Showing 15001 words to 18000 words out of 121037 words

Chapter 6 - RUMBUN QAYA COMPLETE hausa Novel

03 Sep 2024

17327

Yace cike da tsananin mamaki

"Eh." Ta gid'a kanta

"Abun da mamaki, takardar fa tana wajena na bashi dazu, sai dai ko kafin na bashi ya kira kin kenan, maimakon kuma ya sake kira yace ki zauna ya ganta."

"Hmm." Tace kawai

"Shikenan tunda kinzo ma, zo na nuna miki wani waje"

Tashi tayi tabi bayan shi, zuwa wata kofa da take kallon office dinsu, bud'e kofar yayi da key suka shiga ciki, ga mamakin ta sai taga kitchen din madaidaici, dauke da coffee machine, microwave da sauran kayan kitchen dangin su cups da spoon, yar madaidaiciyar kettle me dauke da kananan cups irin ta su Hamman ta ce ta ja hankalin ta, ta matsa wajen ta dauka tana kallo

"Waye yake shan irin shayin nan."

"Mune nan, ni da Aryan, dalilin ma dai samar da kitchen din kenan, dan gwara ni ma, Aryan baya wasa da shayin nan, ya zamar masa addiction wallahi."

"Kamar su Hamma na,suma kullum cikin sha suke, tun ban iya ba har na koya dafa musu, nima kuma na koyi sha."

"Kin iya dagawa?" Yace cike da murna dan dama suna tunanin yadda za'a yi

"Na iya sosai, har majlisa suke kaiwa ayi tasha wallahi."

"Shikenan wallahi, dama muna neman me dafa mana yadda aikin zai dinga tafiya sosai, ta kwana gidan sauki."

"Amma sai dai na dafa maka kai kadai, banda shi."

Ta bata fuska kad'an ita a lallai haushin Aryan take ji, dama kuma ita bata iya rufa rufa ba, idan ka bata mata sai ta nuna amma bata da riko ko tsananin fushi

"Tuba muke, ai yanzu dole muyi miki biyayya, shima ba zai kara ba."

"Allah ko abinci banci ba, daga bacci na tashi kawai naga kira wai nazo, dama ya fada min da ya ganta, amma haka na dauko kafa ga rana wallahi kamar zan narke."

"It's not hygienic ko zauna a kitchen kuna gulmata."

Kofar dama a bud'e take shiyasa ma basu ji shigowar sa ba sam, kusan subucewa kofin yayi daga hannun ta dan bata zata zai shigo a time din ba, kuma bata ma san dalilin da yasa ta ke fadawa Kamal din ba, ko dan taga kamar ya sake da ita kuma yana kokarin jan ta jiki? Ji tayi kamar Hamma Haydar take fadawa wallahi shaf ta manta ma da waye shi da alakar sa da wanda take masa maganar tasa.

"Ba gulma bace ba, gaskiya ce ai Aryan, da sai ka kira kace ta zauna kawai."

"Menene yayi saura da ba'a saka ba?"

Ya share maganar ya sako tambayar,

"Komai an saka, har kuma an samu wadda zata kula da bangaren."

"Wace? Kasan dai i don't trust anyone."

"Raihana ce."

"Who?" Yace kamar be gane wacce yake nufi ba

"Gata nan a gaban ka."

"No, a samu wata dai.."

"Why?"

"We will talk about that later."

"Raihana please ki jirani a office ina zuwa." Kamal yace cikin rashin jin dadin abinda Aryan din yake wa yarinyar, ya rasa dalilin sa kuma ai ba haka yake wa su Zainab ba, ba kuma itace corper ta farko da aka fara kawo musu ba. Ajiye cup din tayi ta raba ta gefen su ta fice ranta babu dadi. Tana fita Kamal ya tura kofar ya dawo wajen sa

"Why are you like this dan Allah? Why are you soo mean to her? Me tayi maka?"

"Babu abinda tayi, aiki tazo ba gulma ba naga, me yasa zata zauna taana fada maka laifi na."

"Tsakani da Allah baka kyauta ba, ka kira ta kace tazo, bayan kasan ka samu paper din."

"Bayan na kiratan ba."

"Then you should have call her again kace ka ganta."

"I forgot."

"Anya? Anya kuwa?"

"Me?"

"Ban gane maka ba kwata-kwata."

"Ba zaka taba ganewa ba kuma ba."

Ya bud'e kofar yayi ficewar sa.

***Ko da ta fito daga kitchen din bata tsaya ko ina ba, tayi ficewar ta dan ba zata iya zama ba, yayi masifar bata mata rai yau din nan, me ya dauki kansa? Me yake ji dashi? Ta manta shaf da kiran da Hajiya Zeenat tayi mata kuma duk shi ya rikitata,sai da taji wayar ta na kara ta tuna tana ciro ta taga Hajiya Zeenat din ce.

"Dan Allah Anty kiyi hakuri wallahi mantawa nayi ban kira ba."

"Ba komai 'yata, nasan ba zaki da gangan ba, ya aiki?"

"Lafiya Lou, ina wuni?"

"Lafiya alhamdulillah, dama kira nayi naji babu wata matsala ko? Ina nufin bangaren Aryan kinsan halin nasa sai hakuri."

Kamar me jiran kiris, kawai sai ta ji hawaye na sakko mata, ta share su cikin muryar kuka tace

"He's very rude Allah Anty, ya tsaneni bansan me nayi masa ba."

"Subhanallah, me ya faru?"

"Bansan me nayi masa ba, komai nayi ban iya ba, a gabana sai yayi ta fadamin magana, ni wallahi na gaji."

"Nasan zai aikata fiye da haka, amma dan girman Allah kiyi hakuri, kiyi hakuri a madadin sa, kiyi hakuri."

Jikin ta ne yayi sanyi jin yadda Hajiyan take bata hakuri, har sai da taji nauyi da kunya, taji dama bata fada mata ba.

"Ya wuce in sha Allah, ba zan sake damuwa ba ma duk abinda zai yi mun saboda ke Anty."

"Nagode sosai Raihana, nagode."

"Ba komai."

"Akwai wata alfarma da nake nema a wajenki Raihana, wani taimako nake so kiyi min dan hakan ne kadai zai taimaka Aryan ya rage wannan halin nasa, taimakon sa zanyi amma baya so kowa ya taimaka masa, yana da yar matsala ne wadda ba kowa ne ya sani ba, kuma baya shan magani ko kad'an, duk da bani da hujjar hakan saboda ya toshe duk wata hanya da zamu gane amma ni nasan baya sha din, akwai in da yake boye su, tun wuri gwara a shawo kan matsalar kafin abun yazo yafi karfin mu, tunda bani da wata shaida shiyasa na kasa yin komai akai, dan ko nayi yunkurin fadawa Alhaji sai na kasa saboda zai bukaci shaida, shiyasa nake so ki taimaka min mu ceto shi daga fadawa cikin wahala. Dan Allah Raihana "

"Bana jin akwai abinda zaki nema a wajena na kasa yi miki in sha Allah, zanyi komai dan ganin kinyi farin ciki."

"Nagode sosai Raihana, nagode zan neme ki idan an kwana biyu, zaki ji abinda ya kamata kiyi ta nan bangaren ki."

"Shikenan, Allah ya rufa asiri, nagode."

"Amin nice da godiya."

Dariya suka kwashe da bayan ta ajiye wayar,

"Wawuyar yarinyar halin ta sak na mahaifiyar ta, dama ai barewa bata gudu danta yayi rarrafe."

"Yaro be san wuta ba sai ya taka ai Hajjaju, ke din duniya ce in dai ta wannan fannin ne."

Dariya suka kara yi a tare.

"Da alamu tarihi ne zai maimaita kansa."



*RUMBUN K'AYA*🔥

*DAUDAR GORA*🔥

*IDON NERA*🔥

*A RUBUCE TAKE*🔥

*KI KULANI*🔥

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥



RUMBUN QAYA*

 
           Page 8

©️®️ *_Hafsat Rano_*

ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F9Fgin7INwl2MLGe0vpoEh

🌹 KUDI KE KIRA

🌹Don Neman Karin Bayani a Tuntubi Wannan number..

🔥 09112842587

🌹Ko kun San akwai Wasu 6oyayyun damar Maki Wanda tun waccan shekarar data gabata mutane suke cin moriyar su..???

🌹 An shirya wannan program din don canza Tsarin kasuwancin matasa da Mata Zuwa kusuwancin zamani

🌹 Inda za'a koyar da Mata sanaoi iri daban-daban

🌹Kamar yadda Sunan Shirin yake wato KUDI KE KIRA... tabbas za'a koya muku yaya ake Kiran kudi su zo kuma su zauna har su dinga Kiran 'yan uwan su...Ta hanyar koyar daku hanyoyin Neman su da kuma yadda za'a dinga kashe su

🌹 Business sai da Traffic is a game of Numbers Dole Sai da jama'a...shin ta yaya ake Nemo jama'ar? Right Target audience sune jama'ar ku

🌹 Kullum kuna sana'a Babu customers..?? To Albishirin ku za'a koyar daku building contacts yadda zaku Kawo mutane what's app din ku...Hatta yadda Zaku hada file na contacts Gain Yana cikin Abinda za'a koyar a wannan Training din..

🌹 Cikin abubuwan da za'a koyar na sanaoi kadan daga ciki sune...Skin Care products, graphics, digital marketing, Gyaran jiki na sudan da chad, turaren wuta,na daki,na tsugunno,na tsinke,humra,body lotion, cream,izal,airfreshner, oils perfumes, wardrobe Balls, Sabulun wanka, Sabulun wanki,hypo,etc

🌹 Program din zai kasance cikin yare guda biyu wato Hausa da Turanci za'a kammala Shirin cikin Kwanaki goma in Sha Allah Stay Turn

🌹Bayan kammala Training din

🌹Zaki Sami certificate na shaidar kammala kyauta

🌹Ba Sai kina da Data ba...kina yin Register kungiya Zata baki Data kyauta har ki kammala Training din

🌹Zasu yi Miki website design kyauta

🌹Zasu koyar dake Kasuwanci Kyauta irin Wanda kika zaba

🌹Zasu yi Miki Logo na company ki kyauta

🌹 Goggle my business account kyauta

🌹Tallata muku kayan ku a yanar gizo kyauta

🌹Zaku Sami Product guda daya Kyauta da kungiyoyin suka tanadar Muku don Gyaran jiki da magance matsalolin Infection da saukar da niima ( Maganin Herbal ne 100%Natural )

🌹 Yiwa Business din ku CAC Register kyauta

🌹 Yadda zaku Sami Rancen Kudi,ko nawa mutum ke bukata ku juya kuyi business ku maidawa kungiya kudin ta ( da yawa suna da ideas na business amma Babu Jari..don haka wannan babbar dama ce ayi amfani da ita don dogaro da Kai)

🌹 Kadan Kenan daga cikin Abinda program din ya kunsa mu kasance cikin group don samun Sauran bayanan Masu yawan gaske

💲ayi Sharing Link din don sauran Mata su amfana da wannan Shirin



_________••••••••••••••••


***A gajiye likis ta koma gida, ga uwar yunwa ga ranta da yake a chunkushe, ko abincin kirki kasa ci tayi duk da yunwar da take ji ta zauna shiru tana bitar abinda ya faru dazun. Wajen la'asar ta tashi ta je dakin Adda Maimuna ta tambaye ta abinda za'a dafa da daddare duk da ba ko yaushe ne take shiga kitchen din ba amma in dai tana nan, tana taimakawa sosai ayi duk aikin da za'a yi da ita, ba zata zauna ta lafe komai sai dai ayi mata ba, irin wannan zaman gundurar masu gidan kake yi shiyasa take shiga ayi duk abinda za'a yi da ita, ta lura kuma hakan na faranta ran Addan shiyasa ma take sake dagewa wajen ganin ta zauna lafiya dasu a dan zaman da zatayi.
Tuwo tayi miyar kubewa daf da magriba ta gama ta gyara kitchen din tas, sannan ta dora indomie dan bata jin cin tuwon kawai gashi kuma tana jin yunwa tunda da rana bata wani ci abincin ba. Tana cikin cin indomie din Oga Kamal ya kirata, ta daga da yakinin dalilin da ya saka shi kiran nata. Hakuri ya bata akan abinda ya faru dazun ya kuma yi kokarin nuna mata sam hakan ba halin Aryan din bane ba, shi kansa be san dalilin da ya saka yayi acting haka toward her ba,amma sam tsakanin sa da ma'aikatan ba haka bane ba. Ta dai ji shi ne ba wai dan ta yarda ba, dan ita bata ga duk abinda ya fada din ba,tunda dai ita be mata ba.
Tattare wajen tayi ta kai plate din kitchen ta dauraye shi sannan ta dawo falon ta samu su Muhammad suna kallon ball ta zauna kawai dan idan ta koma dakin ma babu abinda zatayi, ga Amina yau ba ta dawo ba ta tsaye gidan Anty Saliha babbar yayarsu watakila ma ta kwana a chan.


***Rashin neman sa da Daddy be yi ba jiyan sai ya zata ya manta ya cigaba da sabgogin gaban sa, yana raba kafa yaje nasa office din yaje na gida, baya shigowa gidan sai dare sosai kuma dan baya son abin magana, haka kuma da safe da wuri yake ficewa ya wuce gidan sa ya karasa shiryawa a chan daga nan ya tafi aiki, haka yakeyi a kwana biyun sai dai yau yana shigowa sai ga Daddy a falon k'asa shi da Adam da tarin takardu a gabansu daga gani wani muhimmin aikin sukayi tunda har suka kai wannan lokacin, ji yayi kamar ya juya amma babu hali dan sun riga sun ganshi. Karasowa yayi ciki ya durkusa ya gaida Daddyn wanda ya amsa masa idanun sa na kan wata takarda sannan yace ya zauna. Kallon juna sukayi shi da Adam kafin ya zauna yana zubawa takardun ido yana son fuskantar dalilin zaman nasu.

"Kai da nace ka sameni da daddare shikenan sai kayi batan dabo? Yau kwana uku."

Shafa saman sumar kansa yayi, ya dan yi yak'e kad'an

"Ya tabbata a gidan dai kake kwana, ni ne dai baka son haduwa da, sai ka shigo late ka fice da safe ko?"

"Ba haka bane ba."

"Toh Ya ya ne? Har yanzu maganar nan ce Muhd? Ba zaka hakura ba ko?"

Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, dan be zaci Daddy zai dauko wannan maganar ba a irin wannan lokacin, be taba kawo hakan ba da ya gwammace ya fasa shigowar da ya gansu, ko yayi wata karyar da zai samu ya zille.

"Ya kamata ka sani, ban amince kayi wani abu akai ba, na fada maka ba tun yau ba, ka bar wannan maganar kawai amma na lura kamar baka ji, abinda ya riga ya wuce ya wuce, tsaurara bincike ba zai taba haifar d'a me ido ba."

"Dan haka bana so, ka bar maganar nan na fada maka, ka barta tunda ba akan ka aka fara mutuwa ba, ba kuma zai zama na karshe ba, kana gani nayi iyakar kokari na akan case din, kuma an tabbatar da kanta ta kashe kanta, binciken Yan sanda, likitoci da duk kwararru akan fannin ya tabbatar da haka, akan kishi? Toh me kake so nayi kuma akai? Ko ban iya ba kaine ka iya?"

Kansa a k'asa zuciyar sa na wani irin harbawa, lokaci daya yanayin sa ya sauya, ya dinga jin wani irin tashin hankali na bijiro masa, maganganun da ya tsani ji a rayuwar sa, ace wai ta kashe kanta da kanta, wanne marar tunani ne zai yarda da hakan? Ta ya ya kishi zai saka ta kashe kanta? memory din abinda ya faru ne ya shiga dawo masa filla filla. Muryar ta radau tana neman taimako, cikin tsananin wahala da galabaita. Sunan sa da take kwalawa ya shiga yi masa amsa kuwwa, tamkar a lokacin take kiran sa, tamkar a lokacin komai yake faruwa, idanun sa ya runtse, ya hango ta kwance a cikin jini, cikin tsananin jinin da be taba ganin irin sa ba, Ammin sa a kwance, an mata yanka irin wanda ake wa rago! Jikin sa ne ya hau rawa sosai, gumi ya shiga keto masa, Adam ne ya fara lura da halin da yake ciki, yayi saurin ankarar da Daddy dan tun sanda ya fara masa magaar be ko kalle shi ba, zabura yayi cikin tsananin tashin ya watsar da takardun hannun sa, sukayi kan Aryan din suna kwalla kiran sunan sa.

"Kira Dr, kira likitan sa Adam, innalillahi."

Wayar sa ya ciro da sauri ya shiga dialing number likitan da yake duba shi, ringing daya ya dauka dan har yana shirin kwanciya ma dan be dade da shiga gida ba.

Suna tsaye akan sa suna kokarin bashi taimakon gwaggawa Dr ya karaso, ya taimaka musu aka karasa saka masa nebuliser dan dama gashi asthmatic toh da irin hakan ta faru sai numfashin ya soma yin sama. Kusan minti talatin zuwa awa daya sannan ya fara samun daidaituwar numfashin sa dama kan sa. Rufe idon sa yayi ruf, yana jin maganganun su akan sa da yake masa wani irin ciwo.
Har kusan ukun na dare suna tare a dakin sa harda Hajiya Zeenat, dan nan aka maidashi, yana jin yanayin damuwar da Daddyn yake ciki fiye da duk wata damuwa da ya taba shiga akan ciwon nasa, me yasa yanzu ya nuna damuwar sa sosai? Me ya sauya daga sanin da yayi wa Daddyn na rashin kulawa da damuwa da abinda ya shafe shi? Be san dalilin nuna masa soyayyar ba, bayan be same ta a lokacin da yake da matukar bukata ba, a lokacin da ya chanchanci a jashi a jiki a nuna masa soyayya, sai yanzu? Da ya girma ya mallaki hankalin kansa? Baya bukatar wannan soyayyar, baya bukatar kulawar zai iya kula da kansa tamkar yadda yayi a baya. Suna fita daga dakin ya tashi da k'yar dan jikin sa baki daya babu kwari ya fice daga dakin ya sakko k'asa, ya isa dakin masu gadi ya taso daya daga cikin ma'aikatan gidan yace ya kaishi gidan sa, a daren nan da komai haka suka tafi. Suna isa ya ce masa ya zauna ya karasa kwana anan kawai ya shige ciki yana jin kamar ana daddatsa masa cikin jikin sa saboda wani irin mugun sanyi me hade da zazzafan zazzabi da ya rafke shi a lokaci daya. Gabannin asubah zazzabin ya dan sake shi kad'an, ya tashi da k'yar dan dama ba baccin yake ba. Alwala yayi yana fitowa daddy na kiran wayar sa, be daga ba dan yasan kila dakin sa yaje duba shi da asubah yaga baya nan shine dalilin kiran, bashi da wani bayanin da zai bawa Daddy bama shi da karfin jiki da na zuciyar da zai iya magana dashi, musamman da ya zama duk abinda ya fada ba zai iya ce masa a ah ba. Raka'atanil fajr yayi ya zauna a saman daddumar har zuwa lokaci ya tashi yayi subh sannan ya koma ya sake kudundunewa a cikin blanket. Bacci ne ya dauke shi me karfi cikin yanayin da shi kadai yasan abinda yake ji.





RUMBUN QAYA*

 
           Page 9

©® *_Hafsat Rano_*

ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥

****Karfe tara ya farka daga nannauyan baccin da ya dauke shi, bashi karfin zuciya da na gangar jiki amma hakan ya tashi da k'yar, yayi wanka ya shirya sannan ya kira Kamal yace yazo ya dauke shi dan baya jin zai iya driving. Ba'a dau lokaci ba sai gashi ya iso, ya fito yana tafiya wadda ya sa Kamal din karasowa da dan sauri yana kallon fuskar sa

"Are you ok ?"

Gid'a masa kai yayi, ya wuce shi zuwa wajen motar, bin sa yayi cike da mamakin karfin hali irin nasa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login