Showing 99001 words to 102000 words out of 121037 words
Lamido a waya yace suzo dukkan su part dinsa yana son ganin su, dama suna tare basu riga sun tashi ma daga falon ba dan ko aiki babu wanda cikin su yayi yunkurin tafiya saboda daga Daadah har Raihanan sun rufe kofar dakunan su sun shige ciki suna kuma tsoron wani abu ya same su. Part din Abbyn suka nufa suka same shi a falo yana zaune yana jiran isowar su, zama sukayi ya kalle su daya bayan daya sannan yace
"Na yi tunani na kuma yanke shawarar bawa Raihana zabin zuciyar ta, zan kuma cika alkawari kamar yadda na dauka sai dai na dawo da daurin auren gobe ba sai jibi ba, inaso Lamido ka kira Kamal ka sanar masa, idan mutum daya ne ma ya samu zuwa ya wadatar, idan ba'a samu me zuwa ba, ni nan zan zamar masa wakili sai kawun ku ya yi waliccin uwata. Idan yaso ku dauke ta ku kai ma mijinta ita, ni kuma sai ku fara nemar min visa domin zan bi bayan aboki na."
Wanan karon har Hydar maganar tayiwa dadi, suka yi murmushi dukkan su sannan suka ce alhamdulillah. A take Lamido ya fita daga falon ya kira number Kamal a lokacin yana tare da Aryan din da ake kara masa drip jikin nasa ya sake rikicewa sosai fiye da dah dan ma yana da masifar karfin hali da dauriya. Ba dan sun nuna masa dole dole ba da babu abinda zai sa ya yarda ya kwanta wanda kuma yake da matukar bukatar hutun.
"Lamido ne yake kira."
Yace yana nunawa Aryan din wayar, juyar da kansa yayi Kamal ya d'aga suka gaisa sannan ya tambaye shi idan suna tare da Aryan ne, ya amsa da eh sanann yace ya dan fita waje zasuyi magana. Chan compound din gidan ya fita sannan sukayi maganar, wani irin dadi ne ya lullube Kamal din, ya dawo dakin da Aryan din yake ya tarar dashi kamar me bacci, be fada masa ba dan dama plan dinsu kenan shi da Lamido. Zama yayi a gefen gadon ya hau duba available flight da zasu yolan gobe, yaci sa'a ya samu na safe amma da yar tsada, haka ya siya musu sannan ya dauki key din motar sa ya fita. Yana driving din suna waya da Baba (Malam Hassan) ya sanar dashi abinda yake faruwa sannan ya kira Ya Nabeela ya sanar da ita itama, lokacin tana hanyar zuwa gidan Kamal din saura kiris ta saki steering motar saboda murna. Rokon ta yayi kar ta fadawa Aryan din surprise zasuyi masa kawai.
Su uku suka shirya, Malam Hassan, Dr Farouk mijin Ya Nabeela sai wani cousin din Daddy. Da sassafe driver ya kaisu airport ko tashi Aryan din ma be yi ba suka lula sai Adamawar yola. Duk abin nan dake faruwa Daadah bata sani ba haka ma Raihana, suna dai tare Daadan na bata baki dan ta lura kaamar abinda tace be shige su ba, ganin yadda suka cigaba da sabgar gabansu a ranar. Dangin Ammyn ne suka zo gidan bayan Daadah ta sanar dasu, duk sun dauka ma Raihana sun daidaita kansu da Muhd din ne ashe ba haka bane ba, sai da suka zo sai duk jikin su yayi sanyi haka dai aka cigaba da zama a gidan kamar ba aure za'a yi ba.
Hydar ne yaje ya taho dasu daga airport din suna sauka, ya kawo su gidan suka hadu da Daddy a falon sa suka zauna har lokacin ya kusan karasawa sannan suka dunguma zuwa masallacin. Asabar ce sai kuma tazo da daurin aure da yawa, sai da aka fara na wadanda suka riga su sannan aka shiga daura auren Raihana Nasir Matawalle da angon ta Muhammad Ibrahim Mukaddas bisa sadakin dubu dari da Kamal ya bayar. Kasancewar anyi daurin aure da yawa ya saka ma ba zaka gane wannan mutanen wannan bane haka ma wannan, haka aka gama aka watse suka dawo gidan cikin farin ciki da annashuwa. Matan gidan na zaune aka shigo musu da alawa da goro.
"Kar dai zargi na ya tabbata auren nan aka daura yau?"
"Eh Dadah, an daura auren Raihana da angon ta Muhammadu."
Lamido yace yana murmushi.
"Yanzu har da kai Lamido?"
"Muje ciki zan miki bayani Daadah."
"Me zaka fada min?"
"Muje dai, sirri ne."
Da k'yar ta bishi cikin ya sanar da ita abinda ya faru, sai kuma ta hau murna tana saka musu albarka, ta juya zata je ta sanar da Raihana ya hanata
"Angon yana chan kwance babu lafiya, karki fada mata dan Allah suprise za'a mata."
"Akan me? Yarinya na chan na ciwon so Allah ya share mata hawayen ta za'a ce ba za'a fada Mata ba."
"Dan Allah Dadah, dan Allah."
"Gobe da safe zasu wuce da Kamal, sauran da suka zo dai yau zasu koma."
"Haka da wuri? Me yasa ba za'a bari muyi biki ba."
"Kai Dadah, da fa bakuyi niyyar bikin ba dama."
"Wannan ai auren soyayya ne, wanchan kuma na dole, kai Allah ma yaso na jima ina gyara Raihana, da irin wannan auren bagatatan haka za'a kaita dakin miji ba wani gyara."
"Wannan maganar ku ce Dadah, bari na koma waje."
"Allah dai yayi maka albarka kaji, bari naje na sata tayi wanka ta ci abinci dan wannan ramar da tayi ma Allah yasa kar kasusuwan su ciji mijin."
Dariya ya kwashe da ita, ya barta a ciki yayi waje, ta fito ta nufi dakin Raihanan ta same ta tare da wata kanwar Ammy da tazo ta fada mata an daura auren. Tsabar kukan tayi ta gaji ya ma ki zuwa, ta hakura kawai duk yadda sukayi da ita. Sata taje tayi wanka Dadah tayi babu musu taje tayi ta saka kaya ta zauna da kudaddiyar fuskar ta da ko mai bata saka mata ba bare ta samu arzikin powder. Abinci aka kawo mata taaci kad'an ta koma ta kwanta tana tunanin rayuwar da zata shiga da yadda abubuwan suka faru a dan kankanin lokaci. Tabbas Muhd ba zai taba jin dadin zama dashi ba, tayi biyayya ta aure shi amma ba zata taba son sa ba, har abadah gangar jikinta kawai ya aura.
A ranar Malam Hassan, Dr Farouk da kanin Daddy suka dawo wajen karfe taran dare, shi Kamal sai gobe zasu taho tare da Hydar dan Lamido ranar zai koma bakin aiki Sadeeq kuma yana da abubuwan yi a clinic.
Da duku-duku Daadah ta sakata ta hau shiryawa, tana shiryawar tana kuka sosai har wani jan numfashi take saboda kuka, har ga Allah Dadah taso ta fada mata da ainahin wanda aka daura amma Lamido ya hanata dole ta hakura amma tana matukar tausayin Raihanan ganin har zazzabi ya kamata ga jijiyoyin kanta da suka fito sukayi rado rado saboda kuka. Part din Abby aka rakata ta same shi a bedroom dinsa ya kira sunan ta, ya shiga yi mata nasiha me ratsa zuciya sannan ya rufe da saka mata albarka. Fitowa sukayi zasu tafi airport din wajen sha biyu, mota suka shishiga ita da Daadah ta kwanta a jikinta tana cigaba da kuka k'asa k'asa. Sai da suka zo airport din sannan kukan ta ya karu sosai, ta rik'e Dadah da itama kuka take dan bata taba kawo rabuwa da Raihanan a wannan lokacin haka katsaham ba. Da k'yar aka banbareta daga jikin Dadah Lamido ya rike Dadah ita kuma Hydar ya riketa suka nufi cikin wajen, sai da suka ga shigar su sannan Kamal yazo yayi musu sallama yace sauran kayan Raihanan zasu turo driver ya daukar mata idan an gama hadawa.Daga chan bayan su Kamal ya zauna hakan yasa Raihana bata ganshi ba, ta dora kanta akan kafadar Hydar din bayan ta daina kukan sai ajiyar zuciya da take saukewa a jere.
Ko da suka iso Kanon ma ba mota daya suka shiga ba, driver ne yazo ya dauke su shi kuma Kamal yayi Uber ya bi bayan su, suna sauka ya Aryan wanda yaga missed calls dinsa tun a chan amma be kira shi ba saboda baya so ma ya samu wani clue akan abinda yake faruwa. Yana kishingide a bayan mota kiran Kamal ya shigo wayar tasa. Ya kirashi na dama ya sanar dashi ya tafi gidan sa idan ya dawo sai ya dawo be daga ba,kawai sai ya kira driver Daddy yace ya zo ya dauke shi ya kaishi. Toh suna saukar ne ma Kamal din ya kira ya tambaye shi yana ina dan yaji karar hanya yace ya tafi gidansa, ok kawai Kamal yace ya kashe ya kira driver da ya dauki su Raihanan yace ya kaisu chan gidan Aryan din. Kasancewar daga inda Aryan din yake yafi kusa da gidan akan daga airport din yasa ya riga su zuwa. Har ciki driver ya shigar da motar bayan Baba me gadi ya bud'e masa tunda already ya riga dama yasan motar gidan. Suna shiga Kamal yazo shima a Uber ya sauka ya sallama shi.
Aryan ya riga ya shige ciki amma kofar a bud'e take be rufe ta da key ba kawai murd'awa zaka yi ka shiga. Kofar driver ya nunawa Hydar din ya ce su shiga, ya murd'a kofar rike da hannun Raihanan suka shiga. Kayan Aryan din ne zube akan kujerar wanda ya cire yana shigowa ya wuce toilet ya sakarwa kansa ruwa ko zai rage nauyin da yake ji musamman idan ya tuna daga gobe shikenan bashi da sauran hope. Kasancewar ya kuna ruwa ya hanashi jin shigowar su kwata kwata.
"Ina zuwa kanwata, ki zauna yanzu zan dawo kinji?"
"Dan Allah Hamma karka barni anan, dan Allah."
"Ai ba tafiya zan ba, waje zan je na sallami wanda ya kawo mu."
"Toh dan Allah karka dade." Tace tana share kwallar da ta sakko mata.
"Ba zan dade ba." Yace ya fito ya ja mata kofar ya nufi wajen Kamal da ke zaune tare da Baba mai gadi suna magana.
__*RQ*__
44
***Hydar na fita ta kalli falon sosai da sauri ta mike tsaye domin ta tabbatar da ba wai idon ta ne yake mata gizo ba. Fitowar sa kenan daga toilet din, hannun sa daya yana goge sumar kansa da dan karamin towel sai bathrobe dake daure a jikin sa, sai da ya tsane ruwan kan nasa sannan ya cire bathrobe din da towel din ya wurga su a laundry basket ya zura short trouser ya shafa mild oil perfume. Kwanciya yake so yayi ya dan yi bacci dan har lokacin jikin nasa is weak, dan haka ma be tsaya saka wata riga ba ya fada saman gadon. Yana kwanciya sai ya tuna da wayar sa a falon kuma yana so ya duba ta sannan ya kashe dan kar ma a kira shi. Mikewa yayi ya zura bedside slippers dinsa ya nufi falon kansa tsaya sanin shi kadai ne a gidan. Tana tsaye tana son gasgata in da take tana kuma son gano dalilin da ya kawo ta gidan ya fito. Da karfi ta kwalla kara ganin mutum daga shi sai gajeran wando ya fito, karar da tayi ce ta bashi tsoro dan ko da wasa be yi tunanin ganin ta ba. Juyawa tayi da sauri ta bashi baya tana runtse idon ta kam-kam. Tsayawa yayi chak daga in da yake yana son tantance me yake faruwa? Tunanin zuwan da tayi a wanchan lokacin ya fado masa, me take yi anan? Ya tambayi kansa. Tunowa da yayi da yanayin da yake ciki yasa shi juyawa da sauri zai koma ciki, sai kuma wani tunani ya fado masa, taku daya biyu yayi ya juyo ya shiga takowa zuwa wajen da take tsaye ta juyar da bayan ta ta runtse idonta jikin ta na rawa sosai. A daidai saitin bayanta ya tsaya, har tana jin hucin numfashin sa a saitin wuyanta. Wayar sa ce tayi kara alamun shigowar sako, hannu yasa ya dauki wayar dake daidai saitin sa ya bud'e sakon ya karanta
_"She's your wife man, taka ce halak malak. Sender Babban wa uba."_. Yasa emoji din wink a karshe. Wani irin murmushi ne ya subcewa Aryan, be san lokacin da ya dire wayar ba, sai ji kawai tayi ya rungume ta baya baya da karfi. So tight da har tana iya jin ragowar danshin dake jikin sa
"Na shiga uku."
Ta furta jikin ta na cigaba da rawa sosai,
"Alhamdulillah zaki ce."
Ya rada mata a kunnen ta a hankali. Har cikin kwakwalwarta maganar ta shigar mata, ta haifar mata da wani irin yanayi me wahalar fassarawa. Juyo da ita yayi gaba daya suna facing din juna, idon ta a rufe yake har lokacin ya tsurawa fuskar ta ido da tayi fayau daga ranar da ya ganta. Hannu ya kai ya shafa saman idon nata, yace
"Bud'e idon ki please." Girgiza kai tayi da sauri tana sake runtse idon ta
"Pleaseeeee kinji? Wani abu nake son gani."
"Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan na Hamma Hydar zai kawo ni ba."
Ta fada muryar ta na rawa gashi ya rik'e ta kam kuma very close da jikin sa.
"Hydar ne ya kawo ki?" Yace cike da mamaki, da kai ta amsa masa, sai yayi murmushi kawai ya tauna kasan lips dinsa ya tallafo fuskar ta
"Batan hanya yayi kenan, yanzu ya za'a yi? Ni kuma gaskiya kinzo kenan."
"Dan Allah dan Allah kayi hakuri."
"Um um, ba zan iya ba gaskiya, sai dai idan zaki bud'e idon ki."
"Toh kaje kasa kaya."
"Zafi nake ji, idan kika bud'e kad'an naji zan je nasa amma."
Shiru tayi ya cigaba da kallon ta zuciyar sa cike da farin ciki kal kamar ya zuba ruwa a k'asa yasha haka yake ji. A hankali ta dan bud'e idon kad'an ta kalle shi, dama shi ita yake kallo, idon ta ne ya shiga cikin nasa ya wani narke mata su, da sauri ta maida idon ta kulle kirjinta na wani irin fat fat. Dariya yayi kad'an ya sake matso da ita jikinsa gaba daya, ya kai bakin sa saman forehead dinta ya sakar mata light kiss sannan a kai bakinsa kunnen ta yace
"Tsoron kallon mijinki kike ji?"
Kalmar mijin ta shiga kunnen ta zuwa brain dinta amma sai ta kasa gane ma'anar abinda yake nufi ma baki daya.
"Ok zauna ina zuwa." Yace yana sakin ta, sai kuma ya dawo da sauri yace
"Muje tare kar naje na fito naga bakya nan"
Ya kama hannun ta suka shiga ciki har lokacin taki yarda ta bud'e idon ta, gaba daya ta kasa nutsuwa ta kuma kasa fahimtar ma abinda yake faruwa gaba daya, shi kuwa a nutsen sa yake komai. Ba tare da ya nuna tsantsar mamakin sa ba, yanayin sa kenan. Bedroom dinsa ya shiga da ita ya zaunar da ita a gefen gadon ya wuce wajen kayan sa ya dauki jallabiya ya zura sannan ya dawo in da take zaune ya zauna a kusa da ita sosai yace ta bud'e idon ta. Budewa tayi a hankali amma taki kallon sa tana dan zamewa kad'an ta matsa daga zaman da yayi kusa da ita sosai. Sake matsowa yayi ya kama hannun ta ya juyo da fuskar ta bangaren sa ya cigaba da kallon zagayayyar fuskarta zuwa dan karamin lips. Gaba daya kallon da yake mata ya hanata sakat, gashi da ta dauke kai sai ya juyo da kan nata.
"Please ki bari nayi ta kallon ki, kamar mafarki haka nake ji, how come? Ya akayi hakan ta faru?"
"Oya bani labari, yaushe Abby ya chanja mind dinsa? Tausayi na yaji ko?"
"Nima ban sani ba, bansan nan zamu zo ba."
"Ok wait, bari na dauko wayata na kira kamal, shi zai fada mana komai. Just wait for me yanzu zan dawo kinji?"
Duk yadda ya kware a iya boye mamakin sa ko damuwar sa ya gaza a yanzu, jin sa yake kamar a saman gajimare saboda tsabar farin ciki. Falon ya koma ya dauki wayar sa ya kira Kamal din. Dagawa yayi ya kwashe da dariya
"Ango kasha kamshi." Yace yana kokarin rage dariyar tasa
"Please kun saka mu a duhu, muna bukatar bayani."
"Muma compound din gidan ai, bari mu shigo ciki."
"Ok, kai da waye?"
"Ni da surukinka, bari mu shigo."
"Ok." Yace ya sauke wayar ya isa kofar falon ya bud'e ta, suka karaso Kamal na kallon shi ya sake kwashewa da dariya
"Kasan kuwa angwaye akwai saka jallabiya wallahi, ko me yasa?"
Yace cikin sigar tsokana suka yi dariya dukkan su har Aryan din, sannan ya matsa musu suka shigo. Zama sukayi, Hydar ya mika masa hannu suka gaisa sannan Kamal din ya soma yi masa bayanin duk abinda ya farun da kuma yadda akayi da zuwan da sukayi ya kare da
"Gata nan mun kawo maka ita, sai ku daina ciwon love din ku mike aiki na jiranku."
"Saboda mune agogo sarakan aiki ko?"
"Emana, kaga ba shikenan sai ayi mata new seat a office dinka ba."
"Ni duk ba wannan ba, wato duk kun sani har Ya Nabeela amma babu wanda ya fada min."
"Toh Mr korafi, ai ka fara godiya kafin korafin."
"Surprising naku muka yi ai." Hydar yace yana murmushi
"Mun gode amma kad'an."
"Wallahi idan ban sa ta fito mun tafi ba, babu fa wata wahalar da kayi ta aure ba lefe ba komai kawai aka kawo maka mata amma ba godiya ba komai?"
"Ba komai duk zan yi mata duk abubuwan da ya kamata ne fiye da wanda ake ma kowa ma. Godiya kuma Daadah kawai zan shikenan."
"You are not serious, a gaban Hydar din?"
"Shima ya sani ai, yasan gaskiya."
"You are not nice."
Kamal ya dauki pillow ya jefa masa ya chafe suka sa dariya gaba daya, kallon Hydar kawai Aryan yake amma ya shirya masa rashin m, dole ne ma ya rama abinda yayi masa ta cikin ruwan sanyi.
"Yanzu sai maganar biki, ya kamata ayi biki kamar yadda ake ma kowa ko?"
"A bari hada da na suna nan da wata tara."
Ya basar bayan ya fada kaamar ba shine yayi magana ba, wani pillow Kamal ya sake jefa masa ya mike tsaye cike da mamakin Aryan din
"Muje Hydar."
Yace sai kuma ya kalli Aryan din da shima ya mike tsaye
"Gida zaku koma saboda a fara gyaran nan din ko?"
"Ok hakan yayi, amma ba yau ba."
"Idan kun ga dama karma ku koma, shima a hada da na sunan nan da wata taran ayi."
"Eh hakan ma dai duk shawara ce." Ya fada yana dariya.
"Gobe ma rana ce wallahi, kirawo ta