Showing 18001 words to 21000 words out of 121037 words
Bud'e masa motar yayi ya zauna a hankali sannan ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar gidan. A hanya be ce masa uffan ba, kansa jingine da jikin kujerar ya rufe idon sa ruf dan ma baya so Kamal din ya ishe shi da tambaya, he's so weak dan hatta heartbeat dinsa ya sauya.
"Aryan!"
"Um." Yace ba tare da ya bud'e idon ba
"Baka jin dadi, let go back please."
"Haka nace maka? Na gaji ne kawai."
"Gajiya? Me kayi da safen nan da zai saka ka gajiya,?"
"Ba sai ka sani ba."
"Ai saboda babu shi din ne ma, sanin da nayi maka baka kwana a gidan nan idan har ba wani abu bane ya faru ba, kai da Daddy ne ko? Dan nasan baka saka damuwar Adam a ranka balle har ta dame Ka."
"Kamal please, let talk about it some other time."
"Ok, be strong please."
Yace masa cike da tausayawa, kafin ya maida kansa kan titin ya cigaba da tukin sa ransa duk babu dadi.
Ko da suka isa company be fito daga motar ba, har sai da ya dauki wasu yan dakiku saboda yadda yake jin kansa na juya masa, da k'yar ya cije ya zuro kafar sa ya fito dan yayi ma kansa alkawarin ba zai taba bari hakan yayi affecting dinsa ba, amma kuma daga yadda yake ji yasan yana gaf da breaking alkawarin da yayi ma kansa nan kusa. Jerawa sukayi zuwa cikin building din Kamal na biye dashi a kusa kusa dan tsoron yanayin da Aryan din yake ciki. Har sai da ya kaishi office dinsa ya tabbatar ya zauna sannan ya wuce nasa da niyyar kiran Dr ya samu bayanin abinda ya faru dan yasan ta yadda zai iya kulawa da Aryan din. Be taba jin da gaske Aryan yana bukatar mace a tattare dashi ba sai yau, yana bukatar macen da zata zamar masa tamkar bangon da zai jingina dashi, tabbas zai rage abubuwa da yawa yasan, sai dai wacece zata iya zama da Aryan din da halin sa? Da ciwon sa? Da damuwar sa? Da shariyar sa? Wacece zata jure duk wannan? Dole sai dai wadda take tsananin so da kaunar sa fisabillillah, ba wai dan wani abun duniya ko fame ba, wadda take jin da gaske yana da bukatar a jashi a jiki, a nuna masa tsantsar soyayya, irin wadda ya rasa, wadda zatayi masa soyayyar uwa da danta, tayi masa soyayyar miji da mata. Tunanin sa ne ya katse sanda yaji Dr Ma'aruf din ya daga wayar, suka gaisa ya tambaye shi abinda ya samu Aryan din, yasan waye Kamal a wajen Aryan din shiyasa be boye masa komai ba, har ma da abinda ya kasa fadawa Daddyn, wanda ya sake tsoratar da Kamal din sosai.
System ce a gaban sa yana rike da mouse yana scrolling sai dai har ga Allah be san abinda yake dubawa ba, ga tarin bayanai nan da duk wani abu da yake da bukata a ranar amma ya kasa aiwatar da komai, lekowa Kamal yayi ganin sa a haka ya sashi zuwa office din su ya tarar da Raihana tana zaune babu abinda take dan babu aiki sosai a ranar saboda rashin zuwan Aryan din da wuri, dole sai ya gama dubawa idan ma akwai aikin zai aiko mata dashi ta mail ko ya kirata tazo ta karba. Gaishe shi sukayi dukka a karo na biyu sannan yace ta taso ta dan dafa musu shayin nasu. Ok tace ya fita ita kuma ta wuce kitchen din. Akwai komai da zata bukata nan da nan ta hada abinda zata hada ta dora, ta tsaya a kitchen din har ta gama sannan ta dauka zuwa office din Kamal din, tayi Knocking kad'an a kofar sannan ta tura, waya yake ya kalle ta sannan ya kalli kayan hannun ta
"Kai mana office din Aryan please, thank you."
Yace bayan ya dan zare wayar daga kunnen sa yayi maganar sannan ya cigaba da wayar, bata so ba dan ita bata ma san ya shigo yau ba duk da tasan babu abinda zai hanashi shigowar amma rashin jin duriyar sa yasa ta sakankancewa da be zo din ba. Tana kokarin karasawa office din nasa zainab ta taso da sauri ta tare ta
"Oga yace baya bukatar kowa a office din sa yau."
"Oga Kamal ne yace na kai masa."
"Bani na kai masa da kai na."
Wani kallo Raihana tayi mata,ta rasa dalilin takura mata da yarinyar tayi, gashi ita kuma sam ba'a nuna mata iko da gadara, wanda taga alamun dabiar Zainab din ce, murmushi tayi mata kad'an sannan tace
"Karki damu bari na mika masa."
Tayi wucewar ta, ta barta a tsaye a wajen cike da mamakin yarinyar.
Kan sa ya dora a saman table din bayan ya dan ture system din, sai da ta shigo sannan ya dago, tayi saurin janye idon ta daka kallon sa ganin yadda nasa suka kad'a sosai, kallon kayan hannun ta yayi har ta karaso ta dora su saman dan madaidacin table din dake gaban couch din.
"Good morning Sir."
"Menene wannan?" Yace bayan a amsa gaisuwar a ciki ciki dan ita bata ma ji ba
"Sir Kamal ne yace a kawo nan."
Juyar da kansa yayi gefe da yaji kamar ya makale masa, sannan ya sake dawo dashi tunanin taimaka masa ya fado masa
"Have a seat."
Ya nuna mata wajen zama, dan jim tayi kafin tazo ta zauna a daaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table din nasa ta dayan side din, turo mata system din yayi gaban ta, sannan a hankali yace
"Ki duba min wannan."
Kallon screen din tayi, sai taga same aiki ne da wanda ya saka ta kwanaki .
"In kin gama dubawa ga mails dinsu nan kasa sai ki tura."
"Ok."
Tace ta shiga aikin, yanayin maganar sa tayi mata kama da ta mara lafiya sosai, dan babu wannan zafin a maganar haka kuma babu nacaccen kamshin nan nasa da kullum yake mamaye baki daya ilahirin building din. Kamar ta bud'e baki ta tambaye shi ko akwai matsala ne? Dan tana jin sautin numfashin sa na fidda wata yar kara, sannan tana jin kamar jawo numfashin yake ta karfin gaske. Amma kuma tace masa me? Tasan yanayin sa zai iya bata amsar da zata gwammace dama bata yi tambayar ba. Wayar sa dake saman table din ce ta dinga kara amma yayi biris kamar bashi ake kira ba, so take ta dago taga yanayin da yake ciki amma sai ta kasa dan cike dake da shakkar sa. Tura kofar ya sakata kallon kofar, sai dai ganin wanda ya shigo ya saka gabanta faduwa, fuskar sa ce ta washe ganin ta, ya karaso yana maida kallon sa kan Aryan din da shigowar sa ta saka shi yunkurin mikewa amma kasancewar bashi da karfin jiki sai ya kasa.
"Me ya kawo ka?" Yace muryar sa a shake wadda take kara tabbatarwa da Adam weakness dinsa, shafa saman kansa yayi yaja kujerar dake gefen ta Raihanan ya zauna sannan yace
"Baka duba wayar kane? Daddy yana ta kiranka tun asubah, shi ya turo ni, na duba masa kai."
"Tunda ka ganni sai ka tafi ko"
"No ai ban gama ba,zai kira yanzu sai na hada ku." Yace yana zaro wayar sa da ta soma ringing ma tun kafin ya dire maganar, dagawa yayi
"Eh daddy yana office, eh toh gashi nan dai bari na bashi."
Ya cire wayar ya mika masa, wani kallo Aryan din yayi masa kafin ya karbi wayar ya saka handfree ya dorata a saman table din
"Aryan kana jina?"
"Ina kwana?"
Yadda yayi maganar ya saka Raihana kokarin mikewa ta bar musu office din dan ita bata gane yadda abubuwan suke ba.
"Seat down!"
Yace mata yana zare idon sa akanta, komawa tayi ta zauna ta sunkuyar da kanta. Yadda yake maganar da yadda yake amsawa wanda aka kira da Daddy ne ya daure mata kai, shi kowa haka yake masa kenan? Har mahaifin sa ma?
"Yan mata aiki ake yi ne?"
Adam ya fada yana karyar da kansa hade da wani irin kallo, kallon da yake hana mata sakat idan yayi mata shi dan ta tsani a rayuwar ta yawaan kallo musamman irin wannan da kana gani zaka tabbatar da abinda mutum yake nufi.
"Umm." Ta bashi amsa tana sake kankan da kanta dan ita gaba daya zaman wajen ya ishe ta.
Wayar sa Aryan din ya garo masa bayan ya gama maganar, ya dauka yana mikewa
"Babu kyau wulakanta mahaifa dai, baka ga yadda hankalin sa ya tashi ba, amma kamar ko a jikin ka."
Uffan be ce masa ba, yayi masa wani banzan kallo kawai ya ja siririn tsaki, dama kuma Adam din yasan ba zai tanka masa ba, kuma dama be yi don ya tanka masan ba, yayi ne duk dan saboda aikin da suke kokarin dora Raihana akai ne, shiyasa ba karamin dadi yaji ba ganin ta zaune a office din Aryan din,hakan ya sake tabbatar musu da aikin su zai tafi yadda ya kamata.
Rankwafowa yayi ta saman kujerar da Raihanan ke zaune, ya dora kansa daidai saitin kunnen ta a hankali yace
"Ki kula dashi sosai, kinsan yana da matsalar kwakwalwa."
Daga kanta tayi da sauri ta kalle shi, ya kashe mata ido daya sannan yayi murmushi.
"Get out!" Aryan yace a zafafe, daidai lokacin Kamal ya shigo office din, da saurin sa ya karaso ganin har Aryan din ya mike tsaye, ya kalli Adam din sannan ya kalli Raihana dake zaune da system din Aryan din a gabanta
"Sannu da zuwa Malam Kamal, yau na kawo muku ziyara gashi har zan tafi, sai mun sake haduwa ko?"
Yayi gaba ya bud'e kofar hade da banko ta a lokaci daya. Dafe kai Aryan yayi da yake jin kamar ya cire shi yayi wurgi dashi ya huta tsananin ciwon da yake masa.
"Calm down please." Kamal yace yana matsawa gefen sa
"Raihana, please excuse us kinji?"
Tashi tayi da sauri ta fice sum-sum-sum dan dama hanya take nema.
"Na gaji Kamal, na gaji wallahi, Adam yana so ya kai ni bango, yana so ya kai ni karshe."
"Dan Allah ka kwantar da hankalin ka, yau ne karo na farko da ya fara irin haka? Kasan shi kasan abinda zai iya, kasan kuma komai akan dalilin da yasa yake maka hakan, ya riga yasan weakness dinka, dashi yake amfani wajen bata maka rai."
Dafa jikin table din yayi da hannu daaya, dayan kuma ya rike kansa ya shiga jujjuya shi, yana ganin a karshe sai Adam ya haukata shi sannan zai kyale shi. Dafo shi Kamal yayi yace
"You need some rest Aryan, baka da lafiya."
Zame hannun yayi ya zauna yana sakin kan a hankali
"Me yasa kake punishing kanka haka ne wai? Me yasa ? You are sick tun daga yanayin maganar ka har facial expression dinka ya nuna, amma ka dage sai kayi aiki? Akan me?"
"Bani shayin chan please, mu bar maganar nan haka nan Kamal."
Matsawa yayi ya zubo masa shayin a cup ya mika kasa, ya kafa kansa ya shiga sha a hankali dan zafin na ratsa makoshin sa wanda yake a matukar bushe. Shanye wa yayi tas ya sake kara masa shima ya shanye, sannan ya dan dora kansa a saman table din ya kulle idanun sa. Babu yadda Kamal ya iya face ya fita ya barshi, ya je ya dauki wayar shi ya kira Ya Nabeela yace ta shigo office din, cikin kankanin lokaci sai gata tazo a cikin yanayi, ta same shi kamar ma bacci yake a zaune dan har ta shigo be dago ba, sai da ta taba shi sannan ya tashi. Dole ta tilasta masa bin ta, ta dauke shi daga office din zuwa gidan ta, sannan ta kira Dr Ma'aruf din tun a hanya yace zai same su a gidan.
RUMBUN QAYA*
Page 10
©® *_Hafsat Rano_*
ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥
****Tunda taga fitarsu ta lallaba ta gudu itama, dan dama hanyar tafiya take nema, bata san me ya hada su da Adam ba amma tabbas ta fuskanci yana cikin damuwa matuka, sai dai yadda yake abubuwan nasa ne sam basuyi mata ba. Bata cika son mutum me zafi ba, ko dan bata taso taga irin hakan ba? Hamman ta dukka basu da zafi ko kuma ita ce basa yi wa? Napep ta samu ya kaita makarantar su Amina dan sun yi daga nan zasu hadu su wuce ta rakata kasuwa, bata taba zuwa kasuwa ba tunda take a rayuwar ta, shiyasa take cike da daukin zuwa ta siyo wa yan gidan su abubuwa da first allawee dinta. Da weekend dukkan su zasu zo har Dadan ta, daga nan suje aga Abby wanda daga wannan zuwan sai kuma fitowar sa, shiyasa take cike da murna dan ji take kamar ta jawo ranar saboda tsabagen zumudi. A gate suka hadu da Aminan ta gama lectures har ta fito ma, dan haka ko sauka daga napep din batayi ba, ta shigo kawai suka tafi. Siyayya tayi sosai tunda kudin nata har da wanda Hamma Hydar ya bata ta hade ta sai musu abubuwa ta siya ma Adda Maimuna har ma da Aminan.
A gajiye suka dawo dan saboda tsabar wahala ji tayi kamar kafarta zata tsinke, bata san haka wahalar kasuwar take ba sai da ta dandana, amma idan ta kalli abubuwan da ta siyo sai taji dadi ya kamata. Wanka tayi hade da alwala sannan suka zauna zaman cin abinci, shinkafa da wake da salad favourite abincin ta kenan. Da suka gama ta dauko kayan ta nunawa Adda Maimuna sannan ta bata nata da na Hidaya yar autar ta, aikuwa taji dadi sosai tayi ta godiya hakan ya yi mata dadi sosai.
***Yana zaune a falon Ya Nabilan tunda suka dawo be ce mata komai ba, kansa na saman pillow rabin jikin sa na saman kujerar sai wayar sa dake ajiye daga gefen hannun sa, abinci ta zubo masa a plate daga saman dinning ta kawo masa hade da ruwa sannan ta zauna a gefen sa. Tashi yayi ya daidaita zaman sa ya kalle ta sai yayi mata murmushi kad'an ganin yadda duk ta shiga damuwa.
"I'm fine fa."
"When last kaci abinci?"
Sama ya kalla kamar me nazari, kafin ya daga mata yan ya tsun sa, yayi mata alamar biyu
"Two days ago?" Ta zaro ido, gid'a mata kai yayi
"Allah Aryan kana da matsala, so kake ka kashe kanka? Kwana biyu baka ci komai ba? Akan me?"
"Abinci fa kika ce, nasha tea ai, ko yau ma sai da nasha."
"Tea, tea, tea! Dama tea din na kirki ne me hadin madara da sauran su, ruwa ne fa kawai sai gayyayyaki, me zai maka dan Allah?"
"Yana taimakawa sosai."
"Kayi sauri kaci kafin ya huce." Tace tana mikewa ta barshi a wajen, yasan ranta ne yake a bace shiyasa ma yayi kokarin daidaita kansa dan ta samu natsuwa. Sai ma yaje ya samu Kamal yaji akan dalilin da zai sakashi kiranta, kaamar dai shi din har yanzu baby ne, yasan kuma halin rikicewar ta, gashi duk yanzu tabi ta damu kanta akan abinda da ya bashi some hours ma shikenan zai wuce kamar yadda sauran suka wuce tunda ya riga yasan ba yau aka fara ba ai.
Abincin ya soma ci a hankali duk da bashi da appetite sam amma kuma hakan zai ci ko dan hankalin ta ya kwanta. Chinese rice ce da chicken breast sai lemon kwakwa me matsakaicin sanyi saboda yanayin sa baya shan duk wani abu me sanyi sosai. Sai da yaci fiye da rabi sannan ya ture ya dauki tissue ya goge bakin sa ya koma ya sake kwantar da kansa a jikin kujerar. Fitowa tayi dan dama bashi lokaci tayi yaci abincin dan in ta zauna ya dinga kawo kabali da baadi kenan har sai ya haramtawa kansa cin abincin kwata kwata. Magungunan sa ta dauko ta mika masa ya karba yasha, tun bayan da Dr Ma'aruf yayi masa allurar nan ya samu natsuwa sosai, kansa da yake masa azababen ciwon nan ma ya rage sosai ya samu kwarin jikin sa, allurar ta riga ta zamar masa kamar masifa dan shi yanzu inhaler ma ba yi masa take sosai ba.
"Aryan?"
Ta kira sunan sa tana tattara hankalin ta waje daya, dan gyara zaman sa yayi dan ya fuskanci magana me muhimmanci zatayi masa ganin yadda ta kira shi da yadda fuskar ta, ta nuna
"Aure ne ya kamace ka a wannan yanayin, be kamata ka zauna haka ba."
"Aure kuma?" Yace yana tashi zaune sosai
"Yes aure, kana bukatar mace Aryan, kana bukatar life partner wadda zata tallafi rayuwar ka,."
Bata fuskar sa yayi nan da nan, kamar wanda akayi ma wata magana mara dadi
"Mun yi magana da Kamal, tabbas abinda ya kamace ka kenan, domin ba lallai ne mu kasance da kai a kowanne lokaci ba, Aryan ko zama da yunwar nan da kake matar ka ba zata taba barin ka haka ba, zaka samu nutsuwa hankalin ka zai kwanta."
"Kun gaji dani?" Yace yana tashi tsaye
"Bamu gaji da kai ba, amma duk yadda zamu yi maka ba kamar matar ka ba, aure yana cike da tarin ni'imomi da ba zaka gane su ba sai ka shiga cikin sa."
"Bani da wadda zan aura, I don't trust just anyone, ba zan iya ba."
"Zaka iya, just give it a try, zaka gode mana."
"Ya Nabila, bana son kowa a tare dani,bana son zama da kowa, kune dama kawai tunda kuma kun gaji dani shikenan, i will take care of my self, ba sai an taimaka min ba."
"Don't get me wrong, ni iya gaskiya ta nake fada maka, dole dole akwai abubuwan da ba zamu iya maka ba, sai dai matar Ka."
Shiru yayi kirjin sa na bugawa da sauri, menene a cikin auren idan ba tarin nadama ba? Ta ina ma shi zai fara neman mata? Yace mata me kuma? Ba wannan ne shi yanzu a gaban sa ba.
"Kana jina kuwa?"
"Eh, kiyi hakuri ba yanzu ba, ba zan iya ba, naje na auri yar mutane na shiga hakkin ta."
"Shikenan, amma ka bud'e zuciyar ka, may be sai kaga an samu wata ta samu ta shiga zuciyar taka, shikenan ma ba zaka san sanda zaka zo mana da maganar ba."
"Hmm."
Yace ya koma ya zaune, bata sake ce masa komai ba ta kyale shi dan ta lura ba zai fuskance ta a wannan lokacin ba. Yana gidan har