Ke ki kawo min abinci ya Nasir ya fada a lokacin da nake shirin mike tsaye daga gefe ya Addel ke fadin baka san sunan ta bane yau kuma zaka kirata da Ke.
Baidaiyi magana ba nima ban iya amsa mai ba na shige ciki bandaki na shiga na kewaya kafin na hada mashi abinci nakai mashi wayan nawa har lokacin tana hannun mum tana bincike a cikinsa.
Nasan tana dubane kona saka wani abinda bai dace ba da shekaruna baikai dauka ba a lokacin wanan bashine karon farko da hjy mum takan dauki wayana ba kusan ko yaushe tana dauka tayi bincke a cikinsa.
Alhalin banda komai a ciki sai yan cartoon da film din hausa irin na ibro yan gajeru na ban dariya number kuma baifi na mutum goma bama a lokacin da nake dashi na iyayyena sai nasu mum din dana kawayena shima ba mai yawa ba dai hakana.
Zama nayi ina fadin wallahi wancan mugun ya firgitani mum na dauka dukan mu zaiyi ai yadda ya kallomu din nan tace hauka yayi da zai dukeki kawai bacin raine suma yake damunsu a yau yadda uwar keyi din nan.
Koda yake shi dama yana yarda da haukanta ba kamar Nafisa yake ba don ita tun tana karama bata yarda da wanan shirmen nasu dan dama shi haka kawai yakan dauki fushi dani wani lokaci kamar ba namiji ba.
Ya Nasir daya fara cin abincinsa ya dago yana fadin wai Hafiz take zance dama ai dama ya bal,balaku tunda gulma kuka iya da kunji kyasham ba,a rigaku zuwa kallo.
Dan marairaicewa nayi ina fadin hai ya Nasir ni yaushe nake irin wanan da har kake mun fatan wanan gabjejen katon ya dake shifa yana da saurin hannu hakan yasa nagudu tunkan ya karasa rufe bakinshi.
Suka kwashe da dariya Mum tace wai kin ko san wanan ya mari mutum ai sai jinya nace nima tsorona ke nan yasani shan maganin dole ban shirya ba.
Motsaraciyar banza watau mukika raina dama ko ince ni da bakya tsoro nace kaima ai ina tsoronka yaya na daifi tsoronsu su biyun nan shida ya Addel don ko yaushe fuskansu a daure yakesu.
Ni dai ban kara jin zancen mummy ba gashi har yaranta sun fara ba mutane tausayi a gidan don yadda kallo daya zakai masu kasan suna cikin damu da kewar uwarsu.
Zuwan su baba gidan ranan sun dade da daddy a falonsa ina ta dakon jin yashigo part din amma har yamma saina gane sun gama ganawa da daddy sun tafi don haka na debe rai ga ganinsa a ranan .
Sam mum bata koya min zuwa gidan mu wurin iyayyena ba koda zamuma a tare muke zuwa mu dan dade kan mu dawo gida da tare da ita kuma don haka ban ma samun wani sakewa a yanzu da iyayyena din.
Hjy Mum gaskiya tana kokari matuka dani wajen nuna min kauna da sakani hanya ta yadda ba zan wahala a rayuwa ba nan gaba.
Ma,ana dai ta mayar dani tankar yar cikinta data haifa hakama diyanta sun daukeni kanwarsu sosai ko don ganin yadda uwar ke min ne son basu son suga ko hjy mum din ta bata min rai balle wani a gidan nasu yace zai saba min sai inda karfin su ya kare a kaina.
Muna hutune don haka ba fita muke ko yaushe ba muna gida sai islamiya da yanzu ni kadai keda kokarin zuwa ko yaushe sauran sai sunga dama suke zuwa tunda daddy ba mazaunin gida bane shi .
Ranan na dawo daga islamiya na samu mum bata gida nayi mamaki don haka naje part din su ina tambaya suke fada min sun kai anty Nafisa asibiti wai zata haihu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login