Showing 21001 words to 24000 words out of 121037 words

Chapter 8 - RUMBUN QAYA COMPLETE hausa Novel

03 Sep 2024

17330

yaranta suka dawo daga school, dan dama su ya zauna zaman jira da tuni ya tafi ya shiga wata sabgar, burin sa kawai ya koma office dinsa ya cigaba da aiwatar da abubuwan da ya fara wanda sam Daddy baya so shiyasa ma yake ta dakushe shi.


***A daidai kofar wani gida dake da karancin hadada har ma da karancin gidaje yayi parking. Fitowa tace ya je ya dawo ba tare da ya shigo ba, a duk sanda suka zo gidan ko cikin harabar gidan bata yarda ya shiga da ita da kafarta take takawa zuwa ciki duk kuwa da gidan ya kasance mallakin ta ne. Sai da taga tafiyar sa sannan ta juya ta shiga gidan.
Yana tsaye a compound din yana dakon zuwan ta, sai gata ta shigo, su biyu ne tak suke da mukullin gidan dan hatta Adam bata yarda ya san da zaman wajen ba, dan tasan ba zai taba lamutar abinda take aikawata a wajen ba,amma kuma ya zatayi? Dole ta nemawa kanta biyan bukata dan babu wani abun arziki da take samu ta wannan bangaren. Ta dade a cikin harkar kuma bata taba jin dar ko dana sanin kasancewar ta akai ba.

"Hajjaju kin karaso."

Yace yana tahowa suka hadu a hanya, saurayi ne wanda a shekarun sa ba zai haura Adam dinta ba, idan ma zai haura din be fi da kad'an ba. Harkar computer ce ta hada su daga nan ta siye shi da wasu mahaukatan kudade har zuwa yanzu da suke rayuwa tamkar mata da miji a gefe daya kuma yana mata aikin da take so. Shiyasa Aryan yake a tafin hannun ta domin duk wani motsin sa tana sane dashi duk da akwai abubuwan da ta kasa samu a wajen nasa har yanzu. Babban burin ta shine samun faifan video din wanda take tunanin yana hannun sa, amma kuma idan ta zurfafa tunani sai taga ai da yana wajen sa da tuni ba maganar ake yi ba, dukkan su a yanzu sun yi taraiyane akan samun disk din wanda yake determining nasarar dayan su akan daya.

"Na karaso, hope baka dade kana jirana ba handsome."

Tace tana masa kallon kasa kasa. Irin na tsofaffin yan duniyar nan wanda suke san duniya take kad'a musu gangar shedanci a tsakiyar kansu

"No ba yawa,ban fi 20mint ba."

"Duk da haka ba zan so hadadden saurayi ya zauna zaman jira na har na 20min ba."

Dariya ya kwashe da ita, ta mika masa hannun ta ya rike zuwa cikin gidan.

"Me yasa baka shigo parlor ba,ka zauna a waje."

"Jiranki nake, ba zan iya shigowa na barki ba."

Murmushi ta saki me taushi sannan ta jefar da jakarta gefe hade da mayafin ta, ta zauna tana kashe masa ido.

"Ya labari Hajiyata, ina fatan dai komai yana tafiya daidai?"

"Ba zaka fara kwantar da tarzomar da ta taso ba? Kafin wannan maganar?"

Dariya yayi, itama tayi dariya yace

"Shawara ce dani akai Hajiya."

Hannun ta, ta kai saman bakin sa da sauri

"Ban hana ka ce min Hajiya ba?"

"Tuba nake ranki ya dade."

"Ina jinka toh."

"Ina ganin duk wani communication da zai wanzu tsakanin ki da yarinyar nan ya zama call ne, banda text message kiran kawai sannan ki dinga recording call din, ni kuma zan san yadda zan nayi editing komai."

"Shisa nake kara sansa, kasan deal."

"Kinga baki bar wani sign ba da har zai iya zama hujja akan mu Hajiya, auw ranki ya dade." Ya kama baki da sauri yana dariya

"Naji. Zan kuma yi amma dai for now dai mu shiga ciki, hakuri na ya kare." Tace tana mikewa

"Ok muje." Yace yana murmushi suke shiga daga ciki. Allah ya kyauta


***Kasancewar Thursday yau ya sakata kin tashi da wuri dan ba zuwa zatayi aikin ba, a kaida CDS ya kamata taje wanda ake yi duk ranar Thursday, toh amma bata jin fitar kwata-kwata dan sai wannan satin tayi submiting takardar a road safety akayi mata signing. Tana jin Amina na tashin ta bayan ta shirya taki tashi haka ta hakura ta tafi ta barta, ta kara shigewa bargo dan akwai dan sanyi sanyi a garin. Kiran wayar Dadah ce ta farkar da ita, ta daga cike da zumudin ta. Nan da nan ta wartsake daga baccin jin suna hanya bayan da sai asabar zasu zo, suna Kaduna dama tun jiya yau dan haka tasan kamar yanzu zasu iso Kanon. Dadi kamar zai kasheta,ta shiga wanka a gurguje tazo ta ta hau gyaran dakin nasu, ta gyara ta wanke bandakin tas sannan ta hau shiryawa ta manta ma da wani batun breakfast, kaya tasa masu kyau sosai wanda tasan Dadah zata ganta fes da ita, dan kayan ma sababbi ne ta dinka su. Zuwa tayi ta fadawa Adda Maimuna suka hadu da Muhammad ya shiga tsokanar ta tana ramawa. Dakin ta dawo ta dauki wayar ta, ta dinga kallon lokaci ta kasa zama waje daya ko kad'an. Shigowar kira wayar ta yasa ta saurin zabura ta dauki wayar.

"Hajiya Zeenat?!" Ta furta a hankali kafin ta daga wayar

"Hello, aunty ina wuni?"

"Raihana ta, kin manta dani ko?"

"A ah Aunty."

"Toh kina lafiya? Ya aikin ya komai da komai?

"Lafiya lou alhamdulillah."

"Babu wata matsala ko?"

"Babu komai Aunty."

"Toh Masha Allah, wani taimako zaki min dan Allah idan ban takura miki ba."

"Ba komai Anty, me za'a yi?"

"Nasan kince min yau bakya zuwa aiki ko?"

"Eh bana zuwa, banje yau ba ma."

"Taimaka min ki shirya, zan turo miki address kije ki duba min Aryan."

"Na'am?" Tace tana zaro ido

"Eh ki taimaka min, Aryan bashi da lafiya kwana biyu kenan, gashi duk yadda zamuyi akan sa mun kasa wallahi, Adam yace min ya sake dake har yana saki aiki a office dinsa, kiyi min wañnan taimakon dan Allah kije ki gano min shi, sannan ki dafa masa shayin nan da aka ce kin iya dafa masa, Kamal ya fada min komai, ki taimaka min dan Allah."

Shiru tayi tamkar ruwa ya cinye ta, ita da take jiran Dadan ta yaushe kuma zata fita daga gida, suzo bata nan kuma sai tace tana ina kenan?kuma taje tace masa me? Bayan tasan halin sa sarai, kuma gidan shi da waye? Bata gane ba

"Zaki iya min wannan taimakon Raihana?"

"Zanyi." Tace kai tsaye dan bata jin zata taba iya kin duk wani abu da ta nema a wajen ta

"Nagode nagode miki, Allah yayi miki albarka kinji? Ya baki miji na gari wanda zai kula dake."

"Amin."

"Karki damu, idan kinje gidan akwai mutane ba shi kadai bane, akwai maigadin gidan da matar sa su zaki samu kinji?"

Ajiyar zuciya ta sauke, bata tunanin Hajiya Zeenat zata taba cutar da ita ko tayi abinda zai cutar da ita, dan haka zuciyar ta daya ta yafa mayafin ta, ta dauki yar madaidaiciyar jakarta ta saka waya da kudin napep sannan ta fito




🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_

_DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_

_MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_

+227 90 16 59 91

*Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na*

Maryam sani
0022419171
ACCESS bank

Ku tura shaidar biya ga

+234 903 318 1070

*Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number*

09166221261

Litattafan dai sune kamar haka

RUMBUN KAYA Hafsat rano

A RUBUCE TAKE Huguma

IDON NERA Mamuhghee

KI KULANI Hafsat xoxo

DAUD'AR GORA Billynabdul

*Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥


*RQ*

      Page 11

Hafsat Rano

*****
Tana tsaye bakin titi suna magana da Hajiya Zeenat din motar ta tsaya a gefen ta, sauke glass din yayi nan take ta gane shi, driver da ya bige ta ne. Bud'e kofar bayan tayi ta shiga cike da taraddadin abinda zata tara. Ta rasa dalilin da yasa take wasu abubuwan duk da ba haka tarbiyyar ta take ba. Tasan kuma tabbas idan Dadah suka samu labari ranta zai iya mummunan baci, shiyasa ma taki sanar dasu komai akan Hajiya Zeenat din dan su sam basu da yarda tun abinda ya faru da Abbyn ta wanda an rasa wanda zai iya bata labarin ainahin abinda ma ya faru har ya samu kansa a prison tsawon wannan lokacin.
Jikin ta ne yayi sanyi sosai ganin sun iso cikin layin gidan sannan ya rage tafiya sosai ta tabbatar a daf suke. Gefen wani gida yayi parking wanda yafi mata kama da kango sannan ya zuro wata leda me kyau yar madaidaiciya bayan yace

"Wanchan bakin gate din shine gidan, ga wannan Hajiya ce tace na baki."

Hannu tasa ta karbi ledar bata ko duba ba,tayi godiya ta fita shi kuma ya juya. Kallon gidan take gabanta na faduwa amma haka ta daure dan har cikin zuciyar ta, tana son sanin halin da yake ciki duk kuwa da ba wai tana shiri dashi bane, tana dai jinsa tamkar Hamman ta ne kuma zata iya yin komai dan ganin an san halin da yake ciki.

_"Kiyi hankali dashi dan ba kalou yake ba."_

Muryar Adam a sanda yake mata maganar ta shiga yi mata amsa kuwwa. Damke ledar hannun ta tayi sosai ta durfafi gidan kirjin ta na wani irin lugudan duka. Knocking tayi a kofar a dan tsorace ta tsaya daga baya tana jira a bud'e. Baba maigadi na cikin dan karamin dakin dake wajen gate din ya fito da dan saurin sa a tunanin sa ko Aryan din ne ya fita yana ciki ko kuma Kamal ne yazo. Bud'e kofar yayi ya kalleta da alamun tambaya kafin yace

"Kece kike kwankwasawa?"

"Eh nice Baba, ina wuni?" Ta dan russuna ta gaishe shi

"Lafiya lou alhamdulillah, bismillah."

Ya matsa mata ta shigo sannan ya tura kofar

"Wajen me daki na kike zo?"

"A ah." Ta gid'a masa kanta tana tuno abinda Hajiya Zeenat din tace mata.

"Aryan yana ciki?"

"Na'am?" Yace da mamakin sa

"Eh Ya Nabila ce ta aiko ni da sako na kawo masa, bansan ko ya fita ba amma "

"A ah be fita ba, yana ciki kamar ma dai bacci yake yi."

"Ok." Tace tana kokarin boye yanayin da take ciki na tsoro

"Muje ciki." Ya nuna mata hanya, gaba yayi ta bishi a baya a hankali har zuwa kofar part din, ja tayi ta tsaya dan bata san ta in da zata fara.

"Bismillah yana ciki."

Shiru tayi tana nazari, ta shiga ciki bayan tana da yakinin shi kadai ne a cikin, hakan kuwa daidai ne? Kar tayi abinda zai zubda mata mutunci fa.

"Amm Baba dan Allah a cikin gidan ba Yara?"

"Eh akwai Amma sun je islamiyya, sai dai suna gab da dawowa."

"Toh Baba bari na jirasu sai suyi min jaroranci, bana son shiga ciki ni kadai."

"Toh... Bismillah muje na kaiki wajen iyalina, sai ki zauna ki jira su."

Godiya tayi, suka juya zuwa hanyar bq, ya kaita wajen matar sa Hajara ta zauna. Minti goma da zaman ta yaran suka dawo, daya daga ciki tasa a gaban suka koma part din ta tura kofar da take a bud'e suka shiga ciki. Babu motsi ko alamun akwai mutum a ciki sai rigar sa dake ajiye a saman kujera hade da wayoyin sa da mukullin mota. Kamar munafuka ta shiga sallama tana dan daga kafarta kad'an tana mayarwa.

Yana kwance akan gadon sa, daga gefe daya system dinsa ce a kunne da take nuna masa baki daya part din nasa. Aiki yake akan kara tabbatar da tsaron gidan sosai musamman da yake saka ran fitowar Barrister nan ba da jimawa ba. Kwanan sa biyu be fita office ba domin da gaske yana da bukatar hutu sai dai a gidan ma ba wani hutun kirki yayi ba, dan yan ayyukan sa ya tattare ya dira a kansu yana cigaba da bincike da nemo duk masu hannu a abinda ya faru a wanchan lokacin.
Iska ya furzar me zafin gaske, ya tashi zaune yana bada hankalin sa akan system din. Tunanin sa ne ya tsaya chak ya zuba ma allon computer ido cike da mamakin abinda yake gani. Da sauri ya mike, jikin sa daga shi sai armless da 3-quarter, tun a falo ya zare kayan jikin nasa bayan ya dawo daga salla. Yanayin yadda take tafiya tamkar mara gaskiya ya sakashi yin hanyar waje da sauri.
Juya bayan ta, tayi tana kallon yaron da ya rako ta shima ita yake kallo, tunanin ta kawai ya gama bata tayi tafiyar ta dan bata ga alamun yana gidan ba, idan ma yana nan toh baccin yake dan babu motsin komai.

"Ya sunan ka?" Ta tambayi yaron

"Habu."

"Ok...Mu tafi kawai inaga bayanan."

"Toh."

_"Idan kuma yana nan, amma yana cikin matsala fa?"_

Wata zuciyar ta tambaye ta, tsoron ta ne ya dadu, ta juyo da nufin yin hanyar da ta gani da ta nunaa alamun daki ne a wajen ,sai ta ganshi a tsaye yana kallon ta, kallo me cike da tsantsar tuhuma. Ledar hannun tace ta zame, ta fadi a wajen apple din dake ciki ya tarwatse a kasan tiles din.

"You!"

Ya nuna ta da hannun sa, kafin ya shiga takowa zuwa in da take durkushe tana kokarin tattare apple din da ya zube.

"Me kike anan? Me ya kawo ki nan? Taya akayi kika zo nan?"

"Na'aa amm."

"Me kike a gidan nan?"

Mikewa tayi tsaye bayan ta gama tattare apple din, ta daidaita nutsuwar ta dan kar ta bar masa wani shakku.

"Zuwa nayi na duba ka sir."

"Ki duba ni? Ban gane ba."

"I heard baka jin dadi, kuma kwana biyu baka zuwa aiki shine na tambaya aka ce baka da lafiya ne, shine nayi amfani da address din naje gida, daga nan aka ce in zo nan kana nan."

"Unbelievable!" Yace yana kallon ta

"Shikenan dan bani da lafiya sai kizo ki duba ni? Ke ba mace bace ba? Ya dace kizo ki duba ni kina mace?"

"Um um, ai sai da naje cikin gidan shine aka saka habu ya rako ni."

Kallon Habun yayi sannan ya maida kallon sa kanta

"Shikenan duk wanda bashi da lafiya a office haka zaki bisu gida ki duba su? Kowa ba mace ba namiji?"

Da sauri ta daga kanta

"Eh."

"Ina iyayen ki?"

Yace yana bata ransa

"Mamana ta mutu tun ina yar karama."

Wani abu yaji tun daga kansa har zuwa kafar sa. Fuskar sa dake daure ta fara washewa zuwa kalar tausayi, tausayin rayuwar da tayi cikin rashin uwa wadda ta kasance jigo, tabbas rashin iyaye musamman mahaifiya babban tashin hankali ne, da akwai uwa babu yadda za'a yi ta aikata abinda ta aikata a yanzu, tazo ta duba shi har gida, daga haka kuma za'a iya samun matsala idan ta hadu da mara tsoron Allah.

"Allah ya gafarta mata." Yace a chan kasan makoshin sa, kafin yace

"Ki zauna ina zuwa."

Zama tayi ya juya ciki, dan sai lokacin ya tuna da shigar dake jikin sa. Jallabiya ya dora akan armless din, sannan ya dawo falon ya tarar da ita a zaune tana wasa da hannun ta, habu na gefen ta yana karewa falon kallo dan ba shigowa suke ba.

Zama yayi a kujerar dake facing dinta, ya dan kalle ta kad'an sannan yace

"Karki kara zuwa gidan kowa da sunan duba shi, wannan ba tarbiyya bace ba, duk abinda ya faru ki kira a waya ki duba mutum."

Gid'a masa kai tayi, ya girgiza kansa har lokacin mamakin ta be barshi ba.

"Zaki iya tafiya, nagode."

Tashi tayi tsaye, ta sake kallon sa sannan ta dauki ledar apple din, ya kalli ledar sannan ya kalle ta

"Wannan ba nawa bane ba?"

"Na'am?"

"Eh ba kayan dubiya bane ba?"

"Oh eh shine." Ta mika masa tana yake. Karba yayi ya ajiye a gefe, ita kuma ta sake masa sallama sannan taja hannun Habun suka fito.

Kamar ta kurma ihu haka ta dinga ji, tabbas tayi abun zubda mutunci dan ta kasa gamsar dashi dalilin zuwan ta wanda kuma.dama bata dashi, Hajiya Zeenat tace kar ta ambaci sunan ta idan taje shiyasa tayi wannan karyar amma duk da haka karyar bata hau ba sam, gashi a karshe yana mata kallon marar kamun kai. Tsaki ta jashi yafi kala dari, tana ji wayar ta na ringing amma ta kasa dagawa saboda bacin rai.
Bayan fitar su, ya mike rike da ledar ya kai kitchen sannan ya haye sama cike da mamakin ta.


***Duk abinda ya faru tun farkon shigowar ta gidan har tafiyar ta akan idon su akayi. Plan dinsu yayi aiki domin dama hanyar da zasu saka camera din a gidan suke nema sai gashi da kansa ya nemi ta bashi ledar apple din. Dukkan su ya basu mamakin yadda har ya tsaya ya saurare ta, tabbas Raihana itace kadai zata iya yi musu aikin domin tana da wani tasiri akan Aryan din. Da ace wani ya kama ya shigo gidan ko a cikin ma'aikatan ne ba zai taba aminta da bayanin su ba, rashin yardar sa yayi yawan da hakan ke basu cikas akan aikin su. Sai gashi har yana zama yayi magana da ita duk da zafi da tsaurin sa. Tunda sun samu abinda suke so sai zuwa next plan din, shine samo key din, wanda bata jin a yanzu zai musu wahala.

"Hajiya ikon Allah!" Yace yana kishigida a kujerar da yake kai

"Kaga yadda komai ya tafi ko? Na fada maka yarinyar nan asset ce."

"Bata da wayo sam, sannan sak halin ubanta, da wannan zuciyar tasu suke saka kansu a wahala."

"Wallahi kuwa."

"Mum ni fa son ta nake wallahi, yadda kuma naga yaron chan na kallon ta bana so, I'm jealous kar naje ya fada son ta."

"Kar ma ka fara wallahi, babu wannan maganar na fada maka tun farko."

"Gaskiya ni son ta nake Allah da gaske."

"Kar mu fara haka da kai Adam, so kake ka Latata mana aiki?"

"Toh a cire ta daga aikin mana, she's too young for all this, ni a barni da Aryan din me ma yasa ne sai an dinga bin sa ta bayan kasa."

"Lallai baka da hankali wallahi, toh ban amince ba, ban yarje maka soyayya da ita ba."

"Kana ji kuwa Barrister?"

"Ina ji Hajiya, Adam ka bar wannan maganar dan ba me yiwuwa bace ba, bata mana plan kawai kake son yi, karshe dukkan mu a watsa mu prison."

Mikewa yayi tsaye ransa a bace ya fice daga wajen, baki sake Hajiya Zeenat ta bishi da kallo, ya zai mata haka? Bayan ta gama tsara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login