Showing 48001 words to 51000 words out of 103712 words

Chapter 17 - DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

7855

kuma cije baki.
Ta dan kai zaune tana fadin Sister kira min Mum idan tana nan don Allah ko kuma ki kiramin Dada dai don nasan yanzu mum tana wajen daddy.
Da sauri na juya don in kira mum din har da Dada don ina ganin wanan ba zancen kiran mum bane ita kadai na murda kofan in bude naji ta saka wani salati me karfi a wahalce murya na rawa tana son tashi ta dafa gado ta kasa sai murde murde takeyi a wajen ita kadai.
Hakan yasa da sauri na dawo gareta kuma ina faman yi mata sannu hannu ta miko min tana min alaman inzo in taimaka mata niko a lokacin nagama rudewa ko nace bari na kira Dada dai tazo.
Yadda ta ciji kasa ta yunkura ta mike ta dafa gado haka harafin bakinta ya fito da karfi tana fadin sister ki kamani don Allah zan mutune kila da sauri na rike ta ina fadin baki mutuwa anty bari na kira su mum suzo.
Wani nauyi naji tayi min a hannuna wanda hakan yasa nakai zaune bakin gadon ta dora kanta a kan cinyata gami dayi min rikon da kamar karti goma naji sun rikeni a lokacin.
Saida na dan sake dan kara kafin naji tayi wani irin nishi da karfi saiga da ya fito daga jikinta yana callara ihu irin na jarirai wani irin tsoro ya kamani lokaci guda don ko ance nasake fitsari bani mussu.
Ganin ashe haiwace yasa na dan dake ina fadin sannu anty ina kokarin cireta a jikina ta sake wani irin ajiyan zuciya tana amsa min tare da fadin yi sauri sister ki kira wani yazo ya yanke cibi don Allah.
Na fito a gigice ina kwasan gudu zuwa wajen Dada banko kula da mum na wajen ba tazo tambayan ko nashigo wajensu don taje part dinta ta samu a rufe yake ta dauka nazo nan din.
Ke lafiya ga uwarki tazo neman ki kina ina hakane mum ta tambaya ta tare zancen Dada din nace mum anty Nafisace ta haihu yanzu.
Haihuwa a ina nace ina haki tana dakinta salati suka saka suka kwasa zuwa dakin nata dukan su suna rige rige Dada na fadin dazun fa da uwarta zata fita shine tace ita bata zuwa ina mata sheri.
Kusan tare mukai part din dasu saidai a falo na tsaya don sai lokacin naji tsoro kuma ya kamani Dada ce ta fito muka zauna a falon nan muka barsu tare da mum din a cikin dakin.
Dan tsayin wani lokaci saiga mum din ta fito da abinda aka haifa din nade a cikin wani zanin anty din don a lokacin ba zance ga kalan abinda ta haifa ba don ban tsaya duban kome ta haifo ba saboda firgicewa.
Dada ta mikawa da sai fadin take ikon Allah na yarda haihuwa habone don baifi awa ba da muke zaune da yarinyar nan a waje har inawa uwata fadan kwasa su fita haka su barta ita kadai ga ciki tace min ba dadewa zasuyi ba ai a can din.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/14, 11:11] Aishatu Aliyu Musa=??>?p?: DUBA MIN BAYA FOKON ,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

1?? 6??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Wayan da ya Addel ya kara sai mun ya zama abin hassada ga yan uwana a wanan gidan duk da ba wani dogon shiri muke a tsakanin mu ba wanan bai hanasu sakawa takona ido ba don basu san da wayan ba da farko sai daga bayan nan suka kula da wayan da nake riko din wanda ya Addel ya sayo min din saidai basu san a ina na sameta ba har yanzu.
Don ince a dalilin wayan nan harkal ta da halimatu yayi rauni a yanzu a cewanta ita da uwarta wai asiri iyayyena ke min na farin jini a gidan nake da sa,an mutanen gidan wanda ba haka bane kuma.
Rashin kiuyana da girmama mutane yake jawo min alheri ga kowa a gidan koda mutum bai niyar yimin hakan ba zai mun duba ga irin halina ya kyaleni wanda a lokacin ban masan wanan halin da suke min dubaiya a kansa ba din.
Amma halimatu da uwarta duk sunbi yan uwa suna shelata nida uwayena wai asiri mukewa daddy da iyalinsa yasa baya kallon kowa a cikin dangi saimu a yanzu.
Ga mutane mafi yawa suna yarda da vamfin akan asiri sai kadane suka san gaskiya basu daukan hakan da tasiri a zuciyarsu su dai san hamon jinine bayan hakan kuma daddy din yana fadawa mutane ai uwarsu daya da baba don a hannun maihaifiyar babana ya tasoshi kuma komai da yazama yau itace silar hakan agareshi.
Dawowan anty asibitin nan yasa na zamo mai kula da ita bani kadai ba son har hjy mum da Dada suna bata kula na musamman kamar yadda likitoci suka umurci a bata din.
Sai kuma hakan ya koma hassada don ko yaran hjy mummy sun matsa da kiranta a waya suna mata gulma wai kada hjy mum ta asiceta su juya mata hankali don ko wani irin abu a yanzu bata sukeyi da sunan samun saukin gwiwa wanda hakan ya dagawa hjy mummy hankali sosai.
Nan ta fara bin yan uwa masu fada aji a cikin dangi don sam taki yarda ta koma katsina tun fitanta gidan a nan kano take zama gidan wata aminiyar ta wanda zaman nasu ya fara canza sallo don hjyn ta nuna itafa ta gaji wanan na cikin abinda ya kara dagawa mummy hankali take yawon bin yan uwa abawa daddy hakkuri ta dawo dakin ta.
Tare da alkawarin cewa ta fahinceshi ta daina saka mai ido yanzu ga komai nasa har ta labe ga haihuwan anty Nafisa da take fada masu abin kunyane a gareta Nafisa ta haihu bata gidan nan ai .
Wanan suka duba sukaci karfi daddy din ya yarda hjy mum din ta dawo sai kice wata yarinya karama don ko bata dawo ba saida ta zauna ta gyara kanta irin da mata keyi harsu kumshi da kitso da da bata da lokacin yinsa duk akan daddy ya rude akanta ta tsaya tayishi a yanzu din don dawowanta gidan daddy din.
Saida ta kwana tayini kafin muyi arba da ita koshi anty nafisace ta kirani wai inzo in duba mata abu yasa nashigo part din amma ina jin komai a wajen hjy mum tana fadan yadda mummy din ta dawo gidan tana abu kamar karamar yarinya.
Ina shiga falon mukai arba da ita zaune Asiya da mairo suna gefenta da gani wani zance sukeyi a tsakaninsu na shigo zuwa nayi har inda taken na kai kasa ina gaida ita din da fadin mummy ina wuni an dawo lafiya.
Ta amsa min ciki ciki ba yabo ba fallasa agareni hakan yasa na mike da sauri na nufi hanyar shiga ciki muryan Asiya naji tana fadin ina kuma zaki shigawa mutane haka zikau dake ?
Sallon ki kullawa mutane wani sheri kuma ace ga abinda akayi maki ko don kinga kina da daurin gindi ba dama ayi magana kike zato.
Anty Nafisace ta kirani aida baki gani ba nan na juyo ina fada kafin in kara naji mummy din tace jeki don Allah ina ruwanki da shigowanta ko an hana ta shigo part din ne ?
Nasa kai nashige zuciyana fal da tunane saiga anty Nafisa din mun hade a kofa da ita ina fadin gani anty sai naga ta wuceni tana fadi jirani a daki inzo sister .
Ashe fada tayiwa Asiya din don komai a kunnenta ya faru na gane hakanne don yadda ta shigo tana huci a dakin lokacin tana shigowa tace dani yaran banza kawai suko koyi basayi da halinki su koya basu da auki sai gulma da kisisina da zaman saka ido suna zuga mummy ko yaushe.
Dan dariyan yake nayi mata ina kara fadin gani anty ta kara dagowa har lokacin ranta a bace tace gara da baki biyewa yan iska ai gasu nan komai basu iya ba duk jerabawansu baiyi kyau ba to basuyi karatu ba suna aikin gulma da saka ido mana.
Kiyi hakkuri anty na sake fada a cikin yar murya saita ja tsuki kafin tace barin fadawa yan iska ita mummy din da take biyewa tseguminsu ai tafi laifi.
Wani abu zan makine tace ehh dama wancan jakkar nake son in duba wasu kaya yasa na kiraki don wallahi tun shekara jiya nake son saukesa amma na kasa hakan.
Mikewa nayi na nufi wajen ina sake tambayan wanine a ciki ta nuna min shi da kyar na iya jawo jakar na kawo tsakan daki muna cikin budewa kanin nata ya shigo dakin ban masan yana gari ba sai lokacin.
Gaidashi nayi ya amsa min da kyat kafin ya murde fuska yace mekuma ya hadaki dasu Asiya kedake fama da kanki tace munafunci don basu kaunan a zauna lafiya a gidan nan.
Yarane ai ki barsu zasu bari don yanzu duk fadan da zakiyi masu basu fahintarki sai suce kin matsa masune nayi mamakin jin kalaminsa din ban dauka ya iya kalma mai taushi ba a rayuwansa sai naji tace is Ok ai ya wuce.
Gobe din zaka tafine yace wai haka naso gara nabi file din nan naje ayi komai a gabana zaifi yafi min wanan zaman da nakeyi a nan yanzu tace is better karfe nawa zaka tafi din ?
Yace zuwa dai sha biyu nake son in kama hanya OK ta kara fada tare da furta zan ganka kafin katafi din yanzu muna wani dan aikine da sister nan sai ya dan kalloni inda nake duken idan mun gama zan kiraka a waya kazo mu san yadda za,ayi din.
Ya juya ya fita ba tare da yayi magana ba nidai ina duke da kaina saida ta juyo tana fadin sorry sister na barki da kaya a hannu aiki yake son samu a abuja su kuma sun aje shi a zamfara shine yake so canzawa.
Allah ya taimaka na fada cikin yar siririyar muryana ta amsa min da to Amin abinne akwai wahala mutum ya gama karatu sai kuma aiki yazo yayi tsaye mukaci gaba da gyaran kayan sai kusan magariba na samu kaina kodana fito gun Dada na biya don bamu hadu wunin ranan ba da ita nasan ko sai tayu min korafin hakan.
Gashi kuma kwana biyu bata nan taje gun iyayyena ta zauna dasune tayi kwana takwas da tace sati biyu zatayi amma jin dawowan mummy yasa Dada ta kasa zama ta dawo gida don sa ido.
Aiko ina shiga ta shiga min korafin ba,aganina yanzu ai take zancena da yake halimatu dakilace saita kyaleta bata tanka mata ba sai kuma gani nashigo wurinsu din.
Ina kika shiga hakane ta tare dashi tun jiya dana dawo kowa yazo gaidani banganki ba sai yau din nan har na fara zance ko baki da lafiyane wai ?
Nace lafiyat kalau Dada jiyan dai bana gida ina islamiya kinsan na kusa sauka yau kuma tun safe ina wanki yanzu nagama sai kuma anty Nafisa ta aika inzo tun dazun ina wurinta ina gyara mata kayan ta yanzu nafito.
Ta dan duba kofin tace dada kinga uwarku mara kunya dai ta dawo taga bin boka da malam da kuka a wajen manya saida ta dawo gidan nan don naci Allah ya gani banson zuri,an mahauta gidan nan don ba mutanen arziki bane cikin mu dama tsoho ya fadi tunda isuhu ya shiga dabi,an nan yace zai gurbata masa zuria gashi kuwa hakan yana faruwa yanzu.
Toke Dada ina ruwanki inta dawo tunda ba saman kanki zata zauna ba niko keda ruwa mara kunya tacewa halima data katse zuban da takeyi din tace.
Da ban haifi dan ba zata ganshi ta aureshi har ta nace tana zuba iko da mulki iya son ranta haka au ke kika haifeshi ashe na zata Abu mai gyadace ta haifeshi ai cewa takwarana.
Don naga da ita daddy yake kwantace ai ungo nan ta fada Abu maigyada tayi komai wallahi don yayi alfahari da ita ai baiyi ga banza ba don ya rike amana har bayan ranta.
Niko nasan halima din ta fadi hakane da biyu banko kai karshen tunane na ba sai naji tace wani amana ita kadai ta rike da ai kuma kun rika meyasa ba,a hakan yanzu ?
Kina da wata manufa ke nan ga zancenki diyar nan ke kenan baki son a zauna lafiya kulun kina takalan magana to Abu mai gyada da zurianta dai sunfi karfinki don ki sani don ko suna da abinda baki dashi shine tauhidi.
Nan ko tasa Dada din agaba tana ci mutunci don me Dada zatace mun fita komai a duniya ke nan ita bata arziki a duniya Dada ke nufi kome ?
Nikan nafice na barsu suna rigima a tsakaninsu su biyu a part din na kuma samu mum ta hau fushi dani akan dadewan da nayi saida nace ina gun Dada ne suna rigima da halima na tsaya sai kuma ta koma tambayana akan me kuma suke rigima ?
Na labarta mata abindake faruwa tace wanan yar da tada zaune take yanzu kuma ta bugawa uwarta waya tace ga shirin da akai mata akanki baida wuya a wajenta itako data fita hauka ta hau zancen ta zauna tunda ba kunya garesu ba.
Nasamu hjy mum tagama duk aikin da zanyi a lokacin don haka na nufi dakuna na gyara a gagauce don magariba ban fito ba saida nayi sallah har isha,i na fito don cin abinci faten tsakin masara yaji kayan hadi mum tayi muna shi kuma mukaci matsayin abincin dare a ranan har ina zancen in kwanta ya Nasir ya shigo shine dan farko da mum ta fara haifa a gidan nima sai daga baya nagane hakan.
Don ba zakice bashi ya haifi ya Addel ba gaskiya dubaga irin shakuwan dake tsakaninsu don daddy yafi sonsa da anty Nafisa yana yawan shawara dasu koda kuwa basu kasan zaice ajira Aliyu ya dawo wanda hakan ke batawa hjy mummy rai.
Tayi fadan hakan har tagaji dole ta saka iido a karshe tabar zancen a fili amma tana yawan korafin hakan lokaci lokaci zatace abin yana damunta ga diyasa ya dauko bare ya saka ajikinsa duk da tasan shi din ba bare bane a wajensu mutuwace ta kawo hakan.
Ba wani abu mai wuya bane indomie ne da kwai zan dafa mashi na shigo falon tambayan mum ko kwai nawa zan dafawa ya Nasir din.
A falon na samesu da ya Addel shima yana fadan ba zai iya cin wanan faten da mum tayi ba da daren nan sai gani mum tace ga mama nan saita dafa maku abinda take dafawa Nasir tare dakai ai.
Me take dafa mai ya tambaya yana kallon mum din tace ina zan sani ai gata wai me kike dafawa Nasir ne ta kalloni tana tambayana nace indomei da kwai mum tace shi yafi wanan faten nawa kama ciki ke nan ?
Kwai nawa zan saka mashi mum na tambaya daga bayana naji an bani amsa da hudu muryan ya Nasir ke fadan hakan gareni na dan juya ina kallonsa yayinda mum ke fadin tunda kai kadaine sai a dafama hudun ai.
Draman su bai karewa da Nasir din hakan yasa na juya da niyar komawa kitchen din naji mum na fadin shi baki tambayesa ko kwai nawa zaki saka mai ba nace nasani biyune.
Hakan yasa ya lumshe idanunsa lokacin da mum ke fadin watau har kinsan ko nawa yakecishi nace nasani mana mum naahige na barsu ban fito ba saida naga hada masu komai na kawo masu abincin a gabansu na dire nan na barsu ya Nasir yana zuba masu santi yanaci.
Ban fito ba saida safe nayi duk yan aiyukan da zanyi na koma na kwanta don akwai gajiya a jiki barci na samu sosai nayi lokacin kafin in tashi inyi wanka nafito da zumar in karya don kunun gyada mukayi kuma ina sonsa sosai don haka mum take munashi don itama tana so.
Haka kawai ganinsu yasa girjina bugawa duk da baiko kulani amma masifan tsoronsa nake ji tunda na fahinci baida mutunci ko kadan a fuskanshi.
Masangalin kujera kawai na dafa nace ina kwanan ku wanda jin hakan yasa suka juyo kamar kullun wanan kallom wullakancin nasa ya jefo min sabanin yan uwansa da suka amsa min a cikin mutunci kamar yadda muka saba.
Ai gara da kika fito ki taimaka ki dafa muna wani abu mu hada da kunun gyadan nan zamubi hanya dan anjima kadan don muje da nauyi ya Nasir ya fada.
Saidai kai nikan ba zan tsaya cin jagwalgwale ba in bi hanya cikina ya rude ina tsayawa kai wanan yarinyar ta iya girki harda na indiyawa sarkin barkwanci ya Nasir ya fada yana dan dariya.
Zakace shi ba ciki daya suka fito da ya Addel ba saboda yawan barkwancinsa ga mutum don hakanema nafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login