Showing 36001 words to 39000 words out of 121037 words
zaka je daukar Madam din ne ko na wuce gida?"
"Zanje mana, an gaya maka zan iya kwana ni kadai a gidan nan? Nah ba zan iya ba, sai na rungume matata tsam tsam sannan."
"Dan iska" Aryan yace ya fice ya barshi yana kyal kyala masa dariya
*RUMBUN QAYA*π₯
*DAUDAR GORA*π₯
*IDON NERA*π₯
*A RUBUCE TAKE*π₯
*KI KULANI*π₯
*_uhmmmm_*ππππππππππ
*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*
*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*
*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*βΊοΈβΊοΈ
*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*π₯π₯π₯π₯π₯
0022419171
Maryam sani
Access bank
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*π₯
*RQ*
Β Β Β Page 18
Hafsat Rano
β’β’β’β’β’β’Kokarin motsa ko da karamin dan yatsan sa Daddy yake amma ya gaza, gashi yana jin duk wani motsi amma ya kasa juya jikin sa. Kenan tsawon wannan lokacin Hajiya Zeenat ba san shi take ba? Ko kuma a yanzu ne ta sauya? Baki daya ya kasa tunanin abinda yake faruwa a dan gajeran lokacin.
_"Tunda har ka iya biyewa mace ka bata da duk wani makusancin ka, toh tabbas dama irin wannan ranar ta nadama ta na nan zuwa."_
Wata murya daga chan bayan kansa tayi kokarin tunasar dashi abinda ya faru a lokacin baya. Hawaye ne ya shiga sakkowa yana biyowa ta gefen kuncin sa, bayan ya gama tabbatar da shikenan tasa ta kare, watakila haka zai karasa rayuwar sa har mutuwa tazo ta riskeshi. Kaico! Rayuwar cin amana bata dauke da komai sa tsantsar tashin hankali. Yinkurin ya cigaba da yi har ma da na kokarin yin magana Amma sam muryar sa taki fitowa kwata-kwata, so yake ma ko ihu ne yayi ko wani zai jiyo shi, ko yayi sa'a Aryan ya shigo yazo ya taimake shi. Wayar sa ya hanga ta gefen idon sa tana haske alamar shigowar kira amma ba zai iya kaiwa gareta ba, ballantana ya iya dauka.
A gajiya Aryan ya shigo gidan dan sun dade a gidan Kaamal bayan sun dauko matar sa, sai suka zauna zaman tattaunawa abubuwan da suke tunkaro su, basu ankara da dare yaja haka ba sosai sai da Khadija tayi wa Kamal flashing sannan suke duba lokaci yayi saurin yi masa sallama amma maimakon ya barshi ya taho shi kadai sai yace Khadijan ta dauko Hijab dinta aka shigo da motar Aryan din ciki sannan suka kaishi har gida a motar Kamal din. Sam be yarda da tafiyar a sa lokacin nan ba dan yana tsoron abinda Hajiya Zeenat zata aikata tunda har ta kai ga batun poison duk da ba wai yau ne karo na farko da tayi attempting hakan ba, Allah ne dai be bata sa'a ba. Amma dai duk tsiyar ta ba zata taba yi masa komai a cikin gidan ba sai dai a waje yadda ba zata taba zama abar zargi ba.
Stairs din ya kama ya soma hawa cikin yanayin kasala rike da suit din sa, duhu gidan yayi masa sosai duk da dama duk an kashe kwayayen dake bada haske a ilahirin falon zuwa saman an maida shi me dan gaske kad'an amma duk da haka sai yaga kamar ko ina baki ne kirin, ga wani irin shiru da ya dade be ji gidan ya dauka ba. Cigaba da hawa yayi zuciyar sa ta kasa nutsuwa da yanayin da yake jin sa, tabbas akwai abinda ya faru ko yake shirin faruwa, abinda ya dauka kenan dan a duk sanda yaji irin wannan toh yasan tabbas akwai wani abu da Hajiya Zeenat take kullawa. Dafe kirjin sa yayi da hannu daya jin yayi masa nauyi, ya shiga karanta la'ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin har ya kai kofar dakin sa, ya saka key din sa da yake tafiya da shi ko ina ya bud'e ya shiga sannan ya saka key din ya sake rufewa ya kunna hasken dakin. Ko ina a gyara yake tsaf tsaf kamar dakin mace, da kansa yake gyara komai dan yana da komai na gyara a ciki be yarda kowa ya shigar masa ba duk kuwa da ba wani abun amfani yake ajiyewa a dakin ba. Wajen shoe rack dinsa ya nufa ya dan duka ya hau zare takalmin kafarsa hade da socks din ya ajiye takalmin a ma'adanar sa sannan ya wuce wajen dan madaidacin laundry basket ya jefa socks din sannan ya fada saman gado yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
****Duk yadda suka bincika sun kasa samun bayanin komai akan fitowar MATAWALLE, da kuma whereabout dinsa, kanta ya soma daukar zafi amma duk da haka ba zata ka raya ba, a wannan karon ya shirya mata sosai amma abinda be sani ba shine itama a shirye take. Da wani mugun bacci ta shigo gidan dan haka ne ma bedroom ta wuce kai tsaye ta fada sai bacci. Su kuwa dama sallar asubah kawai sukayi, suka hau shiryawa kafin takwas sun isa airport takwas da wasu yan mintoci suka d'aga daga garin Kano da niyyar dawowa a cikin babban shirin da zai rusa Hajiya Zeenat har ma da Alhaji Mukaddas a cewaar Aby dan har shi babu wanda zai ragawa, duk wani ma da ya zama tsatso ko dan uwan Daddyn babu sassauci ko kyautawawa a tsakanin su.
Bacci bilhaki Hajiya Zeenat take kamar wadda tasha wani abu dan sai da rana ta daga sosai sannan ta tashi tana mika. Wanka ta farayi dan a rayuwar ta bata wasa da kula da kanta da jikinta wanda tun a zamanin baya ya kasance jari da tsanin da ta kai har wannan matakin. Ta kan yi wasa da sallah har ma tayi mirsisi wani lokacin taki yi amma bata taba wasa da gyara kanta da fatarta. A shirye ta fito da nufin zuwa dakin Daddy sai ta tarar da Adam ya kwance yana bacci akan kujerar falon,matsawa tayi ta taba shi ya farka a rikice idanun sa sun yi wani irin ja sosai.
"Adam?" Tace tana dan ja baya saboda bud'e bakin sa da yayi wani irin wari ya bige ta
"Giya Adam?" Tace tana waro ido, dan luu yayi da ya yi kokarin mikewa jiri ya kwashe shi ya koma jagaf yayi baya.
"Wanne irin iskanci ne wannan? Yaushe ka fara shan giya ban sani? Yaushe?"
"Maaa... Bafa giya bace."
"Uban kace, tunda an gaya maka bansan warin ta ba." Tace da karfi tana tura shi baya
"Please stop shouting! ki daina bana so kina min ihu da sanyin safiyar nan."
"Adam!!!"
"Sai kuma kiyi."
Sai ya kama hannun kujerar ya mike yana cigaba da tangadi, yayi hanyar dakin Aryan kamar zai murd'a sai kuma ya fasa ya nufi nasa ya shige gami da banko kofar.
"Na shiga uku, sai dai komai yazo karshe wannan masifun zasu fara kunno kai?"
Bud'e kofar dakin Aryan din da taji anyi ya sakata kallon wajen da sauri, a shirye yake tsaf cikin shigar kamala kufta da hula sai kamshin turare ke tashi me matukar dadin kamshi, be ko kalli shashen da take ba kamar dai yadda ita take masa kallo me cike da tsana, tana kokarin hada yanayin nutsuwar sa da ta Adam wanda dama tun a zamanin kuruciya ba ma yanayin su daya ba.
"ARYAN!"
Ta kwala kiran sa ganin yana neman barin falon. Chak ya tsaya sai dai be juyo ba dan idan akwai abinda ya tsana ya biyo bayan kallon fuskar ta.
"Daddyn ku yayi tafiya a daren jiya, zai kuma dan kwana biyu, ya bar sakon duk wani abu da ya shafi office ka sanar wa dan uwanka..."
Wani irin juyowa yayi da shi kansa be san yayi ba, ya wurga mata wani banzan kallo kafin ya kad'a kansa ya soma kokarin barin wajen, sai da ya kai kofar fita sannan yace
"Karki kara kokarin tsaida ni ki bata min lokaci akan shirmen ki."
Dariya ta kwashe da, ya girgiza kansa kawai ya karasa ficewa.
"Lallai wuyan ka yayi kauri."
Tace tana bubbuga hannun ta da yake cike da bangles na zallar gold. Fasa zuwa duba Daddyn tayi dan tana bukatar sanin in da aka kwana da maganar Matawalle sannan kuma ta magance matsalar Adam da yake shirin bata mata komai bayan da take kokarin maida duk wani business akan sunan sa. Bayan Aryan din tabi suka hadu a compound din gidan yana tsaye jikin motar Daddyn suna magana da Kamal yayi kamar be san ta fito ba, ta girgiza kai ta shige motar ta suka fice daga gidan.
Wayar ya tura a aljihun gaban rigar sa ya taka zuwa gate din, ya samu maigadi a zaune jigum. Zama yayi a gefen sa yayi saurin mikewa cike da girmamawa ya gaida Aryan din, hannu ya mika masa suka yi musabiha sannan yace ya dawo ya zauna.
"Waye ya kawo wadanchan mutanen?"
Ya nuna manyan securities din dake kaiwa da komowa a harabar gidan rike da bindigu kowannen su fuskar sa a tamke zaka rantse basu taba dariya ba
"Hajiya ce ta kawo su."
"Aikin me suke?"
"Kula da shige da ficen gidan, kamar dai hakan ne."
Tabe baki Aryan yayi yana cigaba da kallon su, suna ta safa da marwa tamkar mayunwatan zakuna.
"Ok thank you" Yace ya mike ya isa wajen su, suka zubo masa ido kamar zasu cinye shi.
"Ku gaya wa wadda ta ajiye ku, ko irin ku dubu zata ajiye kewaye da ita sai ta sha k'asa."
"Ok sir!" Suka hada baki wajen fada, tsaki yaja ya juya ya barsu a tsaye suka bishi da kallo.
Kamal ne ya karaso tare da wani da ya jawo motar Aryan din, a waje suka parker ya fice yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa
"Idan kace 5min toh sai ya zama 20min, sam baka abu a exact time din."
Aryan yace yana mikawa Kamal din hannu, dariya yayi ya juya wajen matashin da yake tsaye rike da key din motar Aryan din yace
"Aryan ga Habeeb, sabon driver ka."
Kallon wanda aka kira da driver Aryan yayi, ya ganshi tsaf dashi babu wata wahala a tattare dashi sai ma yanayin yan boko.
"Amma be yi kama da driver ba."
"Gaskiya ne, be yi kama ba saboda dai dan makaranta ne, ya samu matsala da karantun sa ne har akayi withdrawing dinsa, so kasan yanayin rayuwar dole sai an rayu, plus shi yake kula da mahaifiyar sa, ga aiki yayi wuya shine na kirashi a daren jiya ya kuma tabbatar min zai iya, nasan shi nasan gidan su kuma na yaba dashi shiyasa ma na nemo shi."
"Allah sarki."
"Karka damu, yaro ne me hankali."
"Ok
RUMBUN QAYA*π₯
*DAUDAR GORA*π₯
*IDON NERA*π₯
*A RUBUCE TAKE*π₯
*KI KULANI*π₯
*_uhmmmm_*ππππππππππ
*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*
*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*
*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*βΊοΈβΊοΈ
*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*π₯π₯π₯π₯π₯
0022419171
Maryam sani
Access bank
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*π₯
*RQ*
Β Β Β Page 19
Hafsat Rano
https://arewabooks.com/u/hafsatrano
*****Gaba ya bud'e ya fada ba tare da yace komai ba, dan tsaye Kamal yayi kamar zai ce masa ya koma baya amma sai ya kyale dan kar ya matsa sosai yasan halin Aryan sarai zai iya saka wani abu a ransa. Motar sa ya koma ya shiga, ya fara jira Habeeb din ya fara wucewa gaba sannan ya bisu a baya. A gate din company ya tsaya dan yana da dan wajen da zai je kafin ya shigo, wayar sa ya dauka ya kira Aryan din yace masa zai dan je ya dawo sannan ya juya ya bar wajen.
Titin babu kowa dan ko motsin tsuntsaye babu saboda tsabar shirun shi, wajen ya kasance baya biyuwa saboda tsabar tsaron da yake wajen. Tun daga farkon titin suke tsayawa suna maida duk wani da yazo giftawa ta wajen tun mutane basu gane ba har suka gane kowa ya daina bi saboda tsoro. Sai kayi tafiya me nisa a kan titin sannan zaka iso gate din wajen, wanda shima yake zagaye da matakan tsaro. A guje wani rike da wata irin mahaukaciyar bindiga ya taso, yazo ya hau bud'e masa gate din da saurin gaske. Ciki ya shiga bayan ya dan daga masa hannu ya samu wajen yayi parking ya fito da sassarfa. Gari guda ne a cikin wajen domin kuwa waje ne me girman gaske, sannan ga matasa maza da mata wanda a kalla shekarun su ba zasu haura ishirin da biyar ba suna kaiwa da komowa a cikin wajen da ya kasance a kebence dan ba zaka taba tunanin wajen yana existing ba. Kowannen su rike yake da bindigu manyan gaske sai dai suna ta walwala a tsakanin su tamkar babu wani abu da yake faruwa
Kai tsaye office dinsa ya wuce wanda aka rubuta daga saman office din da babban baki LIEUTENANT KAMAL HASSAN SARKI (DSS) Sergeants ne a kofar office din sukayi saurin bud'e masa, ya shiga ya zauna akan kujerar sa sannan ya fito da takardun Aryan din dukka ya baje su akan table din ya hau dubawa a tsanake. Knocking aka fara yi kad'an kafin ya bada izinin shigowa. Captain Mausul ne
"Welcome sir." Yace yana sara masa.
"Thank you, ya ake ciki?"
"Ni da team dina mun samu nasarar kama wannan kasurgumin kidnapper din da ya addabi mutanen Batsari da kewayenta, mun yi ta bibiyar sa tun daga jos har zuwa sanda ya shigo Kano, but sai muka rasa shi kuma, jiya da safe ina kokarin shiga wanka na samu kira daga wajen Lawal, an samu signal na wayar sa a tasha, we quickly set-up a team muka bishi daga Kano har Katsina,anan ne mukayi arresting dinsa yana kokarin shiga garin na Katsina da tarin bullets."
Dagowa yayi ya bar abinda yake yi ya dube shi
"Well-done!" Ya hau tafa masa
"You did a good job!" Ya daga masa hannu alamar jinjinawa
"Thank you sir." Yace yana murmushi
"Yanzu yana ina?"
"Yana cell sir, ga duk bayanin abinda muka samu a gidansa da muka je."
"Ka ajiye min, zan shigo da daddare sai mu duba komai, kwana goma na basu suyi duk binciken da zasuyi su gama, mu tur."
"Ok sir."
"Yanzu ina sauri ne, abubuwan sun fara sauya salo dan haka ne ma nake ganin kai ne zaka jagoranci wannan tafiyar a matsayin team captain din, dan na tabbatar zaka iya."
"Ok sir!"
"Ga record din komai, name, address and phone number, da duk finding dina yana ciki."
"An gama sir."
"Yawwa, thank you."
Fita yayi ya barshi a ciki, ya karasa abinda zai yi sannan ya fito ya nufi office din ogan sa, ya dan dade a ciki kafin ya fito ya tafi ba tare da ya koma office din nasa ba.
A mota ya bar wayar sa da yake amfani da ita a gari dan dama ka'idar aikin kenan dan a kashe ma take sai da ya fito gaba daya daga lungun sannan ya kunna ta. Kamar Aryan yana jira sai ga kiran sa ya shigo
"Wai kana ina ne?"
"Gani nan na taho."
"Me ya samu wayarka a kashe?"
"A aljihu na turata, ashe na danne power button din ban sani ba."
"Ok sai ka karaso."
Yace ya kashe wayar. Ajiye wayar yayi ya jawo dashboard dinsa ya d'aga wasu tarkace ya tura I'd card din sa.
***Kamar wadda ta shekara rabon ta da gida haka taji, wato dai da gaske kowa ya bar gida, gida ya barsh. Ji tayi baki daya ta tsani Kano da duk mutanen da suke cikin ta. Dama zata koma baya da sai ta goge haduwar su da Hajiya Zeenat shikenan da bata shiga wannan masifar ba, da kuma bata hadu da Aryan da Kamal ba. Baki ne suka dinga tuttulowa gidan nasu zuwa yiwa Abby barka da fitowa dan haka sai gidan ya zama ya cika sosai. Dakin ta, ta gudu taje ta kwanta dan har lokacin jikinta be gama yi mata daidai ba, gashi da ta zauna sai tunanin abinda ya faru ya shiga dawo mata. Dadah ce ta biyo ta dakin ganin ta baro falon kuma duk sai taga bata yarda da yanayin Raihanan ba. Zama tayi a gefen gadon tana duban ta.
"Lafiya?" Tace mata dan fuskarta ta nuna ba lafiyar ba.
"Zazzabi nake yi,Amma nasha magani."
"Tun yaushe? Ko dai akwai wata damuwar bayan ta zazzabin Raihana?"
Girgiza mata kai tayi, dan bata san ta in da zata fara yi mata bayanin abinda ya faru ba, musamman a yanzu da duk suke cikin farin ciki mara misaltuwa.
"Ba komai Dadah na, da na sake hutawa shikenan."
"Kayya, babu karyar da zaki yi min na yarda dake Raihanatu, ki sanar dani damuwar ki, na sanki kamar yunwar cikina dan haka kar nake kallon ki."
Zamewa tayi daga kwanciyar da tayi da nufin zama sosai sai wayar ta, ta hau ringing, kurawa number dake kira ido tayi dan bata taba kawo kiran nasa ba.
"Ko dai sabon saurayi kikayi a Kanon Raihana?"
Dadah tace tana rike baki, da sauri tace
" A ah wallahi, ni banyi komai ba."
"Toh waye yake kiranki? Kika zubawa waya ido kuma baki dauka ba? Ko fada kukayi da saurayin?"
"Kai Dadah kinji ki, ni wallahi ba wani saurayi, kawata ce ma take kira na."
"Kawa? Yaushe kikayi kawar bamu da labari."
"Shikenan bani da kawa a duniyar nan Dadah?"
"Baki da ita gaskia, sai abokan arziki."
"Ni me aka maida ni a gidan nan ne? Dole ma nayi sabuwar kawa."
"Oho, kamar gaske. Idan kin gama wayar ki fito cikin mutane bana son kina darere kanki ke kadai."
"Tohm." Tace ta rakata da ido har ta fice. Wayar ta riga ta katse, haka kawai sai taji babu dadin rashin dagawar da batayi ba. Jujjuya wayar ta dinga yi a tunanin ta zai sake kira amma shiru, yunkurawa tayi ta tashi tayi hanyar fita sai ga kiran ya sake shigowa,