Showing 45001 words to 48000 words out of 121037 words

Chapter 16 - RUMBUN QAYA COMPLETE hausa Novel

03 Sep 2024

17334

ya kare

"Na ga karamar wayar sa Ya Nabeela."

Ya mike da sauri yana rike da wayar,

"Sake duba dakin sosai Aryan, babu wani abu kuma?"

Duddubawa ya hau yi amma be ga komai ba, fitowa yayi ya fice da wayar daga gidan.

Asalin office dinsa ya nufa ya kira Kamal yace su hadu a can, yana zuwa Kamal din ma na zuwa kamar wanda yake a kusa, abinda yake faruwa da tunanin da Ya Nabila tayi har zuwa text message din da aka tura masa ya nuna ma Kamal din, shiru yayi kamar me nazari wajen mintuna biyar kafin yace

"It's time da ya kamata muje muga Barrister Matawalle!"

"Yaushe?"

"Zan yi kokarin nema mana ganin shi ta wajen wanda ya sanar min da labarin fitowar sa, ina ganin kar mu wuce kwana biyu bamu neme shi ba, sannan maganar Daddy ka bar komai a wajena."

"I trust you with my life Kamal, ka sani kai kadai na yarda dashi."

"Ba zaka taba dana sanin taraiya dani ba Aryan, I promise you that."

"Shikenan. Allah yasa."

"Amin, muje mu kwantar wa Ya Nabeela hankali, in sha Allah ba abinda zai faru."

"Ok Allah yasa."

"Amin."


***Washegari ya tashi da wani irin ciwon kai sosai, dan dama tun dare yake jin alamar sa, haka ya daure ya shirya ya fito office. Kamal yau ya riga shi zuwa saboda rashin shigowar da be yi ba jiya, wanda aikin Aryan din ne gaba daya ya hana shi shigowa, a yanzu haka yasan komai akan daddy har in da suke kaishi, kuma shine da kanshi yayi wa Aryan din text message bayan ya aikawa Hajiya Zeenat nata akan tayi gaggawar dauke Daddyn daga gidan. Dan hatta gidan da ta maida shi suna kallon ta, tabbas karshen ta ne yazo dan haka cikin kankanin lokaci zasu kammala komai su damke ta, bayan sun samu dukkan hujjoji akanta.

"Ya labarin zuwa gidan Alhaji Nasir din?" Aryan yace bayan ya shigo office din nasu sun gaisa

"Gobe in sha Allahu zamu je mu ganshi."

"Ya amince?"

"Ko be amince ba, zuwa zamuyi dan idan ya ganmu ma dole ya amince, disk din wajensa shine kawai abinda muke jira dan shine yake dauke da komai da ya faru ranar, babban dalilin da ya kaishi prison Kenan, amma duk da haka be yarda ya bada shi ba tsawon lokacin."

"Ina fatan komai zai zo karshe Kamal, na gaji wallahi, inaso nayi rayuwa kamar kowa, amma na kasa, idan ba gani nayi an daure Hajiya Zeenat ba hankali na ba zai taba dawowa jiki na ba."

"Lokacin yazo ai."

"Allah yasa."

"In sha Allah, Amin."

"Bari na je naga Ya Nabeela, kamar bata jin dadi tun ranar ."

"Allah sarki, ka duba ta please, aiki ne dani da munje."

"A ah yi aikin ka, jiya nima haka nayi nawa."

"Na sani kam,sai ka dawo."

Kofar ya ja masa ya fita, ko office dinsa be shiga ba ya sauko kasa. A reception din k'asa suka hadu da ita ta shigo, dauke kai yayi kamar be ganta ba, yana ji tana gaishe shi yyi biris kamar be ji ba, ya wuce kawai kansa tsaye. Tabe bakin ta, tayi kawai yau abin ya motsa, kaamar me aljanu jiya yana ta kula ta amma yau yayi kamar be san ta ba.
Sarai ya ji sanda ta gaishe shi, haka kawai yaji yana fushi da ita tun jiya da ta matsa ana aikin nan sai ta tafi, shiyasa yayi kamar be ganta ba yay wucewar sa, sai dai kasan zuciyar sa na karanta masa rashin kyautawar sa.

Adam na tsaye tun bayan da ta shige be bar wajen ba, magana yayi mata ta masa banza hakan ya kona masa rai, ganin Aryan yasa shi tunawa da abinda yayi niyya. Tarar shi yayi yana shirin shiga motar sa yace

"Na raina wayon ka Malam, kana ganin kamar kana da wayo,amma ina, kana tare da mutanen mu amma baka sani ba, lallai na raina wayon ka."

Yana rike da hannun motar be shiga ba yana jin shi amma be tanka ba, sai da ya kai karshe sannan yace

"Kune baku da aikin yi da har kuke bibiya ta, dan haka wahala ce bata ishe ku ba."

Ya shige ya zauna ya banko kofar, gaban motar Adam ya bud'e da sauri ya zauna yana dariyar shakiyanci

"Da kana da wayo da sai ka tambaya su waye hakan? Ba wai ka share maganar ba, bayan nasan waye kai, hankalin ka ba zai taba kwanciya ba har sai ka gano waye."

"Malam ka fitar min daga mota kafin na kira securities."

"Please ka fita." Habeeb yace

"Shut up, ba da kai nake ba, da ubangidan ka nake yaro, ka bari mu yi dashi. Kai kuma...". Ya juyo kan Aryan

"Check your WHATSAPP!" Yana fadan haka ya fice daga motar gami da banko masa kofar.

*RUMBUN QAYA*

©®_Hafsat Rano_

Page 22



****Sautin bugun zuciyar sa ne ya sauya bayan fitar Adam din, ya runtse ido sosai tsoro na shigar sa, tsoron maganganun Adam din wanda yake da yakinin tabbas akwai wanda yake taimaka musun kamar yadda yace, amma waye? Ba zai iya dubawa ba dan yasan zuciyar sa zatayi bugawa ma baki daya musamman idan ya samu wanda yayi matukar yadda dashi da laifin.

"Ya Allah!" Ya furta a hankali yana sake chusa wayar sosai a cikin aljihun rigar sa yana son dauke hankalin sa wajen hakura da ganin abinda zuciya da gangar jikinsa basu amince masa da gani ba.

"Please oga karka daka ta, tashi dan Allah."

"Ba komai Habeeb, muje kawai."

"Ok ." Ya tada motar suka fita.

Tana zaune a office din suna hira da Abdulhakeem wanda ta kura fiye da rabin hankalin sa na kan wayar hannun sa, chatting yake da alama dan yanayin yadda yake amsa mata wata maganar zaka tabbatar da ya kasa hankalin nasa waje da yawa. Shiru tayi masa ta dauki wayarta itama kawai ta hau dannawa ko ta rage zaman dan babu abinda zatayi har Oga Kamal ta tambaya yace ya bari Aryan ya dawo. Tayi mamakin da be yi mata maganar abinda ya faru jiya ba, gashi tana son sanin halin da Daddyn yake ciki dan kusan kwanan zaune jiya tayi tana tunanin abinda ta ji, tabbas nishin mutum ne me cike da wahalarwa, tana rufe idon ta shi take hasasowa hakan ya hana ta samun isheshan bacci sosai. Wayar tace tayi kara ganin Hamma Hydar ne yake kira yasa ta dauka da sauri.

"Hamma na."

"Na'am kanwata, gani a garin naku."

"Kano?"

"Eh shigowa ta kenan."

"Laaa, shine baka fada min ba?"

"Wallahi zuwan urgent ne, Abby ya taso ni, kina ina yanzu?"

"Office."

"Ok, zan kiraki ki jirani zanzo na dauke ki."

"Ok Hamma, sai kazo."

Tana cikin wayar taga fitar Abdul sai ya kasance babu kowa a office din, Zainab ce ta shigo rike da wani file ta dire mata a gabanta, takardu ne a ciki fal ta daga kai ta kalle ta

"Menene wannan?"

"Aiki ne, idan kin gama wasu na jiranki, dan na lura zaman dumama seat kawai kike yi, ko da yake kin samu masu daure miki gindi, farar kalar ke kwasar su da alama."

"Ke a matsayin ki na waye da zaki sakani aiki?"

"Hehe." Ta kwashe da dariya

"Wato kina da baki ashe, a gaban Oga sai ki dinga yin kamar tsohuwar munafuka, da haka kika yi amfani kenan wajen tura kanki gareshi, sai ayi mu gani ai, aiki kuma shine ya saki bani ba, dan ni bani da lokacin batawa akanki, idan zakiyi gashi nan, idan ba zaki ba ki barshi, idan ya dawo ya sake dole ai."

"Har shi ma bashi da hurumin sakani aiki dole, nasan rights dina dan haka ba zan ba, idan yazo sai ki fada masa nace ba zan ba, ke da suke biyan albashi sai kiyi."

Kusan mutuwar tsaye Zainab tayi, bata dauka yarinyar na da gut haka ba, ganin ta take kamar doluwa a kullum, aikin Cynthia ne ba wani Aryan da ya sata, kawai neman rigima suke da Raihanan sai gashi ta nuna mata itama eh ce, juyawa tayi ta fita ba tare da ta sake magana ba, bayan kwafar da tayi kawai kuma bata dauki file din ba. Tashi Raihana tayi rik'e da file din, ta bi bayanta ta dire mata akan table tayi juyowarta tana sabani

"Gani jaka, ba zan ba wallahi."

Tayi zaman ta, ta ma kunno kallo a wayarta ta dora akan table din tana kalla.
Ta dade tana kallon har ta gaji ta koma game daga nan ta kashe wayar ganin rana tayi har lokacin tafiyar ta yayi, Hamma Haydar ta kira yace mata ta jirashi wani abu ne ya tsaida shi amma yana nan zuwa karta tafi. Jugum tayi a zaune dan wasu har sun soma tafiyar da kad'an kad'an har kowa ya yaye sai ita kadai sai Kamal da yake cikin office dinsa ya dukufa akan aikin da yake yi. Wani kiran Hydar din ne ya sake shigowa, sai dai wannan karon da sauri yace;.

"Raihana, ya sunan wanda kike PPA a wajen su."

"Oga Aryan ne, da Oga Kamal."

"Wai da gaske?"

"Eh sune, Ka sansu ne?"

"Kwarai kuwa, sai dai nazo zamuyi magana kawai."

"Dan Allah Hamma gaya min, menene?"

"Wallahi labarin me tsawo ne Raihana, amma ki bari nazo."

"Toh sai kazo." Ta ajiye wayar cike da zulumi da tunanin yadda akayi ya sansu.



****Zuwan sa gidan Ya Nabeela ya hana shi aiwatar da abinda zuciyar sa take fada masa, kashe wayar tasa yayi gaba daya bayan ya karbi key dinsa a wajen Habeeb yace yaje kawai yayi zaman sa a gidan dan wani irin tsoro ne ya dinga shigar sa, tsoron abinda zai taarar. Har bayan azahar yana gidan sai a lokacin yaji nutsuwar tafiya yayi mata sallama yana sake danne zuciyar sa da ganin abinda zai tashi hankalin sa. Tuki yake a hankali ya ma sauka chan gefen titin dan ma kar ya hana masu sauri sai yan napep da suke ta daga masa hannu suna masa horn be kula su ba, da haka har ya kai office din ya samu gefe daya yayi parking ya ciro wayar ya kunna da niyyar kiran Kamal yaji ko yana office har lokacin dan haka babu mota a harabar wajen ko daya. Message din hoton da ya fito a saman notification bar din wayar ya dauki hankalin sa, hannun sa na wani irin rawa ya danna kan hoton wanda ya dauke shi direct zuwa kan chat din Adam din. Idon sa ne ya soma yi masa dishi-dishi kafin ya bud'e masa tar ya gani, hoton tane a zaune tare da Hajiya Zeenat, a cikin falon gidan su sanda take mika mata key din nan. Da sauri da sauri ya shiga bud'e sauran hotunan wanda duk itace a jiki suna magana da Hajiya Zeenat ko kuma tana murmushi. Audios din ya bud'e yana girgiza kansa da wani irin yanayi. Muryar tace ta bayyana tar a ciki tana shaidawa Hajiya Zeenat ta dauko key din, da sauri ya katse ya shiga wani, sai dai baya iya dire su har karshe yake kashewa ya kunna wani.

"Why Raihana? Why?"

Ya fada da karfi yana balle murfin motar, ya fito ya nufi cikin building din da wani irin sauri.

Tashi tayi daga zaman da tayi da nufin fitowa ta sauko kasa kawa ta jira Hamma Haydar din dan saman yayi mata shiru sosai dan bata ma yi tunanin akwai mutum ba. A hanya sukayi kicibis tayi wani irin mugun ja baya amma duk da haka sai da jikinsu ya hadu kanta ya bugu da gefen kafadarta. Ture tayi da iyakar karfin sa, tayi baya kamar zata fadi tayi saurin dafe bangon dake wajen.


"Me yasa? Me yasa zaki ci amanata?" Yace yana matso ta

Zaro ido tayi dan sai da yayi magana ta lura da yanayin da yake ciki

"Why Raihana?" Karo na farko da ya taba fadar sunan ta kenan, amma a yanayin da yake nuna tsantsar tsana da kiyayya

"Me nayi?"

"Baki sani ba?"

Girgiza kai tayi, ya cije lips dinsa na kasa da karfi yana wurga hannun sa baya, sai kuma ya sake matsowa ya bud'e wayar sa ya nuna mata hoton

"Wannan ma baki sani ba?"

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun."

"Tell me, shima baki sani ba? Ko photoshop ne? Idan kince baki sani ba, wannan ma ba voice dinki bace ba?" Ya danna audio din

"Na sani, na sani, amma zan maka bayani."

"Bana so! I don't want to hear anything from you, babu abinda zaki ce min, i hate you! bana son sake ganin ki a gabana, just goooo."

"Dan Allah zan yi maka bayani, wallahi amfani tayi dani, she used me wallahi, ban aikata abinda kake tunani ba, dan Allah."

"Allah bana son ji, ki tafi kawai and don't ever show your face again."

"Please..." Ta hade hannayen ta waje daya tana kuka

Juyawa yayi da sauri ya shige office din dake kusa da wajen, wanda bashi da maraba da hadadden falon gida. Kuka ta durkusa a wajen tanayi, kamar ranta zai fita, duk abinda ake Kamal yana sama be sani ba, Hydar ne ya kirata yace yazo, amma jin muryar ta yasa shi katse kiran kawai ya shigo office din kansa tsaye dan ko magana ta kasa. A kofa ya tarar da ita tana gursheken kuka, ya dago ta yana tambayar abinda ya faru, a cikin kuka take masa bayani wanda ya kasa fuskantar komai, sai dai ya fuskanci da Aryan ne.

"Ina Aryan din?"

Yace,da hannu ta nuna masa office din, yace su shiga, tayi gaba yana biye da ita, yana son tabbatar da abinda yake zargi. A baya ya tsaye sanda suka karasa ba tare da ya shiga ciki ba.

a Sanyaye ta turo kofar ta shigo, ta hange shi tsaye ya bada bayan sa yana kallon window hannun sa rike da curtains din, takowa ta shiga yi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, zuciyar ta na wani irin harbawa irin wanda bata taba ji ba. Motsin ta ya sashi juyowa kafin ya saki curtains din ya zuba mata ido cikin yanayin da yake nuna tsantsar bacin ransa. Ji tayi tamkar ba zata iya karasawa ba, kamar ta zube a wajen kawai tayi ta rusa ihu saboda tsananin tsoron da yake shigar ta. Da jan kafa ta karasa gaban nasa tayi saurin dukawa k'asa idanun ta na cigaba da zubda hawaye, hawayen bakin cikin abinda yake zargin ta dashi, ko da yake ta aikata din a baya duk kuwa da a rashin sani ne, amma bata taba zaton abun zai dawo musu a wannan lokacin ba

"Me ya kawo ki?"

Yace cikin dashashiyar muryar sa dake fidda amon sautin yadda ransa ya kai matuka a baci. Shi mutum ne mara yarda sam, rayuwar sa ta baya ta sashi rashin yarda da kowa da ma komai, Ya Nabila kadai ya aminta da ita, ita kadai ya yarda ba zata cutar dashi ba, sai Kamal sai kuma zuwan ta rayuwar shi, ya yarda da ita fiye da yadda ya yarda da kan sa, har ya kan ji nutsuwa a duk lokacin da yake tare da ita, amma kuma...

"Dan Allah kayi hakuri."

Tace cikin shashekar kuka, girgiza kansa yayi yana dauke kansa daga kallon ta dan ma kar zuciyar sa tayi masa rawa akan hukuncin da ya yanke, kar tayi rinjaye akan sa har ta sakashi karya alkawarin da yayi ma kansa na rashin kyale duk wanda ya ha'ince shi.

"Ki tashi ki fita daga nan wajen, I don't want to see you ever again."

"Please ka saurare ni, dan Allah ka bari kaji abinda zan fada maka."

Durkusawa yayi a gaban ta kafar sa daya ya choge ta yana duban ta idanun sa sun yi mugun kadawa

"I hate mutane masu fuska biyu RAIHANA , haka nan bana sake yarda da wanda yaci amanata, ki tashi ki fita bana son ganin ki, get out of my life!!"

"Dan Allah..."

"I said get out!"

Ya fada da karfi bayan ya mike tsaye, hannun sa na mata nuni da kofar, rud'ewa tayi kasancewar yau ne karo na farko da aka fara mata irin wannan tsawar, juyawa yayi ya sake bata baya yana jin yadda take kuka sosai, kukan da yake jin tamkar ana daddatsa masa jikin sa, kamar ana zuba masa garwashi a cikin kokon kansa.

Juyawa tayi da sauri harda dan gudun ta, ta fice daga wajen tana rusa kukan sosai, runtse idon sa yayi ya bud'e kansa da yake masa wani irin ciwo ya rik'e ya shiga matsawa a hankali zuwa kujerar dake gefe ya zauna yana tallafe kan nasa

"Sai kayi nadamar abinda kayi Aryan, sai kayi nadama a lokacin da bata da amfani."

Dagowa yayi da sauri ya kalli kofar, matashin saurayin da a kalla zasuyi kusan sa'a ne a tsaye yana duban sa, fuskar sa ce ta shiga dawo masa zuwa wani lokaci me tsawo, kamar sa ce tun a lokacin be chanja ba, ba kuma yana tunanin ko da zata chanja din ya kasa ganeshi, tare aka hada su aka tarwatsa musu rayuwar su, aka raba su da mutane masu muhimmaci a rayuwar su

"Haydar?" Yace yana tashi tsaye da sauri

"Sai kayi nadamar abinda kayi ma kanwata Raihana, kana nan da zuciyar ka da rashin yafiyar ka, kanwata bata chanchanci mutum irin ka, kamar yadda ka rasa mu a baya, haka zaka sake rasa mu a wannan lokacin. Sai ya juya ya buga masa kofar da karfi

"Kanwata? Raihana? Raihana Nasir? BARRISTER NASIR MATAWALLE?" Duk a lokaci daya sunayen suka shiga amsa kuwwa a saman kansa

"Ya salam!!"

Yace da sauri yabi bayan sa, da gudun gaske ya dinga sauka daga stairs din yana hada bibiyu, harabar ya fito babu ko mota daya sai tasa, gaba yayi zuwa wajen masu gadi suka ce yanzu mota ta fita, gate din ya fita ya dinga waige-wage sai dai ko kurar su be gani ba, bare ya san in da suke nufa



*TUNA BAYA*

SHEKARU MASU YAWA DA SUKA SHUDE SUKA HAIFAR DA TARIN ABUBUWA MASU YAWAN GASKE, RAYUWAR GIDAN NASIR MATAWALLE DA AMININ SA IBRAHIM MUKADDAS.🖍️🖍️🖍️🖍️ MUN SHIRYA???? MU HADU A AREWA BOOKS😎😎😎










ZAFAFA BIYAR.....× 2023
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥🔥🔥🔥🔥💥🔥💥🔥🔥💥🔥🔥💥💥💥💥💥🔥💥🔥🔥🔥🔥


INA MAABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR WRITERS? WANNAN KARON MA MUN SAKE DAWO MUKU DA ZAFAFAN LITATTAFAN MU, MASU DAUKE DA ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA

KU GARZAYO. ZAFAFAN NA KU SUN SAKE TAHOWA DA WASU ZAFAFAN LITTATTAFAN MASU DIMBIN DARUSSA NA MATAKAN ILMANTARWA RAYUWAR MU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login