Showing 39001 words to 42000 words out of 121037 words

Chapter 14 - RUMBUN QAYA COMPLETE hausa Novel

03 Sep 2024

17335

da sauri ta dawo baya ta rufe kofar kar Dadah ta dawo tayi wata maganar da zai ji, sannan ta daga tayi sallama a hankali chan kasa. Maimakon ya amsa sallamar sai yayi shiru ya fara tunanin dalilin da yasa shi kiran ta

"Ya jikin naki?" Ya tattaro kalmar da k'yar ya fada yana ciccijewa

"Ina wuni?" Ta gaishe shi a maimakon amsa tambayar da yayi mata

"Lafiya, sai anjima."

Kit ya kashe wayar, saroro tayi da waya a hannu cike da madaukakin mamakin sa, wannan wacce irin waya ce? Dariya abin ma yaso bata ganin yadda yayi maganar kamar wanda aka saka a gaba akayi masa dole ya kirata, saukin ta ma shine ya kira da ita ta kira yayi mata haka da tasha dan banzan kunya. Samun kanta tayi da dariya sosai daga karshe da ta gama tunanin abun, sam bata taba ganin irin sa ba, wai sai anjima, shikenan? Ta dauka ma wani abun ya rasa a office ya kira ta, bata ga amfanin kiran nata ba gaba daya. Toh ko dai kira yayi kawai ya duba ta tunda har yace mata ya jiki a farko. Ajiye wayar tayi kawai a dakin ta fice dan idan ta zauna tunanin son gano dalilin kiran nasa zata iya kaiwa dare a dakin bata fito ba.

****Dukkan wani kokari da Yaron Hajiya Zeenat zai yi mata akan Matawalle ya gaza, tun tana ganin abun wasa ne sai kuma jikinta ya fara bata lallai ya shirya mata, shirin da kuma ta gaza gane in da ya dosa, tasan shirun sa ba alkhairi bane a gareta, dan a sanin da tayi masa tasan tabbas da tuni ya neme ta ya kirata ya tabbatar mata da fitowar sa, dan ko a karshen zuwa ganin sa da tayi a prison ta lura da wata halayya daban da ta Matawallen da ta sani dan har ta dinga tunanin dalilin shi na share ta da kin yarda ya biye mata ba kamar a baya ba, idan taje ganin sa ya kan jaddada mata sai ya kaita k'asa in dai yana numfashi a doran k'asa.
Raihana ce ta fado mata, tabbas ita kadai ce a yanzu zata zame mata garkuwa da kuma tsani wajen samun lagon mahaifin ta, da ita zatayi amfani ta sake kaishi kasa wanda zai fi masa ciwo fiye da kaiwar da tayi masa a shekarun baya dan wannan sai yafi jin zafin ace yar cikin sa ce zata aikata masa hakan.
Wannan tunanin ya dan bata hope har ta kara samun kwarin guiwa sosai duk kuwa da chan kasan zuciyar ta, tana cike da tsoron abinda zai biyo baya idan komai a fallasa, amma duk da hakan ba zata karaya ba, dan ita din ba raguwar mace bace ba, tun zamanin kuruciya kuwa ballantana yanzu da ta kai matakin kuloluwa a matakan nasarar da ta tsarawa kanta cimmawa a tsawon rayuwarta. Gida ta koma kawai dan tun fitar safen da tayi bata komo ba, sai dai tayi matukar tsurewa ganin Adam har lokacin yana gidan a dakin sa yana ta sharar baccin asara. Wani wawan duka ta kai masa a gadon baya wanda hatta takalmin kafarsa be samu cirewa ba dashi ya kwanta ruf da ciki ya dage kafafun sama. Dabiar da ya fara kenan chan baya ta shiga ta fita ta samu nasarar hanashi tun Daddyn be farga ba, sai yanzu da kusan komai yazo hannu shine zai dawo ruwa kenan, ya barta da komai ta ina zata fara bayan ba aikin ta bane ba, wa zai cigaba da kula da komai kenan? Idan haka ne karshe fa kenan sai dai komai ya dawo karkashin Aryan abinda ba kuma zata taba amincewa ba dan duk wata dukiya da Daddyn ya tara kusan tare da ita aka tarata dan ita ta taimaka masa matuka har ya kawo wannan matakin da yake kai shine kuma dan rashin alkawari har ya maida komai da sunan yaransa biyu ita da Adam sun tashi a tutar babu. Bata da plan din yiwa daddy komai dan ta gama sakankancewa zai damka wa Adam kusan komai, rana daya ta ji shi yana waya da lauyan sa, daga ranar komai ya chanja ta shiga neman rayuwar sa tun kafin ya nemi ta ta.
Soshe soshe Adam din ya hau yi wajen da ta dake shi, ya tashi yana kumbura fuska ya wuce toilet ya wanko fuskar sa da bakin sa ya dawo ya tarar da ita a tsaye tana jiran sa

"Yanzu tun da na fita kake baccin asara Adam? Ina chan ina kokarin gina maka rayuwa amma shine zaka zo ka kwanta office din ma ka daina zuwa kenan Aryan ya mallake komai."

"Ni bana son komai idan har ba zan samu Raihana ba."

"Raihana kuma? Wai dama wannan maganar bata mutu ba?"

"Wallahi bata mutu ba, kuma son ta nake auren ta zan."

"Tirkashi, akan hakan kake son maida kanka wani na daban?"

"Lallai baka da hankali ma wallahi, idan ma zaka hakura tun wuri gwara ka hakura, mahaifin ta ko mutuwa zakayi ka dawo ba zai baka yarsa ba wallahi,."

"Akan me yasa ba zai bani ba?*

"Saboda baka san waye uban nata ba ai shiyasa zaka tsaya tambaya, toh yar Barrister Matawalle ce, ina fatan yanzu zaka saita hankalin ka waje daya ka dawo hayyacin ka, kasan in da yake maka ciwo."

Fuuu ta fice tana bambamin fada. Shiru yayi bayan ya fita, tabbas ya san waye Matawalle a wajen mahaifiyar sa, sannan yasan duk wata harkalla da ta ke tsakanin su, babban abinda yake damuwan sa shine yadda yaga Aryan ya damu matuka da al'amarin yarinyar, tunda ko last akan ta sukayi fada sosai ya kuma hangi wani abu a chan cikin idon Aryan din.

"Ba zai yiwu ba, sai dai dukkan mu, muyi biyu babu wallahi." Yace yana yin hanyar barin dakin. Dakin Hajiya Zeenat ya nufa ya tarar bata ciki sai wayar ta, dama abinda yazo nema kenan, da sauri ya bud'e wayar ya shiga wajen audios din dukkan wayar da sukayi da Raihana, yayi copying komai akan wayarsa sannan ya ajiye mata wayar ya juya ya bar dakin. Da wannan zai yi amfani yasa Aryan ya tsane ta, tsanar ta har abadah, shikenan kowa ya rasa dan zuciyar sa ba zata iya daukar nasarar Aryan din ba.


***Daddy na kwance har ya bata jikin sa da fitsari dan gaba daya ranar babu wanda ya leko shi, motsin bud'e kofar yaji sai kuma haske ya gauraye dakin. Takowa tayi zuwa gaban sa tana toshe hancin ta da hannun ta.

"Menene haka?"

Tace tana ja baya ganin kayan jikin sa a jike jagwab, hawaye ne ya biyo gefen fuskar sa tana kallo, ya motsa idon sa.

"Ni zaka ci amana Alhaji? Ni Zeenatu da na sadaukar da rayuwata da komai na akan ka ni kayi tunanin yaudara ko? Har kasa a fito da Matawalle ba tare da sani na ba, saboda kana son farantawa wanda ba zai taba yafe maka ba, duk da abinda kayi yanzu Matawalle ba zai taba yafewa mutum irin ka ba, macuci maha'inci irin ka, da kayi hakuri mun cigaba da yadda muka faro, domin nice daidai da kai, amma sai ka ci amanata bayan ka manta wacece Zeenatu, ba'a taba cin amaanata a zauna lafiya, dan haka sai ka cigaba da zama a haka har zuwa sanda na gama cika buri na,idan zuwa lokacin ka karasa kuma shikenan."

Kokarin motsawa yayi amma ya kasa, gashi yana so yayi mata magana amma sam bakin sa ya kasa, be san me tayi masa haka ba, amma ko ma menene Yana bukatar taimakon gaggawa, dan wani irin nauyi da jikin nasa yayi masa ga wani irin ciwo da idanun sa suke masa tamkar zasu daina gani. A yau yayi nadamar biye wa mace irin Zeenat, ta raba shi da yayansa masu so da kaunar sa, ta nisantasu dashi ya zama na basa iya neman sa face shi ya neme su, da kansa kuma ya kafa musu wannan sharadin a lokacin da yake jin su tamkar wasu nauyi a gareshi. Da ace be hana su, yasan da tuni sun neme shi tun a jiyan, yanzu be san ranar fitar sa daga nan ba,watakila haka zai karasa RAYUWAR sa a wajen ba tare da ya nemi yafiya da afuwar su ba, musamman ARYAN!



Ignore all the typos, I'm super busy wallahi.


*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*


*ZAFAFA BIYAR BACTH A*


1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*


2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*


3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*


1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*


_Duk biyar 1500_

*______________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_*

1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)* 400

2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)* 400

3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)* 400

4... _INAYAH_
*(Mamu gee)* 400

5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)* 400

_Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_




*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥
_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_
_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_

_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_
_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_

1 _*IDON NERA*_
Mamuhgee

2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata
Billyn Abdul

3 _*RUMBUN QAYA*_
Hafsat Rano

4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata
Hafsat Miss Xoxo

5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata
Safiya Huguma


_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_

Guda 5 1200
Guda 4 1000
Guda 3 800
Guda 2 600
Guda 1 400

_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_

_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_

Saiku tura shedar ta👇

_*09033181070*_

Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇

09166221261



TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥
MUNGODE🙏🙏❤️

*RQ*

      Page 20

****A gurguje Adam ya watsa ruwa ya fito ya tarar da Hajiya Zeenat a zaune tare da wata mata, wuce su yayi bayan ya gaishe ta a gajarce suka bishi da kallo Hajiya Zeenat na cike da mamakin in da kuma ya nufa. Office ya wuce kai tsaye ya duba parking lot yaga motar Aryan sai yayi murmushi ya wuce bangaren sa kawai yana sake nanata abinda yake shiryawa a cikin kansa.
Aryan na zaune a office ya gama duba wasu takardu Kamal ya shigo kamar yadda ya saba ya fara zuro kansa sannan ya shigo yana dariya.

"Wai ina kaje?"

"Sabuwar budurwar da nayi ce ta kirani, shine fa na amsa kira kar tayi fushi dani."

"Sabuwar budurwa kuma?"

"Eh karaye zan je, kai ba ka tsaye wasa ba, ta biyu nake shirin yi ka zauna dai."

"Lallai wahala bata ishe ka ba,mace daya ma ya aka kare bare har biyu? Akan me yasa ma zaka kara aure."

"Sunna."

"Yen yen, dama haka kuke fakewa ai, ku tara matan suyi ta neman ranku."

"Hahaha, ko su dinga yar rige-rigen kyautata mana ba."

"Ba wani nan."

"Yanzu kai kenan mijin mace daya ne."

"Ko rabi ba,dayar ma ba dani ba, kai ni bana son wannan zancen please, akwai tarin ayyuka masu yawa suna jiran ka."

"Yanzu zan hau kansu ai."

"Yauwa jeka toh."

"A ah ai yau a office din ka zanyi aikin, bari na kwaso komai na dawo."

Kallon sa Aryan yayi, yana fita ya tashi yasa key a kofar ya dawo ya zauna yana murmushi.

Baki daya yan office din sun dauka Raihana ta tafi kenan, ganin kwana biyu bata zo ba tun ma ranar dai da abin nan ya faru, sosai hakan yayi wa Zainab dadi dan a kwana biyun nan ko yaushe ita Aryan yake kira kamar dai da kafin zuwan Raihanan. Ta fito zata tafi gida kenan Adam ya tsaida ta, ta tsaya tana dan waige-wage, kafin ta dan matsa sosai yadda ba za'a gano ta ba.

"Me yasa Raihana bata zuwa?"

"Ya tambaya dan yana ta lura da shige da ficen wajen amma be ga wucewarta ba ko kad'an

"Inaga ta chanja wani wajen, tun ranar da abin nan ya faru bata sake zuwa ba."

"Damn it!" Ya bugi gefen gini sannan yace taje.


***Zaman Raihana a gidan su ya kara sata sakankancewa sosai har ta manta da sabgar Hajiya Zeenat da kowa ma, sosai Abbyn ta yake samun kulawa ta musamman dan bayan masu zuwa jaje sun zo sun gama wani sabon gida suka tattara suka koma me dauke da part hudu wanda Hamman ta suka dade suna ginawa dan sun yi alkawarin a tare zasu zauna gida daya har Abby. Bata san dalilin komawar su gidan a wannan lokacin ba dan ba'a gama ma sauran part din ba nasun dai kawai akayi sauri aka karasa. Ko yaushe Abby yana falon sa a zaune yana kallon news ko kuma ka same shi yana karatun alqur'ani me girma. Ko yaushe suna tare da Tafeeda dan shine yake kula da Abbyn da koman sa musamman da ya kasance su Hamma Haydar da Babbo Sadeeq suna fita aiki kuma suna kai yamma likis kafin su dawo wani lokacin har dare ma.
Da sallamar ta, ta shiga falon bayan an amsa mata an bata izinin shigowa. Lamido ne zaune a gefen Abbyn sai wata jaka a gefen shi wadda ta nuna da alama lokacin aka rufe ta.

"Uwata ce?" Abby yace yana dan mikewa daga kishingidar da yayi,

"Eh." Ta gid'a kanta tana zama a daidai saitin kafarsa.

"Abby barka da gida."

"Barka dai, ya gidan?"

"Lafiya lou Abby, gobe zan koma Kano."

"Jibi, jibin nan?"

"Umm."

"Kaji Lamido, ba za'a yi wani abun ba akai?"

"Anyi Abby, shine ma har aka samu kanon."

"Toh ka tabbatar babu wata matsala ko?"

"Babu in sha Allah, ko akwai kanwata?" Ya kalle ta

"Babu Hamma." Tace tana murmushi

"Shikenan, Allah yayi muku albarka, sai ka shirya mata tafiyar Lamido."

"In sha Allah."

"Ki kula sosai kinji? Dan Allah Raihana karki wasa da rayuwarki da tarbiyyar da kika samu, karki ga babu idon mu akanki, muna sane da komai."

Shiru tayi kanta a k'asa, har ya gama mata nasihar, tayi godiya ta tashi ta fita wajen Dadah.

***Tafiyar rana zatayi dan haka ne ma ta karasa shiryawa a tsanake, bata son komawa har ga Allah amma kuma ya zatayi? Haka ta karasa hada abinda zata bukata sannan tayi wanka ta shirya. Babbo Sadeeq ne ya kaita airport dan Abby dama yace ya haramta mata tafiyar mota. A boye ta share hawayenta ba kamar wacchan tafiyar da take cike da dauki ba.

***Saukar ta a Kano yayi daidai da shigowar kiran Hajiya Zeenat, ta kikkirata a chan amma duk sanda tazo missed calls dinta take gani kawai kuma bata bi dan bata gama nutsuwa da abinda Kamal yake son tayi ba gashi be kirata ba kwata-kwata bare ta gaya masa abinda yake faruwa. Daga baya kuma kawai sai ta kashe wayar ta tura ta a drawer bata kuma sake kunna ta ba sai yau da zata taho shima dan tasan dole Dadah zata kira kafin su tashi sannan ta kira ta bayan sun sauka. Tsoron da take ji ne taji gaba daya ya dawo mata sabo. Kin dagawa tayi har ta katse sai tayi saurin kiran Kamal din tasan abinda ya kamata tayi.
A lokacin suna tare da a gidan Aryan din kiran ya shigo, yayi murmured kad'an sannan ya daga yana mikawa Aryan din takardar hannun sa

"Raihanatu."

Dagowa Aryan yayi da dan sauri jin sunan da ya kira, Kamal na ankare dashi kawai sai ya bar wajen yayi hanyar fita baya yana amsa gaisuwar da take masa.

"Na dawo yanzu."

"Masha Allah , ya hanya?"

"Alhamdulillah, lafiya lou."

"Good, kin baro kowa lafiya dai ko."

"Eh lafiya Lou."

"Toh madallah."

"Hajiya Zeenat ce take ta kirana a waya, bansan me zan ce mata ba."

"Dagawa zaki kamar babu abinda ya faru".

"Zan iya?"

"Sosai, ki daga kafin ta fara saka shakku akanki."

"Idan kuma ta sani wani abun fa?"

"Karki damu, yadda kuka fara a baya haka zaku dora, kina jina? You have to be strong babu abinda zai faru nayi miki alkawari, trust me."

"Ok." Tace a sanyaye

"Yawwa, call her back karki ji komai, kawai dai duk yadda taso kuyi maganar family dinki karki bata fuska."

"Ok." Ta sake cewa a sanyaye.

Katse kiran yayi hango Aryan yana nufo wajen ta cikin glass, hannun sa rike da ball yazo ya wuce Kamal din ya bud'e kofar da zata kaika bayan gidan. Short ne a jikin sa da rigar sa da alama zai motsa jikin sa ne. Bin bayan sa Kamal yayi yana tattare hannun long sleeve din rigar sa

"Raihana ta dawo."

Yace masa yana durkushe yana gyara igiyar takalmin kafarsa. Be dago ba kawai yace ok ya daga ball din suka soma buga basketball.

***Bata bi kiran ba sai da ta karasa gida ta zauna bayan sun gaisa da Adda Maimuna sannan ta kira Hajiya Zeenat din gabanta na dukan uku uku. Rejecting kiran tayi ta biyo kiran nan take.

"Idon ki kenan Raihana?"

"Kiyi hakuri Aunty, na danyi rashin lafiya ne."

"Ashsh, amma shine babu labari, ranar daga shiga in fito sai na neme ki na rasa ba wani bayani, ko akwai wani abu da ya faru ne?"

"A ah, kira na oga Aryan yayi ya gane bana office din shine nayi saurin komawa."

"Ok, toh ya jikin naki? Kin warware dai ko?"

"Alhamdulillah, na samu sauki gobe zan koma aiki ma in sha Allahu."

"Toh madallah, Allah ya kara sauki."

"Amin ya Allah, nagode."

"Zaki iya zuwa gobe? Ina son ganin ki."

"Na'am?"

"Eh ko akwai in da zaki je?"

"Eh amma zan gani idan na dawo da wuri."

"Toh ba damuwa,sai ki kirani."

"Ok tam."

Baya tayi ta kwanta ta ajiye wayar a gefen ta, anya? Anya ba zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login