Showing 102001 words to 105000 words out of 121037 words
Hydar zai mata sallama."
"Komawa zai?"
"Eh amma sai gobe ko?"
"Eh in sha Allah."
"Ai zaku sake haduwa, idan kace mata sallama yanzu zaka rikita min ita ne."
Kama baki Kamal yayi wanda shi no a jikin sa maganar sa kawai yayi kuma tsakanin sa da Allah har a zuciyar sa haka ne.
"Wai dan Allah Aryan yaushe bakin ka ya bud'e haka?"
"Daga sanda kayi min aure."
"Wato ni na jawo ko? Na karba maka mata yarinya me hankali amma da abinda zaka saka min kenan?"
"Sorry sir." Ya fada yana dariya
"Oga Hydar please ka bari sai gobe dan Allah."
"Ok ba damuwa, zan shigo kafin na wuce."
"Yawwa thank you."
"Inaga kai ma fitowa zakayi kawai mu duba office din chan dan naga ka warke garau, sako kayan ka kawai mu wuce akwai ayyuka masu yawa, kasan kuma next week zan tafi."
Kamal ya tsokane shi yana son Jin abinda zai ce
"Tab wallahi ba zan je ba."
Yace ya juya ya bar su a tsaye kawai suna dariya. Fita sukayi suka rufe kofar ya dawo ya saka key a kofar dan kar ma su dawo sannan ya nufi dakin cike da karsashin sa. Tana zaune a in da ya barta, ta kara jawo mayafin ta sosai ya sakko saman fuskar ta ya rufe fiye da rabin fuskar. Wuce ta yayi ya nufi wajen kayan sa, ya zare jallabiyar ya maida ita inda ya dauko ta dan duk ta takure shi, ya dauko wani wando ash colour da rigar sa masu laushi,wandon ya kai masa wajen guiwar sa sai rigar da take armless ya saka ya dawo wajen ta ya janye mayafin da ta rufe fuskar ya cire shi gaba daya ya ajiye shi akan bedside sannan ya jawota jikinsa ya sakata a tsakiyar kafafun sa ya dora kansa a saman kafardar ta yana shakar kamshin jikinta.
"Naje munyi magana da Kamal yanzu, kina so kiji me muka ce?"
Da sauri ta daga kanta sama alamar eh dan gaba daya ya na neman rikita mata tunani, hannun ta na cikin nasa yana murzawa a hankali ga shi ya dora kansa a jikinta duk maganar da zai yi direct cikin kunnen ta take zuwa. Yanayin yadda yake maganar so deep ma kawai ya isa ya rikitar da ita. Kamar bashi ba, kamar wani ne na daban aka chanja shi ba ainahin Aryan din da ta sani ba, gaba gadi kawai yake koman sa tun farko baya tsaya nuku nuku ko magana ce zai fade ta kawai ko ba zata maka dadi ba shi ba ruwan sa.
"Abby yaji tausayi na ya bani ke, halak malak, naji dadi na gode wa Allah, daga ranar zuwa yau jini na ya hau yafi sau dubu, na rasa me ma zanyi, idan na tuna wannan sahoramin Abby zai bawa ya hanani sai naji duk babu dadi, nasan na fishi chanchantar ki, na fishi bukatar ki kuma na fishi son ki..."
"Tun kina baby, tiny little baby nake son ki Raihana, tun bansan menene son ba ma, ashe ban sani ba matata ce aka haifa min."
"Zan sha ruwa." Tace da sauri tana jin yadda yake shinshina wuyan ta yana saukar mata da wani irin numfashi me dumi a saman wuyan nata
"Um um."
Yace dan ya gano su take ta gudu, ya sake matse ta sosai a jikinsa ya saka hannayen sa ya makaleta ta yadda duk motsin da zatayi a jikin sa zatayi.
"Zanje toilet." Ta sake fada cikin neman hanyar tserewa
"Pleaseeee ki barni, na dade ina mafarkin wannan ranar, ki barni naji dumin jikinki, kiji nawa please."
"Allah toilet nake son zuwa."
"Ok, muje na rakaki."
Zaro ido tayi da sauri, toilet din zai rakata?
"Tashi muje toh." Ya dan cikata yana bata damar mikewa. Kasa tashi tayi dan har gwara su cigaba da zama a hakan da ya rakata toilet din
"Um um na fasa zuwa."
"Bakya so na raka ki?"
"A ah na fasa ne kawai."
"Ok, na fasa raka ki din, jeki ina jiranki, amma idan kika dade zan shigo."
Kallon sa tayi ya daga mata kai
"Na fasa da gaske, jeki."
"Ok." Tace ta mike ya nuna mata toilet din da hannun sa. Kasancewar babu Hijab babu mayafi a jikin ta yasa ta kasa tafiya. Baya yayi shi kuma yana kallon ta yana jiran yaga abinda zatayi. Mayafin da ya cire mata ta saka hannu zata dauka yayi saurin daukewa yana tsare ta da idanun sa masu kashe mata jiki.
"Haka zaki je, ko na rakaki."
Sakin mayafin tayi ta wuce a hankali ya bita da kallo yana sakin murmushi. Tana karasawa toilet din tayi saurin shigewa ta saka lock din jikin kofar ta dafa kirjin ta da yake harbawa da karfi. Wayar sa ya dauka zai kira Kamal yayi masa maganar abinci dan yasan zata ji yunwa sai yaga missed calls din Ya Nabeela,fasa kiran Kamal din yayi ya kirata tana dagawa ta fara gud'a. Murmushi kawai ya dinga yi suka gaisa tayi masa Allah sanya alkhairi sannan tace zata turo driver ya kawo musu abinci zata shigo gobe, godiya yayi mata ya kashe wayar gaba daya tunda dama abinda zai tambayi Kamal din kenan. Dan kishingida yayi sai ya tuna tace zata sha ruwa, sai ya tashi ya dauko mata ya ajiye ya sake komawa yana jiran fitowar, kusan minti goma da shigar ta amma shiru kuma shi be ji alamar motsin ruwa ba. Mikewa yayi ya karasa jikin kofar toilet din ya kwankwasa kad'an. Tace tana tsaye gaban mirror tana kallon idanun ta da sukayi wani irin kodewa saboda kuka, fuskarta kuma tayi wani jaja jaja itama abin ka da farar fata. Sake knocking yayi sannan yace
"Zan shigo fa."
Bata dauka da gaske yake ba, dan tasan kofar a rufe take shiyasa taki amsa masa, sai da taji kamar ana murd'a kofar kafin ta yi aune har ya bud'e ya shigo. Hannun ta kawai ya kama ya fito da ita, dan dama yasan babu abinda take yi a ciki. Kan gadon ya maida ita ta zauna sannan ya mika mata ruwan ka karba tasha kadan ya rufe ya ajiye. Fita yayi ya barta a dakin ta dauki mayafin da sauri ta sake yafawa, ta takura sosai da rashin sa dan riga da skirt ne a jikinta rigar kuma fitted ce wadda ta dan kamata musamman ta sama. Tana zaune ya shigo rike da basket me kyau an rufe shi da wani farin kyale me kyau. Dire shi yayi akan carpet din dake gaban gadon ya zauna ya mika mata hannun sa yace ta taso.
“Nakoshi” wani kallo yayi mata ya bude basket din yana kallon abinda aka rubuta a jikin farin kyallen. HML Aryan and Raihana. Murmushi yayi me dan sauti ya sauke warmers din masu kyau ya bude ya zuba abincin ba da yawa ba ya rufe ya dauki plate din ya dora shi a saman drawer sannan ya kama hannun ta ya gyara mata zama ya zauna yana facing dinta yace ta ci abincin ko ya bata. Duk da tana jin yunwa ga kamshin abincin da yake shigar ta amma kunyar sa ba zata barta ta iya ci ba, ganin ya tsare ta da ido yasa ta ci kadan tace ta koshi, be ce komai ba, ya karbi plate din ya ajiye ya duba duba time yaga lokacin sallar azahar tayi, yace ta yi alwala ya sakè ficewa daga dakin ya hau sama. Tashi tayi taje tayi alwalar tazo ta matsar da kayan ta tada sallah. Turo kofar ya yi sai yaga tana sallah sai kawai ya ja mata kofar ya fita sukayi jam’i tare da babà maigadi yayi amsa Allah sanya alkhaiiri sannan ya dawo ciki. Motsin sa taji tayi saurin sakè gyara mayafin jikinta ta kame waje daya. Shigowa yayi suka hada ido ya sakar mata murmushi ta sunkuyar da kanta ya karaso ya zauna a gefen ta
"Kinsan siesta?" Ya tambaye ta, girgiza kanta tayi
"Ok, bari ki gani."
Yace yana mikewa, ya dan karo karfin AC dakin sannan ya kashe hasken dakin ya saki curtains din da suke bud'e. Rigar jikinsa ya zare ya ajiye a saman sofa ya karaso wajen da take tsoro duk ya gama cikata ya kama mayafin ya zare shi ya je ya saka shi a wardrobe din sa ya rufe ya dawo ya mikar da ita.
"Zo muyi siesta, nasan kwana biyu bakya wani baccin kirki."
"Bana jin bacci" Tace tana zaro ido, da tsakar ranar nan ace tazo ta kwanta, akan me?
"Allah sai kin kwanta, hutawa zamuyi."
"Wallahi wallahi bana jin bacci, rana ce fa?"
"Siesta kenan, bakiyi boarding school ba?"
"Ban yi ba."
"Shiyasa toh, zaki chanja wannan atamfar? Na baki kayana kisa?"
"Um um, ni zan je falo idan ka gama sai na dawo."
Tayi hanyar fita, da sauri ya riko ta, ya sakata a jikinsa gaba daya ya jata zuwa saman gadon, ya kwantar da ita ya kwanta a gefen ta ya saka hannunsa yayi mata rumfa dasu ta yadda ba zata iya ko motsi ba. Zatayi magana ya saka hannun sa a saman bakin ta
"Shssh, don't say anything, ba abinda zan miki so nake kawai naji heartbeat dinki."
Ya dora kansa a saman chest dinta.
"Na shiga uku." Ta furta da dan karfi ganin yadda ya dora kansa a saman kirjinta ya rufe idon sa. Dago kansa yayi yana kallon ta
"Relax please, kinji yadda heart din ki take gudu? Menene ? Tsoro na kike ji?"
Gid'a masa kai tayi da sauri, ya matso da fuskar sa daidai tata a hankali yace
"Babu abinda zan miki fa, heartbeat dinki kawai nake ji. dan Allah ki kwantar da hankalin ki kinji?" Sake gid'a masa kai tayi yace
"Good girl."
Rufe idon ta tayi shi kuma ya cigaba da kallon fuskar tata zuwa lips din nata da yake ta fuzgarshi, yana son ya ji shima yadda ake ji.
_**RQ**_
PAGE 45
***Babban dan yatsan sa ya saka a hankali ya shafa lips din nata a hankali in a stylish way, bud'e idon tayi da sauri tana kokarin tashi. Girgiza mata kai yayi ya matse ta sosai yana hadiye wayun bakin sa a hankali. Maida idonta tayi ta rufe hakan ya bashi damar yi mata light kiss akan lips din nata. Yana jin sanda ta matso da dan karfi yayi murmushi kawai yana jin zuciyar sa wasai. Bacci ne ya dauke shi da karfin gaske, domin hatta bugun zuciyar ya daidaita a lokacin, dama akwai alluran da Dr Mahfouz yayi masa masu saka bacci shiyasa yana kwanciya baccin ya dauke shi. Bud'e idon tayi ta lallaba a hankali da k'yar ta zare jikinta, bata jin bacci bata ma ga dalilin da zatayi bacci a irin wannan lokacin ba da bata gama tantance me yake faruwa da ita ba. Sadaf sadaf ta bud'e dakin ta fice zuwa falon ta samu kujera ta zauna akai ta shiga kundin tunanin abubuwan da suke faruwa da kuma yadda akayi suka faru haka cikin kankanin lokaci. Wayar ta da take ajiye tun dazun akan kujerar ta dauka ta fara da kiran Hamma Hydar tunda dai shine ya kawo ta domin ta tabbatar daga bakin sa. Lokacin yana gidan Adda Maimuna tare da Muhd da ya shiga tashin hankali sosai saboda abinda ya faru dan Alhaji Kabir be sanar dashi komai ba sai jiya bayan an daura auren saboda yadda zai fi karbar KADDARAR sa a yadda tazo masa ba tare da yace zai tada hankali ba. Duk da hakan kuwa sai da hankalin sa ya tashi domin har ya dauki hutu a wajen aikin sa sannan yana ta kiran abokan sa na nesa yana sanar dasu bayan invitation card din da ya buga saboda na kusa duk kuwa da a kurarren lokaci komai ya faru. Shiri yake sosai cike da doki da farin ciki amma sai ya samu labarin yadda abun ya kasance. Ya masifar shiga shock da damuwa me tsanani domin yaga samu yaga rashi gashi ya kwallafa rai akan ta har kwanciya ciwo yayi daga jiyan zuwa yau duk ya zama wani iri abun tausayi. Sosai iyayen sa suka tausaya masa dan basu dauka abun zai taba shi hakan ba. Shine da Hydar yazo ya same shi ya kara bashi hakuri ya kuma nuna masa komai mukaddari ne daga Allah. Toh suna cikin maganar ne Raihanan ta kirashi sai yaki dagawa saboda baya so ya kara sosa ran Muhd din. Ganin be daga ba yasa ta juya akalar kiran zuwa Lamido. Shi ya d'aga ya kuma sanar da ita komai har abinda Aryan din be gaya mata ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta share yar kwallar da ta zubo mata. Yadda komai ya kasance ne yake bata mamaki gashi dai ta zama matar aure a wani irin yanayi da ba zata iya tantance shi ba. Tabbas tana son Aryan dan bata san tana son shi har hakan ba sai da maganar ta da Muhd ta taso. Amma duk da hakan bata so irin wannan auren ba, babu lefe babu kayan daki babu komai ko lalle babu a hannun ta haka nan take kamar ba amarya ba. Ajiye wayar tayi ta sauko daga kan kujerar ta kwantar da kanta a jikin ta shiga tunanin yadda rayuwar zata kasance mata, ya zaman su zai kasance da Aryan din duk da taga sabon Aryan akan wanda ta sani a office a yau, amma kuma zama ne na dindindin, magana ake ta har abadah. Tana cikin tunanin bacci ya dauke ta itama.
Shi ya fara tashi ana kiran sallar la'asar lokacin, yayi salati bayan ya bud'e idon sa, mikewa yayi da sauri ganin bata dakin, sai yaji kamar dama chan mafarki yake yi. Fitowa yayi falon ya hange ta daga chan ta dora kanta a jikin kujerar. Ajiyar zuciya ya sauke ya karasa ya zagaye daidai saitin in da fuskar ta take, ya durkusa a gabanta yana kallon innocent face dinta, bacci take tsakanin ta da Allah amma kuma kana gani kasan bata ji dadin baccin ba kwata-kwata domin akan hannun ta ta dora kan nata wanda ya tabbatar zuwa lokacin hannun ya gama yin tsami. Kallon falon yayi, sai ya tashi ya dauko t-pillow ya ajiye daga saitin bayan ta, ya kai hannun sa a hankali ya zare kan nata daga kan hannun ya gyara mata kwanciyar yana fatan kar ta tashi. Bata tashin ba sai motsawa da tayi kad'an ta jan numfashi ta cigaba da baccin. Komawa ciki yayi ya fada toilet da sauri jin ana kokarin tada sallar. Wanka yayi a gurguje ya dauro alwala ya fito, be tsaya komai ba ya zura jallabiyar sa ta dazu ya fesa turare ya fita zuwa masallacin. Bayan sun idar da sallar ya dawo ciki ya zauna a gabanta ya tankwashe kafarsa yana kallon ta. Kamar mafarki haka yake ji, amma kuma gaske ne komai ya faru ya wuce bayan da ya gama cire rai da komai ma ya barwa Allah zabin sa. Sai gashi Ya yi masa abinda be taba tunani ba. Sunkoyowa yayi daidai fuskar ta yayi mata peck a kumatu anan idanun sa suka gane masa cleavage dinta,tsayawa yayi chak yaja numfashi da dan karfi ganin fararen boobs dinta da suka cika sosai. Damke hannuwansa yayi ya hade su waje daya kwakwalwar sa ta shiga chaji zuciyar sa kuma na masa bitar da yake ji kamar ya kai hannun sa. Daurewa yayi ya cije saboda baya son ya zake har ta samu damar yin tunanin ko jikinta yake so, sai dai ya kasa dauke idon sa daga kai har sake durkosowa yayi sosai yana more kallon su abinda be taba gani ba, hasaso yadda zasu zama a fili idan babu wani shamaki da ya tare shi. Motsi tayi alamun zata farka yayi saurin gyara zaman sa. A hankali ta bud'e idonta sai ta ga mutum a gabanta a zaune dirshen kamar me gadin ta, da sauri brain dinta tayi mata rewinding abinda ya faru, kunya ce ta kamata ta kasa motsawa bare ta yinkurin tashi zaune ganin yadda yake zaune a gabanta kamar me daukar karatu gashi kuma saman rigar ta ya bud'e sosai har ana kirjinta. Murmushi ya sakar mata ya mika mata hannun sa ta kama ya taimaka mata ta tashi zaune tana kin kallon sa.
"Kin tashi?"
"Umm."
"Toh ya baccin?"
"Lafiya lou." Tace muryar ta kalar tausayi
"Shine kika gudo kika barni ko?"
"Wayata nazo dauka."
"Ok, tashi toh kiyi sallah, la'asar ta wuce sosai."
"Tom."
Tace ta mike a hankali, tashi yayi shima suka jera zuwa bedroom din kamar tace ba sai yaje ba amma ta kasa magana. Toilet din ta shige shi kuma ya jawo akwatin kayan ta, ya bud'e mata, ya daddaga ya dauko mata wata doguwar riga me zip ta gaba da yake ganin zata fi dadi da yanayin weather din hade da Hijab ya ajiye mata a gefen gado, ya rufe ya fita domin ya dan mata warming abincin dazun dan ba wani ci tayi ba kuma baya so ta zauna da yunwa. Ganin kayan a saman gadon yasa ta dauka ta koma toilet din ta chanja dan dama sun takure ta kayan. Sallah ta tayar tana sallar ya dawo dauke da abincin a plate da exoctic me sanyi da cup ya ajiye mata ya ja mata kofar dan ya lura nauyin sa take ji. Falon ya koma ya dauki wayarta ya kwanta ya bud'e gallery ya shiga kallon pictures dinta da na yan gidan su ita kuma ganin be dawo ba, yasa ta sauki abinci taci fiye da rabi dan dama yunwa take ji tasha juice din shima. Ji tayi ta samu nutsuwa sosai dama da yunwa a jikinta. Tunanin kwashe kayan tayi ta dauki tray din ta bude kofar a hankali ta fito. Lokacin ya haye sama dauko notepad dinsa shiyasa bata ganshi ba. Kitchen din ta shiga ta ajiye tray din sannan ta cire janye hannun Hijab din nata ta tattare dattin dake kan plate din abincin guda biyu ta kwashe ta zuba a ledar dustbin sannan ta saka su a sink ta wanke su ta ajiye a gefe, sauran warmers din dake da abinci a ciki ta dora su kan dinning din sannan ta dauki hadin salad din ta sakashi fridge. Ya dan dade a tsaye yana kallon bayanta, dan tana shigowa ya sakko kasan yaji motsin ta a kitchen din sai ya taho ya